Showing 114001 words to 117000 words out of 162126 words

Chapter 39 - ABADAN

santalan fararen cinyoyinshi masu wadatar gargasa baqa suduk suka bayyana
ta lakato maganin mak kama da man kadanya ta mutstsuka a hannunta,tamkar wadda zata taba kunama haka ta dora hannunta kan cinyoyin nasa,sai da ta runtse idonta kana ta fara shafa masa a hankali tamkar mai sanda


Shiru ya ratsa dakin dukkaninsu suna ji cikin jikinsu kada ma abdallah yaji labari,ajiyar zuciya ya dinga saki a bobboye idanunsa kan maryam wadda bata sani ba gaba daya wuyan rigarta yayo qasa,tsuntsu biyu ya dinga jifa da dutse tsaya sam ita bata sani ba,har ta gama durqusan nata ta zauna sosai
dan jan qafar tasa yayi yana fadin
''kaiiiii'' da sauri ta dubeshi tana fadin
''da zafi''kai ua girgiza murmushi ya qwace masa don dama idn nata yakeson gani ya gani din ya kuma gano abinda yakeson ganowar
''nikam gaskiya da biyu kike min irin wannan shafar mero''
baki ta muguda masa
''kada ka sake bani sunan wannan baqaiyiyar budurwa tak,ni ba suna na kenen ba''mirmushi ya kuma saki saboda tsabar iya tsokana
''ke da ita din ai duka jirgi daya ya kwasoku,gwara ma ita tunda ta iya ta sace miki miji''haushin da ya bata yasa ta kasa tanka mishi,sai qara speed din shafar da take masa da tayi
ya sake fadin
''wayyo Allah''bata ko kula shi ba har sai data gama ta rufe man tana shirin miqewa sai ya sake fincikota jikinsa baki daya ya matseta,tana sonvta qwace amma yaqi don riqon tsauri yayi mata
''ki hutar da kanki yau a jikina zaki kwana,ina zaman zamana kin jawomin,dole ki ragen zafi kafin nayi aure tunda ke kika jawo komai''


Da gasken kuwa yake don tuni har ya fara sakin layi,hannunshi ta riqe tamau tana kiran sunansa,a hankali ya janye hannunshi yana fadin
''am sorry na manta''ya fada yana kissing goshinta kana yaja musu bargo ya rufesu,tun tana a darare a jikinsa har ta saki jikinta jin shiru bai qara motsawa ba,da alama ma bacci yayi awon gaba da shi,don dole ta saki jikinta amma still tana jin yadda zuciyarta ke gudu,daga bisani ita din ma wani daddadan bacci ne ya sureta






*mrs muhammad ce*๐Ÿ‘‘



๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“šโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ *ABADAN*๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐Ÿ’–

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ๐Ÿ’–
๐ŸŒบ๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–๐ŸŒบ
๐Ÿ’–
ยฉ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*๐Ÿ’ก
*_home of expert and perfect writers_*

5โƒฃ4โƒฃ

*_Allah yana cewa cikin alqur'aninsa mai girma''haqiqa ji da gani da zuciya dukkansu akwai tambaya a kansu''(ranar qiyama game da abinda suka ji ko suka gani)_*







lokacin da mami ta koma gida ita da baaba uwani bayan tayi horn an dage mata makeken get din gidan ta wuce ciki sai ta lura duka ma'aikata da security na gidan na tsaye ne cirko cirko a guri guda
kan ta fito daga cikin motar ibrahim ya qaraso cikin girmamawa
''lafiya ibrahim,me ya faru na ganku a tare guri guda๏ผŸ''
mamin ra fada tana kashe motar tare da qoqarin fitowa daga ciki



''wallahi mami hajiya nene ce๏ผŸ''
''nene๏ผŸ,me ya faru๏ผŸ''ta tambaya don wata irin tsanarta tame ji na mamaye zuciyarta,macan da ta jefa tilon danta cikin bala'i,macen da taso ganin bayan su ita da yaran da tafi qauna abdallah da maryam,ta mata alkhairi ita kuwa ta maye gurbinsa da sharri,ta zauna da ita zuciya daya yayin da ita take zaune da ita da ziciyoyo barkatai marasa kyawun manufa,ko a mafarki daidai da rana daya bata taba qullatar nenen da sharri ba sai gashi abun mamaki ita din taso abzata cikin wani rami mai tsananin hadari badan Allah ya dibi ysarkin zuciyqrta ba ya tsallakar da ita daga dukkan wasu tarakuna data dana wa rayuwarta


''ina baya ina rangadin gidan su husaini kuma suna nan zaune da sauran abokan aiki,kawai saiga husaini yazo yayi kirana waiga nene can babu ko kaan arziqi sai daurin qirji ta fito a guje daga bangarenta wai fita zatqyi nemansu adnan,kuma idan ta gansu sai ta kaagesu don sun cuceta sun ha'inceta sun gudu da dukiyarta,da farko na zata ma qarya yake saboda naga ko motsi bata iyawa komai sai an mata,amma da na bisi sai na gasgata maganarsa,to muna shawarar yadda zamu hanata fita sabida kowa yana tsoron tabata tunda ba muharramrsa bace kawai sai ta faki ido ta fice a guje,muka bita tuni har ta fita daga gidan,muna daf da zamu cimmata wata mota ta tsaya,wadan nan mutanen da kika ce kada mu sake barinsu kwanaki su shigo gian nan sune aahe a ciki suka figeta suka jefata ciki,na sa bindiga na harbi tayar har sau biyu saidai ban samesu ba''



shiru mami tayi tana jinjina kai,ibrahim ya kuma cewa
''amma mun dauki nimber din motar,gata''tsaidashi tayi
''babu bin sahunsun da zamuyi ibrahim ka qyaleta da su,qila hakan da Allah ya mata shine mafi alkhairi a gurinmu,bata dace da zama cikin mu ba shi yasa Allah ya hadata da mutanen da suka dace da ita''tana maganar ne yanayin fuskantar ya sauya saboda bacin rai da tashin hankali,ibrahim ya dubi mamin,shekara da ahekaru suna zaune tare,macace mai tausayi jin qai da taimako ga na qasa da ita,ya tabbatar ba qaramin abu bane zai sanyata tace a qyale nene ba,duk da idanuwansu sunga wasu muggan ayyukan na nene da yadda ta so maida uwar dakin tasu mamin amma ya tabbata da abinda ta aikata din yafi haka,take kuwa ya cukuikuye takardar ya yagata gutsi gutsi
''ku koma bakin aiminku ibrahim,kowa yasa cikin zuciyarsa tamkar ma baiga abinda ya faru,irin nata hukuncin da Allah zai mata kenan,don na tabbatar ba mutanem arziqi ne suka dauketa ba,kowa ya shuka na gari kai nasa''
''gaskiya ne mami,Allah ya shige gaba''
''ameen''ta fada tana juyawa cikin gidan,cikin zuciyarta tana qara jin imani kan cewa duk abinda zakayi kayishi domin Allah,matuqar kace don wani zakayi shi to kana tare da wahala,zaka kyautatawa mutum iyakar iyawarka da zuciya daya amma shi sam bai gani,qarshe ya buge da cutar da kai ko ya shiga sahin manyan maqiyanka na farko,amma idan kayi ne don Allah koda shi din wanda ka yiwan bai gani ba baka da kaico ballantana asara zaka samu ladan aikinka ne gaba ga Allah,Allah kasa mu dace,ka bamu ikhlasi


Sai data sake wanka tayi sallah tana kan abun sallar ta dau wayarta ta kira daya cikin qannenta sa'adiyya sukayi magana kan saukar qur'ani da aka raba makarantu makarantu,ko dq can lokacin marigayi alhj abdul-kareem mai nasara an musu,bayan mutuwarshi ne daga baya ta watsar,a yanzu kam ta dauki dambar ci gaba da sawa ana mata don ta fuskanci duk yadda kakai ga kirkinka kamun kai da kayuatatawa mutane wani yana nan duk duniya babu wanda yaqi jini sama da kai koda naman mahaifiyarka zaka dinga yanka kana dafawa kana bashi yana ci tsabar so,sadiyyan ta gaya mata an kammala kaso na farko gobe zasu dora kana sukayi sallama


cikin 'yan uwan nenen mami ta nemo matar babanta tace suzo su kwashe duk wani abu da ya danganci nene daga gidan don tuni kowa ya sani alfarma karamci sa darajar zaman tare yasa mami ta bar nenen a gidan,matar baban nata cewa tayi gaskiya babu abinda ya shagesu da kayan nenen,don bata manta irin cin mutuncin da tayi musu kan gadon mijinta na farko,hatta da mahaifinta ya dade da zare hannunsa cikin lamuranta
mamin tace dole kam su debe don sun gama zama tare da nene
matar baban nata ma yaba mata sukayi zaman datayi da ita don sunga namijin qoqarinta ma data zauna da ita ba dangin iya babu na baaba tsawon shekarun nan


Da qyar suka zo suka debe komai na natan suka loda a kodi kura,part din ya koma wayam babu ko tsinke nata bare na 'ya'yanta,sai a lokacin mamin ta fara jin sanyi cikin zuciyarta
''na barki da Allah nene,ko iya haka ma ya ishi yan baya ishara''abinda mamin tace kenan


๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿ‚๐Ÿƒ

Qal gidan yake a share kamar kowanne lokaci,rairayin filin gidan tas kamar an zauna an tsince dattin cikin,banda shati shati na tsintsiya da alamun yayyafar ruwa da suka sa qasar ta danyi danshi da qamshi babu komai


gidan shiru yake kasancewar babu kowa sai ita da abdallan kawai,inna wuro ta je cikin garin gaya bikin sunan wata jikarta,tsoho alhaji kuwa kano ya tafi karbo jakarsa a hajj camp da yake kayan sun dan samu tsaiko sai ranar suka iso,ya dauki mustafa suka tafi tare don yafi jin dadin tafiyar


qasan rumfar yake a zaune kan wheelchair dinsa sanye da baqar t.shirt da red din trouser mai sulbi da kyau,yayin da maryam keta kai kawo na hada abincin dare
idan ka dubeshi a haka sai ka zaci tabbas karatunsa yake tuquru saidai ina zaman sa'ido yayi don da zarar ta kuya zqi zuba mata ido har sai ya fuskanci tana shirin sake waiwayo wa,wani kyau yaga ta yi masa cikin baqi da ja din pakistan riga da wando,duk da rigar har gwiwa take amma gefe da gefe an tsaga shi wanda hakan ya sake taimakawa wajen fidda sharp dinta,ta nanade kanta da baqin dankwali da ya sake fidda hasken fatarta muraran,sau tari yakan raya cikin zuciyarsa kodai ta hada jini da larabawa ko indiyawa


Darensu na shekaran jiya yake tunawa har yau daren yaqi fita daga tunaninsa,wani babban matsayi ya bashi don bai taba samun dama kamar ta ranar ba,har hanzu idan ya tuna yadda take shafa masa maganin sai yaji taikar jikinsa ta zuba,taushi ta laushin tafin hannunta kamar auduga,itakam ta bada hankalinta ne kan girkinta saboda haka bata lura da kallon da yake mata ba,saidai lokaci lokaci tana jin gabanta na faduwa ko taji tafiyarta na hardewa


ta fito daga kitchen zata ja ruwa a rijiya,a wannan karon kam ta kamashi dumu dumu yana kallon nata,saboda wani tsabar qarfin hali irin na abdallah tare suka hade rai hakanan kowa ya janye idonsa daga kan dan uwansa ta ita ta wuce bakin rijiya shi kuma ya bude shafin gaba na qur'anin hannunsa ya shiga sabuwar sura suratul jinni bayan ya gama suratu nuh daga sama yaje gangarowa qasa surori kadan suka rage masa ya hada saukarsa don yau yake son kammalata gobe juma'a za'ayi sadaka wa mabuqata


ta debi na farko cikin rijiyar mara katanga don kowa yasan yadda bakin rijiyar qauye yake a bude take kuma daf da qasa ta kai rumfar girki ta sake dawowa ta zuba cikin botiki duk yana satar kallonta ta gefan ido don baiso ta kuma kama shin kuma gashi bai gajiya da kallon nata,ta daga botiki kenan santsin lakar dake bakin rijiyar wadda ta jiqu da rya ya debeta,luuu gaba daya ta tafi tayi kan rijiyar
''maryam''ya fada cikin wata iriyar gigitacciyar murya idanunta a rufe tana ambaton sunan Allah,zuciyarta na bugawa kamar zata fito waje da kanta,ta gama saddaqarwa yau kam sai yanda Allah yayi da ita don ba makawa cikin rijiyar zata yiwa masauki don


qafarta ce ta fara gjrdewa wani zafi ya kuma ratsata ta saki qara,jikin mutum taji ya fada gaba dayanta kana aka janyeta gefe,a mamakance ta bude idonta saboda ta gama bayarwa zata jita tsamo tsamo cikin ruwan rijiyar ne,sai kuma ta sake haduwa da wani abun mamaki da yaso sandarar mata da jinin jikinta


Abdallah ne tsaye bisa duga dugansa kan qafafunshi kamar yadda yake a da,ta dan janye jikinta daga gareshi da fuska mai dauke fal da mamaki tabi tsawonsa da kallo,tabbas shine abdallah ne,the gentle giant man din nan,abdallah dai abdallah mami,kasa daina kallonsa tayi don har yau tana jin kodai mafarki ne daga irin mafarkan da saba yi,baya dai ta sake ja saidai wani zafi daya ratsa qafarta ya sata durqusaqa tana fadin''wash''wasu hawayen farinciki suka aulmiyo daga idanunta


Cak taji ya dauketa baki daya bai direta ko ina ba sai kan kujerarsa da ya tashi ya ajjiye ta a kai bayab ya dauke alqur'anin dake kai ya maida man window din dakin inna wuro,reshe sai ya juye sa mujiya a maimakon abdallah dake kallonta a sace dazun,yanzun ita ke binshi da kallo baki sake kuma kai tsaye


Gabanta ya dawo ya durqusa baiko damu da rairayin dake gurin kada ya bata masa kaya ba,ya kama kyakkyawar qafarta da yake tunani anan ta gurde din
matsawa wani guri yayi sannan yace
''nan ne๏ผŸ''bata fahimci ma da ita yake ba don ta tafi cikin duniyar mamaki,saida yasa bakinsa ya hure mata brown oily eyes dinta da suka qara sheqi sakamakon sabuwar qwallar dake ciki tana yawo,bata kai ga fitowa ba


''kada ki cinyewa mero ni mana,ina ne gun ciwon๏ผŸ''ya tambayeta yana sake duban qafar tata
''abdallah ka warke๏ผŸka fara tafiya fa abdallah ko baka gani ba๏ผŸ''kyakkyawan murmushi ya saki kana ya dago ya dubeta kana ya sake maida kansa ga qafarta
''na sani kuma na gani,tun shekaran jiya na warke maryam,ranar da kika kwana a qijina,ranar da tsoho alhaji ya baki magani kika shafan da hannayenki masu albarka''


qwallar ta subuce ta zubo ta ido daya,muryarta so cool tace
''amma abdallah kaci gaba da zama a maysayin mai lalura๏ผŸme yasa ka boye samuwar....''
''shshsh๏ผ''ya fada bayan ya sa qwayar idonshi cikin nata
''akwai dalili,sannan yanzun ba muhallin nganar bane''
kai ta girgixa ya gane so take ta fake ne ta masa borin nan nata,don haka ya rigata ta hanyar matse inda ta gurde din,ai kuwa tuni ta saki abinda takeso ta fada din ta maida gurbinsa da fadin
''wayyo qafata''tare da runtse ido ta kuma damqe hannun abdallahn,sake surarta yayi daga kan kujerar ya maida ta kan rabarmar kabar dake shimfide kusa da kujerar ya ajjiyeta,zama yayi ya miqe qafafunshi ya jawo qafar tata kan cinyarsa,idanu a warwaje tace
''me zaka yimin haka abdallah,kada ka fama min ciwo''ta fada a tsorace don tasan irin wannan gurdewar ta taba irinta taja bakinta tayi shiru taqi gayawa mama,sai data yi kwana uku maman ta lura,ta takura mata sai taje an duba mata,da taje ashe targade ne,taqi yarda a gyara mata qarshe sai da maman ta kaita da kanta,ai kuwa har suma tayi kafin a gama gyaran din qafar ta gama yin tsami,shi yasa yanzun ma ta tsorata kada taje irin wancan ne


Bai tanka mata ba kamar yadda bai kalleta ba ya kama gurin,kamawar farko ra saki qara tayo jikinsa baki daya ta nanade shi saboda azaba,kasa ci gaba yayi saboda irin riqon da tayi masa ma baki daya ua zare masa lakar jikinsa,tuni ta fara hawaye tana roqonsa kada ya sake taba mata wlh zafi
shiru yayi yana kallonta yadda taje faman kuka kamar yar baby,sai kukan ya bashi sha'awa saboda duka eye lashes dinta sun jiqe sa hawaye sun sake zara zara


Tazara ya sake bata ya faki idonta ya kuma damqar ciwon,ta qara shigewa jikinsa gumi yana karyo mata tare da wani sabon kukan,har cikin xuciyarsa yake jin kukan amma yasan idan ya qyale mata gaba zafin da zatajin sai yafi haka don ya gane targade ne a qafarta,qarfinsa yasa bai qyaleta ba sai da ya gyara,tuni ta jiqe sharkaf da gumi da hawaye harda majina,ya kalli fuskarta sai yaji dariya tazo masa duk fuskar ta hada ja,miqewa yayi ya nufi daki ta bishi da kallo don har yau mamakin takawarsa bata saketa ba,ya fito da handkherchief mai kyau da kansa ya dinga goge mata fuskar har sai da tayi tsaf kana ya gyara mata zaman ya miqar mata da qafarta ya jinginata da bango


gabanta ya dawo ya zauna dirshan,ganin yadda take jefa masa harara ya sashi daukar qur'aninsa ya bude yaci gaba da tilawarsa a zuciya
sai ta tsinci kanta itama tana qare masa kallo,ko ta ina abdallah cikakken namiji da samun irinsa sai an tona,kyau zubi da tsarinsa kadai ya isheshi ya godewa ubangijin daya qerashi



Komai nashi daidai yake,babu abunda yayi kodan ko yawa a tare da shi
''ya dai yammata akwai magana ne๏ผŸ''taji ya fada,kunya ta kamata ta rasa na cewa sai kawai ta soma qoqarin tashi,hannunta ya riqe yana fadin
''take it easy''sannan ya maidata ya zaunar
''idan kin tashin me zakiyi,ina kuma zaki je๏ผŸ''
''girki na dora kuma ban kammala ba,gashi yamma na dada yi''
sai ua dinke girar sama da ta qasa kana yace
''tab,ai kuwa yai saidai kada kowa yaci abinci cikin gidan nan,babu girkin da zakiyi''baki ta saki tana kallonsa yadda yabi ua hade rai tamkar wanda ta zaga,sai taga ya ajjiye qur'anin bayan ya saka alama ta inda zai tashi ya nufi rumfar girkin,kallo ta bishi da shi,sai ta tsinci bakinta yana furta
''ahamdulillahil lazi bini'imatihi ta timmus saalihaat kana ta limshe idonta tana sake gaskgatawa da miqa dukkan imaninta ga Allah,shine mai kun fa ya kun,yadda duk yakeso haka yakeyi haka kuma za'ayin''


Tana kallonshi yana tura wutar iccen tuni hayaqi ya bulbuleshi sai gashi ya fito da sauri daga rumfar idanu jajur hawaye na diga,dariya taso kamata,dama idan banda rigimar sa ina shi ina wutar icce,wataqila ma tunda gake bai taba zuwa gaban murhu ba balle ayi batun girki,yana goge qwallan yana fadin
''kai kai kai,yanzu baby haka kike shaqar wannan abun kamar kanka zai juye,gaskiya daga yau kin gama''dauke kanta tayi kamar bata jishi ba bayan kuma ta gefab ido take satar kallonshi


Baikai ga zama ba nero tayi sallama ta shigo gidan,turus tayi ta tsaya tana kallon abdallah,gani take kamar ba shi ba,sam ta kasa dauke idonta daga kanshi
''wannan kallon fa๏ผŸ''yace da ita sai ta sunne kai wai ita kunya,qarasowa tayi tana fadin
''yaushe ka warka abdullahi๏ผŸ''
''kinga ga girki can inna ta bari jeki qarasa tukunna kya zo muyi hirar''
miqewa tayi ta isa nufi cikin rumfar tana sake mamakin warkewar tasa har ta gaza boyewa tana zaune a rumfar girkin tana waiwayensa


hakanan maryam taji wani abu ya takoreta,ta dade tana qaryata kanta akan irin abunda takeji idan mairo ta rabi kanta da sunan kishi ne saidai a yanzu a yadda abun yaqi barinta ta tabbatar cewa kishin ne
baifi saura awa daya a kira magariba ba inna wuro ta dawo gaggauce don bata kaiwa magariba a unguwa


itama dai da mamakin take kallona abdallah dake tsaye kan maryam ya harde hannayensa a qirji yana kallonta kamar wanda aka baiwa gadinta
''bawan Allah๏ผŸ,Allah mai iko,kaine a tsaye da qafafunka๏ผŸ''
kyakkyawan murmushin nan nasa ya saki kana ya qarasa ga innar yana karban daurin buhu dake hannunta ya sa mata shi daga gefe
''ni ne inna wuro''
tana kame da bakinta tace
''bari malam yazo yaga ikon Allah,Allah gwanin iyawa ya amshi addu'ar bayinsa,kai Allah mun gode maka,sannu bawan Allah,Allah ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login