Showing 201001 words to 204000 words out of 209775 words

Chapter 68 - DUNIYATA BOOK 1 By HUGUMA

Kunnuwanta ba zasu iya ci gaba da sauraron wannan quruciyar ta kawun da bibo ba,wanda har yanzu suka kasa dainawa,duk kuwa da cewa kansu da bakinsu a hade yake,yanzun ne abun duniya yake shirin hadasu,don haka suna tsaka da sa'insarsu ta tajuya tana takawa da nutsatsiyar tafiyarta dinnan da 'yan bani na iya suka sawa suna

"Maciji me tafiyar mutuwa" Nutsuwarta a tafiya a cewarsu sam bai dace da halinta ba a tasu fahimtar.

A falo tayi wurgi da jakarta ranta yana susa,tun komai baiyi nisa ba har kawun ya soma!shiga gonarta da kuma nuna mata iyakarta?. Dankwalin kanta ta zame sassalkar sumarta ta zare daga ribbon din data matse gashin,ta koma da zafi zafi ta zauna saman kujerar tana furzar da iska daga bakinta

"Ta yaya ma zata zauna a maida rayuwarta haka?,ya zata zauna ta rayu kaman haka?,dole ta matsa qaimin tattare komai dama kowa nata zuwa bigiren da zata ci gana da gudanar da rayuwarta cikin 'yanci kuma a yanayin duk da takeso.

Idanunta dama kunnuwanta gaba daya suna a tsakar gidan nasu,tana bibiye da kowanne motsi na gidan. Jira takeyi kawai kawun ya matsa daga gidan ya tafi tashi sabgar itama ta fice nata. Kaman yadda takeji koda sama da qasa zasu hade ba zata taba daga waya ta kirayi mutumin da bata taba jin burbushin muhimmancinsa cikin rayuwarta ba......hakanan fitarta a yau ta zama wani abu na tilas don laluba yadda zasu gusa daga wannan muhallin zuwa wani 'yantaccen gurin.

Tana ji a jikinta idan bata aiwatar da hakan ba a yau tamkar bata da wani sauran lokaci da ya rage mata,kamar lokaci ya riga ya qure mata,kamar yaune kawai damar data rage mata.

Saidai duk yadda take zirga zirga da sanya idanu,kowanne motsi sai ta juyo muryar kawun ko gilmawarsa. Tun lokacin dawowar yara daga makaranta baiyi ba har yayi. Ba nutsuwa a tattare da ita sanda suka shigo,don ko abinci bata dora musu komai ba,burinta kawai kawun ya matsa ta samu ta fice,amma qemem wunin gaba daya yau a gidan ya yishi.

Bata samu ya bar gidan ba sai kusan biyar na yammaci,tasan kuma yayi hakanne saboda yasan ita din bamai fitar dare bace,saidai a wannan rana ta karya record dinsa,ta shirya a gaggauce ta fice abinta.

Cikin nasara ta kammala komai,saidai hakan ya dauketa har zuwa bayan sallar ishai,tanata fargaba ta shigo gidan,ta wuce kai tsaye cikin dakinsu,wanda tana sanya qafa shima ya sako tasa qafar,saita zarce bedroom kawai,don tasan dole zai fahimci ta fita,koda bai fahimta ba a cikin gidan nasu ba zaa rasa masu gaya masa ba,a yadda suka canza su kansu,komai yana shirin canzawa gaba daya.

*******K'arar wayarta shine abinda ya farkar da ita daga nannauyan baccin daya dauketa,hannunta daya mata nauyin ta miqa ta jawo wayar tana duba me kiran. Ganin sunan titi ya sanyata miqewa ta zauna sosai tana amsa wayar.

"Anjima da yammaci jirginmu zai tashi zuwa qasar India,najeeb ya gama komai"

"Alhamdulillah" Ta furta a sarari tana jin kamar an cire mata daya daga cikin nauyayan duwatsun dake danne saman zuciyarta. Ciwon aishatu shine cikar burinta na farko da take fatan gani kowacce rana.

"Zan shigo naga aishatu.....zan shigo da wuri titi in sha Allah" Ta fada tana jin farinciki yana ratsata . Murmushi titi din tayi

"Koda baki shigo ba sabreen kin gama yiwa aishatu komai ai,tsakaninmu dake sai fatan alkhairi".

Idanunta ta maida kan agogo bayan sun gama wayar,takwas saura na safe. Tayi mamaki da motsinsu huda bai tasheta ba,suma kuma cikinsu ba wanda ya tadata,sai ta jawo dan qaramin farin hijab dinta data cire sanda zata kwanta ta aza saman kanta ta zuro qafafunta qasa ta sauko tana fitowa falon.

Dukansu sun gama shirinsu,kowa sanye da uniform,fitowar tata taja hankalinsu,suka soma gaidata sanda take zama kusa da haneefa,saita karba saka mata socks din tana cewa

"Auta ta daina neman me saka mata socks yanxu ko?,girma yanata zuwa" Dariyar jin dadi tayi tana cewa

"Amma adda kullum ya nadra cewa takemin yarinyar nan...."

"Rabu da ita,harda ke za'a raba aiki idan muka koma sabon gida" . Furta sabon gidan da tayi sai dukansu suka zuba mata ido,bata bada hankali ba sai data gama sawa haneefa socks din.

"Adda......wani gidan zamu koma?" Haneefa ta riga 'yan uwan nata tambaya fuskarta na nuna farinciki sosai.

"In sha Allah.....gobe.....kaman ko yaushe bana buqatar masaniyar kowa,idan an tashi daga school yau ba islamiyya.....koda kun dawo baku sameni ba zan shiga duba aishatu,ku fara shirya kaya huda cikin manyan bags din can kafin na dawo"

"Tom" Huda ta amsa mata saidai nata jikin a sanyaye yake. A nata hasashen tana ganin kaman idan addan nata tayi auren shine zaifi dacewa da ita......auren zai zama wata hanya ta wanketa daga dukkan zargi da mummunan kallo da society din da suke rayuwa a ciki suke mata,bataga alfanun ture wannan auren ba.....duk da tayi mata nata bayanin gwargwadon yadda zata fahimta.

Addua ta musu na dawowa lafiya,saita jawo wayarta tana son taba JIB ya qara mata bayani akan wanda titi tayi mata,sannan shima suyi handing over akan komai.....tana buqatar sabuwar rayuwar da babu kowa cikinta daga ita sai qannenta da kasuwancin da takeso ta fara wanda shi take sanya ran zai zame musu madogara

_ni kuwa nace ummmm inji me ciwon haqori,anya kuwa sabreen?,haka siddan zakici bagas?😂,to bari dai mu gani_

Wayar bata shiga ba saiga nadra da haneefa sun dawo cikin dakin,ta ajiye wayar ta maida hankalinta a kansu tana shirin tambayarsu lafiya huda itama ta shigo. Tsoro sosai saman fuskarta,ta qaraso cikin falon tana dubanta.

"Adda.....ina tsoron faruwar wani abu"

"Me kenan?" Sabrin ta tambayeta tana tattara hankalinta sosai a kanta

"Wasu manyan qatti ne guda biyu a qofar gidan nan.......duk wanda zasu shiga ko zai fita su zasu bude masa qofa.......nayi qarfin halin tambayarsu su waye amma ba wanda ya amsa min a cikinsu". Shuru sabreen tayi tana qanqance idanunta cikin alamun zurfafa a tunani. Kwanyarta ta gaza cafko komai,sai ta maida dubanta kan haneefa.

"Akwai wani alamu na cutarwa a tare dasu?,hayaniya tsawa ko wani abu daban?". Kai ta girgiza

"Ba daya,kawai zasu kalli fuskarka ne sannan su bude maka qofar"

"Haka kowa yake fita daga cikin gidan?.....akwai wanda kukaga sun hana fita?"

"Kowa yana fita,amma cikin tsoro,ba kuma wanda suka hana".

Sosai ta jijjiga kanta zuciyarta tana d'arsa mata wani abu,saidai kuma bata tunanin hakan zata kasance.

" Ba damuwa,ku wuce kuma ku fita kaman kowa,basu da alaqa daku". Cak sukayi suna kallonta,da alama dukkaninsu itace damuwarsu,kada ma huda taji labari saboda sanayyarta da abubuwa da yawa da sauran basu sani ba.

Tattausan murmushin nan nata dake tsananin qara mata kyau ta saki tana girgiza kai

"Karku damu......muna da yawa a gidan,ba abinda zai faru damu,a dawo lafiya" Tana ganin yadda suka kama hannun juna da kyau kaman kowa na shirin karewa dan uwansa wani abu me cutarwa,wannan sai ya tsinka mata zuciyarta sosai,ta sake jin ruwa da iska zata ci gaba da zamewa rayuwarsu garkuwa har abada.

Tana dauke idonta daga kansu kankatsin salatin bibo ya rusketa

"Daada.......tani......wai bakuga yau kuma bala'in da muka wayi gari dashi bane yau?,karta kartan garada sun tsare mana qofar gida kamar gidan tsaffin 'yan damfara.....koda yake biri yayi kama da mutum.....kuma sai da karen gidanka kake ganin na wani gidan......wannan masifa da take shirin afko mana gida ya ubangijin Allah ka tsaidata iya kan wansa ya jajibota....."

"To wannan balai mudai bamu taba ganin irinsa ba tsahon rayuwarmu da mijinmu sai a wannan karon" Tani da suke dan juma da dan jummai wani lokaci ita da bibo kafin su hautsine kuma ta fada tana tafa hannuwa

"Yo kome zamu gani aisaidai mu nemi tsari.....wanna masifa duk yadda akayi silar wannan gafalallen auren ta samemu.....wai daada ba zaki fito bane sai an cimmaki?".

"Me zan fito nayi?,ina ruwan biri da gada?,tunda dai basuce ni suke nema na ina ruwana ni dasu?,maza ku zafafa damuwa dasu sayi awon gaba daku idanma zuwan nash ba naku bane ku jawa kanku da shegen bakinku"

"Bakinki ya sari danyen kashi wallahi,.....saboda abun arziqi bai karbi kare ba,daga abun arziqi sai ki juye mana da fatan tsiya?,sha zamanki idan an cimmaki wani cikinmu aka cimmawa"

"Ke kika sani" Daada da bata fiya jurewa dogon cece kuce ba ta fada.

Tana danna number jib kunnuwanta suna saurarensu. Wannan dabiar tun bata mallaki hankalin kanta gaba daya ba tasan bibo da ita,har kwanan yau kuma ba abinda ya canza a tattare da ita.

Waya sukayi da jib din ta minti talatin kacal,daga nan sai ta soma shirin shiga wanka. Ta dawo daki ta tsane jikinta da towel,ta shirya cikin glitter wax me tsananin kyau data dace da kalar fatarta da kuma yanayin qirar jikinta,dinkin half bubu da straight skirt da aka tsaga bayansa,ta dauki Chantilly veil me asalin tsadar peach color adon jikin atamfar,ta hada da plate shoe da hand bag dinsa bagco.

A tsaitsaye ta hada tea da biscuit tasha,ta yafa mayafinta ta daura agogon hannunta don buri take taje taga farincikin dake kwance fuskar aishatun.

Hankali kwance take takawa a harabar gidan nasu tana nufan qofa,tana jin ta gama da dukka wata matsala yanxu dake gabanta,so saura ya rage na wadanda suka gayyatota cikin matsalar susan yadda zasu warware qullinsu.

Tana taba handle din qofar taji an budeta,sai ta daga kanta a hankali ba kaman dazu da yake a qasa ba tana kallon gabanta.

"Good morning madam" Kakkaurar muryar ta fada cikin tsananin girmamawa har yana rusunar da kansa duk kuwa da cewa ya ninkata a tsaho da shekaru,girman jiki kuwa sam ba'a maganarsa don bata kawo koda gefansa ba.

"Good morning madam" Ta sake jin wata muryar ta daban a daya gefan nata shima ya fada a girmame.

104

Da idanu ta sake binsu,murdaddune a tsaye,wanda babu alamun tsoro ko shakka a tattare dasu,zubin tsayayyun masu damarar nan da akan samu akan hanyar shiga fadar shugaba wasa,wanda rana ko ruwa basa sanyasu motsawa ko canzawa daga muhallin tsaiwarsu.

Sosai ta tattaro dukka dauriya da qwarin gwiwarta,ta azawa fuskarta wani mugun daurewa,tasa hannu tadan tura qofar tana amsawa ciki ciki da

"Morning" Tana sanya qafarta zuwa waje

"Sorry maaa........kiya haquri ki koma ciki..... Isn't allowed maaa". A mamakance ta dakata gami da ja baya saboda yadda yayi bake bake a gabanta,bataga ma hanyar wucewar ba komai qanqantarta

" Isn't what?......waye kai?" Tayi masa tambayar kai tsaye saboda bata da lokacin batawa tayi wani dogon nazari.

"My name is abdulgafar......ni da abokin aikina kuma duka munzo ne don tsaronki" Ya fada da matuqar girmamawa kansa a qasa,baya iya wani cikakken hada ido da ita. Haushi da mamaki duka suka hadu waje daya suka tsaya mata a wuya

"Tsarona like how?.....ni na buqaceku?"

"No maaa.....bake bace......umarni ne daga wajen boss" Dayan da baiyi magana ba sai yanzu ya fada da tasa girmamawar

"Who's boss?" Ta fadi da mugun fusata saboda ta fara shanshano wani abu

"Sir muhammad jadda....."

"Enough......ya isa.....ku bani hanya na wuce,daku da boss din naku da gadin nawa duka matsalarku fe ba tawa ba".

Rusunawa kadan yayi yana hade hannayensa waje daya

"Am sorry maaa......ba'a yarda mu barki ki fita ko ina ba har sai boss ya dawo". Kadan ya rage bakinta ya furta kalmar ashar saboda tsananin mamaki,sai tayi tsaye kawai tana kallon baqar fuskar mutumin mamaki yana zagayawa da ita duniyar tunani,yayin da shi kuma yake ci gaba da furta mata kalmar rarrashi da kuma ban haquri duka a cakude cikin harshen hausa da karyayyen turancinsa.

A wannan karon tana jin tura takai bango,ta inda kuma aka hau ta nan ake sauka,bata kuma da sauran lokacin batawa tayi sa'insa da yaranshi,don haka ta juya a mugun fusace zuwa cikin gidan. Tana tafe da dan sassarfa tana neman number kawu Rufai,abinda ta manta rabonta dayi kenan,saidai shi ya kirata idan neman abun duniyarsa ya motso,shima din ba kasafai ba,don yafi ganewa yayo tattaki suyi ido da ido.

Wata muguwar guda taji an sake mata data ratsa har tsakiyar kanta sanda take taka tsakar gidan nasu,ta runtse ido gudar bibo tana sake birkita mata kwanya,tana so taji da matar nan,amma kuma wani sashe na zuciyarta yana gaya mata tukunna dai ba yanzu ba,wannan qurar data taso miki a yanxu ita tafi cancan ta a kasheta.

"Yar arziqi irin albarka......kiranki alheri ne.....yanzu haka ina cikin layin naku ai,gidan zanzo akwai bayanin da zan miki"

"Basai kazo ba kawu... .Amma inaso ka kira wancan mutumin da kake iqirarin ka bashi aurena......ka shaida masa yayi gaggawar janye wadancan gumakan daya dasa mana a qofar gida da zummar hanani fita sabgogina"

"Kajimin shashasha.....macen da aketa tattali amma ta kasa gane hakan......banda abun ki wacce macace kaf unguwar bama gidan ba ta samu darajar samun masu tsaron lafiyarta idan bake ba?,ke wannan kawai bai isheki alfahari ba?"

"Kawu!" Yau din ta kirashi da dan tsauri a muryarta saboda yadda ranta yakai maqura a baci

"Fadi abinda kikeso ki fada......gani nan ma na shigo gidan" Ya qarasa fada yana datse kiran.

Da kallo bibo data maida yanzu zaman tsakar gida sana'arta qarfi da yaji ta bishi dashi

"Allah ka rabamu da mutuwar zuciyar da 'ya'yan cikinmu zasu dinga juya mu" Ta fada qasa qasa,yaji tana magana amma bai fahimci me take cewa ba,don shi a yanzu hankalinsa nakan lamarin sabreen da me jadda,bazai samu cikakken bacci ba sai ranar daya tabbatar an miqa musu ita.

A tsaye take don ta kasa zama,ba abinda zuciyarta ke maimaita mata sai kalmar

"Wai waye wannan muhammad jaddan?,me ya dauki kansa?,wa yafi?,wa ya damu dashi?".

Koda kawu ya shigo kallo daya yayi mata ya tabbatar lallai abubuwa sun fara cabewa. A yadda yayi mata farin sani fuskarta kawai ta gaya masa lallai ta fara cika,kuma dab take da fashewa,fashewar kuma da yayi imanin ba zata taba zame masa alkhairi ba musamman shi,bata da tsoro,tana iya yin komai idan har ta tsara zatayin,gwara tun wuri yayiwa tufkar hanci......ya gayyato masu tayashi yaqinnan don ya samu ya tsira da mutincinsa da sauran 'yan canjinsa.

"Ka kirashi ka gaya masa......idan ba haka ba zan gaya masa ta hanyar da bazata yiwa kowa dadi ba kawu!" Ta sake maimaita maganar da sautin da zai tabbatar maka kai tsaye daga zuciyarta maganar ke fita.

"Oh.....Allah na gode maka" Abinda kawai ya iya fada kenan. Tako ina yana jin gumi yana tsatsafo masa,tsakanin me jadda da sabreen baima san wanda yafi wani sakashi a masifa ba.

Hannun kujera ya samu ya zauna yana share fuskarsa da hannun babbar rigarsa,yana jin gaba daya duniya ta juya masa baya cikin qanqanin lokaci. Number da a kullum kiranta yake yawan sakar masa da fargaba da kuma faduwar gaba ya kira,duk da ya fuskanci cewa mamallakin number mutum ne me tsananin sauqin kai da kuma fahimta qwarai,hakanan kiran number wayarsa yafi masa sauqi akan kiran wancan mutumin da yake jinsa tamkar wani mala'ikan daukan rai a wajensa.

Daidai lokacin da yake tsaye cikin malam aminu kano international airport,zagaye da guard nasa,gefe daya kuma farouq ne da yayo masa rakiya.

Kusa da kusa suke tsaye sosai shi da farouq din,da alama akwai magana me muhimmanci da sukeyi shi dashi din. Hannunsa ya zura kawai cikin aljihun kaftan dinsa ya zaro wayar,ya maida dubansa ga fuskar fuad dake qoqarin sanya wayarsa a silent,don ba kasafai ya fiya son kiran waya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login