Showing 180001 words to 183000 words out of 209775 words

Chapter 61 - DUNIYATA BOOK 1 By HUGUMA

****takardun gabanta ta jawo ta rufe a nutse tana maida dubanta kan fuskar hajja dake shan lafiyayyen nonon da aka zubawa madara aka kuma niqeshi cikin 'ya'yan itace masu dadi.

"Na gode sosai qawata.....na gode qwarai da gaske......tabbas banda ke koda komai zai tafi zai kasance me wahala a wajena..... Banda abinda zan iya biyanki dashi,kedai Allah ya bawa autarki miji na gari". Wani qasaitaccen murmushi hajja ta saki tana Ajiiye mug din dake cike da furar idanunta akan fuskar maamah. Ita daya tasan me take tsarawa cikin zuciyarta,ita kadai kuma tasan me ke kai kawo a ciki

"Ameen mariya......banda abinki mene ne amfanin amincin?,mene ranar amincin?......yanzu kawai abinda ya rage shine.....muyi tattaki har zuwa cikin gidansu don mu sake tabbatar da komai a kanta.....daga nan sai mu saka rana ta daban da zamu tunkari yarinyar.....komai ina ganin bazai mana wahala ba......ina ji a jikina zata karbi komai cikin sauqi da hanzari,tunda kudi ta fito nema......mu kuma biyan buqata kawai mukeso". Kai maamah ta jinjina farinciki yana lullubeta. Hasken nasararta da dukkan wata lamba ta nasara tana walqawa cikin idanunta.

"A shirye nake na rasa komai don wannan abu ya tabbata" Maamah ta furta

"Ba zaki ma rasa komai din ba.....don komai zai fito ne daga jikin wanda ake abun don shi" Hajja ta fadi tana sake sakin murmushi.

"Ina jin me zai hana yau mu shiga gidan nasu?,tunda ga adress nan da komai jikin takardar?" Maamah dake sake duba takardun ta fadi

"Da zafi zai haka?......"

"Bakiji abinda bahaushe ya fada ba?,da zafi zafi ake dukan qarfe?" Maamah ta katse maganar hajja,sai kuma suka saki dariya dukkaninsu.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 92

Cikin wani dan banzan lace peach colour da torches na purple maamah din ta shirya,sannan tayi amfani da wani irin luxury veil me wani irin lafiyayyen jiki ta lullube jikinta dashi. Tun daga takalmi da jakar hannunta zaka sallamawa shigartata,ballantana azo ga sarqa da awarwaraye zuwa zobunan gold data sanyawa yatsunta guda hudu kowanne hannu bibbiyu.

Cikin motocinta ta sanya driver ya fidda wadda bata fiya shiga ba,aka gogeta tas ainihin kyawunta da qyallinta ya sake bayyana.

"Gaskiya kin fini gaggawa mariya" Hajja dake shiga cikin motar ta furta tana 'yar dariya.

Ajiyar zuciya maamah ta saki tama girgiza kai

"Mariya kenan,ba zaki gane yanayin da nake ji ba,saboda ke komai ya miki daidai cikin rayuwarki,yara biyu?,amma ba guda daya wanda zaka juya yadda kakeso?......zaiyi wahala idan har yarinyar tana cikin gidan ma ban nemeta ba......gwara mu yita ta qare hajja.....idan na samu yadda nakeso ma zuwa qarshen watan nan a gama komai ta tare na fara aiwatar da aikina.....don na samu labarin dab yake da kammala ginin wannan gidan da nake burin kasancewa a ciki ni da duk wanda naso naga dama". Kai hajja ta jinjina tana sauke boyayyar ajiyar zuciya. Tafi kowa buri da kwadayin wannan gidan,saboda bahaushe yace gani ya kori ji.

Tayi yawo da qafafunta tsakanin katangun gidan,ta kuma samu ganin iya abinda Allah yayi tana da rabon gani,don hatta ginin da akeyi qarqashin kulawar security ne,so shiga ko fita din yana qarqashin kulawa.

"Karki damu.....komai zaizo yadda muka tsara qawata"

"Haka nake fata" Dukkaninsu sukayi maganar cikin ransu suna gamsar da kansu tasirin tasarrufinsu ba tare da sun tsarma kalmar IN SHA ALLAH a ciki ba.

Idanunsu kaf cikin layin lokacin da motarsu ke gangarawa,suna lissafe da kowanne gida da suke giftawa har suka qaraso babban qofar gidan

"Yauwa......tsaya a nan,shine wannan da alama" Hajja ta fadi tana baiwa driver din umarni.

Tare suka fito kowa ta qofa daban daban,maamah ta soma gyara lullubin kanta tana duban gidan. Gida ne da kana masa kallon farko zaka fahimci a wani zamani da can mamallakin gidan yana cikin sahun masu arziqin wancan lokacin,to amma duk da hakan data fuskanta sai tadan tabe baki

"Banda lalura da neman biyan buqata babu abinda zai sanya na nemawa fuad aure a irin wannan gidan........bari amma ba komai.....ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba,muddin komai ya kammala,xan sanya binciken qwaqqwafi sai na nema masa auren yarinyar da tafi kowacce 'ya gata a al'ummarmu.....sannan kuma wadda zata dace da tsarina". Murmushi hajja ta saki tana jin maamah tana motsa mata wani abu cikin ranta.

"Qwarai kuwa qawata......dan gata ai sai 'yar gata,amma naji dadi da kika fahimci nema masa wannan ba matsala bace.....tunda AUREN WUCIN GADI NE AUREN BIYAN BUQATA".

Ranta a sake tana murmushi suka fara kutsawa gidan suna magana da juna qasa qasa.

Har suka dangane da babban tsakar gidan gidan basu hadu da kowa ba. A irin wannan lokacin lokaci ne da yara da sauran wadanda suka tasa cikin gidan suka jima a makaranta har wasu ma suna dab da tasowa,don haka ba kowa din sai tsakar gidan dake a tsaftace kamar kullum.

"Salama alaikum.....gafaranku dai mutanen gida" Hajja ta ware muryarta ta kwarara sallamar idanunsu yana yawo bisa tsaftataccen tsakar gidan.

A hankali ta bude idanunta dake a lumshe,kimanin awa guda tana kwance a haka saman doguwar kujerar falon tun bayan kiranta da JIB yayi ya shaida mata an rarraba wasu cikin kudaden a account din mutum dubu d'ari tsaffin 'yan pension da suka rasu da bashin banki,wanda hakan ya sanya ake cirewa daga cikin abinda gwamnati ke bawa iyalansu duk wata. Hakan ya tagayyara iyalai da dama,domin basu da qarfin biyan kudin bare su tsira daga zari d'ai d'ai da banki yake musu. Cikin ranta da jikinta takejin wani irin sanyi kamar ta aiwatar da wani wajibi da yake kanta. Ta zame ta kwanta cikin mutuwar jiki tana tuna yadda bashin bankin ya zamo silar shigarsu halin ni 'yasu bayan rasuwar abbansu,duk da cewar bashi yaci bashin ba ci masa akayi babu saninsa babu kuma yardarsa,rayuwar ta dinga qwallo dasu har zuwa sanda tasu mahaifiyar ta sake tafiya ta barsu da tsanani da uqubar rayuwar. A yau tasan iyalai da yawa zasu kwana cikin farincikin da take fata ya zama sanyi da haske cikin qaburburan mamatansu ciki harda iyayenta.

Ta jima a kwancen tana tunanin me gobe zata haifar mata?,a wanne gurbi zata dora rayuwarta wadda daga rana irin ta yau takeso ta koma aminatu dinta ba sabreen fateema minal da sauran tarkacen sunayen data yita rabawa maza ba. Ta zauna taci gaba da kula da rayuwar qannenta dake da matuqar tsada da muhimmanci a gareta.

Tanaso subar gidan,tanaso su bar kano ma gaba daya idan zaiyuwu,saidai kuma tana hasaso irin qalubalen da zata iya fuskanta a sanda ta koma rayuwa cikin wata al'ummar da basusan ainihin wacece ita ba. Wanne kallo zasuyi mata sanda take zaune cikin gidan da daga ita sai qannenta mata?,wannan ne kadai abinda yake sake taka mata burki,sai kuma ga sallamar ta ratso har dakinta.

Sallama ta uku taji an sakeyi,dole ta miqe daga kwanciyar ta sauko da qafafunta qasa ta miqe tana takawa a hankali don amsa sallamar da kuma duba waye. Don tasan lokaci irin wannan da yawa cikin matan gidan suna bacci.

Har ta sanya hannu zata yaye labulen muryar daada ta dakatar da ita,sai ta koma a hankali ta zauna a inda ta tashi tana jawo wayarta ta bude.

"Wa'alaikumussalam" Ta amsa tana binsu da kallon rashin sani. Saidai kafin ita ko su su sake cewa komai bibo ta bankada nata labulen ta fito da buta a hannu.

Itama sakin bakin tayi tana kallonsu,saidai ita tana musu duban farko ta karanto zallar wadatar da suke ciki da kuma arziqi. Atamfar jikin maamah ta kalla,saitaga tana mata kama da atamfar da sabreen ta saka rannan har musu ya barke tsakaninta da hadiyya,inda daga qarshe hadiyyan ta tabbatarwa da bibo kudinta ya kusan kaiwa dubu sittin da biyar idan ma baifi haka ba.

Wannan abun data tuna ya sanyata saurin ajiye butar hannun nata sannan ta kawo fara'a da murmushi ta aza saman fuskar tata. Idanma arziqi ne kamata yayi ace kai ka fara tararsa a dakinka ya fara sauka

"Marabanku sannunku da zuwa lale" Ta fadi cikin haba haba da tsananin kulawa.

Hausawa sukace shimfidar fuska tafi shimfidar tabarma,wannan da suka gani ya sanya suka karkatar da hankalinsu akan bibo suna amsa mata,wannan ya sanya daada salin alin sakin labulenta ta koma ciki don ba kasafai ta fiya shiga shirgin da ba bata ba,musamman kuma data ga bibo din ta zaqe.

"Ku shigo ciki mana,kwa tsaya daga nan?,ai baqonka annabinka" Ta fadi da sauri tana juyawa ciki.

Idanu suka dinga bin rumfar bibo din dashi sanda take rawar jikin aje musu ruwan sha,akwai wadatar tsafta amma ba wadatar arziqin da yakai koda quarter din nasu.

"Bismillahir rahmanirrahim" Ta fadi tana zama a gabansu.

"Mu sake gaisawa ko?,ina wuninmu zaa ce?" Tayi zancan tana sake fadada fara'arta.

Hajja da tasan takan duniya ta washe mata bakinta tana amsa mata itama cikin madaukakiyar fara'a da nuna sakewa.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 93

itama,tana hango qishi qishin halayen bibo da kyau daga yanayinta da idanunta dake nuna zallar wayo.

Itama maamah data zurfafa a tunani ta sake waiwayawa suka gaisa,sai kuma dan shuru ya biyo baya na wani lokaci kadan kafin bibo ta kasa daurewa

"Kuyi haquri fa bayin Allah,abubuwan da yawa,ban shaida ku ba" Tayi maganar tana basu hankalinta sosai.

Murmushi hajja tayi tana gyara zamanta

"Eh ai gaskiya ba zaki shaidamu ba,don bana jin mun taba gamuwa kam.....mu din baqi ne,sunana hajja harira.....wannan kuma mariyatu amma muna kiranta da maamah" Hajja ta fadi tana nuna maamah din da hannu

"To....to ma sha Allah,ni hafsatu nake.....kuma nice mace ta uku cikin gidan nan.....duk da me gidan Allah yayi masa rasuwa,ya rasu ya bar kowaccenmu da 'ya'ya". Fuskokinsu suka nuna jimami suka masa addu'ar samun rahama sannan hajja ta dora

"Muna tambaya ne akan wata yarinya da muke kyautata zaton itama 'yar gidan nan ce" Sake daidaita zamanta bibo tayi,zuciyarta tana zillo da fatan jin wacece

"Mun sanya an biyo mana sawunta ne saboda muna son nemawa d'anmu ita". Murmushi bibo ta tsinke dashi hade da faduwa kuma da gabanta yayi. Wannan dan mutanen ko makaho ya shafasu yasan cewa tabbas masu arziqi ne,masu dukiya ne,ba kuma qananun mutane bane,akwai arziqi daula da dukiya a wajen,iya zamansu a wajen kawai qamshin turarensu ya cika wajen,wannan kawai ya isa ya gaya maka matsayinsu a rayuwa.

Zuciyarta cike fal da fata take dubansu,don tana kyautata zaton ba wanda za'a nema haka cikin gidan cikin dattako haka irin d'iyarta dake karatun kiwon lafiya.

"To......to ma sha Allah,ai kowa kukeso a gidan nan 'ya'yanmu ne dai.....wacce ce a ciki?,hadiyya?". Kai hajja ta girgiza tana kallon bibi

"A'ah,Sabrina ce".

Tamkar hajja ta kawo ruwan zafi ta watsa ma bibo a sassan jikinta haka taji,ta dinga jin wani abu yana tsarga mata tun daga saman kanta har tafin qafafunta.

Wacce Sabrina din ga nasu 'ya'yan a zazzaune kamammu?,wadannan mutanen masu alamu na damshin arziqi sune za'a ce sun tattako neman auren Sabrina din?,wacce daraja ko kamala take da ita data cancanci wannan?. Ji tayi ba zata iya daurewa ba,tako wacce fuska sai ta barar da dan guntun mutuncin da qila dansu yaje ya musu qarya ya labarta musu tana da shi yarinyar,dole ta farke mata laya don ba zata iya bari wannan abu ya faru ba.....idan ma Allah ya bata sa'a ta musu nuni da tata kamilalliyar d'iyar.

"Tofa......amma dai hajiya d'anku ya rufeku gaskiya,duk da bansan ko irin cikin mutanenta shima yake ba?".

" Kamar yaya kenan?" Maamah ta jefa mata tambayar cikin fargabar kada ta kasance an kusa aurenta ne da wani,wanda muddin hakan ya faru sai inda qarfinta ya qare wajen baza dukiya har sai an fasa an dawo da abun kan fuad din.

"Abinda nake nufi shine maganar gaskiya baku yiwa yaronku zaben macen aure ta gari kaman yadda addini ya shardanta ba......ni da kuka ce Sabrina ma abun mamaki ya bani,waye zai nemi auren wannan idan ba asharari ba?,danku dan gidan girma da dattako bai cancanci auren mace irin Sabrina ba......yarinyar da duk cikinmu ba wanda yasa sana'arta data wuce KARUWANCI.....sam bata kwana cikin gidan nan sai anci sa'a qwarai....ni nan da hannuna nasha tsareta amma ta tsallake ta gudu,rubutun shiriya ba irin wanda bata sha ba,fada duka ba wanda ba'a yi ba......ga sata kaman bera,yanzu haka kwanaki muna kyautata zaton cikin shege taje ta zubar,ba wanda take ganin mutuncin sa ballanta ta raga masa,dan tsoro irin na diya mace fa sam ita bata sanshi ba,gaba gadi take komai cike da rashin kunya da rashin albarka......son abun duniya a wajenta abun har ba'a magana......zata iya komai akan kudi.....idan nace komai ina nufin komai da komai fa......har kisa...."

"Wadannan dabi'un su suka sanya mukeson aurenta da yaronmu". Maamah da dogon sharhinta ya fara isarta ta fada tana kallon bibo,dogon sharhin da yayi Mata dadi ma,don ya qara tabbatar mata da cewa tabbas zata iya.....Sabrina din ita tafi dacewa ta kuma fi cancanta da deal din.

Idanu bibo ta gwalalo tana kallonsu maamah cike da zallar mamaki.

"Amma ta yaya za'a aikoku neman aure kuje ku nema musu irin wannan baragurbin diyar?, bayan ga gaskiya kun gani daga bakin iyayenta sun gaya muku ba'a rufeku ba?,anya ku din ba kishiyoyin uwa bane zaku rufi uwarsa ku cutatar mata da d'a?,ku nema masa auren tantariyar hatsabibiyar KARUWA ba tare da saninsu ba?"

"Ni nan nice uwarsa kuma mahaifiyarsa data dauki cikinsa wata tara ta kuma haifeshi ba tare da taimakawar kowa ba.....a haka nakeso ta zamewa d'ana matar aurensa,wannan din zabina ne!".

Dukka sai aka gogewa bibo hadda,sun sanyata a rudani gaba daya ta rasa fahimtar komai. Uwa kuma?,uwa da kanta?,anya da gaske uwar ce?.

Tana tsaka da wannan tunanin ta tsinkayi miqewarsu suna aje mata wasu adadin kudin data tabbatar ba 'yan kadan bane.

"Ga wannan ki soma riqewa......ki nuna mana kawai dakinsu ko dakinta cikin gidan nan" Maamah data qagu ayi komai a wuce wajen ta furta tana duban bibo

"Daki me kallon wannan dab da matakalar bene" Ta furta a sanyaye.

"To mun gode fa" Hajja ta fadi tana bin bayan maamah da tuni ta fice.

Zumbur ta miqe tabi bayansu tana leqensu ta tsakanin labule,salati da sallallami kawai takeyi zuciyarta na wani irin bugawa. Tunda take a rayuwarta bata taba ganin baragurbin iyaye ba irinsu,shin anya ma da gaske kuwa suke?.

Tsaf nutsuwarta ta dauke,tana jin ba zata iya zama haka ba tare data labartawa kowa wannan zancan ba. Balaraba bata nan tun dazun ta fita.....bata jin kuma zata samu cikakken hadin kan yin magana da daada,don tasan ba kasafai ta fiya shiga shirgunan da ba nata ba,ballantana ma kuma lamarinsu Sabrina din.

Wuf ta fito ta kuma fada dakin daada hankalinta a kansu sanda suke cire takalmansu suna shiga parlor dinsu Sabreen.

"Lafiyarki meye haka bibo?" Daada dake zaune tana gyaran zogale cikin rumfarta ta fada idanunta akan bibo.

"Muhammadur rasulillahi daada.....zo kijimin wata lalacewa....zo kiji wata almara,wai zuwa akayi neman auren yarinyar nan Sabrina?". Tayi zancan tana zama d'aid'ai a gaban daadan.

"Wa'alaikumussalam" Sabreen ta fada a hankali tana daga idanuwanta zuwa ga bakin qofar falon nasu.

Idanu ta zube musu sanda suke shigowa cikin falon,haka kawai taji gabanta yana faduwa akan baqin fuskar da batasan su waye ba. Sai ta samu kanta da miqewa tsaye tana fadin.

"Sannunku da zuwa"

"Yauwa sannu 'yar nan" Maamah ta furta cikin murmushi yayin da hajja ke qarewa sabreen din kallo wadda ke sanye cikin soft Egyptian bubu me mayafi,amma madadin mayafin sai ta sanyawa kanta hula wadda santsin gashinta ya hanawa hular zama daidai,kaman ma ta mata kadan sakamakon nannadadden gashin data daure a qeyarta.

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login