Showing 72001 words to 75000 words out of 209775 words
bata kulawar da babu yadda za'a girka abinci cikin gidan ba tare da nama ko kifi ba. Ba irin nau'in nama ko kifin da babu shi cikin gidan muddin musulunci ya halasta cinsa.....hakanan babu nau'in cima da babu ita a gidan muddin halas ce cikin addininsa.....kamar yadda abun sha ba nau'in da babu.......ana kuma sake shiga da wani duk qarshen kowanne wata ba tare da damuwa da cewa akwaisu bila'adadin ba bash kuma qare ba
"Maahma?......wanne abu ne yafi qarfinki?" Ya tambayeta murya a tausashe yana son ya kaita muhallin da yayi imani can takeson zuwa
"Kudi fu'ad.......a matsayina na mahaifiyarka......bani da wani abu da zai shiga tsakanina da kai sai dubu dari a wata?" Ta furta tana jin ciwon abun sosai cikin zuciyarta.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 37
Ya riga ya sani tun kafin ta fadi,yasan abinda zata fada din shine burinta na qarshe da zai kaita ga cikar muradinta. Yana da cikakken sani na haqqin uwa.....yana da cikakken sani na duk wani haqqi da yake wuyansa daya zamewa rayuwarsa tilas ya saukeshi......a ciki kuma babu wani abu guda data rasa sai KUDI. Kudin kuma da yakejin ba zaya iya mallaka mata sama da abinda yake bata din ba saboda wani babban dalili. Inda zai yiwu cikin abinda yake batan ma zayaso ya zama qasa da hakane ke shiga hannunta. Barin kudi a hannunta GANGANCI NE. Barin kudi a hannunta KUSKURE NE da ya tabbatar aikatashin zai zamana babu wani abu da zai goge wannan kuskuren.
"Am sorry maahma....." Ya fadi da lallausar muryarsa data karye. Shi daya yasan abinda yakeji a qirjinsa idan ya daga idanu ya kalli maahma a matsayin mahaifiyarsa.....shi kadai yasan abinda yakeji idan ya tuna dalilin da yasa take neman kudade haka masu yawa daga hannunsa.
"Idan akwai wani abu ba wannan ba da kike buqata.....ko musaddiq kina iya shaidawa.....am sure zaiyi handling komai.....na barki lafiya" Ya qarasa maganar yana zame wayar daga kunnensa.
Zazzafar iska ya fitar a bakinsa sanda ya zubawa titi idanu......ya tabbatar duk yadda ubangiji ya ni'imta rayuwarka.....tabbas akwai jarrabawa da ba'a raba ruhi da rayuwa dasu.
"Sadiq" Ya kira sunansa a hankali,sai sadiq din dake zaune a gaban motar yana fama shirya bayanai kan yadda ganawar su da kamfanin zata kasance yadan waiwayo
"Na'am"
"Banaso mu wuce awa biyu a kamfanin nan.....inaso kome mukeyi cikin satin nan mubar Korea......gida nima nakeso mu koma"
"In sha Allah hamma" Ya amsa masa cikin girmamawa sannan ya daidaita zamanshi yana ci gaba da aikinsa.
Sai data tabbatar ta kammala gyara gashin tsaf,ta saka siririn ribbon ta daureshi. Sosai fuskarta ta fita tarwai,silky skin din nan nata kaman tana amfani da wani abu daban na gyaran fata.
A nutse ta taka don dauko wayarta dake saman gado,idanunta ya sake sauka kan luggage din da har yanxu ta kasa budewa,sai ta koma ta zauna sosai saman dan madaidaicin rug na gaban gadonta,ta jawoshi jikinta ta soma zugewa
Tsala tsalan abayas ne suka fara mata sallama. Abayas masu tsananin kyau da tsadar da suka amsa kudinsu na qasashen dubai da oman da Morocco. Kowacce abaya da shoe din daya dace da ita wanda yawanci takalman kamfanin Gucci Hermes kitton da tom Ford ne. Tsala tsala agoguna na kerewa sa'a data tabbatar kudade ne ba qanana ba aka zuba aka siyesu. Sai wasu siraran abun hannu masu shining da sukafi mata kama da na gold,daga gefensu kuma turaruka ne turmus masu mabanbantan qamshi da kuma tsada. Dan aljihun dake jikin luggage din ta zura hannunta,sai ta fiddo kyakkyawan kwalin,ta juyashi kadan a hannunta,tun bata bude ba ta fahimci kwalin waya ne,saita zazzage ledar kwalin ya fado. A nutse tayi unboxing wayar data jima da sanin kudinta. Aqalla kudin wayar ya tasamma miliyan hudu,sabuwar Samsung 3screen da bata gama fita hannun jama'a ba. Ta riqe wayar a hannu tana juyawa tare da duba qaramin takardar dake nuna a qasar da aka qerata da zafi zafinta acan Ya'aqoub ya siyeta.
Ajiye wayar tayi a gefe tana bin kayan da idanu,kaya ne masu tsada dukansu,siyayya ta masu aji masu ji da naira. Babu abinda baiyi kyau ba a ciki amma sam ba abinda ya burgeta. Idanunta ta lumshe zuciyarta tana motsawa. Ta tuna mata da yawa,a daidai yanzun 'yammata nawa ne kamarta suke can suna neman yadda xasu tsira da mutuncinsu?,'yammata nawa ne suka rasa darajarsu saboda neman yadda zasu rufawa kansu asiri?,mata nawa ne suka hadu da abubuwa marasa dadi saboda an rasa me taimakonsu?,bayan al'ummarmu cike take da mawadata irinsu Ya'aqoub din,wanda kyautar dubban daruruwa zuwa miliyoyi ba komai bane don su fita da aljifansu?.
Zuciyarta ta tabu sosai,ta shiga tuna wasu shekarun baya da suka shude da rayuwarta,shekarun da sukaso girgiza duniyarta,sukaso jefata wani baqin duqununun ramin da inda ta afka babu rana ko wata na fita daga ciki ko tsere masa?.
Sautin qarar daya daga cikin wayoyinta ya katse mata tunaninta,ta bude idonta tana wurgawa inda wayar take,ta miqa hannu a kasalance ta jawota.
Mk kamar yadda tayi saving number dinshi haka ya nuna mata.
"Mika'il" Ta furta sunan muryarta qasa qasa,yayin da zuciyarta ke wassafa abubuwa da dama a kanshi.
Ci gaba tayi da kallon wayar,batayi yunqurin dagawa ba har zuwa sanda wayar take dab da tsinkewa.
A kunnenta ta kara wayar,sannan ta maida idanunta ta rufe gami da jan bakinta ta tsuke.
"Hi" Ya furta cikin zamudi tamkar ya mance gurin da yake a zaune. Qaramin tsaki taja qasan zuciyarta,ta motsa labbanta a hankali
"Assalamu alaikum" Ta fadi a nutse.....sallamar da ta sanyaya masa jiki,ta kuma jefa shakku a cikin zuciyarsa. Itace macen da yakewa kallon bariki ta farko da take matuqar masa kwarjini. Itace ta farko da yake hangen wasu kalan dabi'u da suke jefa shakku da kokwanto cikin zuciyarsa. Baisan kala da adadin matan da yayi mu'amala dasu cikin rayuwarsa ba,amma sai take neman zame masa ta daban.
Dan gyaran murya yayi sannan ya amsa mata da
"Wa'alaikumussalam.....afuwan.....banyi sallama ba ko?,na matsu da naji muryarki ne.....na kwana da kewa na kuma tashi da ita......ina fatan kin tashi lafiya?" Sai da tasha qamshin nan nata da yake a halittarta sannan ta amsa masa
"Lafiya qalau......"
"Naji dadi dajin hakan.....yaushe za'a bani damar sake ganinki?" Yayi mata tambayar abinda yafi damunsa kuma cikar burinsa a kanta.
"Sai lokacin yayi......idan yayin da kanshi zai kawoka gareni". Sam ba haka yaso ba,sai kuma yake ganin kaman daga gareshi ne,ya kamata ya gyara wasanshi.
"Zan iya haqurin jiranki koda na shekara nawa ne......amma inaso kisan akwai zuciyar da tayi matuqar mutuwa a kanki take kuma da buqatar soyayyarki....."
"Mika'il......" Aka kira sunanshi daga gefe,muryar ta fusgi hakalinsa,yadan waiwaya kadan ya dube kamilar fuskar nan,daya daga cikin fuskoki biyu dake masa kwarjini cikin kamfanin
"Am sorry......zan yanke kiran,ina fatan samun wayarki a bude zuwa anjima,ba kamar yadda nasha wahala jiya ba" Boyayyen tsaki ta saki tana yanke kiran hadi da zame wayar daga kunnenta. Ta wurga fararen idanunta gefe tana sauke qaramar ajiyar zuciya. Wato namiji akan mace tamkar mayen qarfe ne da qarfen kansa?,musamman idan zaki bashi abinda yakeso?,ko kuma yana hasashen samun wata riba ko ganima a kanki?.
A nutse ya zuba masa idanunsan nan yana kallonsa lokacin da yake jefa wayarsa a aljihu yakuma iso bakin zagayayyen table din da yake zaune a kai.
Muhammad fuad jadda CEO abinda ke rubuce kenan jikin wani dan siririn katako dake zaune sosai saman table din daga gaba gaba. Saidai a maimakon muhammad jaddan,farouq hamza kibiya ne zaune saman kujerar yana duban mika'il da kyau har ya zauna kujerar dake fuskantarsa.
"Sassaucina fiye da oganku kamar yana son jawo sakaci da aikinku ko?" Ya jefawa mika'il tambayar yana debe dukkan wani wasa da haba haba da ya saba yi dasu dake saman fuskarsa. Shafar kansa kadan mika'il yayi cikin rusunawa
"Sorry sir.....urgent call ne shi yasa....but hakan bazai sake maimaituwa ba"
"Mituna nawa nayi ina kallonka ba tare daka sani ba,hankalinka baya jikinka?,ka kuwa san girma da matsayin position da kamfani ta baka mika'il?" Ya sake masa tambayar yana riqe habarsa da yatsarsa guda gami da kafeshi da idanunsa sosai. Yanayin ya tabbatarwa mika'il na gaske ne,a irin wannan lokacin da yake buqatar kusanci na sosai da JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES bai kamata ya bari BOSS muhammad ya dawo ya samu wani shaidan banza a kansa ba
"Sorry sir.....it will never happen again" Kaman bazai daina kallonsa ba sai kuma ya fesar da iska daga bakinsa,ya tura masa wani folder yana cewa
"Ruwanka ka riqe aikinka da kyau,ruwanka kayi wasa dashi.....daga rana ita yau ba zaka sake ganina a company dinku ba,wataqila saidai ziyara......ka kuma fini sanin waye boss dinka" Ya qarashe maganar yana tashi daga saman kujerar.
Yadda hankalinta yayi kan zuwa duba aysha yasa gaba daya ta manta da batun wayar da ta bada address din aje a karba. Gaba daya ta manta ma da zaman wayar cikin dakinta. Sai data tabbatar su huda sun dawo daga boko sun wuce islamiyya sannan ta shirya cikin wani dinkin atamfa doguwar riga data bude sosai daga qasa ta zauna mata daga sama cas jikinta,ta kuma lullube kanta da Chantilly veil,takalmi da jakan D&G su suka zama cikamakin adon nata.
Kamar ko yaushe tsakar gidan nasu zuwa farfajiyar gidan bata rabo da kai kawon jama'a jifa jifa. Kamar kullum haka ta ratsasu a nutse ta fice ba tare data damu da idanun dake zube a kanta ba.
Kamar dai kowanne lokaci,abinda ta baro cikin gidan shine a waje. Yawan idanun jama'a dake kanta ko kadan basu dadata da qasa ba. Tun asali mutum ce me damuwa da lamarin gabanta.
Abubuwa da dama da suke cikin zukatan mutane a kanta bata isa ta gogeshi ba. Abune da tun yana damunta ya zame mata jiki. Suna mata kallon biri ne tana musu kallon ayaba. Anyi walqiya me hasken data haska mata abubuwa masu tarin yawan da suke boye cikin hijabin idanuwan jama'a da wani irin shamaki da tsinkaye da idanuwa basu kaiwa wajen.
Wasu mutanen a riga kawai suke mutane.....wasu dattawan a suna ne kawai kuma a baki.......wasu jama'ar da ake tunanin suna gyara ko bada gudunmawar gyaruwar al'umma su din GUBA ne,guba ce wadda bata da magani,guba ce me d'aid'aita komai da wargaza komai.
Daidai sanda takai qarshen tunaninta sai ta fidda eye glasses dinta da ba kasafai ta fiya amfani dashi ba ta manne qwayar idanunta. Daya daga cikin abinda ya sanya suke mata mummunan kallo da mafi munin fassara. Eye glasses ne me duhu dake qarawa fuskarta kyau da kuma kwarjini,yake kuma iya hana mutane ganin ainihin qwayar idanunka.
A nutse takai bakin titi,saidai yanayin kai kawon abun hawa kadai zai gaya maka akwai qarancin motocin haya
"Ki siya mota kawai ki huta sabreen" Ta tuna kalamin qawarta qwaya daya da take da ita duk duniya wato haseena. Karon farko tun wayewar garin ranar ta saki murmushin da batayi niyya ba,abinda ya sanyashi tsaiwa da motarsa cak. Duk da cewa ta daki zuciyarsa tun daga nesa daya hangeta,amma sai gashi farat daya ta sanyashi tsaiwar da baiyi niyya ba.
Taga gilmawar farar motar amma saita dauke dukka wani hankalinta zuwa wani sashen,qasan zuciyarta tana fatan bawai ya tsaya bane saboda ita,don a yanzun bata da buqatar qaruwar kowanne namiji cikin rayuwarta. Tana da tarin matsalolin da takeson ta kammala dasu tukunna,mazajen dake cikin rayuwarta kuma a yanzun ta sallami kowa da kalar sallamar data dace dashi kafin ta sake sabon zubi.
A hankali motar ta dawo daidai gabanta ta kuma tsaya cak,sannan aka sauke glass din motar,abinda ya bawa sassanyan sanyin ac din dake gauraye a motar damar fitowa waje ya kuma daki fuskarta.
Sallamar da yayi mata ta tilastata waiwayowa ta dubeshi. Nutsatse kuma kamili a ido,wankan tarwada wanda ko bai miqe tsaye ba ta tabbatar dogo ne. Zagayayyar Fuskarshi da gemu ya yiwa qawanya,sai idanunsa dake saye a cikin glass.
"Bai dace ace zafin rana yana dukan wannan kyakkyawar fuskar ba.....shigo don Allah na rage miki hanya". Jin kai da miskilanci cikin jininta yake,duk daga yanayin kamalar data gani a fuskarta ya mata kwarjini amma saita sake dauke kai ba tare da tace masa kanzil ba.
Murmushi ya saki,ya miqa hannu yana bude mata motar
"Ki shigo domin Allah". Ya furta yana tsareta da idanu har zuciyarsa yana jin tayi masa. Duk da cewa akwai wani irin kwantaccen kwarjini akan fuskarta wanda bayajin cewa ita kanta tasan tana dashi.
Kaman yadda magiyarsa ta dauki hankalinta haka bullowar kawu ta dauki hankalinta. Duk da cewa daga nesa yake amma ta zuba masa idanu da kuma wannan komar tata dake saurin karanto lissafin me lissafi. Cikin qasa da minti daya ta gama karantarsa,zaiyi wuya ace ba ita yaje nema gida ba bai sameta ba ya fito. Batayi shawara ta biyu ba ta juya a hankali ta kama murfin motar ta bude ta shige ta maida ta rufe,daidai sanda motar ke tashi ya iso gurin.
"Kaga shegiyar yarinya?,ni zaki gudarwa?,don ubanki ai duk tantirancinki dai idan dare yayi gidan adamu kike dawowa ki kwana ko?,to mu zuba dani dake.......meye amfaninki muddin ba za'a moreki kudi ba?,ai amfaninki kiyita kawo mana kudi tunda hanyar da kika zabawa kanki kenan" Ya fada yana yarfe hannuwa shi daya a gefen titi,kai kace ya samu matsalar kwanya.
Juyawa yayi da zummar barin wajen,saidai taku biyu rak yayi wayarsa keypad dake aljihunsa ta dauki kururuwa.
"Kai jama'a......Allah yasa ba bala bane.....kash.....shine wallahi" Ya fada yana qoqarin danna madannin wayar da yayi tsananin tauri saboda ganin rayuwa da yayi.
"Hel.....helo bala.....don Allah kar ka damu.....ai in sha Allahu ina me tabbatar maka damu za'a shiga wannan cacar.....yo ta ina zamuyi wasa?,bayan kai da kanka ka tabbatar min mutumin nan attajiri ne......ai ina maka rantsuwa da Allah baka bina bashin rantsuwa wannan karon arziqi ne yake kiranmu....inata buga buga naga na samu adadin abinda akeso a shiga cacar dasu....kada ka damu,zuwa nan da dare in sha Allahu zaka jini,yauwa na gode" Ya fada yana sauke wayar,ya soma laluben aljihunsa don maidata ciki yana sake magana a fili.
"Idan ma Allah ya taimakeni na haye da wadannan kudaden ina zaki sake jina?,ai nima na zama attajirin kaina don ubanki" Sai yaja qwafa sannan tsaki ya biyo baya,ya juya yana sauya hanya.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 38
Sau biyu yana sake juyawa yana kallonta. Tun bayan sallamar da tayi yayin shigowa motar bata sake cewa wani abu ba.
A nutse take da dukkan nutsuwarta,nutsuwar data sake janye ra'ayinsa a kanta matuqa.
"Erhmmm" Ya danyi gyaran murya kafin ya dora da
"Na gode qwarai da baki wofantar da magiyata ba.....hakan ya nunamin kinsan darajar dan adam....." Maganarsa ta sanyata dawowa tunaninta tare da tunasar da ita a inda take. Batace masa komai ba,tadan dai motsa kadan alamun tana saurarensa,hakan ya bashi damar ci gaba da magana.
"Da farko dai sunana alhassan.....ko zan iya sanin sunan malamar?" Sunan daya kira kanshi dashi ya sanyata juyawa kadan ta kalleshi sannan ta maida dubanta ga kwaltar da suke bisa kanta. Kaman ba zatace komai ba sai kuma ta motsa bakinta
"Sunana....." Sai tayi hanzarin dakatawa. Shima kaman sauran?,yana buqatar a bashi stamp?,yana buqatar personal suna nashi tamkar dai sauran 'yan uwansa jinsinsa?. Eh yana buqata,saidai shi din bata jin zatayi wani doguwar mu'amala dashi da har zai buqatu ya zuwa stamp na musamman
"Da alama sunan nan me tsada ne ko?,sai na siyeshi?" Ya fadi yana dan satar kallonta kadan fuskarsa dauke da murmushi. Kai ta girgiza a hankali
"Sunana sawwama"
"Nice and good name.....me azumi kenan?" Ya fadi yana dubanta kadan. Kafada ta daga,koma meye ma'anar sunan bai zame mata damuwa ba,kawaidai ta bashi sunan ne don shine sunan da yazo kanta.
"Ma sha Allah......gashi mun iso inda kika cemin,kuma ina da tarin abubuwan fadi don