Showing 129001 words to 132000 words out of 209775 words

Chapter 44 - DUNIYATA BOOK 1 By HUGUMA

Ba wanda ya musa mata,suna dai binta da ido da kuma hankulansu har xuwa sanda ta jawa kowannensu kujerar zama tana fadin

"Bismillah" Inda ta kasance daga kujerar dake facing dinsu.

Serving nasu komai da komai tayi,tana yi tana jansu da hira tare da qoqarin tuna musu wani abu na daga quruciyarsu. Shidai fu'ad idanu ne kawai nashi ba tare daya iya maida komai ba,har ta kammala tana fadin

"Gashinan kowa ya dauki nasa". Duban abincin yayi da kyau,gaskiya ta fada batayi kuskure ba,a baya baida abincin da yakeso irinsa,amma tun daga ranar data dafa abincin cikin gidansu,ta kuma yiwa mahaifinsu haramiyar abincin a sanda yake kwance yana jinya.....yunwa take sake take rawa wajen galabaitar dashi,ta hana masa abincin,abinda yayi silar kwanansa da yunwa,tun daga ranar har kawo yau bai sake saka irin abincin a bakinsa ba,daga ranar ya fita a ransa,fita ta har abada wadda har yau bai sake dawowa zuciya da rayuwarsa ba.

"Shikam hamma ai maamah yanzun wannan ba cimarsa bane......nima kuma kin manta dama ba kasafai na fiya ci din ba?" Musaddiq ya fada yana shafa kanshi idanunsa cikin na maamah din.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 65

Wani abu ne yaso ya tsaye mata a rai,tunzura takeso tayi amma kuma tana gayawa kanta ba yanzu ba......idan ma basuci na yau ba ai na gobe yana nan,muddin kuma zasu ci gaba da taka qafarsu cikin gidan yau ko gobe nasara tana nan tare da ita.

"Yaushe Muhammad ya daina ci?" Ta yiwa musaddiq tambayar sai kuma ta maida dubanta ga fuskar fu'ad din a mamakance,saidai kuma sanda suka hada idanu dashi sai komai daya faru a wancan ranar ya dawo mata a take,amsar tambayarta ta fita kamar budewar shafukan littafi.

Wani abu taji me nauyi wanda sam baiyi kama da kunya ko nadama ba,tabbas a baya din don ba cikin daidanta take ba.....ba yaran bane a gabanta ballantana abinda ya shafesu da har zata lura da meye ya damesu da wanda bai damesu ba.....amma tabbas sai yanzu ta tuna,tun daga ranar yake bar mata kwanonta gaba daya yadda ta zuba.

"To amma bai kamata ace bakuci komai ba koda lemo ne" Ta sake fadi tana jan jug din gabanta tare da qoqarin raba kofunan ta zuba musun kada ya zamana komai da komai ma tayi asararsa a yau din.

Idonsa still a kanta,ya miqa hannu ya jawo gorar ruwan daya tabbatar a kulle take ya soma budeta,qarar budewar ya sanya ta daga kanta zuwa gareshi tana dubansa

"Ruwa kuma muhammadu?,ga lemo dai" Ta fada tana tura masa wanda ta zuba

"Maamah dare ya soma yi.....idan kuma dare ya fara bana iya cin komai...." Dubansa ta sakeyi kadan sai kuma ta dauke kanta tana qirqiro murmushi

"Kowa time table zai bani na abinda yakeso yaci kullum har sati guda koma sati biyu.....masu girki na musamman zan ajiye muku.....burina naga kun kusanta dani......na maida tsohuwar alaqar dake a tsakaninmu" Ta qarasa maganar tana duban cikin idanunsu.

"Fu'ad" Ta sake kiran sunansa,ya daga fararen idanunsa da suka fara rusuna saboda gajiya da zama a wajen,sam baya jinsa comfortable sam sam

"Me yasa kabar musaddiq tare da farouq......duk da ba laifi bane.....amma kaman zaifi cancanta ya kasance tare dakai qarqashin naka kamfanin" Shuru ya biyo baya na second uku,sai ya maida idanunsa ya kulle yana jan boyayyen numfashi. Shikam yayi imanin ba zata canza ba,ya tabbatar abune me wahala da girman gaske da zai sauya mata hali farat daya. Wannan ya sanya kowanne taku ko motsi nata yake sanya masa ayar tambaya,wani lokaci idan tayi wani move din sai yaji gaba daya kanshi ya juye yana tambayar kansa anya da gaske maamah din itace uwa ta asali a garesu?.

"Kowanne bawa da abinda yafi shaawar yi yafi qwarewa a rayuwarsa......yadda abba ya ginemu shine kowa ya dauki zabinsa da ra'ayinsa a rayuwa muddin bai kaucewa hanya ba....inda kikaga farouq da musaddiq su suka zabi wannan sashen duk kuwa da cewa tare da farouq mukayi gwagwarmayar samar da abinda na gina din a yanzu.....ba wanda ya zaba masa ko ya tursashi gashinan maamah ki tambayeshi" Juyawa tayi tana duban musaddiq ranta duka a jagule,bata son kowa ya rabi fu'ad a duniya idan ba dan uwanshi ba,batason kowa yasan sirrin dukiyarsa idan zaiyuwu sai ita daya,wannan tunanin ya sanya ta yanke shawarar sanya ido me tsananin a alaqar fu'ad din da amna......don ba zata taba yarda amina ta dauki d'iyarta ta qwaquma masa ba su qarasa nadeshi.

"Shikenan,Allah ya taimaka" Ta fadi tana sauke numfashi bawai don ta haqura a zuciyarta ba. Kawai tana ganin tunda komai yana kan turba bai kamata ta bata lokacinta tana dogon zance dasu ba,lokaci kadan take jira ta soma bada umarnin wanda zai shiga ko ya fita daga rayuwarsu.

"To yaya sunan surukar tamu musaddiq?....koda wasa baka taba attempting kawota ta gaida mamarka ba?" Ta yiwa musaddiq tambayar tana dubansa da murmushi,cike da zaquwa da son jin kalar matan da suke shirin kawowa rayuwarsu. Wani babbab abu da yake cikin tsarin abubuwan da takeso ta yiwa garambawul idan damar da take tsimayi ta samu,tanason surukanta su zama qarqashin ikonta fiye da yadda hajja ke juya nata mulkin a gidan.

Murmushi kadan ya saki,karon farko da yaji 'yar kunyarta ta sauko masa

"Minal bata iya zuwa ko ina,daga makaranta sai gida.....zata zo wataran in sha Allah". Ba haka takeson ji ba,don haka ta gyara zamanta tana sake sakin fuskarta

"Aah wataran yaushe kenan?,ina buqatar ganinta mu tattauna ka shaida mata mamarta nason ganinta......" Ta fadi din don da gaske tanason ganin wace ita?. Zuwan nata kuma a nan ne zata samu amsoshin tambayoyib data tabbatar ba zata samesu daga bakin musaddiq ba.

"In sha Allah" Ya fadi a taqaice yana auna yadda abun zai kasance.

"Kai kuma fa?" Ta waiwaya tana duban fu'ad daya tattara hankalinsa duka saman wayarsa tamkar ma baya jin abinda suke fadi. Gajiyayyun idanunsa dinnan ya daga ya kalleta,sai kuma ya maida dubansa ga musaddiq. Kan musaddiq din a qasa yana satar kallon fu'ad din ta qasan idanunsa,boyayyan murmushi nason qwace masa.

"Me maamah?" Ya tambayeta da sautin muryarsa da tayi laushi sosai.

"Wa ka daukomin a matsayin suruka?" Ta sake maimaita tambayar tata.

"Babu fa maamah...." Musaddiq ya fadi muryarsa na nuna murmushin da ya boye.

Debe kallonta kacokam tayi ta maida kan musaddiq tanason sake samun tabbacin hakan

"Kamar yaya kenan?" Satar kallon fu'ad yayi sannan ya dubi maamah,yayi qasa sosai da muryarsa,duk da yasan dole ya jishi don yana da wannan baiwar ta kaifin ji

"Ba wata budurwa.....tsoronsa ma suke......ba wadda take iya tararsa maamah tace tana sonshi"

"Very good" Ta fada qasan zuciyarta. Tsananin farincikin da taji ya bayyana har saman fuskarta,tadan danne tana hada rai

"Garin yaya?.....har yanzu halinka dinnan bai canza ba?" Ta watsa masa tambayar . Karon farko kenan da magana kwatankwacin wannan ta taba hadasu,don haka ya rasa ma da abinda zai bata amsa illa cewa da yayi

"Ba yanzu ba....lokaci baiyi ba.....in fact ma da sauran lokaci"

"Lokacin lokaci na ne,yana kuma tafe" Ta bawa kanta da kanta amsa a zuciyarta,amma a fili sai tace

"Allah ya nuna mana lokacin".

Duka hirar ba wani armashi gareta ba,amna haka suka sadaukar da lokacin har zuwa sanda ta basu izinin tafiya sukayi mata sallama suna ficewa.

Suna tafe ne kawai suna dosar gidan,daga shi har musaddiq din ba wanda yace da dan uwansa komai. Sai da sukazo mabanbantan qofofin sassansu,fu'ad din ya murza key yana bude qofarsa yace da musaddiq

"Shigo ciki ka zauna muyi magana" Ba tare daya dubeshi ba,ya gama budewa ya shige musaddiq din yabi bayanshi.

Zaune kawai tayi tana duban kwanukan abincinta da suka barta dashi,banda ruwan gorar dukkaninsu ba abinda suka taba ko qanqani. Lemon data zuba ta turawa musaddiq din ma tana saka ran zaiyi koda kurba daya ne amma baiyi din ba shima sai ya buge da shan ruwa. Ta fahimci yana bin sahu tare da matuqar kwaikwayo ga fu'ad,iya wannan ya isa ya bata amsar cewa,muddin ta samu fu'ad ta samu musaddiq......wanda kuma wannan din shine babban qalubalen da aikin data sake amanna ba qarami bane.

Furzar da iska tayi me zafi daga bakin ta,kusan komai data tsara ya wargaje babu shi,dan abinda ta amfana dashi daga zuwan nasu bai taka Kara ya karya ba.

Akwai damuwa sosai a ranta da take da buqatar abokin tattaunawa,don haka ta sauka daga dining area din zuwa ainihin falon ta dauki wayarta ta lalubo hajja.

"Musaddiq" Ya kira sunanshi kai tsaye sanda yake zaune saman wata qawatacciyar kujera da irinta qwaya daya ce tal cikin falon.

"Na'am" Ya amsa masa. Shuru kaman bazaiyi magana ba,sai kuma ya zauna sosai yana goye hannuwansa a qirji

"Inaso ka zama me takatsantsan sosai......inaso kuma ka zama me kula.....bazan hanaka zuwa gidanmu ba duk sanda kake da muradin hakan......amma kayi aiki da hankalinka da kyau......yanzun kai ba yaro bane.....ba wannan musaddiq din da ko yaushe sai hammansa yana gefansa bane don ya kula da abinda zai cutar dashi ko ya amfaneshi bane.....abubuwa sun yiwa hammansa yawa......kula da rayuwarsa yana hannunsa".

Wadannan kalaman na hamman su suka dinga juyawa cikin kanshi. Duk da bai fito qarara ya masa bayani a bayyane ba,amma kamar yadda yace din shi ba yaro bane yanzun,hakanan shi a karan kansa hankalinsa ya fara dauko masa wasu abubuwan a iya zuwansu gidan yau kawai.

Haka kawai ya kasa bacci a daren,har yanzu musaddiq baisan ainihin wace maamah din ba. Iya matakin da idanuwan basira da hankalin musaddiq kadai ya kaishi bai sadar dashi da ainihin wacece maamah ba........meye zata iya yi?,da wanda ba zatayi ba.......dole koda a fakaice ne ya sake nesantashi da tunkudeshi daga dukkan abinda yake ganin zai iya zama cikas a rayuwarsa.

Bugu biyu tak hajja ta dauka,hakan ya yiwa maamah dadi,sai ta miqe da wayar tana nufar bedroom dinta

"Na zaci kinyi bacci ai"

"Aah inadai shirin tashi.....labaran ne ya zaunar dani muna lissafin abinda kamfaninsa ya samu na shekara". Ido maamah tadan fiddo cike da mamaki

"Kamfaninsa fa?,yanzu lissafin shima tare kukeyi?". Dan qaramin murmushi me sauti hajja ta fidda tana aza hannunta saman kan budurwar dake kwance saman cinyarta tana amsa waya itama

"To meye a ciki?,nice uwarsa fa?,akwai wani abu da suka isa su boyemin?,koda cikin gidajensu akayi abu koda da darene da safe kuwa rana bata bullowa bansan komai ba......ke banda ma ina taka birki ma wasu abubuwan......ai hatta sunnar aure da matansu sai sanda na bada iznin a yita,kuma idan anyin sai an fada min"

"Innalillahi......ke hajja?" Maamah ta furta cikin tsananin mamaki

"Ke?.....zauna kina wasa da lamarin yaran yanzu,kina sake musu hanya sai linzaminsu ya koma hannun matansu,keda wahalar raino da daukan ciki amma wata ita keda d'an,kin zama 'yar kallo,sai abinda tace a tsakuro a sammiki.....tun daga kan yahaya na fara daukan izina.....ban kuma zauna ba har yau har magajin gobe" .

Duka mamaki ya gama kashe maamah,amma kuma bayanan hajja din sai suka gamsar da ita,ta kuma yarda cewa gaskiya ta fadi,gashi yanzun ita tana fafutukar karbar 'ya'yanta daga hannun wata ma tun basuyi aure ba?.

"Yanzun ya ake ciki?,komai ya tafi dai dai ko?" Ajiyar zuciya maamah ta saki tana maida hankalinta ga hajjan

"Hajja ba abinda sukaci fa?.....duk wahalar nan kin ganni da kayana suka barni....."

"Karki gaggawa,idan ba yau akwai gobe,idan ba gobe akwai wani satin"

"Haka nake gayawa kaina......kana iya target din abu amma shekara goma gaba kake hangowa.....zamu zuba dasu in sha Allah......wannan karon banga abinda ya isa ya hanani ko ya dakatar da burina ba" Ta fadi har qasan zuciyarta tana jin confidence akan wannan.

"Sirrin samun nasararmu dama itace jajircewa naci da kafiya". Hajjan ta qara mata qwarin gwiwa.

Sun tattauna sosai har na kusan mintuna talatin kafin su yanke kiran. Hajjan ta sauke wayar wani murmushi na fita daga fuskarta,tadan tsuke bakin ta lissafinta yana tafiya da nisa sosai.

"Mommy ga adeel zaku gaisa" Budurwar ta fadi tana daga kanta daga saman cinyarta hadi da miqa mata wayar. Sai data kalleta sannan ta amsa wayar ta sanya a kunnenta.

Ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar nashi,ba jimawa sukayi sallama ta miqawa yarinyar wayar tana kallonta. Kallon hajja kawai a garesu yana da fassarori,don haka tayi masa sallama ta katse wayar ta ajiyeta a gefe tana kallon hajjan

"Momy lafiya?" Numfashi ta ajiye tana dubanta duba na kai tsaye

"Ina sake gaya miki......nayi miki tanadi,kada ki kuskura ki zurfafa a soyayya da kowa....don kowa a cikin rayuwarki temporary ne......akwai target dina.....kuma bazanyi missing target dina ba tabbas" Tayi maganar da sautin da zai gaya maka tayi maganar ne da gasken gaske daga zuciyarta,ta kuma yi maganar tana kafe autartata da idanu don ta sake jaddada mata girman maganar.



*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 66

Itama duban momyn nata take yi,ta sani tabbas momy din nata tana matuqar ji da ita.....kaman yadda ta sani taci buri sosai a kanta. Duk da hakan tana da buqatar qarin haske a maganarta,don haka ta motsa kadan

"Momy.....wanne irin buri ne?,ta yaya zan iya sallamar dukkan kuma wadanda muke tare dasu yanzu?"

"Bance ki sallamesu yanzu ba,tukunna dai.....amma dai abune da kika sani cewa.....ke din ba kalar qananun maza bace....ban haifeki don wani me jaririn arziqi a hannunsa ya aureki ba.....plan dina kuma idan lokaci yayi zakiji....don ku yaran yanzu kwata kwata bakusan me ake nufi da sirri ba".

*****Ta jima zaune gefan gadonta tana juya wayarta a hannu. Mikail takeson kira,ta kuma shirya haduwarsu kaman yadda ta tsara zata kammala da babinsa ta kuma rufeshi kwata kwata cikin shafukanta kamar yadda ta binne maza masu yawan gaske. To amma haka kawai duk sanda tayi attempting na kiran nashi sai taji kaman kada ta kira din.

Wani sashe na zuciyarta na bata qwarin gwiwar ta kira

"Ya cancanci ya fuskanci komai......ya kuma cancanci kowanne irin hukunci,jin kunyar mara kunya asara ce!" Ta sake jin wani sauti daga can qasan zuciyarta yana rada mata maganar har zuwa kunnuwanta.

Danna kiran tayi,ta kuma tattara dukka nutsuwarta akan wayar tana sauraren yadda Kiran ke tafiya kai tsaye zuwa layin mika'il din.

A kasalance yake shiryawa,kasancewar daren jiya ya shawu. Duk da ya tsagaita shan ma,bai wani sha yadda yakeso ba,saboda ya sani safiyar yau din litinin tana cikin ranaku masu muhimmanci da zai gana kai tsaye da CEO. Mutum na farko kaf rayuwarshi dake masa wani irin kwarjini,kwarjinin daya tabbatar yana da alaqa da kamewarsa......da yadda fara'a ko murmushi sukayi nesa da fuska dama rayuwarsa gaba daya.

Ya jima yana so ya shiga rayuwarsa fiye da matsayinsa,amma kuma ya gaza samun wannan fuskar. Mutum ne da idan ya zauna aiki kawai,baya daukan wata magana da ba cikin aiki take ba,kamar yadda baya daukan wasa ko kuma wargi.

Yadda dukkan ma'aikatan dake aiki qarqashin kamfanin suke da iyakoki......haka nan dukkan wata magana da zaiyi dakai akwai iya adadin lokacin da yake baka.

Qarar wayarsa ta ja hankalinsa sanda take saka links na rigarsa,sai ya dakata cak daga abinda yakeyi din cikin tsananin mamaki yana kallon wayar.

"What a wonderful day" Ya fada qasa qasa yana daukan wayar ya zauna gefan kujera. Wani mamakin yana sake kasheshi da idanunsa suka tabbatar masa eh itace take kiransa

"Yau kuma da kanta?,da wanne irin sa'a na tashi?" Ya yiwa kansa tambayar yana daga kiran ba tare daya tsawaita dogon tunani ba.

Kamar kowanne lokaci tayi masa sallama wadda shikam ba kasafai yake iya tunawa da ita ba. Sai yadan daburce kadan kafin ya amsa sallamar ya dora da fadin

"Good morning queen....nayi kira nayi kira har na gaji anqi a dagamin waya.... Kwatsam sai gashi na tsinci wani abu da ban taba kawowa zai faru ba".

Murmushi ta saki kadan wanda ko kusa da gefen zuciyarta bai kai ba,yayin da shi kuma kunnuwansa yaji kaman zasu narke da fitar sautin sassanyan murmushin nata. Kowanne tsiga na jikinsa sai ta shiga tashi

"Ka sani ko yanayin alaqa da dangantakarmu ne suka dauko hanyar sauyawa?"

"Da gaske!" Ya fada da wani irin murna daya kasa boyuwa yana fidda idanunsa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login