Showing 150001 words to 153000 words out of 209775 words
b'ara ko kaji kukanshi.
"Kaman akwai wani abu ko?" Ta jefa tambayar gareshi don batason fitowa kai tsaye ta Qureshi da tambayoyinta
"Ba komai anni" Ya fada cikin bata tabbaci,don yayi imani ya nuna mata akwai damuwar,to yinin yau gaba daya haka zasu barta cikin rashin sukuni.
Kai ta gyada ba don ta yarda ba,sai don tasan koma meye idan ya dace ta sanin shine mutum na farko da zai fara gaya mata
"Ubangiji ya kauda dukkan abunqi,Allah yayi jagora"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu anni,na gode" Daga haka ya juya yana fita. Har cikin ransa yakeji irin wannan addu'o'in nata,duk kuwa da cewa bawai shi daya takewa adduar ba kowannensu ne,amma yakanji a ransa kamar tasa ta dabance.
Bai shiga mota daga parking lot na gidan ba,sai yace su fiddo motocin su sameshi waje. Ya soma takawa a nutse suna jerawa shida farouq suna tattaunawa kadan kadan har suka fito a gidan.
Sanda suka doshi gidan nasu yayi tsammanin farouq zai dakata daga yi masa rakiya amma sai yaga yaci gaba da binsa har suka isa bakin gate. Sun gaisa da malam saidu cikin girmamawa sannan suka kutsa kai ciki,guards dinsa guda biyu dake biye dashi suka dakata suna jiran fitowarsa.
Tunda ta wayi gari ta kasa tabuka komai,tana kwance kawai a daki tana kwancewa da saqawa bayan doguwar wayar da sukayi da hajja harira. Anya kuwa nasarar da take sanya ran samunta zata cimmata?,zata ma iya haqurin kwana ukun da bokan ya deba mata kuwa ba tare data koma ta sanar dashi komai ba?.
Maida tunaninta tayi tana sarrafa shawarar da hajja hariran ta bata. Bata jin cewa shawarar zatayi aiki har ta lanqwaso mata me babban suna yadda takeso?.....anya bazai zama doguwar hanya me wahala ba?.
"Waye ne?" Tayi tambayar cikin izza sanda taji an nace da knocking mata qofar bedroom
"Nice hajiya.....yallabai ne yazo" Me aikin ta furta a qasqance
"Yallabai?,fu'ad kenan?" Ta tambaya a mamakance tana duba lokaci
"Eh shine" Ta sake amsawa a ladabce. Cike da mamaki ta kalli agogo. Wannan ba shine lokacin da suma saba shigowa gareta ba,me ya kawoshi yau da safe?,ko dukka cikin dabaru da salon son kauce mata ne?.
"Ina zuwa" Ta amsa mata sannan ta fara yunqurin saukowa daga saman gadon.
Tun daga nesa ta zuba idanunta a kansu,hira suke qasa qasa da wani irin kusanci da emotion da zaka tsammaci su din tagwaye ne da ska rayu qarqashin mahaifa guda daya. Bata ga wani banbanci ba ko kadan tsakanin danta muhammad jadda mamallakin kamfanin haqa da sarrafa diamond ba.....da kuma farouq hamza kibiya me kamfanin saida tsabar abinci da taki ba!.
Meye ribar suna da yayi?,meye amfanin salon banbancin kasuwanci tsakaninsu muddin a idanu zaka dinga hangar yanayin sukunin rayuwa iri daya tsakaninsu?. Kamata yayi ace ana hangen tazara tsakaninsu,kwatankwacin tazarar dake tsakanin bawa da uban gidansa.
Wani irin abu yayi mata tsaye a wuya,amma dole ta saita yanayin fuskarta sanda ta isa gabansu
"Wato farouq kayi wuyar gani,har gwara sadiq ya fika kirki anfi ganinka" Dukkaninsu ba wanda zancanta ya kwantawa,saidai kawai sun bita da irin yanayin da tazo musu dashi. Wannan faran faran sa sabuwar maraba da iyalan Alhaji hamza kibiya sabuwa a idanunsu da basu taba ganinta ba.....koda kuwa sanda ta dawo ta iske iyalinta cikin kyakkyawan rayuwa qarqashin jagorancinsu da tallafawar rayuwarsu.
"Wanne irin aiki ne ya riqeku jiyan kaida dan uwanka kuka saka halartar kira na?" Tayi masa tambayar daketa cin ranta,don har xuwa lokacin bata gamsu wai aiki ne ya riqeshi ba
Yana murza yatsun hannunsa idanunsa samansu,zuciyarsa na wani irin motsa cikin yanayi maras dadi. Koda yaushe maganarta babu komai ciki sai zallar son kanta a ciki......ba wani sauti alama ko yanayi na kulawa ko nuna damuwa......ba wannan shaquwar da maganadisu dake tsakanin uwa da danta da har zata iya karantar yanayin damuwa walwala ko farinciki da yake ciki,abinda dukka ta rasasu anni kuma ta haye kansu ta zauna sosai.
"Yanayi ne na aiki da zai iya rutsawa dakai ako wanne yanayi ko lokaci" Ya amsa mata a taqaice don bawa kansa kariya .
"Yau kuma fa?" Ta sake fadi tana tsareshi da dukka idanunta
"In sha Allah" Kawai ya fada shima nan a taqaice.
Duka duka zaman bai wuce na mintuna goma zuwa sha biyar ba suka wuce. Mintuna goman da suke da matuqar tsada da daraja a wajensa......don ita din itace.....yana jin ya wajaba ko yaya ya bata wadannan mintunan don tserewa tuhumar ubangiji.
Fadin ma yanayin daya kwana a cikinsa a wannan ranar dare har ya zuwa safiya bata baki ne. Duk sanda ya waiwaya ya sake duba wayarsa sai ya dinga jin abun kamar mafarki......kaman baccin daya kwanta shi yakeyi,kaman har yanzu idan ya farka zai samu komai ba gaske bane.
Daga sallar magariba har ishai saida safe ya hada da asuba ya ramasu. Gaba daya ya wani firgice ya fita hayyacinsa a tsakanin. Ba abinda yake iya tunawa sai wanene Muhammed jadda da kuma irin hukuncin da zai iya dauka a kansa.
Duk yadda yaso ma ya yiwa kansa hasashen ta inda zai fara kare kansa a gaban mutumin da a fagen aikinsa baida maraba da zakin daya fito farauta sai yaga sam zantukan daya tsara ko kadan basu hau kan saiti ba,basu kuma dace da hankali ba. Tsananin tsoron da firgicin ya sanyashi kashe wayoyinsa gaba daya,saishi kadai cikin dakin tamkar tsohon mahaukaci.
Ba abinda kunnuwansa ke gaya masa sai sautin sallamar talauci cikin rayuwarsa,an debi kudin da ya tabbatar baida abun biya koda kuwa zai saida komai daya mallaka shi da danginsa su koma yawo tsirara.
Taku biyu yayi don shiga toilet ya rage gudawar da yake fama da ita tun faruwar abun idanunsa suka fada kan dan kunnen.
Gabansa yayi wani mummunar faduwa sanda kwanyarsa ta haska masa wani abu lokaci guda tamkar haskawar walqiya cikin duhun dare.
Tsugunnawa yayi ya dauki dan kunnen.....sai yanzu ma ta dawo kwanyarsa,sai yanzu tunaninsa ya soma haska masa wani abu
"Fateema?" Ta maimaita ainihin sunan da shine nasa STAMP din data bashi.
Komawa yayi ya zauna saman kujerar dake daura da qofar bandakin yanason tuna yininsu na jiyan a tare.
Yayi dukkan wani flash back daga qwaqwalwarsa zuwa zuciyarsa da kuma idanunsa,ba wani motsi nata guda daya daya bashi alamun rashin gaskiya a tattare da ita
"To amma me yasa na farka na nemeta na rasa?" Ya jefawa kansa tambayar data sanyashi miqewa ba shiri,ya jawo wayarsa da baiyi shirin kunnuwa ba ya kunnata,cikin ransa yana jin gamsuwar tabbas ita ta aikata ko kuma tana da hannu wajen afkuwar komai.
Sanda wayar ta daidaita sai ya fara yunqurin kiranta,saidai a duk sanda zai kirata din sai computer ta datse kiran ba tare da an masa bayanin komai daga danganci network ne babu a area din da take?,ko kuma wayarce dungurun gum a kashe?.
Ci gaba yayi da gwada kiran babu qaqqautawa,har sai daya sare,energy dinsa yayi qasa,ya tabbatar bazai cimmata a waya ba.
"Sai kayi tattaki ka sameta a inda take" Wannan shawarar ta sakashi zabura ya miqe,ya zura takalman qafarsa a gaggauce,saidai yana daukan key din motarsa komai ya tsaya masa cak
"A ina take?,a ina kuma zaka sameta din?" Zuciyarsa ta jefa masa tambayar data kusa tsaida numfashinsa
"Na shiga uku" Ya fada yana jin dukka jikinsa yana rawa
"Bansanta ba,bansan komai a kanta ba" Ya fadawa kansa da kansa idanunsa suna tara hawayen da babu makawa sai da suka yiwa kansu qofa
"Garin ya akayi haka?" Ya sake tuhumar kansa da kansa,abinda ya sanyashi sulalewa ya zauna a wajen.
Yafi qarfin awa biyu zaune ya kasa hasalawa kansa komai,kafin daga baya wata zuciyar ta bashi wata guntuwar shawarar data dan bashi nutsuwa kadan,har ya iya miqewa ya gyara rigar jikinsa ya maida hularsa ya lalubi qofar fita.
Dukkan wani muhalli da yasan sun taba haduwa,cin abinci,shan ice cream,shopping da sauransu ba wanda baije ba. Saidai duk inda yaje din dogon bayani ne maras fa'ida ko kuma alfanu,domin ba wanda ya ganeta. Abinda bai sani ba shine......ita din tamkar tarwada take a cikin ruwa......tana da matuqar santsi da idan taje waje zai wahala ka sake samunta a nan... Muddin taje waje dakai sau daya ta kansile wajen kwata kwata cikin jadawalin rayuwarta,ba guri bane da take mu'amalantarsa ba a koda yaushe ballanta fuskarta ta zama sanniya a wajen mutanen dake yawan xiyartar wajen ko kuma ma'aikatansu ba.
Tun yana zagayawa da qarfin gwiwarsa har ya sare. Zuwa sannan yanajin zai haukace ne idan bai gayawa kowa halin da yake ciki ba,don haka yana isa Bristol baiko koma dakinsa ba ya kira mato a waya.
Tazarar minti ashirin kacal ya iso,ya shigo dakin yana cewa
"Kai matsala ne dakai,wani lokacin sai ayita faman kiranka baka dagawa,tun jiya nake danna maka kira kaqi dagawa......gobe ne za'a zauna cacar nan fa......"
"Shut up mato!" Ya dakawa mato din tsawa,don maganarsa a sannan daidai take da yana buga masa abu me qara a kunne.
"Lafiya uban gidana?,me kuma ya faru?"
"Mato na hadu da 'yar damfara......na hadu da gagarumar barauniyar data yasheni tas......bama ni ta yasheba tukunna......ta taba dukiyar kamfanin jadda ne!".
Zaro idanu mato din yayi waje yana janye jikinsa baya da sauri kaman yaga wani abun tsoro tattare da mika'il din
"Anya yau bakasha barasar da kanka baya dauka ba?,kasan maganganun da kakeyi?,barauniya fa kace,kuma macace?,sannan data tashi dukiyar Muhammed jadda ta kwashe?" Ya qarasa maganar kaman zaiyi ruku'u. Ba kuma ruku'u din zaiyi ba,kawai yayi hakanne don ya samu damar ganin fuskar mika'il dake zaune sosai,yanason kuma samun tabbacin maganar haka take ko kuma akasinta.
"Duk yadda kaji ka sake kuma fada hakanne" Ya fada a galabaice yana tsananta fatan samun mafita daga wajen mato.
Ga mamakinsa sai yaga mato ya juya yana neman hanyar fita daga dakin. Da wani irin hanzari mikail ya miqe ya damqo rigarsa yayi qarfin halin jawoshi baya sannan yasha gabansa
"Ina zakaje kuma?" Kicin kicin yayi da fuska
"Ka dauko bala'in da yafi qarfinka ai me gida,ni kuma bani da wani gatan da zan iya tareshi,kaga gwara na yiwa kaina qiyamulallaili nasan nayi". Sakinsa mikail yayi har yana taga taga kaman zai fadi. Cikin fusata da fushi yake duban mato,yayi taku biyu a gabansa sannan ya tsaya yana sake kallonsa
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 78
"Kai butulu......na dade da sanin alaqar bariki bata da riba.....kuma bata wanyewa lafiya qalau.....amma inaso ka sani.....ni mikail baka isa ka gwadamin wannan halin ba saboda yadda kaci a jikina,komai ka zama ta silata ne.....to ga hanya nan......kana iya tafiya......amma ka sani,wallahi.....wallahi duk abinda zan shiga zan bada sunanka da tabbacin tare mukayi komai".
Ji mato din yayi kaman ya debo qarfe ya jibga masa saman kanshi,sai ya koma ya sulale ya zauna
"Ya zakayimin haka oga?,kasan tun safe naga qishin qishin abun?,ya baza jaridu da jafafen yada labarai?,amma ban taba tunanin kaine a ciki dumu dumu ba?"
"Mune dai a ciki,kuma zanyi maka haka muddin kaima kayimin hakan". Ya bashi amsa kai tsaye yana duban tsakiyar idonsa.
Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke yana yin collapse. Nadama da dana sanin taba sanin mikail a rayuwarshi tana sauko masa. Shikam ina zai iya tarar case da Muhammed jadda?,wanne ganganci ne ma zaiyi saken da koda sunansa zai shiga list na sahun wadanda ake tuhuma.
Shuru yaci gaba da wanzuwa a dakin tamkar dukkaninsu ba xasu sake magana ba kafin mato ya magantu
"Ita yarinyar wacece ita?,zaifi kyau kabi sawayenta ka bincikota ka damqawa jadda ita a sauqaqe su tuhumeta". Wani banzan kallo ya watsawa mato
"Inda nasan ita din wace da ta yaya ma zan batawa kaina lokaci ina neman shawarar butulu irinka?......tun haduwata da yarinyar na karanci tasha banban da sauran yammata dama mata gaba daya.....tun daga yanayin kyau siffa da kuma jan ajinta......bata sake shallake tunani ba sai a yau dana karade dukkan guraren da muka saba haduwa ko na saba ganinta amma na kasa zaqulota,......ta shafe dukkan wani footprint nata,bani da sauran hanyar da zan iya lalubota".
Shuru mato yayi abun yana tsimashi shima. Duk iya yawan duniyarsa bai taba cin karo da abun mamaki irin wannan ba.......duk budewar idanunsa da kuma son duniyarsa baiga gangancin da zai sanyashi tunkarar fada ko jayayya da mutum irin muhammad jadda ba.....hakan daidai yake da saida rai.....daidai yake kuma da Rungumar mayunwacin zaki. Amma irin wadannan maquden kudaden kuma ace diya mace ce ta diba?.
"Me afkuwa ta afku yallabai.......yanzu lokaci ya qure ya kuma matse da zaka tsaya nemanta da bayyanar da gaskiyarka.....don koda ka samota dinma ka gabatar musu da ita to ba shakka dole saika rasa aikinka.....na tabbatar zasu sallameka ne". Wannan maganar ta mato ta sanya gumi tsatstsafowa mika'il. Ya koma baya yana zama sosai tare da kamo habar rigarsa yana sharce gumin goshinsa.
"Don ubanka mafita nace ka bani bawai ka dinga haskomin makomata ba" Ya fadi da mugun tsaron ci gaba da jin sautin xai rasa gurbin aiki da kamfanin jadda diamond rashi na har abada,bayan a nasa mafarkin yana hangoshi ne wataran a kujerar CEO din ma gaba daya yana juya nasa kamfanin diamond din.
"Mafita kam na samota......amma sai idan ka amince.......zaka juya hankalin kowa kayi wasa dashi.......ka kuma binne batun kwashe kudin asusu ba tare da kowa ya fahimta ba".
Kaman an watsa masa ruwan sanyi haka yaji rahama tana sauka a zuciyarsa,baisan sanda ya kama hannun mato ya riqe qam qam ba abinda bai taba yi ba tsakaninsu
"Dama za'a samu irin wannan hanyar na kasa yarda da ita mato?,maza gayamin......gayamin don Allah".
Hannunsa ya zame yana mamakin yadda yau masifa da bala'i suka sanya ubangidan nasa zama maqasqanci a gabansa.
"Caca......a caca ne kawai zaka ciyo maquden kudaden da zaka iya cike babban gurbin da zai sauke fushin me jadda daga kaso dari zuwa ashirin". Ido ya zubawa mato alamun me gama Fahimtarsa ba.
"Nasan baka gane ba ko?,me gida......kana da nasibin da muddin ka zauna teburin caca saidai ka kwashe badai a kwashe ka ba,tunda kake baka taba zama teburin caca an cinye ka ba tsahon shekarun daka dauka,saidai ma ka tashi da gwagwabar ribar dake lunka arziqinka.......wannan zaman da za'ayi a gobe babban zama ne......akwai manyan gidadawan masu kudin da basu gama wayewa a sabgarba.....basu kaika qwarewa ba,sun sanya mugayen kudade masu nauyi cikin cacar saboda romon bakan shigowarka cikinta da nayi musu da yawan kudade masu nauyin gaske.......kudin da kowanne zai zuba ba qarami bane me gida......kuma ina da tabbacin kaine zakayi nasarar wawashesu......ka zuba kudade sosai ka saki jiki don ka sarqafo dukkan abinda zasu zuba.....bana jinka.....nasan da qwarewarka.....na kuma yarda dakai".
"Nima na yarda da kaina" Ya fadi kai tsaye cikin confidence da kuma yarda da cewa lallai ba shakka waraka tazo. Rungume mato yayi yana jin tsananin farinciki kafin ya sakeshi yana cewa.
"Muddin muka gama da wannan,na rantse da sarki Allah saina nemo yarinyar nan......saina nuna mata cewa ita din ba komai bace cikin duniyar bariki,sai na bar mata tarihi,saina sanyata tayi danasanin zuwanta duniya!!".
Tunda gari ya waye yake kwance kawai lamo,ita bame bacci ba hakanan ita ba idanunta biyu ba. Su biyu ne a dakin tun bayan wucewar nadra da haneefa makaranta,tana daga parlor huda na cikin uwar dakin qudundune a bargo da sunan bata da lafiya ba zata samu daman zuwa makaranta.
Ta shirya hakanne don tana sanya ran sabreen din zata fita ta barta a dakin kamar jiya,tasha hirar soyayya da