Showing 135001 words to 138000 words out of 209775 words
zasu hadun yana dab da cika.
Wajen SMS ya shiga,ya rubuta gajeran saqo ya tura mata,idanunsa suna kan wayar yana fatan samun amsa daga wajenta,duk da kuwa yasan abune me wahalan gaske.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 68
Tunda suka dawo daga makarantar hankalinta yana kan wayar,dama kawai take nema da sabreen din zata fita ta samu ta fidda wayar. Ta tabbatar yayi kiranta har ya gaji,yanzun haka qila yana cike ne da kewarta.
Sunyi hira me tsaho dashi jiya cikin toilet,wanda ta dinga mamakin yadda yasan wasu abubuwan a kansu,saidai amsar daya bata ta cire dukkan wani zargi nasa daga ranta
"Indai zakiyi mamakin yadda akayi nasan rayuwarki huda ashe son da nake miki ma baikai nan ba......kina wasa da kalar soyayyar da nakeyi miki ko?" Idanunta ta lumshe har cikin zuciyarta tana jin a yau din bayan yaa sabreen din ta sake samun wani barin zuciyar wanda ya damu da rayuwarta ya kuma damu da damuwarta. Har yake iya sanin wacece ita a rayuwa ba tare data sani ba saboda tsananin son da yake mata
"Inason na daukeki daga gidanku huda.....na killaceki daga rayuwar da kike ciki......na hana kunnuwa da idanuwanki ji ko ganin duk wani mummunar kalma duk don saboda yaa sabreen....". Ta riga tayi amanna yasan komai kawai a kansu har akan sabreen din,don haka sai ta lumshe ido zuciyarta tana karyewa
"Ba rayuwar da tafi rayuwar aure daraja da martaba a wajen mace.....qila idan yaa sabreen dinki taga zakiyi aure itama tayi" Ya fada cikin salon karya harshe dason nuna yadda zuciya ta karye,saidai a gefe guda yana sone kawai ya cusa wani kakkaifan abu a zuciyarta.
"Banji dadin shaidar dana ji daga bakunan mutane a kanta ba.....don nima a yanzun ina daukarta kamar yaya take a gareni".
"Hameed....." Ta katseshi cikin rauni.
"Muyi kowacce magana dakai amma banda ta yaa sabreen,don zuciyata me rauni ce a kanta,ita din komai namu ce....."
"I know huda.....i know,but inason na killaceki huda na daukaka darajarki.....inason ta silarki ya sabreen dinki ta zauna waje daya,ta samu martaba irinta....." Sai kuma yayi shuru bai qarasa ba,shurun da itama hudan da zuciyarta ke mata zugi ta zabi yinsa.
"Zamuyi waya anjima idan kin samu lokaci.....i so much love you....please take care" Ya fadi yana katse kiran ya barta da yawa a hannu.
Zare wayar tayi daga kunnenta jikinta yana yin sanyi. Kenan kowa ma yana dora tuhuma akan yaa sabreen?,kowa ma yana da zargi a kanta?. Idan dai har Hameed da yake baqo a unguwar dama rayuwarsu gaba daya zai iya samun wani abu a kanta to ya kenan sauran jama'a suke kallonta?.
Shin gaskiya Hameed yake fadi?,tayi aurenta kawai ko hankalin yaa sabreen dinta zai dawo daidai?. To shin me yasa yaa sabreen din ba zata zauna kaman kowacce mace ba?. Me yasa bayan ta samu kudaden da sun isa ta riqe musu rayuwa?.....me yasa ba zata haqura ba?....me yasa?,meye dalilinta?,idan a baya tana da hujja tana da dalili yanzun meye dalilinta?.
Wadannan tarin tambayoyin su suka dinga yi mata kai kawo,sannu a hankali sai taji kaman tana da ja akan sabreen din,tana kuma qalubalantarta duk da harshe ko aikinta bai nuna ba....... Amma tun daga sannan can qasan zuciyarta wutar hakan tana ruruwa sannu a hankali.
Kamar wadda ke ciwon jiki haka ta dinga aiwatar da komai. Duk da tana da daukan lokaci wajen wanka da shirinta amma a yau din sai abun ya sake ninkuwa.
Ta gyare gashinta ta kuma dameshi cikin band madaidaici,ta gama shafa cream dinta na musamman dake qarawa fatarta glowing cikin kowanne yanayi,amma kuma saita kasa ci gaba da yin komai.
Bata taba ayyukan da suka tsaye mata a rai takejin ta takura ba irin aikin Mikhail dana mashkur da cikin qarshen satin nan zata yishi. Batasan dalili ba......amma ta alaqanta hakan da canzawar salon aikin. Ma'ana kowannensu zata kasance dashi cikin dakin hotel daga awa daya har zuwa sanda aikin zai kammala. Shin tana da tabbacin kubuta daga hannun miyagun kurayen da dama dama suke nema irin wannan?,mutanen da suke kallon diya mace cikin idanuwansu da wani irin duba kwatankwacin duban da mayunwacin zaki kewa nama a yayin da sukayi arangama?.
Tana zaunen amma tana lura da yawan shige da ficen da huda keyi tsakanin falon zuwa dakinsu. Kaman zatayi mata magana sai kuma ta basar,don tana da wani irin dabi'a nabin komai da idanu har sai sanda ta samu cikakken hujja ko makama a kanshi.
Qarar yar siririyar wayar da tasan kiranta na dabanne shine ya dauki hankalinta. Wanda ta zata din shine kuwa,Jib ne,sai ta daga kiran tana rage volume na kiran.
"Hello jib?" Ta furta daidai sanda huda ke ficewa a dakin. Samun kanta tayi da jan qaramin tsaki can qasan ranta. Jib?....ko waye kuma da wannan sunan?,zai iya yiwuwa wannan shirin da takeyi ma fita zatayi,kuma wajensa zata je,idan mace da namiji suka kebanta a waje daya kuma me zai biyo baya?,idan taje gurinsa me zasu aikata?..... Tambayar data yiwa kanta kenan ta qarshe data sanya bugun zuciyarta qaruwa,saita samu kanta tana saurin dakatar da kanta daga wannan tunanin tana furta
"A'uxubillah" Wani sashen na zuciyarta kuma yana gaya mata
"Yaa sabreen ce fa?" Idanunta ta lumshe tana son sake jaddadawa kanta eh.....ya sabreen ce,amma wani sashen kuma yana qoqarin maidata baya.
"Yadda kika tsara abun bazai yiwu ba sister.....dole ya kasance kuna tare nan da awa guda......mafi kyau kuma ku isa wajen tare koda xaku shiga ta qofa daban dabanne......don na bincika a yanzun kamar suna dakin meeting da boss dinsu..... Meeting din kuma zai zamana sun tattauna muhimman abubuwa.....na lissafa zasu soma lissafi na kudaden da company ke dashi a qasa......zasuyi musayar documents da bayanai,zaa tashi ba tare da sun kammala ba don bayanan yana da yawa,kuma owner na kamfanin jadda baya saba lokaci......wadannan bayanan da zasu kasance tare dashi ina da buqatar wasu abubuwa a ciki da zasu sauqaqamin kutsa kai cikin account din muyi aikinmu da wurwuri mu gama.......inaso kuma aikin na gamashi ne a daidai lokacin da masu kula da komai nasu suka tafi hutun fitowa daga meeting din....idan zaiyiwu ki samu kaiwa office dinsa,akwai wani ajiyayyen code cikin files na office din da zaki ciromin,kin fahimta?"
Dukkanin bayanan sa ta fahimta ta kuma gamsu,to amma kimarta fa?. Bata saba yin magana ta dawo ta warware ta ba
"Kada kiyi tunanin komai.....wannan ce rana ta qarshe tsakaninki dashi.....kuma wadannan sune awannin qarshe da aishatu keda chance na tsallakewa siradinta".
"Ba damuwa" Ta bawa jib amsa a taqaice tana yanke kiran.
Wayar ta aje a gabanta kawai tana kallonta tare da tunanin da yadda zata sake requesting wa mika'il din su kasance tare tun yanzu?. Kaman ana jira ta yiwa kanta tambayar saiga shigowar saqonsa.
Tana duba saqon tana jin sanyi da yadda komai yazo mata a sauqaqe. Duk da hakan ya faranta mata amma saita ajiye wayar bayan ta gama dubawa,ta miqe kawai ta isa wardrobe dinta tana laluben suturar da zata dace da jikinta da kuma yanayin.
Shurun nata da rashin samun amsarta ya qara masa yawan rashin sukuni. Ya dinga duba wayarsa duk bayan wucewar wasu mintuna,har sai daya kasa jurewa ya sake tafa massage dij har sau biyu ya tura mata a jere.
Saqon ya shigo mata sanda take daura agogon hannunta ne,tun taga sunan tasan shine,bata bi takai ba sai data gama daurawar,ya qara barima a kunnenta tayi Rolling mayafin Turkish dress din,ta kuma jawo kimono din kayan da suke zuwa tare da shirt me dogon hannu da skirt din ta aza saman kayan sannan ta dauki wayar ta bude tana maida masa amsa
"What's the adress?.....zan taddaka har inda kake don farincikinka".
Sai data maimaita karanta saqon kusan sau hudu,tana mamakin yau itace da kanta zata turawa wani d'a namiji saqo da yayi kama da wannan?. Ji tayi kaman ba zata iya turawar ba,ta aje wayar saman madubi tana furzar da iska daga bakinta
"No way out" Taji zuciyarta na gaya mata,dole ta tura muddin tanason cika mission din. Tana so ta rabu ne da mikail.....ba kuma zata iya barinsa salin alin ya wuce hakanan ba,sai ta miqa hannunta ta sake bude wayar,ta danna send sannan ta maida wayar ta ajiye.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 69
Bayan maimaita karanta saqon da yayi,har sai data kaishi ga murza idanun nasa don ya tabbatar daidai ya gani ko kuwa akasin hakan?.
Jikinsa har rawa yake wajen maida mata reply,har bai lura da yadda Muhammed jadda ya zuba masa idanu ba yana karantar yanayinsa.
"Mr mika'il" Ya kirayi sunansa da husky voice dinsan nan dake ratsa zukata su kuma maida hankalin mutum zuwa jikinsa.
"Yes.....yes sir" Ya fada adan daburce yana qoqarin tattara masa nutsuwarsa bayan ya tabbatar da isar saqon zuwa wayarta. Bawai address kawai ba,harda code da zata samu zarafin bude office dinsa ta shiga ta zauna tayi tsimayensa.
Murmushine ya subuce mata da ganin yadda ya bata komai in details. Ba wani shakka ko kokwanto. Wato shi namijin bariki akan mace susutacce ne?.....sannan fiye da rabin maza ta fuskanci ba kasafai suke iya mallakar kansu ba idan batu ake na mace. Wani zaka hangi fuskarsa cike da kamala amma muddin aka raba masa mace a nan dukka rauninsa yake bayyana. Bai tsoro shakka ko kwanton ita din fa baquwa ce cikin rayuwarsa gaba daya?.
"Good job mika'il" Ta fadi murya can qasa tana forwarding ma JIB komai.
"Kana tare damu?" Muhammad jadda ya sake jefa masa tambayar yana dage girarsa dukka biyun
"Yes.....yes sir" Ya fadi yana sakar masa murmushi don ya amintar dashi. Idanu yadan tsareshi dashi kaman meson karantar wani abu,wanda duka duka cikin mintuna biyar ya dauke idanun yana cewa
"Bismillah" Tare da maida idon nasa saman farar takardar gabansa da daya daga cikin ma'aikatan ya gabatar.
Sai da yayi namijin qoqarin daidaita nutsuwarsa sannan ya fara gabatar masa da komai daki daki.
Sai data buda qaramar handbag dinta ta tabbatar ta sanya komai a ciki sannan ta fiddo dubu biyu a ciki ta miqawa huda dake tsaye a gabanta
"Masu kamfanin pure water zasu kawo ruwa....ki basu wannan idan sun kawo.....naso saikun wuce islamiyya kafin na fita.....amma it's urgent.....kiyi qoqari ku fita da wuri kada kuyi latti"
"A dawo lafiya" Ta fadi bayan ta karbi kudin. Qasan ranta fal farinciki,a yau din zatayi hira da hameed yadda ranta keso,don zata saitawa su nadra hanya zuwa islamiyya ne ita kuma ta baje kolin soyayyarta yadda ranta yakeso.
Gaban haneefa ta qarasa tana sakin murmushi,itama haneefa din murmushi ta saki,hannunta ta dora saman sumarta data cirewa dankwali. A kullum fuskar haneefa ba wanda take tuna mata dashi sai umminsu. Akwai shaquwa da sabo me tsanani tsakaninsu.......amma duk da haka saida mutuwa tayi aikinta ta raba tsakaninsu.
"Ayimin addua auta....zan kawo miki abun dadi"
"A dawo lafiya yaa sabreen........amma yau kam sabuwan teddy nakeso ki sayamin"
"Ke kuwa ki rasa abinda zaki zaba sai Teddy?" Nadra ta fada tana qyalqyala dariya
"To madam tsokana.....ba ruwanki" Sabreen tayi hanzarin katse nadra data wuce daki tana ci gaba da dariyar tsokana din hadi da yiwa sabreen a dawo lafiya.
Tana takawa don fita daga layinsu ta isa bakin titi amma tunanin qannen nata ne a ranta. Batason ko kadan yadda kullum sai ta fita ta barsu,wani lokaci su fita tare saidai su rufe dakin,harma wasu lokutan su rigata dawowa. A yanzun huda tafi tsaye mata a rai,tunda har ta cika shekara sha biyar ta shiga ta sha shida tana da buqatar sanya idanunta a kanta,don mataki ne da komai daga nan yake farawa daga rayuwar yarinya. Duk da inda ace ita din me gata ce,ita dinma tana buqatar kulawa ne tare da qarasa rainon tarbiyyarta.
Ko kusa ko alama bata lura dashi ba,don tayi nisa a tunaninta,sai muryarsa taji daga gefanta.
"Um uhmmm......sai ina kuma haka?" A nutse ta waiwaya tare da sake rage yanayin tafiyar tata tana kallonshi.
Tsaf yake kallonta,ya turo hula gaban goshinsa yana mata wani irin kallo. Idanunta ta dauke don bata buqatar yanayin kallon da yake binta dashi. Ta sani haushinta yakeji qwarai,tun waccar ranar data hanashi kudi. Wannan duka ba damuwarta bane,don idan da sabo ta saba,sai ta watsar da wannan batun kamar kullum tace dashi
"Barka da warhaka kawu.....an yini lafiya?"
"Ras na wuni.....ko kin dauka zan mutu ne saboda kin hanani kudinki?,to kisha kuruminki 'yar nan......cikin satinnan da yardar me duka arziqi zai fashemin......sunana zai fantsama a duniyar masu arziqi......daga sama'ila zan koma alhaji ismai'il sha maka Allahu". A mamakance take kallonsa,tadai sani bashi da wata sana'a data wuce caca,kuma muddin ka jishi yana lissafin maquden kudade irin wannan to wata caca za'a buga kuma yake sanya ran zai cinye.
"Allah ya bada sa'a.....amma dai kawu.....caca"
"Akul naji bakinki.....dani dake ai dan juma ne da dan jummai... Ke har gwara ni duk tsiya".
Kanta ta dauke tana hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya,bata sake tanka masa ba sai ta fara takawa tana barin wajen. Har tayi taku hudu qwarara ya qwala mata kira da ainihin sunanta
"Aminatu" Dakatawa tayi don ba zata iya ci gaba da tafiya ba,ba'a canzawa tuwo suna,duk duniya kawu sama'ila ubanta ne.
"Ke wato baki jin ko dar idan an miki gugar zana ko?,to miqomin wani abu nan,ki rubuta shi a lissafi duka cikin satin nan zan biyaki" Ya fada yana miqa mata hannu tamkar ya bata ajiya. Idanu ta xuba masa,sai kuma ta sanya hannu tana sauke jakarta daga kafada,ta zuge ta fidda dubu dubu guda hudu ta miqa masa.
Karba yayi yana juyasu alamun a raine suke a wajensa,sai ya yatsina fuska
"Ki rasa abinda zaki ban sai wannan?,kai Allah ka dawo mana da arziqinmu za'a sha kallo wallahi......" Daga haka ya juya yana cusasu a aljihu tare da barin gurin bai kuma sake bi takan inda zataje din ba.
Kasa ci gaba da tafiya tayi har sai daya bacewa ganinta,ta kada kai ta na yin gaba kamar kullum zuciyar nan cike da nazarin rayuwa . Tun daga rasuwar mahaifinsu har ta mahaifiyarsu bai taba miqo komai yace musu gashi ba wai don su rayu.....amma ita ba zata iya qirga ko lissafa adadin sau nawa ya karba daga hannunta ba,kuma a raine,ba godi bare na gode.
Ya riga ya bata shaidan da zata nuna na cewa shi take nema,wannan ya sanya bata samu matsalar shiga kamfanin ba tun daga gate din farko gate na biyu,ta zarce zuwa main entrance,ta ratsa reception da sauran guraben da kamfanin yake dashi kai tsaye kuma ta isa ga office din.
Tayi amfani da code din ya kuma bude mata successful. Ta tura qofan a hankali kamar me tsoron shiga qaramin murmushi na sauka saman fuskarta
"Quda a wajen kwadayi akan mutu" Ta furta qasa qasa tana sanya qafafunta cikin office din. Har ta fara takawa sai kuma ta tsaya cak tana wurga idanunta sassa sassa na qawataccen office din da aka narka kudi akayi masa wani irin lafiyayyen tsari me daukan hankali. Tabbas tasan babu yadda za'ayi guri irin wannan ya rasa CCTV camera,indai kuma hakanne ta yaya zata iya gudanar da komai ba tare data samu wata matsala ba?.
Dan wani abu cikin kunnenta ta matsa,muryar JIB ta bayyana,sai ta danja da baya kadan ta raba qafa tsakanin office din da veranda din da jerin gwanon office din yake don bataso ta fito gaba daya ko ta shiga gaba daya don kada camera din ya samu damar nunata
"Ni dakai duka bamuyi tunanin CCTV ba jib?".
"Ya salam" Ya fadi