Showing 30001 words to 33000 words out of 209775 words
da kai kafin ka baro gida ai ya kamata ka tsaya kaji dalilin kiran da nake maka babu qaqqautawa,bayan ka fito ciwon suhail ya tashi,a yanxu haka muna asibiti,amma babu ko sisi a hannuna,baka barmin komai ba,already kuma account dina yana buqatar naje banki na gyara bare nayi hidimata da kudina yadda na saba_.
Wani abu me tauri taji ya tsaye mata a wuya,ta zura hannu a jakarta ta ciro wayarta,tanason taga nawa ita ya kashe mata?,nawa ya saka mata alhali ko sisi matarsa bata amfana dashi ba?.
Naira dubu dari ta tarar. Wani matsiyacin tsaki ta saki,cikin dukkan arziqinsa ya rasa da meye zaiyi mata kyauta sai naira dubu dari?. Bata tsaya batawa kanta lokaci ba ta sauka ta koma mobile app dinsa da bai jima da fita a kai ba.
Daga password har username dinsa fes cikin kanta,tamkar hadaka ko gamayya sukayi dashi wajen creating dinsu a sanda zai bude manhajar. Cikin qasa da second goma komai ya bude,tarin miliyoyin kudaden dake kwance cikin account din nasa suka bayyanarwa idanunta,sai ta koms ta jingina da kujerar motar tana kallonsu,kamar ma bata tsoro ko shakkar dawowarsa.
Numfashi take fitarwa d'ai d'ai qirijinta na sake quntata. Tarin zallar rashin imanin maza yana sake tabbatar da kansa a zuciyarta.
"Yana da wannan kudin ya fita yabar matarsa babu ko sisi?,yana da irin wadannan kudaden yabar yaronsa cikin halin ciwo?,yana da wannan kudin ya gaza siya masa abun hawan da idan lalura irin wannan ta taso baya kusa zata kaisu zuwa ga asibiti cikin gaggawa?.
Tsanar MAZA tsanar SOYAYYA da kuma tsanar AURE suka sake linkuwa cikin ranta. Irin wannan shaidojin na gani da ido ta din saidai ta bada labarinsu. Shi din ma ba komai bane a cikin maza......bata kuma san namiji na nawa bane shi din da a yau xai shiga makarantarta.......a yau zata sanyashi ya koyi darasi kaman sauran,saidai nasa darasin yazo ne a gaggauce saboda gamawa da babinsa da tayi,da kuma dadewa da tayi da sanin shi din wayeshi?.
Beneficiaries dinsa ta duba,cikin sa'a tun batayi nisa ba taci karo da sunan da yayi daidai da sunan matar
*ameena mu'azzam*.
Kai tsaye ta saka amount din da yayi mata ta kuma karkatasu zuwa ga account din.
Daidai lokacin data hangi tahowarsa,ta daga hannunta ta zare wania abu daga jikin qofar,sannan ta maida hankalinta kan wayar kamar ba me wayar ne yake dosota ba.
Hankali kwance ta koma ta goge alert massage din da kamfanin sadarwa suka aiko,ta kuma koma zuwa ga email a gaggauce ta goge nashi tayi minimize ta maida wayar mazauninta tana karanta sunan banking da yake amfani dashi,sannan ta zaro tata wayar tana duba ma'ajiyar lambobi dake cikin wayar.
Sunayen dake ajjiye cikin wayar ta fara bi,cak ta tsaya saman wani suna da yayi daidai da sunan banking nasa,ta danna malatsi na tura saqonni,ta kuma aika da saqon a gajarce
"Done" Ta jefa wayar a jaka daidai sanda ya iso bakin window din suna sake yunqurin buda motar.
Ja daya bakaniken ya yiwa murfin ya bude,sai ya waiwaya yana dubansa cikin mamaki,wanda shima cikin manakin ya iso
"Oga ina tunanin kaine baka jawo ta da kyau ba"
"Kai amma nayi mamakin faruwar hakan" Ya matsa yana kama hannun motar ya matsashi har sau uku. Mamaki yadan sake kamashi,amma kuma kiransa da tayi d nuryarta me laushi ya dauke hankalinsa daga nan.
"Okay na gode to" Ya fadiwa bakaniken yana cirar wani abu a aljihunsa adan gaggauce saboda kiran nata.
Bude mata qofar yayi,ta sako qafafunta ta fito tana gyara zaman abayar jikinta. Cikin nuna kulawa yake fadin
"Da alama motar bata gaji dake ba,kamar yadda me motar shima bai gaji da kallin wannan kyakkyawar surar ba......don Allah ayimin lamuni a bani exact gurin da zan sameki.......da gaske nake,banzo da wasa ba,ni din ba irin sauran samarin yanxu bane......da niyyar aure nazo" Ya qarasa maganar yana lanqwashe murya.
A nutse ta watsa masa idanunta da suke sake narkar dashi. Batajin daga rana irin ta yau ma zai sake samun damar tsaiwa da ita a muhalli daya irin yanzun. Wannan itace dama ta qarshe kuma lokaci na qarshe a wajensa tsakaninsa da ita.
"Ba damuwa......ka samu number dina ai.....komai zaizo da sauqi?"
"Are you sure?" Ya tambayeta yana kallonta cikin kokwanto. Saboda shi kansa yasan samunta din abune me wahala.....ta subuce masa wancan karon.....hakanan haka ya qaraci karakainarsa da nemanta amma ko me kama da ita babu ballantana ita karan kanta din. Kai kawai ta gyada masa sannan ta juya ta soma takawa tana barin wajen gami da cewa
"Godiya nake......fatan alkhairi"
"Nike da godiya kyakkyawa" Ya fada murya a lanqwashe yana binta da kallo da zazzafan so,yana jin kamar ya saceta ya gudu da ita ya mallakawa kansa ita.
A nutse take taka kowanne step da zai sadata da ainihin makeken store din. Murmushi ne kwance saman fuskarta ita daya,duk da bata juya ba amma ta tabbatar yana tsaye ne yana kallonta,tana hasaso yadda fuskarsa zata koma a sanda ya laluba asusun bankinsa ya taras da barnar datayi masa,tana hasaso yadda wannan tattausan kallon zai koma zazzafan kallo da kuma zurfin tunanin TA YAYA AKAYI HAKA YA FARU?.
Yadda take daukan hankula da idanuwan wasu daga cikin jama'an dake sabgoginsu a waje da cikin shagon bai dameta ba,don ba wani baqon abu bane a wajen ta. Itadai ta sani,akwai dubbai zuwa miliyoyin mata da suka zartata a kyau.....don bata tana daukan kanta ta sanya a sahu ko jerin kyawawan mata ba,amma batasan mene a tattare da ita me matuqar jan hankali irin haka ba.
K'annenta sune gaba da komai da kuma kowa. Buqatunsu kuma sune gaba da nata buqatun. Don haka duk list na abinda suke buqata ta fara dubawa. Tana tsinta tana jefawa a cart.
Ta kwashi a qalla minti ashirin tana nasu siyayyan sannan ta fara nata. Siyayyarta bame sauqi bane,tana da tsari tana zabi,ba komai yake burgeta ba kaman yadda a rayuwarta na zahiri ba kowa ke burgeta ba,komai nata yana da tsari,don haka ta bata lokaci sosai akan nata kayan,ta saki jiki kuma kamar ba zata bar shagon ba.
Sai data gama tsaf sannan ta gangara bangaren kayan maqulashe. A duk sanda ta samu kudi irin haka bata rabo da siya musu kayan taba ka lashe,harda ajiye wasu ma cikin daki. A duniya idan akwai abinda taqi jini shine taji sunce BABU ko BANI DASHI ADDA....kalma ce da bata yarda a yanzun ta shiga tsari da babin rayuwarsu sam sam.
Sashe ne dake danqare da chocolate kala kala da kuma biscuits. Masu tsananin tsada da kuma masu matsakaicin kudi. Da ido ta dinga bisu daya bayan daya,wani lokaci can baya daya shude bata isa ta sanyasu cikin idanunta ba,wani lokaci can baya daya shude sunfi qarfin tabawar hannuwanta ballantana akai ga batun sanyasu a bakinta.....wani lokaci can baya daya shude saidai ta hangesu......hangema daga nesa.....wannan ya sanya tayi alqawari......ta kuma ci alwashin muddin tana raye ba zasufi qarfin rayuwar 'yan uwanta ba.
Tana cikin dubawar ta hangi favourite chocolate dinta,ta kasa jurewa sai data daukota ta bareta ta jefata a baki,daidai sanda taji anyi kiranta da daya daga cikin sunayenta data mallakawa wani.....sunayen da suke zama tamkar tag ne ga kowanne namiji daya taba shiga rayuwarta.
"Basma" Iya sunan daya kira tun kafin ta waiwaya ya gaya mata waye. Duk wanda ta bawa sunanta wannan sunan nashi ne shi daya,wannan sunan shita mallakawa shi kadai.....wannan kuma ya zame mata stamp kuma alama ta kowanne mutum daya taba shiga DUNIYArta.
Murmushi ta saki tun kafin ta juya tayi tozali da wanda yayi kiran.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 19
________________________
*_Katafaren sansanin UMMUMAHNOOR LUXURY,TA SHIRYA TSAF DON SAMA MUKU TSALA TSALAN KAYAN ADO DA SUTURA NA KECE RAINI IRIN NA 'YA'YA MATA,IRINSU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes
Numbers
08034469681
08135142610
Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries
___________________________
Iya sunan daya kirata dashi ya bayyana mata kanshi tun kafin takai ga waiwayowa.
Sanda ta juyo din yana tsaye daga bayanta,ya kafeta da wadannan jarababbun idanun nasa data sanshi dasu tun a lokacin,idanuwan data tsana fiye da kowanne ido a duniya,idanuwan da kuma tafi tsana bayan baqin mugun halayen dake rataye da jiki da zuciyarsa.
"Malam nasiru....kana lafiya?" Ta fada calmly tana dauko wani box na chocolate din ta jefa cikin kwando. Takowa ya soma yi yana sake kusantota,har yanzun dai bai dauke idanunsa a kanta ba.
Sake daga kai tayi ta kalleshi,sai ta fara tura kwandonta gaba
"Kana mamaki ne?.....kayi tunanin bazan iya shaida ka ba ko?" Ta tambayeshi da murmushi a saman wannan miskilar fuskar da zaiyi wahala kaga fitar murmushin daga samanta.
"Wannan basman bata manta fuskar mutanen da suka taba shigowa cikin rayuwarta.......hakanan wannan basman bata manta fuskar mutane irinku......hope kana lafiya ko?" Ta sake tambayarsa tana tafiya a nutse,tana kuma ci gaba da zaban abinda yayi mata tana jefawa a kwandon.
Tarin mamaki ne ya lullube masa zuciya ainun......tsahon lokutan yayi tunanin duk ranar da sukayi haduwa ta farko da ita zata razana......zata kuma tsorata,idan da yiwuwar ma ta nemi guduwa duka zatayin duba da girman laifin data aikata masa.
"Tana da wayo......tana kuma da hadari......da alama akwai abinda ta taka" Maganar abokinsa kenan ta dawo cikin kansa bayan wani zama da sukayi dashi,wannan ya sanyashi Maida hankalinsa jikinsa sosai,ya kuma tattaro bacin rannan da ta dasawa zuciyarsa wanda har yanxu a cikin bala'i da masifar data sakashi yake
"Idan kika mantani ai baki cika 'yar halali ba......ai dama idan kere na yawo zabo na yawo dole wataran zasu hadu" Ya farta cikin fushi.
"Yar halak?" Ta furta a sarari,sai ta dakata da abinda takeyi ta waiwayo ta zuba masa idanu
"Akwai bashi ne tsakaninmu da kake nema na har kalmar kere da zabo zata gitta tsakaninmu?" Kansa ya daure tamau,zallar raina masa hankali da tayi yaga ta fito muraran. Ji yayi bashi da sauran abinda ya rage illa ya fiddo mata makamansa.
"Kina iya cewa komai,amma kafin sannan shawara daya zan baki.......ki maido min dukka kudade na da kika samfe daga account dina sawunki a likkafa.....ko kuma hukuma ta matsaki ki fito dasu" Idanunta ta watsa masa tana sakin murmushi
"Kasan a inda kudadenka suke?,za kuma ka iya zuwa karba din idan na gaya maka?" A tunzure cikin fushi da yadda takeson maida maganar wata mara alfanu ko muhimmanci ya kalleta
"Duk duniya akwai wanda ya isa ya hanani karbar haqqina?,akwai wanda ya isa ya cimin haqqina ban karba ba?"
"Kwantar da hankalinka mana...." Tace dashi still tana murmushi,saita dafe kwandonta ta soma takawa tana nufar ficewa daga gidan kuma tana fadin
"Gidan marayun nan......a wannan ranar kowanne yaro ya rabauta da duk wani abu na buqata da bashi dashi,suttura kayan ado na 'yanmatan da kuke sakawa ana musu dauki d'ai d'ai cikin dare ana kai muku su gidajen shaqatawarku da hotels kamar yadda ka gayyaceni nima zuwa naka dakin hotel din......kana iya zuwa ka karbi komai dake hannunsu ka sanyashi a kasuwa ka maido kudinka......muddin kuma ba zaka iya hakan ba,to ina baka shawarar ka fita daga rayuwar SABREEN......ka kuma daina bibiyarta......idan bakaji ba kuma......zan sake sakaka fidda wasu kudaden masu ciwo da baka shirya fitarsu ba kamar dai wancan lokacin" Ta qare maganar tana kaiwa qarshen wajen ta karya kwana tana niyyar bacewa ganinsa.
Daya biyu uku yahada dukka yaga basuyi masa daidai ba. Wani sashe na zuciyarsa ya soma zugashi da
"Ta yaya kana tsaye qaramar yarinya me qarancin shekaru zata nemi raina maka hankali?".
Ya samu kansa da kansa da tuhumar kansa tare da ganin tsananin baike da wallensa. Wannan tunanin kadai ya qara masa qaimi,ya taka qafafunsa cikin azama da qwarin gwiwa ya soma rufa mata baya lokacin da takeji a ranta ta kammala siyan duk wani abu da suke da buqata ita da 'yan uwanta,wanann ya sanya ta nufi gurin biyan kudin kai tsaye
"Inda zan baka shawara......zaifi kyau ka koma ka tafi sabgaka...."
"Saboda ke kike nema na bani ke nemanki ba?,saboda nine mai laifi bake bace?" Hankali kwance ta maqale kafada tana sakin siririn murmushi
"A'aha.....ba don dukka wadannan dalilan bane suka sanya ni na baka wannan shawarar ba......na baka ita ne don gudun kada ALLURA TA TONO GARMA"
"Ni dake zanga wanda allurarsa zata tono garma......"
"Ba laifilaifi malam naseer....." Abinda tace dashi kenan tana ci gaba da tattaki a bayanta. Yau yanason ganin qarshen gudun ruwanta......yanason yasan ita din wace?......da waye take tare?,su waye suka dauki nauyinta?.
Waye ya turota?,maqarqashiya ce ko kuma hadin baki?.
Hakanan yaci gaba da rufa mata baya tamkar me tsaron lafiyarta ko wanda aka bashi aikin kula da ita. Har cikin zuciyarsa yakejin yau zai nuna mata shi waye,zai kuma tabbatar mata tayi mahaukacin gangancin kuskure data shiga hanyarsa.
Mutum biyu suka samu ana lissafa kayansu jikin qaramar na'urar dake da alhakin qididdige fitar kaya cikin katafaren shagon.
A hankali ta tsaya daga bayan matar wadda bata iya ganin ainihin fuskarta,saidai shigar atamfar chiganvy gold mix match da wani irin danyen lafiyayyen lace da aka yiwa qawataccen dinkin buba da zani ya fito da kamalarta da kuma cikar siffarta. Tsaye yake daga gefanta,matashin da duka duka shekarunsa ba zasu haura ashirin da takwas ba. Ya bata dukka hankalinsa yana sauraren maganar da takeyi dashi cikin muryarta dake bayyanar da tsantsar kamalarta da cikakkiyar nutsuwar ruhi data halitta. Yanayin yadda ya rusuna ya bata hankalinsa yana saurarenta kadai zai bayyana maka zallar ladabi da kuma ganin girmanta da yakeyi,akwai kuma tag idan ka lura sosai daga gaban aljihunsa dake bayyanar da cewa shi din ma'aikaci ne a wani guri na daban.
Mai matsakaicin tsaho ce,hakanan me jiki ce saidai ba qiba me yawa cancan ba,ta lullube saman kanta da 4D Vail me asalin kyau da aka zubawa duwatsu masu daraja akayi adon jiki dasu.
Sassanyan qamshinta ya dinga tasowa a hankali daga jikinta zuwa hancin sabreen dake tsaye daga bayanta tana kallon tulin kayan siyayyar da aketa jera mata cikin ledar dake dauke da tambarin store din.
Hannunta dake dauke da wasu kyawawan banguls masu sheqi ta miqawa ma'aikacin gurin tana cewa
"Bansan me yasa suke son mu'amala da wannan katin bankin ba,duk sun lalace da lamarin cashless" Murmushi ma'aikacin ya saki cikin tsananin girmamawa
"To ai hajiya yafi sauqin sha'ani ne" Kai ta gyada a hankali tana furta
"To Allah ya kyauta". A nutse ta maida dubanta ga saurayin,tun kafin tace wani abu ya sake matsowa a ladabce yana bata hankalinsa
"Ka kiramin wancan yawalen da kuma wancan acicin suzo mu wuce kafin rana ta sake dagawa"
"Okay to in sha Allah" Ya amsa mata yana zaro wayarsa daga gaban rigarsa,yayin da ta fara takawa cikin nutsuwa tana ficewa daga gurin hadi da gyara yafen mayafinta dake qoqarin zamewa.
Wucewar tata ya bawa sabreen damar matsowa gaba don a lissafa mata nata kayan
"Ji mana.......zaki dawomin da duk abinda kika san kin sace ko kuma saimun dangana da hukuma?" Hannayenta ta goye a qirjinta tana kallon qofa yadda mutane ki shige da ficensu hankali kwance. Yana da ban mamaki......saidai ita