Showing 159001 words to 162000 words out of 209775 words

Chapter 54 - DUNIYATA BOOK 1 By HUGUMA

ya zuba!,ya koma tsurar yadda ya shigo musu a wajen!.

Sowa ihu murna da tafi ya cika wajen,ainihin sunan kawu sama'ila na teburin ya soma dawowa bakunansu wato DA BANBANCI!.

Kowacce tsiga ta jikin mikail zubawa takeyi. Idanunsa sun kada sunyi jazur,jijiyoyin kansa sun fito rada rada. Sosai yakejin ya muzanta,ya toxarta. Ta yaya zai bari wani qaramin alhaki tsohon daya bashi shekaru masu tazara ya kafa tarihi a kansa?,tarihin da muddin ya bari ya tabbatu a haka.....to ko shakka babu ya xubar da kimarsa da kwarjininsa a idanun abokan cacarsa dake bashi wani irin girma. Karon farko a rayuwarsa da wani yayi nasara a kansa,shi kuwa ta yaya zai bari haka ta tabbata?.

"Ga wasu kudaden na zuba.....azo a sake zama!!" Ya furta da qarfi,sautin daya sanya wajen yin dif aka zuba masa ido.

Da sauri mato ya kalleshi,ya kuma ja hannunsa da qarfi yana dubansa qasa qasa

"Wanne kudi kuma ya rage maka indai ba motar da mukazo a ciki ba zaka saka?"

"Qyaleni mato.....bakajin habaicin da suke yada min?,dole na aje musu tarihi,dole sunan mikail suma yaci gaba da wanzuwa a kunnuwansu da bakunansu da wajen cacarsu".

"Wanne kudi ya rage maka?!"

"Ragowar abinda aka bari a asusun jadda" Ya fada yana jin zuciyarsa ta qeqashe,kuma tabbas wannan kudin xai dawo da sauran kudin da duka narke,duk kuwa da yasan mugun gangancin dake cikin aikata haka.

"Kada kayi haka!" Mato ya fadi a gigice.

"Anma yi" Ya amsa masa ba fargaba ko shayi saboda ya bawa kansa tabbacin shine keda nasara.

Wayarsa ya fidda yabi dukkan process yayi transfer kudin da suka rage zuwa account din wanda zai ajiye kudin,idan nasara tasa ce ta dawo masa,idan ta kubce kuma dukka kudi sun tabbata mallakar KAWU!.

Daidai lokacin da akayi alerting mutum biyu fitar kudin,sai fuad dake zaune yana bibiyar komai ya lumshe ido yana sauke siririyar ajiyar zuciya,daidai sannan kuma kira ya shigo masa. Ko daya duba sai yaga daga department din da aka kira ya daga yana cewa

"Just keep an eye on it,naga komai" Sai ya kife wayar yana maida dubansa ga allon system din yana qoqarin tracking account na wanda aka sanya kudin.

*_TURQASHI....QAQA QARA QAQA,BAZANCE KOMAI BA😂😂.....amma akwai ZAZZAFAR TURKA TURKA FA.....MUJE ZUWA_*

*HUGUMANKU CE*

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

Page 82

A wannan karon......daga shi har kawu samaila sai da aka basu hutun mintuna ashirin,don kowannensu yayi iya shirin da zai qara yi. Magoya baya kuma jingima kawun ya samu,wanda kusan dukkansu suna murna ne da nasarar daya samu,don sun tabbatar cewa koda basu maida dukkan abinda Milakil yaci nasu ba,to tabbas kawun zai maida musu wasu abubuwa kasancewar shi din nasu ne.

"Me gida......ka tsaya iya waccar asarar da kayi......kada kayi kuskuren sake yin wani ganganci......ka fini sanin waye muhammad jadda"

"Sosai kuwa mato.....amma jikina yana bani nasarata tana tare dani wannan karon......bazan bari nayita asara ba" Ya amsawa mato cikin yanayin da yake alamtawa mato cewa mikail din yayi nisan da bazaiji kira ba.

Cikar mintuna ashirin aka sake zama,zaman daya dauki sabon salo ya kuma dauki hankulan kowa dake wajen. Tsahon wasu mintuna ana fafatawa,inda daga qarshe komai yazo qarshe. Kawu samaila ya sake wawushe kudin,ya kuma bar mikail cikin wani irin yanayi tsakanin mutuwa da rayuwa.

Dukka kururuwar murna da muryoyin abokan kawu samaila dake tashi a wajen baya iya fayyace komai. Abu daya kwanyarsa ke iya fahimta gami da maimaita masa

"An qarasa cinye kudin jadda diamond resources,ba abinda yayi saura".

Kowanne sashe na jikinsa ya dauki rawa da wani irin kalar tashin hankali mara misali. Yana jin komai ne tamkar yana mafarki.....yana ganin kamar xai farka ko zai tashi,yana ganin kamar ba haka bane har sai daya damqi hannun mato

"Mato da gaske ne?,ko mafarki ne?"

"Da gaske ne maigida......ai na gaya maka dama". Taga taga mikail din yayi zai fadi mato ya taroshi,jama'an dake kusa suka kuma karanci hakan suka kawo masa dauki ta hanyar tallafe masa mikail din suka zaunar dashi suna masa sannu

"Kaima banda abinka oga ai kayi wauta.....hausawa sukace idan bakasan gari ba saurari daka......na tabbatar rashin sanin waye sama'ila ya sanyaka sakin jiki dashi kan teburin caca......amma ita dama yau gareka ne gobe ga dan uwanka,idan an sake wani zaman ta yiwu ka samu nasarar maido wani abun naka"

"A wajen wa?......lallai garba ka manta waye sama'ila ne" Dan uwansa da suka kawo daukin tare ya fadi yana murmushin aikin gama ya gama.

"Kaini gida mato.....mu fita daga nan" Mikhail ya fada kaman wanda ya hadu da ciwon makanta,don gaba daya sai yakejin wajen ya matse masa ainun,kai......kamar ma baya shaqar numfashi yadda ya kamata a wajen.

Tsoro fargaba da mutuwar jiki suka saukarwa mato sanda ya tayar da motar da yake tunanin ita daya ce Allah ya mantar da Mikhail bai sanyata tsaiwa takarar na ciyo ko a cinyeni ba wato caca. Kuka rurus mikail ya fashe dashi. Yana ji har a cikin zuciyarsa bashi da wani sauran abinda ya rage masa,to wai shin idan baiyi kuka ba me zaiyi?.

Yana hango kawai yadda zai qare sauran Rayuwarsa ne a gidan kaso......yana hango yadda me jadda zai qarasa murqusa Rayuwarsa bayan rasa dukkan wata dama daya fara jiyo qamshinta a baya. Ba shakka fateema ta cuceshi.......har a zuciyarsa yana jin inda zai iya ido hudu da ita a yanzu babu abinda zai hanashi hallakata.

Sun dan dauki lokaci da malam suna hira tana ta juya yadda zata gaya masa batun tallafin data kawowa dalibansa da rabon jarin da takeson yiwa duk wanda ya isa munzali a cikinsu. Cikin kudaden tanaso ta yiwa malam din alherin kudaden da zasu taba rayuwarshi sosai. Sosai mutumin yake burgeta........namiji na farko baya ga mahaifinta da taji dabi'u da halayensa sun mata,namiji na farko da takeji nagartarsa ya mata......kuma namiji na farko da idan ta zauna suna magana dashi takejin kamar wani sashe na mahaifinta ne ya dawo duniya.

Duba da yadda lokaci yake qara tafiya,ta tabbatar qanqanin lokaci ya rage ya fita don yin sallar magariba. Sai ta daure ta gyara zamanta.

"Magana nazo muyi malam,saidai bansan yadda zaka karbi abun ba" Ta fadi kanta sunkuye a qasa.

"To ina jinki mana aminatu.....lafiya dai ko?" Zamanta ta gyara tana jin nauyinsa da kuma kwarjininsa yana ratsata

"Eh lafiya malam......akwai tallafi ne da wata qungiya ta sa kai ta kawo don a rabawa makarantun tsangayu..... To banyi qasa a gwiwa ba na sanya sunan makarantarka a ciki,don nasan akwai dalibai da qarfinsu ya kawo kuma suke da buqatar sana'a......hakanan kaima malam na saka naka sunan a ciki......an kuma dace sun bada kaso me tsoka"

"Toooo.......ikon Allah" Ya fada a tsanake yana nazarin abun

"To sannu da qoqari,Allah ya saka da alkhairi......to sudai yara ba za'a hana raba musu jari ba......saidai komai zai zama bisa tsari don kada su saka a gaba su cinye.......kuma tallafar Rayuwa ne don bakasan ta sanadin jarin abinda Allah ya hukunta wani zai zama ba......amma zaki raba musu da kanki......hakanan zaki rubuta da kanki......batun sunana da kika saka ni na yafe....na gode miki da dukka qoqarinki a kaina.......amma basai kin bani komai ba".

Shuru gurin yayi,qasan ranta tana jin wani abu maras dadi. Har ga Allah malam uba ta daukeshi........tana masa kallo ne irin na d'a da uba......to amma kuma tasan halinsa,ba kasafai yake canza hukunci ko magana ba idan ya zartas

"Lokaci yana gabatowa,zan fita na shaida musu su zama cikin shiri.....wanda kuma yasan baida sana'a kar ya shigo ciki"

"Hakan ma yayi malam" Matar malam din ta amsa masa,sai ya dauki butarsa da rumasa'u ta cika masa da ruwa yana ficewa.

Yammaci lokaci ne da kowanne ma'aikaci yayi handing over aikinsa na ranar......ya kuma tattara ya nasa ya nasa yayi guda ko kuma guraren da mutum keda ra'ayin zuwa.

Company din yayi tsit.....don hatta da masu danyin late kafin subar office din a yau sun fice,ba kowa sai muhammad fuad......saddiq da musaddiq ke zaune saman sofa,jifa jifa yana daka kansa ya kalli muhammad fuad da yaketa aiki haiqan saman system tamkar a nan zasu kwana ko bashi da niyyar barin office din a yau.

A hankali ya zare idonsa daga system din ya maida saman agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa. Mikhail ya fado masa a rai,sai ya jijjiga kai a hankali ya maida dubansa ga musaddiq. Idanu yadan zuba masa kadan yana jin tausayinsa yana saukar masa. Ya tabbatar a gajiye yake,kuma bashi da burin daya wuce ya wuce gida,saidai kuma komawarsa gidan a yanzu babban hadari ne ga lafiyarsa dama rayuwarsa.

"Mu qarasa gidan malam muyi sallar magariba a can" Ya fada yana dan ture table din gabansa ya kuma miqe yana ware hannun rigar suit shirt dinsa daya nannade,sannna ya juya yana dauko suit din yana qoqarin maidawa.

Suna hanya kadan kadan yana jin saddiq da musaddiq din suna hira abinsu jifa jifa.....yayin da shi kuma ya tattara nasa hankalin kan wayarsa yana rage saqonnin da bai samu dubawa ba.

A zahirin gaskiya ya gaji,yana kuma buqatar hutawa ne daga gangar jikinsa har ma qwaqwalwarsa,to amma ya sani.....a cikin matsalolin dake cunkushe cikin kansa,muddin zai zauna na second biyar shuru tunanukane zasu addabeshi,wanda yayi imanin zasufi jigatashi fiye da gajiyar da yakeji yanzu haka a jikinsa.

Kamar kowanne lokaci malam din bai taba karbar komai a hannunta ya eabawa daliban da kanshi ba,yau ma ita da manyan dalibansa ya bawa dama suka tattauna,ta kuma rarraba kudin da zata raba musun sannan aka tsimayi sauran wadanda basu kusa suka dawo aka soma hawa layin karbar tallafin.

Har qananun cikinsu bata tsame ba,saidai kowanne tayi kudin girma girma,adadin na qananu daban,na manyan daban.

Ita da rumasa'u suka fito zuwa rumfar gaban gidan malam din,rumasa'u na riqe da jakar tana miqo mata,ita kuma tana miqa musu. Duk wanda ya karba sai ya balbaleta da adduar data dinga sanyawa tana jin saukar wani irin sanyi cikin ranta,wannan ya qara mata qwarin gwiwa taci gaba da binsu da kudin daya bayan daya.

Kaman yadda ya saba a kowanne lokaci ya sanya mota uku cikin motocin dame tsaron lafiyarsa tsaiwa su kuma jira fitowarsa daga ainihin bakin titin unguwar,motoci hudu harda tasa suka fara gangarawa zuwa ainihin layin gidan.

Suna shiga yana ci gaba da duban tsari da yanayi da banbancin unguwanni da al'umma ke rayuwa a ciki. Unguwannin da suke buqatar tsari me yawa da kuma tallafi don samun daidaiton rayuwa.

Kusan dukkan guard's dinsa har yanzu suna mamakin yadda yake zuwa unguwar lokaci lokaci. Ko tsoron lafiyarsa baya yi baya kuma duba girman matsayin da Allah ya bashi?. Saidai a nashi bangaren malam din tamkar wani jigo ne a rayuwarsa.......ya zame masa fitila me haska masa duhu.....domin shine mutumin daya shayar dashi ilimin addinin da a yanzu haka ya zamewa rayuwarsa haske da kuma garkuwa.

Silalowar motocin da kuma nishin isowarsu wajen yadan dauki hankalin da yawa daga cikin almajiran. Saidai da yake daliban malam auwalu daban suke da sauran almajirai ba wanda yayi wani motsi na hayaniya ko fita daga tsari,saidai idanu da suke bin motocin dashi wanda ke qoqarin gyara parking a muhallin da suke ganin zasu iya tsaiwa. Idan ka duba da kyau fuskokin manyan cikinsu murmushi ya sake wadata,domin sun sani mutum daya ne tak me irin wadannan motocin sak....dake zuwa wajen malam,wanda duk ranar da yazo kuwa kakar kowa ta yanke saqa,duk da cewa qalilan daga cikinsu ne suka samu nasarar shaida fuskarsa.

"Bari hamma na fita na duba ko yana ciki" Musaddiq ya furta yana duban fuad da ko sanda motar ta tsaya bai daga kanshi ba,hankalinsa still yana kan waya

"Okay" Ya fada a hankali kaman wanda bayason yayi magana.

A nutse ya bude motar ya fiddo qafarsa dake cikin rufaffen takalmin kamfanin Hermes. Ya qarasa fitowa daga motar yana gyara hannun rigarsa sannan ya fara takawa a nutse yana dosar rumafar malam din daya daga cikin guard yana biye dashi.

Daga shigowar motocin har tsaiwarsu a wajen bata wani basu muhimmancin da zasu dauke hankalinta daga aikin da take ba,don Allah Allah take ta kammala ta wuce gida saboda yadda tunanin huda yaketa mata yawo saman kai abinda bata taba tsintar kanta a ciki ba kenan.

"Hamma malam fa idan ba da gaske akayi ba bazai koma sabon gida da makarantar daka gina masa ba" Sadiq da idanunshi kekan almajiran ya fada yana leqo kansa first set din da fuad ke zaune.

A nutse ya zare lumsasssun idonsa akan wayar yana waiwayawa gefansa ya kuma aza idanunsa a muhallin da yake kyautata zaton a kanshi Sadiq yake magana. Saidai kuma duk da tarin almajiran daketa miqa hannu suna karbar wata takarda idanunsa basu sauka a ko ina ba sai a saman fuskarta.

"Yanzu banda abun malam.....ga gini can a wadace,ga makarantar zamani amma yace sai yayi shawara?,har yanzu kuma bai gama shawarar ba?" Sadiq ya sake fada yana dariya qasa qasa,dariyar da bata samu isuwa ga kunnuwan fu'ad ba duk kuwa da cewa yana wajen.

Sosai ya zuba ma fuskartata idanu bawai don tayi masa kyau ko kuma taja hankalinsa ba......aah.....sai don tuna a muhallin daya soma ganin fuskar duk da ba wani kyakkyawan kallo yayi mata ba.

"Office din mikail......a ranar da incident din zai faru" Sashe mafi saurin harbawa cikin kwanyarsa ya bashi amsa

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 83

"Exactly....." Ya furta har labbansa suna motsawa,yayin da wani qaqqarfan tunani ya darsu a ransa.

Bai dauke idanunsa daga sashen ba musamman ganin musaddiq ya doshi inda take kai tsaye......amma kuma kafin ya qarasa din ta juya tana takawa zuwa cikin gidan malam din,abinda ya sanya musaddiq da bai kula da fuskarta ba ya soma tambayar wanda yafi kowa girma a wajen kan ina malam?,kafin ma ya bashi amsa muryar malam din ta ruskeshi yana basu umarni su fara daura alwalar sallar magariba.

"She's a suspect" Ya fadi a hankali yana zare idanunsa daga kanta sanda ta kammala shigewa malam ya bayyana. A nutse ya waiwaya ga sadiq yana kallonsa.

"Kiramin jordan" Ya furta a nutse yana qoqarin bude side din da yake zaune. Baiyi wahalar komai ba ya janye dogon hannun rigarsa ya danna wani abu,cikin qasa da minti daya hotonsa tsaye jikin motar ya bayyana ta qaramin allon computer dake maqale a set din gaba fu'ad

"Ka fita ka cewa malam gani nan shigowa.....ka cewa jordan din ya shigo". Ya danyi mamaki kadan da hakan,amma bai damu ba ya amsa masa yana bude murfin motar sannan ya fice yana gayawa jordan saqon boss din nasu.

"come in" Yace ma qaqqarfan mutumin da yayi tsaye bakin motar cikin rusunawa.

Cikin jin nauyin hada mazauni daya da boss din nasa ya shigo. Sai fu'ad din ya bashi umarnin rufe motar. Yayi kaman yadda yace din yana maido dubansa ga fu'ad din yana satar kallonsa.

Duk yadda yakejin qarfi a ginannun tsokokin jikinsa a yanzu da yake zaune kusa da boss din nasa sai yaga ashe bai fishi da komai ba.

"Kayi noticing wata girl a cikin yaran can tana raba musu wani abu?" Yayi tambayar kanshi tsaye,don yasan mutum ne shi me tsananin kula da motsin kowa

"Yes sir" Ya gyada masa kai cikin qwarin gwiwa da confidence

"Good.......i want every single details of her.....but don't forget.....make it secretly"

"Done sir" Ya fadi a yanayinsa da muryarsa suna bawa fu'ad din tabbaci.

Tun daga fitarsa a motar ya soma aikinsa,tun tana daga cikin gidan malam din fitowarta da tafiyarta hankali kwance saboda tasan bata da wani issue da kowa a nan area

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login