Showing 93001 words to 96000 words out of 209775 words
girma qwarai,mamaki kuma ya lullubeshi har sai daya tsaya kawai yana duban yadda maamah din ta haqiqice.
".....bazan yarda ba a rabamin kan yarana,bayan a mahaifa guda suka kwanta......don wannan zalunci ne kawai,duk yadda zakayi ka nema komawa sashen da dan uwanka yake aiki,shima kuma zan masa magana kaji?" Sai ta qarashe kuma cikin kwantar da harshe saboda magana ta gaba da takeson yi.
"To" Kawai ya iya cewa da ita,ya sani basai an gaya masa ba,maamah din tayi nisan da batajin kira,hakanan dukkan wani bayani da zaice zaiyi mata yana zaman bata lokaci ne kawai a wajenta.
"Yanzu bayan kamfanin diamond ai ina sanya ran zuwa yanzu addu'ata ta cicciba Muhammad izuwa mallakar wasu boyayyun mafanunnukan ko?" Ta fada tana murmushi tare da tsare musaddiq da kallo.
Dubanta yayi sosai,yana ji har cikin zuciyarsa da gangar jikinsa bai gamsu xa yanayin tambayar tata ba,don haka girgiza mata kai kawai yayi
"Bansan komai a kanshi ba maamah tunda ba sashe daya muke dashi ba" Wani abu ne ya tsaya mata a wuya,amma sai tayi qarfin halin danneshi ta amsa masa da
"Haka ne......amma dai baka ce bakasan qarfi da nauyin kudaden da suke shigo masa ba ko?" Sake daga kai yayi yana dubanta zarginsa yana sake tabbata
"Bana ce ba maamah.....abune da ya shafi sirrinsa kuma ba a qarqashinsa nake aiki ba.....ni ina qarqashin farouq"
"Eh to.....maganar gaskiya sai yanzu na fahimci kimiyyar da ta sanya amina tayi kutin kutin din cusa danta wa Muhammed kai kuma ta rabaka dashi.....kana jininsa wanda bashi da na biyunsa a duniya amma bakasan komai nasa ba?.....wanda ni nayi imanin a yanzun inda zan zaunar da shi saddiqun nayi masa ire iren tambayoyin da nayi maka din yana da amsar kowacce fes?.....wannan itace hanya mafi sauqi da zata samu salwantar da fu'ad da dukka abinda ma ya mallaka". Idanunsa ya runtse yana jin zafin mummunan zaton da maamah din ke jifar 'yar tahalikar dashi.....matar data zame musu bango majingina,matar data zabi farincikinsu akan nata.....matar da silarta ne a yau suka zama dukkan abinda suka zama din.....suka kawo izuwa matakin da suke kai a yanzu......matar da banda ita da yanzu shi da muhammad din duka da take taqama dashi ba'asan a wacce shiyya nahiya ko yanayi suke ba.
"Maamah..." Ya fada yana bude idanunsa a kanta ba tare da ya shirya tsaida maganarta ba.
"Duk yadda kike tunanin anni fa ba haka take ba.....idan baki godewa anni ba bai cancanci ki jefeta da mugayen zato ba......kamfanin nan da rayukanki suke baci akai asalin diamond din da aka samu ba hamma bane kawai ya sameshi ba.....a lokacin suna tare da BB farouq......"
"Amma shi ya haqo shi kuma ya samu nasarar tsira dashi.......ka dauka bansan dukka wannan ba?" Tayi maganar tana tsareshi da idanunta da suka cika da bacin rai. Lallai sai sun nuna mata fifikon matar can akanta?,bayan bata da masaniya akan sanda ta dauki cikinsu bare kuma haihuwarsu?.
"Eh hakane.....amma shi BB farouq baida sha'awar harkar diamond noma yafi so shi yasa......"
".......shi yasa aka fidda haqqinsa aka bashi nasa kason......dukiya ta zama ta muhammad sh kadai......amma duk da haka basu qyaleshi yana amfana da abarsa shi kadai ba.....saboda nasa kason da nasa bangaren na haqar ma'adanai yafi noma albarka da kawo samu,shi yasa suka tattare shi suka kuma dora masa dukan lalurarsu suna zuqeshi sannu a hankali.....suka kuma nesantaka dashi.....suka haramta maka sanin komai daya shafeshi ta cusa danta" Ta qarashe maganar da wani irin ciwo da emotiona daga zuciyarta
"Maamah....." Ya kira sunanta yana son dakatar da ita. Baya qaunar ko kadan wadannan kalaman marasa dadin sauraro suna fita daga bakinta zuwa kawunan mutanen da suka yiwa rayuwarsu tsaiwar da babu wani mahaluki daya taba yinta
"Ni na zabi fannin noma da kayan abinci......basu suka sani ba....ba wanda ya bani shawara....."
"Musaddiq!.....ina fada kana fada duk akan mutanen can?,to waishin ko zaka koma cikin aminatu ta sake haifarka a matsayin danta bani mariya ba?". Maganar yaji tayi tsauri da yawa,kuma ya sani uwa uwa ce komai lalacewarta,hakanan ba'a canzawa tuwo suna,don haka ya miqe tsam,don dama a qagare yake da wannan zaman da baiga ma'anarsa ko alfanunsa ba. Ya dauka zasuyi hira ne irin ta d'a da uwa?,ya dauke zata tambayeshi bayan ta barsu yaya suka rayu?,ya dauka zata nuna nadaman barinsu da tayi sun basu gama zama mutane ba?,sai gashi gaba daya hasashenta da hangenta ba'a nan yake ba?,da gaske ne abinda zuciyarsa take raya masa ta biyo DAUKAKARSU DA DUKIYARSU NE?.
"Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki,sai da safe.....na barki lafiya" Ya fada yana juyawa a hankali yana fita daga falon zuwa farfajiyar gidan.
Da kallon takaici ta bishi,shi kansa me sukuni da wadata ne wanda zai iya kashe mata ko nawa take buqata ballanta a gangaro kan muhammad,mahaukatan kudade ke shigo musu daga harkar noma kayan abinci da sauran kayan masarufi da sukeyi,kuma su rabasu cikin qasashen Africa dama qasashen qetare. Tana da dukka information daidai gwargwado a kansu.....amma sai gashi wadatar kowannensu yanason zame mata hoto.
Yadda ranta yake a bace sai zama ya gagareta,takai ta kawo kusan sau uku tana ji har cikin zuciyarta ya dace ta gaggauta daukan mataki,ya kamata tayi wani abu akai kada komai yaci gaba da tafiya a haka. Daidai sanda takai dab da qofar taji horn na mota da kuma shigowarta farfajiyar gidan,bata bi takai ba amma zuciyarta tana mamakin baqon daren da sukayi.
Mintina uku kawai tayi sallama cikin falon. Sallamar data sanya maamah din waiwayowa tana amsa mata fuskarta babu walwala.
Sanye take cikin wani lafiyayyen lace ruwan zuma. Kallo daya tak zakasan cewa ba na qananun mata bane,ba kuma qananun kudi aka sanya aka mallakeshi ba haka dinkin boubou din da aka zuba masan. Zagayayyen dauri ne saman kanta da zai gwada maka adadin wayewarta da kuma zurfinta a sanin data yiwa duniya. Mayafinta na yafe a kafada daya,daga hannayenta har zuwa wuyanta adon sarqa zobe da bangles ne da babu ko tantama da shakka na gold dinne. Ita din idan ka kalleta baifi ka bata shekaru arba'in da biyar ba,saidai kuma ta dara hakan,don a yansu tana dosar cika shekaru sittin ne a duniya.
Daga bayanta wata macece wadda duka ba zata haura shekara arba'in ba. Riqe da wata kyakkyawar handbag wadda babu ko tantama jakar matar dake gaba ne saboda dacewa matuqa da tayi da kayan jikinta.
Maimaita sallamar tayi a karo na biyu tana duban maamah fuskarta a sake. Wannan ya sanya maamah din tayi qoqarin sakin tata fuskar gami da sakaya damuwarta a gefe,cikin mamaki da tarba me kyau ta matsa gareta tana tararta
"Hajiya......isowar yaushe?" Ta tambayeta tana murmushi
"Tun shekaran jiya fa?,gajiya nayi ma na gudo,amma ason dan ahalan sai farkon sabon wata zamu dawo" Ta furta tana neman wajen zama.
Zaman itama tayi a kujerar dake fuskantar tata
"Da kyau.....ai ya kyauta wallahi,ko yanzu aikin huta ko?"
"Yadda ya kamata kuwa.....wai nikam musaddiq nake gani yana fita sanda nake shigowa da mota?". Dan tabe baki kadan maamah din tayi sannan ta amsa cikin salon rashin bawa maganar muhimmanci
"Shine mana"
"Hala bai ganeni ba,don baiyimin magana ba"
"Ko ya ganekin ma babu lallai ya miki magana ai harira" Ta amsa mata boyayyar damuwar fuskarta tana bayyanar da kanta.
Kallon tsanaki hajiyar mamallakiyar sunan harira ta yiwa maamah kafin tace
"Ban gane me kike fada ba mariya" Qarasa bawa sauran boyayyar damuwarta qofa tayi ta fallasa kanta,don tambayar sa harira tayi mata ta zama tamkar susa ce tayi mata akan ciwonta
"Ina da damuwa harira.....ina da damuwar da har kwanan gobe na gaza gano maganinta".
A nutse hajja harira ta waiwaya ta dubi 'yar aikinta,wadda ke tsaye daga gefe,tunda suka shigo taketa faman gaida maamah din amma bata ma jita ba bare ta amsa
" Ajiyemin jakar ki fita daga waje ki jirani" Ta fadi mata. A ladabce ta ajiye jakar sannan ta juya da hanzari tana ficewa,abinda ya bawa hajja harira damar maido hankalinta ga maamah
"Nayi tunanin kawo yanzu kinyi nisa daga dukkan wani abu me suna damuwa daga randa dan cikinki ya zama mamallakin kamfanin diamondchore?"
"Daga sannan sabuwar damuwa ta fara hajja harira" Maamah din ta furta ranta yana matuqar quna
"Idan na kalli yadda kike fantamawa hajja sai na sake tabbatarwa kaina lallai akwai aiki a gabana......aikin kuwa shine YADDA ZAN MALLAKE 'YA'YANA". Wani irin duba hajja hariran take mata,sai kuma ta kyabe baki
"Keda wanne baccin kikeyi da baki aikata hakan ba mariya?,wanne gangancin ya kaiki?,bakisan daga ranar da Allah ya yiwa 'ya'yanki arziqi ba.....akwai tarin mutane da dama da suke marmarin juye matsayinki su haye kai ba?.......kin ganni nan mariya?,kaf 'ya'yana babu wanda ya isa ya aiwatar da wani abu komai girmansa kuma komai qanqantarsa ba tare da sanina ko yardara ko sahalewata ba.....ke koda matansu ko 'ya'yansu zasu yiwa kuwa sai da sanina da yardaya,a cikinsu babu wani gida da bansan me yake gudana a cikinsa ba 24hrs......yanzu haka katafaren gini na sanya sukeyi na bai daya duka zamu zamana a muhalli guda....." Kai kawai maamh ke gyadawa,a yau ta yarda ta miqa wuya ta kumayi surrender kan cewa harira ta fita shu'umanci,iya yadda tae bada.labarin cike da izza da alfahari kawai ya isa gaya maka gaskiyar haqiqanin zahirin abinda ke faruwa kenan......jikinta ya isa ya sake qarfafa maka zancanta.....tsanin alfahari da takeyi yayin bada labarin kuma zai gaya maka yadda take jin dadin yadda take tafi da rayuwarta.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 48
"Inaso na zama uwa mafi gata a duniya harira,inason na zama uwa mafi izza akan yaranta......inason na zama uwa mafi zama abar alfahari abar nunawa a duniya....inason 'ya'yana su dawo qarqashina.....na mulkesu kaman yadda ubangida yake mulkar bawansa......su zamana a tafin hannuna kamar yadda jariri sabuwar haihuwa yake zama a hannun mahaifiyarsa".
Wani murmushi hajja harira ta saki tana duban maamah
"Lallai mariya burinki me girma ne......amma dai kinsan ki baro kari tun ran tubani ko?,ko mu da muka raini yaran har suka girma muka aurar dasu,bamu gusa ko nan da can ba muna gabansu suna gabanmu sabunta ayyukanmu mukeyi akai akai.......munayi matansu sunayi,wanda keda nasara shike samun rinjaye.....ballantana ke,yaranki ina da tabbacin suna buqatar gagarumin aiki kafin samun saituwarsu akan bigiren da kikeso".
"Abinda ya wuce ya wuce hajja harira.....yanzu meye abinyi?" Gyara zamanta tayi sosai tana bawa maamah dukkan hankali da nutsuwarta
"Akwai plans guda biyu,plan A da plan B......idan A baiyi aiki ba zamu wuce zuwa na biyu"
"Kamar?" Ta tambayeta cikin matsuwa da jin bayanin komai
"Yauwa......na farko akwai wajen mutumina da zan kaiki wanda shi yakemin aiki akan komai da kowa......"
"Kai....kai.....amma kin gama min komai" Maamah ta fada tana gyara zamanta da kyau fuskarta na washewa da madaukakiyar fara'a,saboda ta hangi zuwan nasararta a nan kurkusa......ta hangeta tana fantamawa fiye da yadda hajja harira ke fantamawa din.
"Ba komai fa.....zaman tare ai ba qarya bane....zaki zayyane masa dukkan abinda kike da buqata wanda nake da imani a kansa mallaka sai yadda kika juyasu.....akan mansur ya fara yimin aiki,lokacin da yayi aure sai na fuskanci wani abu,maganata qasa take da maganar matarsa,dukkan umarni da zabi nata ne sai abinda taga dama sai kuma abinda tace.....a sannan na farga,amma in gaya miki inayi yarinyar nan tana nata har daga qarshe na hadu da DAN DUMA....tuni na saka ya qara mata wuta a gidan,mansur ya saketa tayi gaba,tun daga ranar dukkan wanda zaiyi aure a cikinsu nice nake zaba masa yarinyar da nakeso ya aura din,wadda zan cimma buqatuna ta hanyarta,wadda zan juyata ba musu ba kuma damuwa......to kema wannan shine plan B dinki idan na farko yaqi aiki"
Shuru maamah tayi tana jinjina kai,lallai duk iya yadda take ganin mulki da isa da kuma izzar hajja harira ta wuce nan. Wannan shine cikakken ma'anar HAMSHAQIYAR UWA ko kuma CIKAKKIYAR UWA. Idan so samu ne tana son kamar haka ko sama da haka
"Amma banajin musaddiq zai qara watanni shida ba tare da yayi aure ba"
"Ko yau yau zaa daura auren kina iya ruguzawa,ki maye gurbinta da wadda kikeso" Ta fada kanta tsaye cikin confidence.
"Waye babbar damuwarki a cikinsu?,muhammadu?" Kai ta jinjina. Tafi damuwa da kamashi a hannu fiye da musaddiq. Tasan waye fuad din,yana da tsauri da tsananin da ita kanta tayi imanin mafi rinjayen aikin a kansa zaa gabatar
"To ki manta da batun musaddiq me sauqi ne"
"Haka ne wannan" Ta fada tana murmushi,tana jin cewa qarshen matsalarta yaxo,tana jin cewa lokaci yayi da zata cika muradanta
"Yaushe zamu tafi zuwa wajen DAN DUMA?,kinsan ba'a bori da sanyin jiki" Ta karkata tambayarta ga hajja hariran cikin zumudi da farinciki,tana jin bacin ranta yana zagwanyewa.
Tunda suka fito daga wajen a cikin jikinta kawai takejinta uncomfortable. Haka kawai take jin kamar akwai wani abu,tayi dukkan research da idanunta hankali da kuma tunani bata ga wulgin kowa ba,hakanan bataga alamun ana bibiyarsu ko wani abu da yayi kama da hakan ba. Saidai har suka soma nisa da wajen bata samu nutsuwa ba,abinda muddin ta soma jinsa a jikinta zaiyi wahala idan baby afkuwar wata matsalar.
"Me napep idan zaiyuwu ka kaini madabo.....zan qara maka wani abun" Tacewa me abun hawan. Malam ne yaketa fado mata a rai,dattijo kuma kamilallen mutumin,ma'abocin nutsuwa karamci da kuma ilimin addini.
Asalin haduwarsu ta fara ne a ranar da zasu rabu da ameen,daya daga cikin mazan da suka taba shiga rayuwarta dama tarihinta. Abun yaso ya kwabe mata har ameen din yaso fahimtar ainihin wace ita ba tare da takai ga fita daga layin ba. Ya sanya aka biyo sahunta tiqa tiqan qattin dake gadin qofar gidan nashi harda rakiyar karensu guda daya.
Malam din shi ya musu kaca kaca,ya kuma hada harda ameen din daya tako da kansa,ya nuna masa daraja da martabar mace,sunaji suna gani yayi saving nata a hannunsu ya wuce da ita sukaci gaba da takawa a qafa har titi.
Ita dinma a hanya bai qyaleta ba,ya dinga yi mata fada bawai don ya fahimci wacece ita ba?,ko ya fahimci ainihin abinda ya hadosu. Donme tana diya mace zata bari takai gefin magriba a irin wannan unguwannin?. Haka kawai taji ranta ya nutsu da dattakonsa da kuma addininsa,rana ta farko da wani ya taba yi mata fada irin wannan tun bayan shudewar iyayenta. A daren ranar tayi kuka tayi kuka,kukan kuma kukan dadi ne na yadda yau aka samu mutum qwaya daya daya tsaidata da zuciya daya yana mata fada kanshi tsaye. Tun daga wannan ranar malam din ya zame mata daya daga cikin mutanen da suke da martaba a idanunta. A duk lokacin da kudi suka samu takan dauki wani abu tayi tattaki taje ta gaidashi,ta kuma bayar wa almajiransa tace ayi ma iyayenta da suka rasu sadaka.
Matarsa tana da matuqar kirkin da ta dauketa kamar diya kaman yadda malam ya dauketa diya a wajensa. Duk sanda zataje gidan bata gaza fahimtar wasu abubuwa daga sabreen. Macace mai matuqar hikimar da sai da takai daga qarshe ta karanci wace sabreen din,sai ya zamana itama bata fiya boyewa inna komai ba muddin ta tambayeta din,gidan sai yake zame mata wajen samun nutsuwa a wadansu lokutan.
Unguwar madabo,daya daga cikin tsaffin unguwanni dake birnin kano,wadda take da dadadden tarihi. Hakanan ta tara malamai da masana addini masu yawan gaske.
Tsukukun loko ne da ko adaidata sahun a matse yake shiga,wannan ya sanyata ta nemi ya ajiyesu daga bakin babban lokon da zaka karya ka shiga qaramin. Ta bude jakarta ta sallameshi,sannan suka fara takawa ita dasu zuwa ciki.
Tun a rumfar dake qofar gidan ta tabbatar malam baya nan,don babu tabarmin karatu,hakanan daliban nasa sai jifa jifa kowa yana sabgar gabansa,don haka kai tsaye suka wuce zuwa ainihin cikin gidan.
Da sallama a bakinta suka kutsa kai,gidan yana nan kamar kullum cike da tsafta. Ba kowa a filin gidan sai hayaqi dake fitowa daga kitchen da alamu ana gab da kammala tuwon dare. Yaransu bakwai da malam,maza hudu mata uku kuma dukkansu sun aurar dasu,don haka inna ce kadai ke rayuwa cikin gidan,sai babbar jikarta da aka kawo mata don ta tayata zama.
Sake sallamar tayi,kusan lokaci daya aka amsa mata daga kitchen din da kuma rumfar dakin inna. Cikin qasa da second daya wadda ke kitchen din ta fito. Matashiya ce da duka duka bata wuce sa'ar huda ba,murmushi sosai take saki,ta baro cikin kitchen din tana goge hawayen fuskarta da hayaqi ya sanya mata tana takowa
"Adda sabreen.....kece yau a gari?" Miskilin murmushin nan nata ta saki
"Inji maqi baqo ko rumasa'u?"