Showing 27001 words to 30000 words out of 209775 words

Chapter 10 - DUNIYATA BOOK 1 By HUGUMA

maganar,saidai a yanzu baya jin yana da lokacinta,dukka tunaninsa yana ta'allaqe akan sabreen. Yasan halinta sarai,muddin ya haura mintunan data dibar masa,yayi imanin da gaske zai iya zuwa ya tarar ta wuce din abinta.

Tana rungume da hannayenta sanda take tsaye a qofar gidan nasu ta bashi baya. Fuskar nan dake shimfide da wani irin kwarjini yau din cakude take da ninkin rashin fara'a da walwala na tun asali da aka santa dashi. Har tsakiyar zuciyarta takejin wani abu yana tsikarinta duk da yadda iskar dake yawo sararin subhana ke kada doguwar riga da dan mayafin saman kanta tana watsa daddadan qamshin turaren dake tashi a jikinta. Turaren da ita kanta yake sanya mata nutsuwa da kwanciyar hankali,dadinsa ya sanya ta zabeshi a matsayin turarenta na dindindin,duk da batayi tunani matsayinta zaikai a nan kusa ta mallakeshi ba.

Ta kalli agogon hannunta,yaci mintuna hudu cikin minti biyar din data bashi,don haka ta fara takawa sannu a hankali tana matsawa daga gaban gidan nasu.

Tun batayi nisa ba ta jiyo taku da kuma muryar kawun nata,bata da buqatar kallon fuskarsa ko doguwar magana ta hadasu,buqata gareshi zata sallameshi.....kamar yadda tun tale tale.....kaman yadda tun can baya bashi da amfani a garesu a yanzun ma bata tunani akwai wani sauran amfani da yake dashi a rayuwarsu,don haka ta sabule jakarta,ta zuge ta zaro wani abu daga cikin kudin da yayi saura a ciki ta dunqule a hannunta tana jiran isowarsa

"Ke sabreena......sabreen" Ya hada da qwala mata kira tamkar ya bata bashin kudi tana kuma shirin gudar masa dashi. Ranta ya sake baci,ta tsani kwakwazo,a banza ma idanun 'yan unguwar da dukka kunnuwansu harma da hankulansu suna kanta,kowanne motsi ko taku nata a biye suke dashi,sauraro suke.....jira sukeyi na samuwar dukkan wata dama da zasu samu abun magana a kanta. Wannan ya sanya tadan saurara daga tafiyar da takeyi tana dakon isowarsa. Ko a sannan tana iya ganin idanun tsirarun mutanen unguwar da suka samu sararin fitowa da safen kamar ita yana karakaina a kanta.

Irin wannan kallon nasu gareta ya zama tamkar jarrabi ko masifa cikin rayuwarsu. Akwai abubuwa da yawa tasan da akeson gaya mata amma babu wannan fuskar. Bataga dalilin zallar rashin adalci irin nasu da suke gwada mata ba suke kuma gwadawa rayuwarta ba. Sun sany hannu dukka da qafafunsu sun tankwabeta sun kuma tankwabe rayuwarta a sanda take da tsananin buqatarsu......a yanzu kuma data yankema kanta bata da buqarsu.....a sannan su kuma suke qoqarin dawo da ita su dankwafar da ita.....suka kuma fidda makamansu da harsunansu wajen illata mata gangar jiki da zuciya.

"Me na samu?" Ya iso gareta yana tambaya sanda motar da take da tabbacin waye a ciki ke dab da isowa inda take. Kowanne mutun da zatayi mu'amala dashi ko kuma tayi mu'amala dashi din......sau daya tak take masa wani karatu a taqaitaccen lokaci.......fahimtar waye kai?......meye qudurinka.......meye motsinka?.....mene manufarka......da sauran dukkan wani abu daya shafi rayuwarka yana zama RUBUTACCE cikin shafin qwaqwalwarta. Bata fiya manta abu ba,haka bata missing target saidai idan bata nufaci abu ba.

Ta baya ta miqa masa kudin sannan ta fara takawa zuwa ga motar da tuni ta iso inda suke harma ta samu wajen tsaiwa.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 17

daga inda yake a zaune din yakejin kamar gilashin window din motar ya masa shamaki daga kallonta duk da yadda yake tarwai yake kuma iya baka daman gano komai dake ta wajen motar......duk da haka yana jin kamar ya rage ma idanunsa armashin kallonta,don haka ya kasa haqurin isowartata,ya sanya hannu ya sauke dukka gilashin nasa qasa.

sau daya tak ta taba ganinsa ido da ido,amma ta haddaceshi tsaf,tun daga abun hawansa har zuwa halayya da kamanninsa.......

Kakkaura kuma faffada da zaka iya kiransa me jiki saidai bai cancan ba. Maabocin iya ado sosai da murza hula ta zauna a kansa kamar shi yake saqa ma kansa ita. Yadda turarensa da shigarsa keda kyau da tsari haka ma kalaman bakinsa,saidai kash!.....daidai da wucewar daqiqa guda bata taba jin wani abu me kama da SO K'AUNA KO BEGE nashi ya tsartu a ranta ba.

Waishin mcikina meye SOYAYYA ne?. Ita kanta jerin kalmar SOYAYYA da yadda mutanen duniya suka daukaketa na daya daga cikin abinda ke sanyata dariya koda bata shiryawa hakan ba. SHIRME shine cikakkiyar ma'anar da take ganin yafi dacewa da a kirata ko kuma CUTA,idan akwai sunan da yafi haka lalacewa ma a nata ganin daidai ne a kirata da wannan sunan.

Yadda yake tsareta da kallo ya sanya qirjinta ya dinga suya duk kuwa da cewa ta saba da irin wannan shegen kallon. Kwarjininta na daya daga cikin abinda ya sanya take tsira daga guba da dafin MAZA duk kuwa da cewa ita da kanta take tsalle ta afka tsakiyar tarkon bisa tsananin lissafinta,ta kuma samu sa'a da nasarar zame kanta cikin SALO da kuma qwarewar iya wasa.

Da hanzarinsa ya fito ya zagaya don bude mata qofar motar,hakan ya bawa kawu dake lafe yana kallon komai qare masa kallo.

"Iya shaddar jikin yaronnan kawai ta isheni jari wallahi,wannan tsinanniyar yarina,yanzu meye aibun wannan da ba za'a aureshi ba?" Ya tambayi kansa da kansa yana naniqe da kudin hannunsa.

Idanunsa ya aza a kanta bayan ya bude mata motar,sai ya sakar mata murmushi,tadan lumshe ido tana qaqalo nata murmushin cikin dauriya da son maida masa. Gefe guda zuciyarta na cike fal da qarin wani mamakin akan D'A NAMIJI. ta tuna kalamansa akan matarsa dazun dazun nan,amma a yanzun gashi a gabanta ita kamar zai narke. Ta yaya zata yadda tayi aure a duniya?,ta yaya zata bari zuciyarta ta kamu da soyayyar wani namiji?,yaya za'ayi ta banzatar da lafiyar zuciyarta cikin soyayyar wani?,soyayyar halittar da babu tausayi ko jin qai a tare dasu?,halitta mafi son kai cikin halittun duniya gaba daya?,halitta me tsananin mugunta da son cutar da halittar mace 'yaruwarta?.

Ba zata iya sadaukar masa da murmushinta na dogon lokaci ba,duk kuwa da cewa fake smile ne,don haka ta zame jiki ta shige cikin motar ya mayar ya kulle yana sauke ajiyar zuciya. Yana jin duk duniya ba wanda ya kaishi sa'a a yau din. Yana jin kamar duka ranar tashi ce.

A kujeran driver ya zauna yana qoqarin tayar da motar amma duka ido da hankalinsa yana kanta

"Ina muka nufa my life?"

"My life?" Ta sake jaddada maganar a ranta

"Ko ina ya baro matarsa ta sunna da har ita ya danqara mata wannan sunan?" Wannan ba baqon abu bane a wajenta,saidai har yanzun mamaki da lamarin maza bai gama sakinta ba.

"SAMHG store" Ta amsa masa a nutse tana gyara agogon hannunta daya goce

"An gama ranki ya dade" Ya fadi cikin zumudi yana tayar da motar.

Sun jima akan hanya yana tauna abinda zaice da ita,don a taqaitaccen saninsa da ita.....mutum ce me matuqar tsari,nutsuwa da aje komai a bisa gurbi da muhallinsa. Bayaso ya kwafsa kaman waccan karon,bayaso damarsa ta sake kubce masa,duk da cewa har kawo yanzun baisan me ya aikata daya rasa wancan damar a wancan karon ba.

Yaji babu dadi ainun saboda ya qwallafa rai sosai a kanta. Ta yiwa zuciyarsa wani mahaukaci kamu a ganin farko. Yayi tsammanin kudinsa da ajin mataki na rayuwa zai saya masa ita cikin qanqanin lokaci,sanin da ya yiwa 'yammata kenan a yanzun,ballantana ita dake da kyau da aji irin wannan.

Sanda yake wannan tunanin nata nazarin da karatunsa duka a kansa yake. Yadda yaketa rejecting kiran dake fama shigowa wayarsa a jejjere. Duk kiran da zai shigo sai ya katseshi. Tuni hankali da kuma jikinta ya bata wanda ke kira.

Idanunta tadan lumshe,koda yaushe su dinne dai,cikin wahala,qasqanci,tozarta da kuma wulaqanta zaune cikin gidajen aure. Ko meye kuma zai fito yaje yazo su din yake afkawa.

"Zan iya cewa wani abu?" Ya tambaya a ladabce yana murza steering motar cikin qwarewa

"Kafin sannan ya kamata ka daga wannan kiran ko?" Ta fada idonta akan fuskarsa.

Motsawa kadan yayi yana duban wayar ta qasa idanu,bai zaci ma ta lura da hakan ba. Haushi ya soma kamashi akan kiran da take masan babu qaqqautawa. Yasan zancan gizo baya wuce na qoqi,tunda bai jima da fita a gidan ba,yasan kuma abinda ya fito ya baro a gidan

"Tarin damuwa ce da matsaloli kawai take dauke dashi" Ya furta yana jan siririn tsaki.

Har tsakiyar ranta taji saukar maganar,ta lumshe ido kadan tana budesu. Yana nan din a haka,yana nan yadda ta karanta. Tayi qoqarin tureshi daga shiga layikanta,tayi qoqarin hanashi shiga cikin tarkonta don baya cikin irin mazan data zana bisa layi da gurbin rayuwarta,taso ta barshi ya samu me hukuntashi a gaba.....amma tunda har ya sake dawowa cikin rayuwartata cike da karsashi da zumudi,to tayi imani hukuntashi yana cikin qaddararta ne. Ba kuma zata qyaleshi ba,a wannan karon saita hukuntashin yadda ta saba hukunta maza irinsa. Maza irinsa basa tsira daga tarkonta......basa tsira daga kamunta,hakanan basa tsira daga hukuncinta.

Cikin salo na dabarar da yake gani kaman ba zata gane ba ya latse wayar,ya kuma jefo mata maganar da tafi damunsa

"Hanan.......wannan karon bazan bari ki kufcemin ba"

"Nima bazan bari ka tafi ba" Ta furta,a bakinta bisa mizanin ma'ana qwaya daya tak da hankali zai iya fahimta,amma kuma an aje ajjiyayyar ma'anar da ake nufi da maganar can qasan zukata.

Wani irin dadin daya sabbaba masa lafiyayyen murmushi ya ziyarceshi. Bai taba kawowa ko kusa a ransa samun wannan gwaggwabar nasarar a kurkusa haka ba,amma kuma,sai wani sashe na zuciyarsa ke gaya masa

"Duk kyau ko matsayinta zata sauko......a yanzun fa mata ke neman mazan aure idanu rufe" Hudubar data shiga kunnensa kenan,kuma ya yarda da hakan dari bisa dari.

"Amma hanan banga alama ba......bansa inane mazaunin da kike rayuwa ba,gida unguwa da sauransu"

"Gaggawar me kakeyi?,kada ka samu damuwa" Ta amsa masa tana jin ya ginsheta gaba daya,tana jin ta damu qarshen zamansu yazo,ta qagu su isa SAMHG store ya ajeta ya bata sarari.

A hankali ya kutsa motar babbar harabar kantin saida dukkanin kayan buqatar rayuwa,wanda zaifi kyau ka kirashi da kasuwa a sauqaqe amma kuma a zamanance. Ba abinda basu hada ba na kayan buqatu,tun daga tufafi zuwa kayan masarufi. Wajen nada matuqar girman da idan ka kirashi da duniyar siye da siyarwa. Girmansa ya sanya yake da mashigu daban daban da kuma guraren fita mabanbanta.

Cikin tafkekiyar harabar wajen ya aje motarsa,ya kasheta cikin mutuwar jiki da kasala yana waiwayowa inda take zaune tana qoqarin rataya jakarta gami da daukar wayarta ta riqe wadda ke aje saman cinyarta.

"Idan ban damuwa zan dan tayaki tattaki zuwa ciki......don naga wajen kamar cike yake da maza da yawa......ni kuma ina kishin na barki ki fita ke daya a kallemin ke" Ya furta cikin kulawa da wani irin narkakken so dake ragargazar zuciyarsa.

Da wani sassanyan kallo ta jefeshi,qawataccen murmushin nan dake qawata fuskarta da kuma labbanta ta sakar masa. Ta rausayar da kanta gefe tana juya idanunta. So take ta sallameshi a iya haka,bata buqatar doguwar damuwa. A lokaci irin wannan da takai qarshen mission dinta,ko fita unguwa ba kasafai take damunta ba sai idan buqatar haka ta taso. To amma hakanan taji akwai buqatar ta fita din,akwai kuma buqatar ta fita tayi musu siyayya.

"Baka da damuwa akan duka wannan......wannan hanan din ba komai idanunta ke kalla ba ballantana su burgeta" Ta bashi amsa a nutse.

Murmushi ya saki yana qara narkewa a sonta,yana ji cewa zai iya yin komai don ya mallaketa,yana jin cewa muddin ya sake barinta ta subuce masa a wannan karon ya tafka babbar asarar da bazai iya maida madadinta ba,baya jin ma zai bari hakan ya faru dashi sam sam.....kai koda tuna hakan na iya faruwar bayason yayi.

"Na ga zahiri......na kuma tabbatar wannan halittar ta daban ce......gamu cikin neman sa'ar kasancewa da ita" Ya fada yana lumshe idanu. Kai ta kawar amma tana murmushin yaqe. Ya numfasa bayan ya gama qare mata kallo cikin shauqi ya dauki wayarsa dake aje tun sanda ya maidata silent ya bude.

Tarin miscall a qalla guda goma kyawawa daga gareta. Ya jawo maballin sama ya sharesu yana sakin tsaki can qasan ranshi tare da wucewa mobile app na banking da yake ajiyar kudadensa.

Sosai ta jingina da makarin motar idanunta a lumshe sosai,sai kayi tsammanin bacci ko kuma gajiya ne sukayi mata yawa,saidai a cikin biyun duka babu ko daya a ciki.

"A taimaka a karantomin account number na dan bada wani tukuici" Idanunta ta janye daga saman wayar nasa,saita tashi ta zauna sosai tana dan sakin murmushi

"No need" Ta amsa masa a yangance kaman yadda ta saba magana

"Please.......ba wani abu bane me yawa.....just tukucin bani damar ganinki da kikayi a yau ne" Bata sake ce masa komai ba,sai ta zura hannunta cikin jakarta,wani dan siririn card me ruwan zaibar gold ta ciro ta aje a gefansa. Ta dauke kai tana qoqarin bude murfin motar wanda ita kanta tasan ba zata budu ta sauqi ko dadin rai ba......ta kwana da sanin meta aiwatar mata.

Cikin qasa da minti daya taji ya furzar da iska daga bakinsa gami da cewa

"Done.....ina fata zakiyi appreciating"

"Why not?,godiya me kima......godiya nake qwarai......but motarka tana nema ta riqeni fa"

"Da zatayi hakan data taimakeni ai" Ya amsata yana sake lafewa jikin kujerar. Kyawawan sexy eyes dinta ta waro waje kadan,sai kuma ta daga hannunta tana duban agogo

"Akwai alqawari da nayi,bana so kuma na saba......idan ka sani na saba kuma......next time kafin na baka daman sake haduwa dani....." Katseta yayi yana dariya ta hanyar hada hannayensa biyu waje daya sannan ya saukesu ya juya yana buda side dinsa

"Lemme check meye ya riqemin amaryata haka".

Da lumsassun idanunta ta bishi da kallo har zuwa sanda yake zagayawa gaban motar zuwa daya side din da take zaune. Yayi dukan dabarunsa amma hakan baiba,don haka ya zagayo yana fadin

" Bansan me yake faruwa,lafiya lau qofar yake,bari nasa a duban.....am really sorry" Ya sake apologizing yana hade hannuwansa.

taka Kai kawai ta daga masa tana irgen lokutan cikar target dinta. Cikin saa kuwa ya juya ya fara takawa yana barin wajen,wanda hakan ya bata damar janye kallonta sannu a hankali daga kansa,ta kuma maida saman wayarsa dake ajiye a wajen tana bada haske,tabbacin yunqurin hanata komawa key yayi daidai kenan,saita katse kiran da takeyi daga tata wayar zuwa tasa don sanya wayar awake.

A nutse ta jawo wayar ta wuce zuwa ga maballin kira.

Tarin miscall dinne kuwa ta samu kamar yadda tayi zato,dukka kuma daga number dake ajiye cikin wayar da sunan MOM SUHAIL.

"SUHAIL" Ta ambata a fili,idan har bawai ta manta ba suhail din shine sunan first born dinsa kamar yadda T.j ya tabbatar mata.

Wani irin tausayin matar da batasan ko wacece ba ya fara ratsa ta. Tana shirin karkata akalar binciken nata zuwa wani sashe na daban saqon SMS ya shigo wayar.

MOM SUHAIL kamar yadda yake a rubuce ta bangaren kira. Bata tsaya dogon jinkiri ba ta bude,gajeran saqo ne kamar haka.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 18

_Nayita kiranka baka dauka ba,kome meye mukayi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login