Showing 126001 words to 129000 words out of 209775 words

Chapter 43 - DUNIYATA BOOK 1 By HUGUMA

wannan ragamar kawai ya miqawa fu'ad din,don tunda shi ya faro barota shine zai iya. Qaramin murmushi farouq din ya saki,fu'ad ya dage masa gira alamun tambaya

"Ba komai.......kawai na tuna temple run dinka ne......rigimammen dan bautar qasar da yaje garin wasu ya musu barna.....ya kuma gudo da abinda suke ta buri da nacin samu......Allah inda a zamanin yaqe yaqe ne zakayi barna da yawa fa" Maganar dole ta sanya murmushi kubcewa daga fuskar fu'ad,ya zauna sosai yana sake duban farouq

"Mazantaka a zuciya take farouq......sannan dukkan namiji muddin zai amsa wannan sunan dole kalmar TSORO ta fita daga dabi'arsa......bai halatta ba sam sam namiji ya zama me tsoro ba..... Idan hakan kuwa ta kasance a matsayinsa na shugaba kuma jagora,dole al'amura su lalace..... Adinga ganinsu kuma ba'a yadda suke ba".

Duk da tsananin gajiyar dake a jikinta bayan dawowarsu daga wajen boka DURGUJI amma hakan bai sanyata zama ta huta ba bare akai ga batun kwanciya. Kai kawo kawai takeyi tsakanin kitchen da dakunanta cikin sabgar dafawa da saukewa. Wani tsari da takeson fara qirqiro dashi a yau din,don shine hanya guda daya da zata samu ayyukan da aka tsara mata su tafi yadda takeso.

Ta bata lokaci sosai tana son tuna wanne abinci da wanne abinci sukafiso ta dafa musu lokacin quruciyarsu?. Da qyar ta dinga tuna wasi abubuwan da suma shafesu saboda yadda ruhi da zuciya suka jima da yin nisa daga rayuwarsu dama komai daya shafesu.

Tayi lissafin abubuwa guda hudu duk da tasan sunfi hakan,saidai sauran ta barwa ranta zata nemi ganin ma'aikatansa da yake yawan rayuwa dasu don samun wasu amsoshin. Anni ce tasan wadda zata samu amsar kai tsaye daga gareta,saidai zuwa yanzun tana jin cewa tafi qarfin anni ballantana ta sake neman wani abu daga wajenta akan 'ya'yan da ita tayi cikinsu ta kuma haife abinta. Alwashi taci......tana nan kuma riqe dashi......hakanan ba zata runtsa ba ba kuma zata huta ba har sai ta samu cikar wannan alwashin nata.

Tana aikin masu aikinta suna mamakin shigarta kitchen yau da kanta. Duk kallon da suke binta dashi bata samu nasarar tantancewa ko kuma kula ba,saboda hankalinta yayi matuqar nisa akan maganganun da suka tattauna da durguji.

_"sau daya nakewa mutum aiki na gama dashi.....muddin kuma nayi aiki baici ba yana da wahala na sake na biyu indai ba sa'a ka taka ba......aikinki me hatsarin gaske ne......duk abinda kikaji ko kika gani kada ki wuce wata guda kacal baki dawomin ba"_

Ita batun sake aiki da rashin sakewar duka ba damuwarta bane,tunda ta riga data sani kudi suke juya akalar kowa su kuma sauya tunaninsa. Muddin zata zube masa kudi ta tabbatar duk taurin kansa sai ya sake waiwayarta. Kawai abinda yake damunta a yanzu shine yadda zata samu dawowar hankulansu a kanta,ta yadda cinsu da shansu zai dawo qarqashinta,wanda wannan shine abu guda daya tal da zai sanya aikinta ya tafi yadda ya dace.

Tana kammala white rice sai ta kasa haquri ta fita a kitchen din. Dakin gadonta ta wuce ta samu saman sofa bed ta zauna tana latsa wayarta. Number fu'ad din ta fara kira,daidai sanda yake zaune suka ci gaba da tattaunawa da farouq yana nuna masa tsarin taswirar ginin kamfanin.

Fararen idanunsa ya daga yana azawa saman wayar. Zubawa wayar idanu yayi yana kallon yadda sunan ke wucewa ta saman screen din. A duk sanda zaiga shigowar kiranta sai yaji wani abu tun daga qasan ransa har tafin qafafunsa. Inda yana da iko bazai daga wayar ba sam sam,to amma wata fuskar tafi gaban mari

"Ina zuwa" Yace da farouq yana daukan wayar ya daga ya saka a kunnensa.

Cikakkiyar sallama tayi da kwantacciyar murya da zai iya cewa ya manta rabon da yajita daga bakinta,wani abu guda daya sake jan hankalinsa,saidai bai hanashi amsa sallamartata ba hadi da dorawa da fadin

"Barka da yamma" Dan murmushi ta saki kadan

"Yauwa barka kadai Muhammadu" Ta fada cikin nuna kulawa

"Ka wuni lafiya kai da dan uwanka?,tunda har yanzu ban cancanci a kullum naga lafiyarku ba......hasalima kamar kuna mantawa ne da rayuwata" Yadda tayi maganar ya taba ransa kadan,yaji sautin da amon da ya jima baiji daga gareta ba

"Kiyi haquri ba haka bane" Ya maida amsa wani abu yana kai kawo a ranshi

"To idan ba haka bane yaya ne Muhammadu?,kamanhar yanzu kun kasa manta abinda ya faru ne kawai" Idanunsa ya lumshe kawai yana saurarenta. Zuciyarsa nadan qara bugun da takeyi yana jin wani abu sosai can qasan ransa da kuma wani sashe na zuciyarsa

"Idan zaku iyayimin alfarma,inaso ana gama sallar ishai ku shigo kai da musaddiq....inason ganinku duka ku biyun"

"In sha Allah" Ya amsa mata kai tsaye. Wayar na a kunnensa har ta yanke Kiran,sai shima ya zame wayar daga kunnensa yana kallon screen din.

Sanda ya daga idanunsa sai suka hada ido da farouq,murmushi farouq din ya sakar masa kawai. Har yanzu bai taba saka baki ko shiga lamarinsa da maamah ba,infact ma shi bai taba masa magana a kanta ba,ko yaushe shida sadiq suna qoqarin kiyaye iyakokinsu ne.

Wani irin murmushi ta saki bayan ta ajiye wayar idanunta akan qofa tana jin wani farinciki yana shigarta. Nasara ce a kusa take shanshanarta......kuma jikinta yana bata komai yana kusa da qofarta.

Plan dinta guda uku ne qwarara,ta fara da wannan na farkon,idan yayi aiki shikenan,idan baiyi ba zata wuce plan B,idan shima yayi aiki shikenan,idan kuma shima baiyi ba tana da plan C......wanda shine tsororuwar shiri mafi tsauri da tauri.....plan din data tabbatar zai yamutsa hazo iya yamutsawa........ita kuma zata saki dukkan wata iyaka da ikon da Allah ya bata don ganin tabbatuwar plan din da kuma wanzar dashi.

Ranta fes,Zuciyarta wasai ta ajiye wayar ta koma kitchen tana shirye shirye shirye gadan gadan.

Haka kawai yakejin yanayinsa wani iri,jikinsa da zuciyarsa dukka ba'a sake suke ba,a haka ya shirya cikin Moroccan abaya ne sulbi ya wuce zuwa sallar magariba.

Kafin ya isa masallacin suna hanya shi da farouq musaddiq da saddiq suka biyo bayansu. Wannan din wata kyakkyawar al'adarsu ce da anni ta renesu a kai. Muddin suna garin ko suna qasar,hakanan ba wani babban uzuri ko aiki bane ya riqesu a kamfani,to zaka samesu a gida duk inda magariba tayi. Kwata kwata basusan yawon dare ba,farouq ne ma medan sha'awar fitan daren,to sukan fita jifa jifa su zaga a mota su dawo. A nan zasuyi sallar magariba suyi ishai,suyi dinner tare me uzuru ya wuce nasa uzurin.

Sanda yake sabule tattausan flip flops din qafarsa yace da musaddiq ba tare daya waiwayo ba

"Bayan ishai ku shirya kaida saddiq zamu shiga wajen maamah" Dan kallon yayan nasa kadan yayi,kaman zai magana sai kuma ya fasa ya amsa da to.

Tun bayan magariba ta sallami kowa tare da kafawa kowa sharadi da dokar bataso kowa ya sake tako mata parlor sai gobe idan Allah ya kaimu.

Ta duba doormat din bakin qofar falon yafi sau goma daga zamanta,ta kuma tabbatar komai yana nan intact kamar yadda ya kamata ace ya kasance din,sai ta koma ta zauna tana sauya tashar Tv din zuwa mbc Bollywood bawai don tana jin dadin kallon ko yana burgeta ba,dukkan hankalinta yanzu da nutsuwarta shine takowarsu cikin falon,su zauna kuma su cika cikin su da abinci da abin shan da ta tsumashi ta kuma tanadashi musamman saboda su.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 64

Saddiq da musaddiq dinne a gaba shi kuma yana biye dasu a hankali a hankali,hakan ya sanya suka dan masa tazara kadan. Wayar Mika'il yake amsawa,wanda yakeso ya tabbatar komai ya zama daidai zuwa ranar Monday da zai koma office. Yanason ya gabatar masa da dukkan wasu mu'amala na kudi da banking ya samu bayan tafiyar tasa,komai na shige da ficen kudi.

Yana wayar ne amma hankalinsa yana kan saddiq da musaddiq,tamkar 'yan biyu kamar yadda kowa yake musu kallo hatta da makarantun da sukayi. Suna hira abinsu ne cikin wani irin shaquwa da jituwar jini. Malam saidu ne ya bude musu qofan da kanshi,ya rusuna kuma yana miqa masa gaisuwa sai ya gyada masa kai hadi da daga masa hannu saboda wayar da yakeyi din,ya taka a nutse yana bin bayansu.

Dab da zasu isa steps din da zasu sadasu da ainihin falon yaji gabansa yayi wani mummunar faduwa

"Zamu qarasa anjima" Yace da Mika'il a gaggauce yana katse wayar ba tare daya jira amsarsa ba

"Kai saddiq" Ya furta da muryar da taja hankalin maamah dake falon,wadda dama dukkan tunaninta yana fa farfajiyar gidan tana sauraren kowanne motsi.

"Saddiq kuma?" Ta tambayi kanta da kanta a mamakance,sai ta tuna kuma bata da sauran lokacin batawa,don muddin ta bari wani bayan yaran nata ya taka wannan shirin akwai matsala,don haka ta zabura tayi zumbur ta miqe ta kuma nufi bakin qofar falon da sassarfa.

Wancakali tayi da doormat din,ta sanya hannu ta dauke abun da yake qasan,sannan ta finciki tsintsiya dake ajiye a can wani gefe daban ta fara tattara sauran abubuwan da suka rage.

"Kunyi addu'a ne?" Ya fada yana tsaresu da idanu duka su biyun. Juna suka kalla shi da musaddiq din

"Hamma ai daga masallaci muke" Saddiq din ya fada dukkaninsu suna sauke qafafunsu daga saman steps din da suka fara dorawa

"Kuyi addu'a kafin ku shiga.......haka musulunci ya koyar damu,kome zakayi akwai addu'ar da akeyi masa" Ya fadi idanunsa akan musaddiq

"To hamma" Suka fadi sannan suka maida qafafunsu kowa bakinsa yana dan motsawa.

Da kallo ya bisu zuciyarsa cike da wani wasi wasi da baisan daga inda ya samo asali ba. Sosai hankalinsa yana kan musaddiq da ya tabbatar baisan komai akan shirin maamah nason raba tsakaninsu da iyalin alhaji hamza ba. Shi kansa abban baisan komai ba akai,shi daya yake juya maganar tsakanin qirjinsa da zuciyarsa.

Dan ja sukayi suka tsaya sanda suka sameta duqe tana tattare wani abu da basusan meye shi ba. Ta daga kai tana dubansu,wani irin bacin rai ya cika mata zuciya fal.

Ta yaya banda sun raina umarninta zata ce tana buqatar ganinsu su biyu su rakito mata wani?. Fushin yanason yayi galaba a kanta amma tanata qoqarin danneshi. Yanzun ba lokacin nuna fushi bane ko fada..... Lokaci ne na sauke kai da maida komai ba komai ba muddin nasara take da buqata,wannan shine abinda hajja ta gaya mata.

Dole ta qirqiro murmushi tana cewa cikin nuna kulawa a garesu gaba daya

"Maraba da 'yan samari na" Saita zubda abun cikin kwandon shara ta kuma taka zuwa ciki tana fadin

"Ku qaraso mana". Sai da suka fara shiga sannan yabi bayansu yana kula da hagu da damansu

"Ina ma'aikatan suka barki kina shara?" Fuad ya furta da nutsatsiyar muryarshin nan yana zama hannun kujera hannunsa goye a qirjinsa yana kuma qoqarin karantar komai dama motsin komai dake a falon.

Dan murmushi ta saki tana zama saman daya daga cikin kujerun alfarma dake falon

"Ina buqatar kebewa da 'ya'yana,nayi sirri dasu irin na uwa da 'ya'yanta,shi yasa na sallamesu yau da wuri". Maganar tata sai ta kasance kamar ta jefi tsuntsu biyu ne da dutse guda,don haka saddiq sai ya rusuna kawai yana gaidata.

"Lafiya alhamdlh saddiq......ya mutanen gidan?"

"Suna lafiya maamah"

"Ma sha Allah,don Allah kace ina gaidata da kyau da kyau"

"Zataji in sha Allah......hamma zan qarasa,saikun fito" Idanu fuad din ya zube masa,yayin da maamah ta bata fuska tana cewa

"Ina kuma zaka daga shigowarku ko zama bakayi ba?". Dan murmushi yayi yana saukar da kansa qasa cikin girmamawa

"Gida zan qarasa,jibi zamu koma company ban kuma gama shiryawa ba,kinsan kuma hamma......bazai dagan qafa ba idan aka samu kuskure" Tabe baki tayi kadan ta yadda ba lallai bane su fuskanta,qasan zuciyarta kuma cike fal da baqinciki da bacin rai,amma kuma a fili saita saki murmushi

"Gaskiya ne,to Allah ya taimaka,ka gaisheta"

"In sha Allah" Ya fadi yana waiwayawa gefan musaddiq ya bashi hannu yadda suka saba yana yin gaba.

Shiru falon ya dauka sanda saddiq ke ficewa,cikin ranta take gayawa kanta da kanta saura kadan komai yazo qarshe.... .watan watarana saidai ya gifta katangun kamfanin ya ratse ya wuce ta bayansu,komai na wata dama ta shiga cikin kamfanin baida ita.

Sai daya kammala ficewa tsaf sannan ta maida dubanta garesu,dukansu ta fahimci kamar hankalinsu baya tare da ita,don haka ta danyi gyaran murya,gyaran muryar daya sanya dukansu suka dubeta,sai ta saki musu murmushi.

Amsa gaisuwarsu dukka su biyun tayi,a yau sai take jinta kamar a aljannar duniya,sai takejin kamar burinta ya gama cika duk da an samu matsala a karon farko,amma akwai tafiya ta gaba,ta tabbatar ba zasu tsallakewa abincinta ba.

Tanaso a yau tasan abubuwa masu yawa game da rayuwarsu,tanason tasan adadi da zurfin dukiyar da kowannensu ya mallaka,koda batasan duka ba,tanason ta karanci kaso me tsoka.

"Ina fata dukkaninku kuna lafiya"

"Alhamdulillah" Suka fada kusan a tare kowa ba karsashi a tattare dashi.

Ta fahimci hakan,don haka ta gyara zamanta tana fadada fara'ar fuskarta

"Ina fatan zaku cire komai daga zuciyarku,kuci gaba da kallona a matsayin mahaifiyarku,komai zai wuce mu fara gina sabuwar rayuwa tsakanina daku.....ina buqatar 'ya'yana a kusa dani kamar yadda kowacce uwa take da buqatar 'ya'yanta. Inaso na kasance daku tamkar komai bai faru ba,nayi alqawarin baku farinciki da kariya kaman yadda kowacce uwa ke bawa 'ya'yanta" Ta qarashe maganar cikin matuqar raunin zuciya da karyewar murya kamar wadda ke shirin sakin kuka.

Dukkaninsu dubanta suke,kowannensu da mabanbancin feeling a zuciyarsa,saidai kuma dukkaninsu akwai mamaki danqare qasan ransa.

Ci gaba da dubanta fu'ad yayi mamakinsa yana qaruwa. Tunda ta fara magana baiji inda tace tayi nadama ba......nadama koda qwaya daya akan abinda ta yiwa abbansu ba,su din basu da buqatar ta nema yafiya ko afuwarsu,tunda itace ta haifesu,tayi silar kowasu duniya.....ba wani abu da zasuyi mata wanda zasu saka mata da iya wannan aikin......amma kuma abban fa?,kota manta cewa itace silar komai?,ta manta itace silar faruwar komai?. A yanzun ya Fatimid tafi buqatar hankalunsu a kanta da abinda suka mallaka sama da nadama neman afuwa ta zahiri da yafiya daga mutumin da aka zalunta wanda yanzu haka yake kwance a qarqashin qasa.

"Banaso ku dinga nesa dani suka nesanta kanku dani,bani da wani abu dana mallaka a yanzu sama daku.......ina zaune ni kadai,idan mutuwa ma nayi kenan saidai kuji labari daga wajen bare?" Ta maida tambayar kan fuskar musaddiq. Kanshi ya girgiza mata yana sauke kan nasa qasa. Har yanzu idanunsa da sauran tunaninsa sun kasa goge masa komai,ballantana hammansa daya tabbata komai yana rubuce ne a allon zuciyarsa. A duk sanda ya kalleta sai ya tuna ruwan data watsa saman fuskar majinyacin mahaifinsu sanda ya buqaci ta bashi ruwa,shine ya zame masa rumfa yaje ya kwanta a samanshi da zummar kareshi saboda sanyi da yadda ya jiqe din sosai,a sannan ta taka ta fice a dakin hankalinta kwance tana waqe waqe abinta.

"Don Allah koda abincin dare ne ku kasance tare dani ko na safe... Ku bani koda awa daya kowacce rana mu zauna ni daku nasan na haifi 'ya'ya nima kamar kowacce uwa.....don Allah" Ta sake fada da muryar roqo sosai,raunanniyar muryar daka iya sauko da tausayi a zuciyar wanda baisan manufar me magana ba.

"In sha Alla" Kawai fu'ad din ya furta. Ya sani koma me zaice yanzu ba maslaha zai kawo ba,ba kuma zata taba fahimta tunda akwai banbancin manufa a tsakaninsu. Kowanne a cikinsu abinda ya ajjiye a zuciyarsa daban.

"Muje ga abincin dare can na shirya muku.....abinda nasan kunfi so sosai" Ta fada tana murmushi ranta yana mata dadi da yadda suka karbi request dinta suka amince da xuwan nasu.

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login