Showing 156001 words to 159000 words out of 209775 words
duba lokaci.
Wata irin zazzafar tattaunawa ce ta wanzu tsakaninsa duk wani dake under security team. Jiki da zukata sunyi laqwas da wani irin tsoro da kuma firgici. Bacin ran da suka gani a fuskar boos din nasu ya sanyasu cikin tashin hankali,domin kuwa wani abune da basu taba ganinsa a tattare dashi ba.
Dukka bayanan da suka bashi kusan yazo iri daya akan nasa da wanda baki suka bashi,saidai akwai wasu sauye sauye cikin nasu
"Na baku 2days to find full details na dukka team din da sukayi wannan aikin......na tabbatar ba aikin mutum daya qwal bane......team work ne tabbas!" Ya fadi yana doka file din saman table din da yake kai.
Zuciya da qwaqwalwarsa duka a zafafe ya dawo office,yayi nufin yin alwala don yayi salat dhuha kaman yadda ya saba sai yaga lokaci ma duka ya qwace,duk da haka bai fasa daura alwalar ba saboda ita kadai tana saka masa sanyi cikin zuciyarsa
"I need rest please.....duk meson ganina ka gaya masa sai after one hour......kayi shutting komai saina nemeku" Yayi magana da mutanen dake tare dashi. Da daya da daya kowa ya fice har saddiq. Farouq ya miqe a hankali
"Ina zaka kai kuma?"
"Zan bar CEO ya huta haka nan......da gaske brain dinka yana buqatan shuru na wasu lokuta".
"Ko zan huta da ganin kowa banda kai farouq" Ya amsa masa yana jingine bayansa jikin sofan da ya canza mata siffa daga kujera ta koma qaramin gadon hutawa cikin sakan talatin.
Murmushi farouq ya saki,sai ya kalli agogonsa sannan yace
"Na sani.....but now dai dole farouq yadan matsa kadan Shima.....zanje nayi waya da fanna......yau duka ban kira naji lafiyarta ba". Kiran sunan fanna kawai da yayi ya sanya ya daga masa hannu ba tare da yace masa komai ba,sai ya sake sakin qaramar dariya yana takawa
"Anyi zancan SOYAYYA zaka birkice.....bari na qara matsawa da hanzari......hala daya cikin matan naka ne ma zasu kawo maka ziyara". Yayi zancan yana kaiwa qofa.
Maganarsa ta sanya fu'ad sakin murmushin dole duk da bai shirya ba,sai ya bude idonsa a hankali yana bin bayan farouq da kallo har ya qarasa ficewa,ya maida idon ya rufe bayan ya saita security na qofan nasa da wani qaramin remote a gefansa ta yadda babu me iya damunsa,duk da ya bada warning ma reception nasa da kuma saddiq. Shi a wannan ire iren situation dinma idan har yace soyayyar zaiyi baisan ta yadda zai fuskanceta ba.....baisan ma ta inda zai kwasota ba. Yasha ji daga bakin farouq rashin bada kulawa da bada lokaci yana kawo macewar soyayya.....shi kam ya tabbatar wannan shine dalili na farko da zai saka tasa soyayyar mutuwa murus. Ya tuna 'yammata biyu da farouq ya takura ya hadasu.....abinda dukka ya rabasu dashi shine lack of caring. Sometimes ma mantawa yakeyi da babinsu,koda kuwa ta hanyar tura tex bare kira bare aje gayin tattaki zuwa gidajensu. Da kansu suka fahimta baida lokaci,suka kuma samawa kansu salama zancan ya mutu murus,shima suka shafa masa lafiya.
A hankali kekenapep din ke gangarawa da ita layin gidan malam din,ya kuma tsaya daidai gidan.
"Na gode......kana iya tafiya,gobe idan Allah ya kaimu zan nemeka saimu qarasa komai,ka gaida ummaah da kyau"
"Zataji in sha Allah....tace zatayi tattaki da kanta don miki godiya". Murmushi kawai ta saki tana sauka daga napep din,idanunta kan muhallin da malam ke bada karatu. Ba jamaa wajen,ta kalli agogon hannunta,da sauran lokaci akan lokacin daya saba xama,sai ta taka a nutse tana wucewa cikin gidan.
Kamar kullum ta taras da rumasa'u tana aikace aikacen gida,matar malam na daga rumfarta a zaune tana tsince busashen zogale.
"Maraba da diyata" Ta fadi cikin fara'a da murmushi tana sauke farantin zogalen daga cinyarta gami da karkade zaninta da ya d'an baci da kadan. Har qasan zuciyarta kuma tana jin dadin dawowarta da wuri,ba kaman wancan karon ba data tafi ta jima bata waiwayosu ba.
Itama tata fuskar da murmushi tare da jin dadin yadda aka samu wasu halittu da suka damu da rayuwarsu ta qarasa shiga cikin rumfar,bayan ta zame halfcover din qafarta
"Aah.....ina sauran jikokin nawa?" Ta furta tana duban bayan sabreen. Murmushi ta saki tana zama saman shimfidaddiyar daddumar da matar malam din ta shimfide mata
"Ba daga gida nake ba gwaggo" Ta fada Kaman yadda taji rumasa'u tana kiranta wani lokaci.
"Kash.....to ai naso ganin kishiyata haneefa ne ai" Ta furta tana dariya tare da yunqurin miqewa
"Itama kullum zancanta kenan.....amma zan kawosu na kusa in sha Allah"
"To Allah ya yarda" Ta amsa mata tana bude fridge din dake ajiye a rumfar gaban falonta ta ciro mata ruwan pure water me matsakaicin sanyi da lemon zobo,rumasa'u ta hado da kofi ta shigo mata dashi.
"Nima inata sanya ido naga huda" Ta fada tana murmushi. Kiran sunan hudan ma ya sanya hankalinta dawowa kan huda din data barosu gida.
"Zasuzo in sha Allah rumasa'u" Ta amsa mata cikin kulawa.
Zama tayi suna dan taba hira,tana son su sabreen yarinyar,wanda su kansu basusan dalili ba,saidai ba ruwan ubangiji shi yakan sanya qauna da jituwa tsakanin bayinsa a duk sanda yaso hakan ya kasance.
"Hala malam baya nan?" Ta tambayi gwaggo
"Yana nan,yadan fita ne kasuwa,amma da wuri yau din zai dawo,yana da karatun dare na manya da yakeyi". Kai ta jinjina,tana jin dole zata jirashi har ya dawo,duk da tanason komawa gida da wuri,don a yanzun hankalinta bai bata ta dinga nisan kiwo ba.
Jikinta da zuciyarta sun gaza samun nutsuwa sam sam akan huda,cikin jikinta takejin akwai wani abu ba daidai ba.
Iya yadda tayi magana da ita dazun kawai ya isa gaya mata akwai wani abu,saita rufe babin wannan tunanin tana maida hankalinta tsakar gida hadi da taya su gwaggo amsa sallamar malam din.
*Tsaye yayi kawai gaban madubi yana duban fuskarsa da kyau tare da son bawa kansa qwarin gwiwa. Yana buqatar cikakkiyar nutsuwa da kuma qarin tattara dukkan wani tsohuwar fasaha da qwarewarsa wajen ganin ya cimma nasara a cacar. Tunda yake bai taba caca mafi hatsari ba irin wannan. Caca ce da zata iya zuwa masa da sakamako guda biyu......nasara wadda zata wankeshi daga dukkan wani rudani da tashin hankali.....ko kuma faduwa wadda daidai take da daukan guduma ta kuma tarwatsa rayuwarsa gaba daya.
Hasashen sunan faduwa kawai sanyawa zuciyarsa wani irin mugun bugu yakeyi,tuna sunan FADUWA kawai sai yaji kaman qirjinsa zai tarwatse,don haka a yanzu da yake tsaye gaban madubin ya daga murya don baiwa kansa da kansa tabbaci tare da qwarin gwiwa
"Ba faduwa a hanyata,tabbas nike da nasara......ni zan cinye!" Ya fadi da wani irin qaraaji yana sake sanyawa ransa nasarar da gaske tasa ce.
Qofar aka dan qwanqwasa,ko ba'ayi magana ba yasan waye,don haka ya waiwaya yana fadin
"Gani nan,tayar da mota" Sai ya juya ya dauki waya da maqullansa ya fito.
Baice da mato komai ba ya bude gaban motar ya shige,mato kuma ya bawa motar wuta,ya danna hon me gadi ya dage musu gate din suka fice.
"Ina fatan yau baka shawu ba" Mato ya fada yana sake bawa motar wuta saman kwalta. Harara ya waiwaya ya maka masa kafin yace
"Mahaukaci ne ni?,idan nasha ta yaya zan samu isa ga abinda nakeso?,......zan shawu iya shawuwa bayan mun dawo da talin himilin kudin da zan cike gibin asarata". Kai mato ya jinjina yana dan dukan steering
" Inaji a jikina kam wannan nasarar tana hannuwanka......munkaila me da'ira?.....ka manta sunan naka ne?". Wata wawiyar dariya ya saki,sunan da mato ya tuna masa ya sake jinsa cikin alfahari......wani rubutaccen suna ne daya samoshi daga wajen abokan cacarsa. Muddin zai hau tebur din caca to ko kai waye ka zama nama,baisan iya adadin abinda ya tara ba da dukiyoyin al'umma shekara da shekaru,sai yau gashi dare daya wata qaqqarfar guguwa tanason yin gaba da tsohon arziqinsa?......inaaaa......ai bazaya bari ba,sai inda qarfinsa ya qare. Iya sunan da mato ya gaya masa ya sanya masa qarin karsashi tare da jin dokin isa wajen.
"Ni kaina inaji a jikina lokacin nawa arziqin ya gabato,don gagarumar caca ce ina gaya maka me gida.......tsaffin 'yan caca za'a zuba wadanda suka sanya kudi masu ciwo......don Allah banda ganganci ina tsohon hannu zai kara da sabon jini?,yaro masanin dabaru da siddabarun kayar da mutum?"
"Tsautsayi ne mato" Ya bashi amsa wani murmushi yana subuce masa,don nasararsa kawai yake hanga muraran.
Tafiyar mintuna kadan suka isa gidan cacar,tun daga waje ya fahimci gidan a cike yake,abinda ya sake tabbatar masa da maganar mato. Ya fito a motar yana murmushi suka jera da mato zuwa ciki yana sake bashi bayani akan komai.
"Amma me gida......nayi mamaki da me jadda bai nemeka ba".
"Har gwara ya nemeni da wannan shurun da yayimin......shirunsa yana nufin komai mato......shi yasa nake bidar nasara a wannan karawar.......daga nan wajensa zankai kaina ayi a gama......bani da tabbacin a yanzun baida masaniyar inda nake.......tsaf yana sane da motsina duka zai iya yiwuwa". A mamakance mato ke duban mikail,tsoron girman izza da qarfin ikon Muhammed jadda tana sake saukar masa,saidai bai samu cewa komai ba suka qarasa ciki.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 81
Daga yadda yaga wajen ya sake amanna da maganganun mato din. Duba daya ya fahimci tabbas masu tsohon arziqi da kudin caca ne,kuma da alama a yau din kowa cikin buri yake,hakanan kowa yayi guzurin dukka wata dukiya da yake alfahari da ita.
Saura kadan dariya ta fashe masa,don dukkaninsu shi a nasa idanun kallon gidadawa yake musu,kuma cinyayyu da zasu qare wasan cikin hasara da rashin nasara.
Su biyu rak ke zaune daga wata kwana cikin farfajiyar wajen. Kawu kenan,wato kawu sama'ila shi da nasa aminin barau.
Cikin nutsuwa da shegen kwanyar da yake dashi yake karance mikail da idanunshi sunkai kan kawo amma banda kan kawu din. A nutse yake karantar mukail,har zuwa sanda suka zauna da'irar da za'a zuba caca ta farko.
"Me ka karanta ne sama'ila?,kayi shuru ko ka fasa ba zaka buga wasan ba?" Murmushi kawu ya saki yana tura hularsa gaba.
"Tun bayan mutuwar yaya daya haramta min yin caca,ban qara zama gagarumar caca irin wannan ba.....inaji a jikina silar arziqina ne yazo.....bazan zauna ba har sai naga iya nashi takun......baka ruftawa wasa baka san yanayin hannun kowa ba"
"To me ka fahimta sama'ila?" Barau ya sake tambaya idanunsa akan yadda wasan ya fara tafiya
"Dan zamani ne fa wannan da zai kara da tsaffin 'yan wasa......gogagge ne kana kallonshi,kuma shima qwararre ne da irin tasa qwarewar,wanda idan kowa baiyi takatsantsan ba komai zai iya faruwa"
"Shege sama'ila" Barau ya fada yana qyaqyacewa da dariya
"Ka zuba ido kawai kayi kallo" Ya amsa masa yana maida hularsa daga gaban goshi zuwa qeya.
A duk sanda yakeson samun nutsuwa ta qwaqwalwa da ruhi sararsa shine kwanciya,ya rufe idanunsa yayi kuma shuru a waje da muhallin da ba hayaniya ko kuma motsin kowa. Ko yanzun hakan yayi cikin office din,saidai qarar wayarsa ya sanyashi miqa hannu ya lalubota don yasan ring din na daban ya sakawa kiran don kirane da yake buqatarsa
"Sir........yana gidan caca na green card"
"Good" Ya fada a nutse yana bude idanunsa
"Don't let him go.....ina buqatar information na wuninsa na yau gaba daya"
"Yes sir" Ya furta cikin girmamawa. Wayar ya ajiye,sai ya miqe a nutse ya zauna ranshi na wani mahaukacin baci. Ga wani zargin ya sake shigo kasa akan mikail yanason kore uzurin da zuciyarsa keson bashi. Muddin ya kuskura bincike yazo masa caca yayi da kudinsa na halal tabbas!,zai nuna masa ainihin kalarsa......zai gane waye zahirin muhammad jadda. Dukiyar da aka tarata da gumin halak?,dukiyar da ake takatsantsan wajen jefa haram a ciki komai qanqantarsa?,kudin ruwa da ruba dukkaninsu haramtattu ne a cakudasu cikin dukiyarsa,amma yau din zanyi ganganci ko kuskuren zarar halalinsa ya jefa a qazantaccen guri irin wannan?.
Tsam ya miqe,sai ya koma saman table dinsa ba tare daya sanya takalma a qafarsa,ya kunna system dinsa ya tattara hankalinsa akai.
Karo na kusan goma barau ya kalli kawu sama'ila kaman yadda mato ke zaune yana murmushi daga gefan mikail yana kuma tayashi lissafin maquden kudade da dukiyar da yaketa cinyewa ta abokan bugunsa.
"Sama'ila?,dama wannan shine hasashen naka?". Murmushi kawu ya saki yana karkacewa kaman abun ya masa dadi
"Gaskiyar kenan barau.....amma barshi ya gama iya tasa dabarar......uwayensa na nan zuwa su koyar dashi darasi" Wata dariya barau ya saki bayan ya gama fahimtar abinda kawun yake nufi
"Yanzu naji batu,amma ta yaya muna da kai zaka bari wannan jaririn yazo gidanmu ya cimu wasa?" Murmushi ya sake saki idanunsa akan mikail daidai sanda ya cinye alhaji wada miliyoyin kudi
"Talala ce me kaman sake.....barshi ya gama karbarmin kudaden tukunna da gidajen" Dariya barau ya sake saki harda buga qafa.
Cikin awa uku ya daurewa kowa jijiya a wajen. Cikin tumbatsa da izza mato ya miqe
"Akwai wani sauran wanda zai kara da sarki?" Yayi shela yana ji a ransa sun gama da kowa,babu me sauran motsi. Shuru ne ya biyo baya,sai ya sake maimaita tambayar yana duban kowa d'ai d'ai
"akwai" Barau ya fada da qarfin murya. Mato da mikail din duka suka waiwaya suna duban kawu dake qurya,sai suka dubi juna tsakanin mato din da mikail
"Waye kenan a cikinku zai shiga?" Tsam kawu ya miqe yana nuna kansa
"Nine" Ido suka hada sai suka bushe da dariya tsakanin mato da mikail
"Qaraso mana dattijo....koda yake ba dattijo a nan......inajin akwai rabona a jikinka ne kaima.....ko giya ta kwana daya na sha da canjinka". Boyayyen dariya kawun ya saki,ya fara takowa zuwa wajen kowa ya zuba masa idanu yana mamakin qarfin halinsa,kamar ba'a gabansa aka cinye kowa ko ba amma shi zai jefa kansa?.
"Dame zaka shiga?" Ya jefa masa tambayar a raine. Karkacewa yayi ya zaro wasu takardu yana dubansu. Takardun dake dauke da sunan alhaji aliyyu ahmad zaki......mahaifi ga sabreen..... Takardar dake matsayin mallakin magadan kuma marayan yaran da yayi Qundumbalar shiga cacar da ita,cikin jin cewa zata ciyo masa tarin maquden kudaden da zasu zame masa silar arziqinsa gaba daya.
Saman teburin ya aza takardar yana kallon mikail,hannu ya sanya ya dauka ya duba ya karanta ya kuma tabbatar original ce wanda gidan ya haura miliyoyin kudi
"Ashe.....kudinka baaba ai ya haura 'yan canji ma ai.......idan na samu nasarar cinye gidan nan ko?,rusheshi zanyi na maidashi gidan shaqatawa,ayita shigomin da 'yammatan unguwa ina hutawa dasu ina biyansu".
Wani abu ne ya cakewa kawu a rai,ya tsani zina,ya tsani harkar neman matan banza,kaman yadda ya tsani shaye shaye,barshi kawai da cacarsa data zame masa masifa wanda dama tana da shiga jiki. Kai tsaye yaji tsantsar cin fuska ce ya tanadeta zaiyi musu wannan ya sake aza wutar qaimi a zuciyarsa,ya karkace kaman yadda yakanyi a yanayi irin wannan,ya kalli Mikhail da kyau
"Idan dai har ya zama mallakin naka kana da wannan damar" Ya bashi amsar da wani irin kakkaifan kallon dake gaya masa kai tsaye na SAI NA BAKA DAMAR CINYE GIDAN SANNAN ZAKA AIKATA HAKAN.
Izza da jin cewa zai samu nasara akan kawun ya sanyashi ninka abinda kawun ya zuba shima ya zuba cikin cacar aka fara buga wasan. Tashin farko kawun ya maido takardun gidan yayi tafiyar ruwa da kudaden da mikail ya zuba,abinda ya jawo hautsinewar wajen,hankula dukka suka komo wajen,aka fara yo dafifi,wadanda aka cinye suke alhini dukansu karsahinsu ya dawo,sai aka fara zuba sabon wasa.
Da daya da daya ya dinga zuba abinda ya ciyo kawu sama'ila yana kwashewa. Duk abinda ya zuba kawun ya cinye shaidan zuciya da kuma mato saisu gaya masa ya sake zuba wani,zai iya yuwuwa ya samu nasarar dawo da abinda aka cinye masa a baya.
Tafi tafi cikin qasa da awa biyu sai gashi yana tashi daga Mikhail me manyan kudi yana komawa asalin mikail dinsa kaman yadda ya shigo wajen. Cikar awa biyu cif komai ya qare!.kawu sama'ila ya wawushe duk wata kadara daya cinyo daga wajen wasu