Showing 165001 words to 168000 words out of 209775 words
dinsa. Yanaso ya sani,yanason yayi bincike ta yadda komai zai tafi masa a daidai.
Cikin qasa da awa daya komai ya fito masa yadda yakeso. Ainihin wanda kudin suka koma account nashi daga account din wanda aka bawa ajiyar sunanshi ya fito baro baro da taimakon shigabannin bankunan da dukka suke amfani dashi,wanda yakan nemesu idan buqata irin haka ta taso
"Rufa'i ahmad mu'azzam" Ya mamaita sunan yana zuba masa idanu.
"Wayeshi?" Amsar da bashi da ita,babu kuma me bayar da ita sai mikail,kasantuwar hakan kuwa ya zama tilas a gobe mikail ya miqo kansa ko kuma shi yasa a kawo masa shi.
Kadan yadan daki table din,sannan ya sake jawo wayar gefansa ba tare da duba da yadda dare yayi ba. Duk da daren hakan bai hana a daga wayar ba da bugu daya tak.
"Barka da dare sir" Aka furta da muryar dake nuna kiranne ya tasheshi daga bacci
"Barka abdus_samad....i have a work for you"
"Okay sir...." Ya fada yana watsakewa daga baccin nasa.
"Zan tura maka through email then sai muyi magana.....but ina buqatar bayanan as soon as possible"
"Yes sir" Ya furta cikin matuqar bada girma.
Kiran ya katse don duk wani abu me muhimmanci ba kasafai ya fiya magananshi ta waya ba,duk da layinsa yana da tsaro sosai......to amma ya sani a kowanne motsi akwai maqiya abokan gaba da abokan burmi.
Komai ya tura masa,sai a sannan yaji idanunsa sun fara yaji yaji alamun suna da buqatar bacci,dole ya tattare komai ya tafi ya kwanta don yana da buqatar ya qarasa hada abinda dukka ya rage masa a gobe tunda jumaa bai fiya fita office ba,koda ya fitan baya dadewa sosai,ga kuma alqawarin tafiya abuja da ya yiwa farouq. Bayason ya sake karya alqawarin,duk da yasan farouq zai fahimceshi zai kuma bashi uzuri fiye da yadda yake buqata ma.
A wannan yanayin kawai yaji ya kamata ya fara amfani da private jet dinsa,sai ya lalubi me haqqin kula da zirga zirgarsa ya tura masa bayanai sannan ya ajiye wayar yana nufar qofa bayan ya kashe komai ya kuma kwashe komai da yake da buqatar fita dashi.
*******Duk wani motsi nata saman idanun sabreen din take yinsa. Tana sake karantar duk wani yanayi na huda din. Zuciyarta na sake tsinkewa yana kuma saukar mata da fargaba hakan. A duk sanda zatonta da zarginta ya bata akwai wani ne a rayuwar huda din?. Abu daya dake sake gigita tunaninta da sanyata jin ya zama tilas ta nuna nata salon maganar nan da ake cewa duk wanda ya rigaka kwana dole zai rigaka tashi.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 85
Ba wata kalma data sake hadasu da ita,har suka kammala shirin makaranta,ta dauki jakarta kaman kullum,ta kuma fidda kudin transport dana break. Wannan karon nadra ta miqawa a maimakon huda
"Ki kula sosai nadra......ana tashi kada ku tsaya ko ina"
"to adda" Ta amsa mata tana kama hannun haneefa suka fara takawa zasu fice.
"Nifa?" Huda da ta kasa fahimtar abinda sabreen din tayi ta tambayeta. Kai ta daga a nutse ta watsa mata kallo. Sai ta janye idonta daga kallon da takewa sabreen din saboda yadda idanun sabreen sukafi nata kaifi.
"Na dakatar da zuwanki makaranta" Amsar data bata kenan ta miqe,amsar kuma data girgiza huda din.
Ta dakatar da zuwanta makaranta kamar yaaya?. Dakatar da ita daga zuwa makaranta fa kenan yana nufin yankewar ganinta da bassam?. Idan haka ta kasance kenan sunyi bankwana da bassam?,saidai ta zauna ta zuba idanu tana ci gaba da rayuwa cikin wannan quntataccen gidan nasu da babu farinciki ko guda daya a cikinsa?.
Bata sake bi ta kanta ba,dole kuma data gaji da tunanin taja qafarta tana komawa cikin dakin,yayin da sabreen taci gaba da kai kawo tsakanin falon da dakin,tana shirya zata kasance da huda a dakin tsahon wuni da kwanakin da zasu biyo baya. Ta tabbatar idan ta lazimci hakan dole koma meye huda take boyewa ya fito fili.
Tayi juyi tayi tayi juyi har batasan iyaka ba. A duka hukuncin abinda yafi damunta shine yanke mata qofar fita. Fitar da itace hanya guda daya da zata bata damar samun bassam ta kuma shaida masa sabon dokan da adda sabreen din ta kafa mata. Ta yita zuba ido taga ko zata fita?,saidai yau qiyau miyau,banda toilet data fita tayi wanka ta dawo ba inda taje,haka suka wuni tana sabgoginta don ko tayin abinci batayi mata ba,sai data gaji don kanta tana rara gefe ta fada kitchen din ta diba taci ta koma taci gaba da kwanciyarta.
Ko da akayi sallar isha'i tana jiyosu a parlor suna assignment da sauran bitocin karatunsu kaman yadda suka saba. Ba wanda yabi ta kanta a tsakanin su ukun. Gaba daya dakin dama gidan ya sake gundurarta ya kuma fice mata a kai. To wai shin ita adda sabreen dakeyi mata haka?,ita waye ya takurata haka?,waye ya dameta haka?,kullum Allah shike da kullum sai ta sanya qafa ta fita waye ya taba dakatar da ita ballanta ya sanya mata dokar fita.
Miqewa tayi ta zauna bakin gadon nasu tana jan qaramin tsakin baqinciki. Tana masifar son gadonta da jin dadin kwanciya akai,amma yau gaba daya sai taji ta tsaneshi ya kuma fice mata a kai.
Wayarta dake haske ta jawo ta buda tana dubawa. Wayar na cikin personal wayoyinta da ba kasafai take bari saqo ko kira a ciki ya wuceta ba.
"Kina da tafiya on Saturday da mushkur......ina fata baki manta ba?" Saqon da jib ya tura mata kenan.
Yatsunta ta cusa cikin sumarta tana yamutsawa kadan kadan. Har cikin jininta taji batason tafiyar,komai kuma ya fice mata a kai,to amma batasan dalilin da ya sanya wani sashe na zuciyarta ke zugata yana gaya mata BAI KAMATA TA BARI MASHKUR YACI BULUS BA,KODA DAGA KAN MASHKUR TA RUFE QOFA YA KAMATA YA DANDANI DACIN QWACE ABU DAGA HANNUN ME SHI.
Idanunta ta juya ta kalli sashen dasu nadra ke zaune. A irin wannan yanayin ma da take qoqarin fuskantar inda rayuwar huda ke neman dosa,sam sam bata qaunar tayi nesa da kowannensu don sanya ido akan motsinsu
"Ko ta buqaci friday?,gajeriyar rana ce......sannan kuma tana da tabbacin zai wahala ta rasa ticket din juyowa a ranar" Tayi zancan cikin ranta,don haka ta soma rubuta tex tana turawa kowa tsakanin mashkur da jib da zai kula da komai.
Kamar jira akeyi ta kammala muryar ta mamaye ilahirin tsakar gidan nasu. Da wannan madaukakin sautin nasa da babu komai ciki face takura wulaqanci da kuma saukar azal akan duk wanda ta ratso dashi.
"Yau kuma akan waye da waye ta fada?" Ta fada qasan ranta,don tasan wajibi sunanta a sahun farko. Bai taba shigowa gidan ya fita salin alin ba tare daya takalo wani abu da ita ba,wannan ya sanya ko yaushe take shiryawa zuwansa da ko wanne irin yanayi ma zayazo dashi.
"Kowa da kowa ya fito,maza da mata,yara da manya,yau dai Allah yayi arziqin me arziqi ya dawo......rabon bawa da arziqi mutuwa......Allah ya lamuncemin nima......ku futo yau arziqin rufa'i ya dawo,wanda yayi biyayya aci dashi,wanda kuma ya bijire saidai yaga ana ci" Ya qarasa maganar yana bin dakunan da qofofinsu suke a rufe yana bubbugawa.
A nutse ta maida idanunta kan su nadra da suma ita suke kallo. Tana iya hangen wani boyayyen murmushi akan fuskar nadra din,da alama idan so samu ne tanason fita ta ganewa idanunta kamar yadda ya gayyaci kowa ta kuma fara jin alamun suna fita din,don muryar bibo har nan inda suke muryarta zaqwai tana karadi. Batasan me yasa duk gidan nadra tafi kowa maidashi kaman kakanta ba. Ada muguj balain tsoronsa sukeyi,amma yanzu kwata kwata bata tsoronsa. Duk sanda ta kwasheshi idan yana tambotsansa ya dinga zaginta kenan amma ita ko a jikinta,hasalima dariya take binsa da ita,yayi dukan yayi dukan sabreen tayi fadan amma ko a hancin takalminta
"Kada wanda ya motsa,ku gama aikin da yake gabanku" Ta dan hade rai tana fada. Idanunsu suka maida kan litattafansu suna ci gaba da aikinsu,saidai daga ita harsu kunnuwansu yana tsakar gidan suna tsintar wasu daga kalaman kawun.
A qalla ya kusa mintuna arbain da shigowar gidan kafin suji an banko qofar dakinsu.
"Barin hali sai mutuwa,miskili kafi mahaukaci ban haushi....halin ne ya motsa ko baqinciki ake da komawata mawadaci?" Ya qarasa maganar sanda yake sako jikinsa cikin falon yasha shadda dinkin babbar riga da 'yar ciki yanata bazata.
"Ko daya kawu......ina maka murna.....amma Allah dai yasa ba daga aikin da abban ya hana bane...." Tayi masa shaguben data tabbatar kaf jama'ar gidan ba wanda ya isa ya gaya masa hakan,wasu saboda tsoronsa wasu kuma saboda kwadayin abun duniya.
"Sannu ja'ira maras kunya.....ke harni zaki gayawa haka?,yo dani dake waye zaiwa wani gori?,Allah na tuba ba har gwara nawa kudin ba gwagwarmaya da fargaba nasha na kuma zuba nawa jarin kadan suka jawomin masu yawa?,ke nawa kika zuba kike samun naki kudin?" Ya fada cikin bambamin daya sanua huda dake daki kwance yin bakam tana jinsu,maganar kawun kuma ta sake tsaye mata a rai tare da sake jin wani baqon yanayi akan sabreen din da yafi kama da haushi haushi da son shinfida tata rayuwar......ita da aure ma zatayi?.
A hankali ta sauke idanunta zuwa wayar hannunta,maganganun kawun suna mata wani irin daci cikin zuciya har zuwa saman harshenta. Ba wannan bane karon farko daya jefeta da magana irin wannan ba muddin zata sako masa zancan caca.....amma wannan din yayi mata zafi ne saboda ya ambata tsakanin su nadra da huda da taketa qoqarin gano bakin zaren matsalarta.
"Kome meye dai sama'ila ya shallake......ba kuma zai sake zuwa tambayar komai a hannun kowa ba.....kuma daga yau har na mutu sunana mawadaci.....munyi hannun riga da talauci" Ya qarasa maganar yana wara hannayensa kaman me jiran wani yazo ya rungumeshi.
Sai daya gaji ya sauke sannan ya gyara zamansa yana sake kallonta
"Yauwa......batun kudadenki.....zuwa nayi muyi lissafin abinda kk taba bani na rage.....don bazan iya biya duka ba domin kuwa tattalin dukiya akeyi yanzu......yauwa". Badon yanayin daya jefa zuciyarta ba tabbas murmushi ne zai qwace mata,amma a yanzun sai kawai ta dubeshi ta dauke kai
"Bana buqatar komai a ciki.....hasalima dama kyauta na baka ba bashi ba" . Washe baki ya fara yi yana shafa habarsa
"Aah......kaga farar diya irin albarka.....diyar da babu kamarta kaf haife haifen da ahmadu yakeyi baiyi kamar taki ba har yabar duniya.....Allah dai yashi miki albarka" Ya fada yana sake sakin dariya.
"To ni zan wuce......sai kunzo ganin hamshaqiyar fada ta tarewa nan kusa da kuma qarin auren mata ta biyu". Kadan ta dubeshi,saita kasa cewa dashi komai,har ya juya ya fice yanata sakin qarin bayani.
Hannu ta sanya ta dafe goshinta kadan,abubuwa da dama suna mata kai kawo saman zuciyarta. Kwata kwata DUNIYARTA bata jinta daidai bata kuma kallonta daidai da duniya kowa. Akwai abubuwa da yawa da takejin suna ba daidai ba cikin rayuwarta......WAI SAI YAUSHE KOMAI ZAI DAIDAITA?.
_Tambayar data yiwa kanta kenan da bata da amsarta,wadda batasan wannan din shine MAFARI na komai ba_
*******K'arfe goma na safe ne sanda yake takawa cikin farfajiyar gidan nasu. Sanye cikin farin lallausan yadi daga lallausar auduga mafi tsada da daraja.
Fari ne qal yadin maras nauyi dake iya bayyana shatin fara qal din vest din jikinsa sama sama. Kusan komai da yayi amfani dashi a yau din fari ne,tun daga sutura takalmi da agogon fata me tsada dake daure a tsintsiyar hannunsa. A irin wannan rana ma ta juma'a motor din hawansa yakan canza zuwa fara duka don sabunta sunnar ta'ammali da farin abu.
Hularsa tana hannun me sunan malam dake tsaye daga gefe bayan ya karbi news paper din daya kammala dubawa. Ameh ya sallama daya biyoshi da tray din teen da zaitun da kuma jan inibi da bai zauna yaci ba,ya juya yana duban me sunan malam
"Ka shiryamin zama da shugaban gidan jaridu a gobe.....don yau din zamuje abuja.....but zuwa yammaci zamu juyo"
"Okay sir" Me sunan malam ya furta,sai fu'ad din ya sanya hannu ya karbi hular ya juya yana nufar qofa,abinda ya sanya duka guards dinsa tsaiwa don sunsan inda zashi,mutum biyun daya saba tafiya dasu sukabi bayansa.
Dab da zai fice a gate din farko yaji tana qwala kiran sunansa da shagwabar na tata
"Hamma......hamma na". Tun kafin ya waiwayo murmushi ya subuce masa duk da bai shiryawa hakan ba. Yasan zaisha qorafi saboda haduwa da tayi wahala a tsakaninsu a kwanan nan.
Barin hali inji hausawa sai mutuwa,tana isowa taja tunga kuwa tana tura baki gaba
"Hamma.....kace kada na yarda da abinda BB farouq ya fada......kuma ni Allah alamun nake gani". Wani lafiyayyen murmushi da ba kasafai ake katarin ganinsa saman fuskarsa ba ya saki yana juya fuskarsa dama da hagu kafin ya tsaida dubansa saman fuskarta.
"Amneeen hamma amneen anni......zaki yarda magauta su rabamu?" Kai ta girgiza da sauri tana sake fuskarta qasan ranta kuma tana fata inama saddiq yana kusa yaji yadda hamma yake ji da ita.
"Kwana biyun nan school ya saki gaba.....nima duka aikace aikace sun tasomin......ko bakison mu bude company n jewelry sample din farko da zamu fara fiddawa ya zama naki......kinsan sunan da zamu bawa brand din?" Kai ta sake girgizawa cikin tsananin jin dadi
"To sai kin kawo cin hanci zan gaya miki" Yayi maganar yana juyawa tare da ci gaba da tafiya.
Da hanzari ta tattaka ta cimmasa sukaci gaba da tafiya tare
"Please hammana.....ka gayamin cin hancin me kakeso?,kome kakeso hamma zan bayar"
"No....ki canka da kanki kawai ki bada din sai na gaya miki" Shuru tayi tana zurfafa nazarinta na abinda ya dace ta bashin,dab da zasu fice a gidan tace masa
"Yauwa.....hamma........zanyi maka mata ka huta da gorin yaa farouq akan kaqi nemo mata......na baka friend dita nasreen...." Dan rage speed na tafiyanshi yayi ya waiwayo yana jefa mata harara da fararen idanunsa.
Ya yarda autanci da kuma quruciya suna damun amna din da gasken gaske,da alama fa da gaske take,don daga yadda tayi masa maganar tana zumudi tare da jij ta masa bajinta kadai zai gaya maka iya gaskiyarta kenan.
"Wannan ba cin hanci bane......saidai ma ki jawo komawa ta biyu da za'a bawa product din" Hannu ta sanya tana rufe bakinta gami da zaro ido. Sai yanzu ta gane tayi wautar,ta tuna sunanshi da farouq ke gaya masa,ta kuma tuna shi lamarin yin budurwa ko zancan aure abune da bata taba gani ya zauna ya bashi muhimmanci ba.
Kunnenta ta kama daidai sanda suke isa qofar gidan wanda sam bata ma kula da gidan da suke nufa din ba saboda yadda hankalinta ya dauku
"Am sorry hamma.....please,wallahi idan ka fasa yaa saddiq zaiyimin dariya".
"Ki canza wani abun.......but this" Sai ya girgiza mata kai yana maida dubansa ga muhallin malam Sa'adu wanda bai ganshi wajen ba da alama ko ya zaga ne.
Tun daga shigowarsu gidan har takowarsu farfajiyar gidan idanunta yana bisa kansu. A yadda tasan hali da dabi'arsa ya akayi yarinyar ta samu sakewarsa har irin haka?,anya abinda take tunani kowanne dare kuwa bazai afku ba?.
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
PAGE 86
Ita kuwa ta yaya zata bari wani abu ya hada zuri'arta data hajiya amina?. Muddin da rai da ruhi da kuma numfashi a gangar jikinta.... Koda zata rasa komai data mallaka.......koda shine abu na qarshe da zata aiwatar cikin rayuwarta ba zata taba bari wannan tunanin ya wanzu a kwanyar kowa bama bare akai ga haifar tunanin a zahiri.
Labulenta ta saki zuciyarta na mata wani irin suya. Kwanaki biyu kenan suna sanyata yin asarar komai data shirya domin su. Yaune cikar kwanakin da bokan ya diba mata,muddin a yau ma nasara ta qwace mata to lallai zancan bokan ya tabbata na cewa aikin