Showing 129001 words to 132000 words out of 132995 words
ba.
A hankali ya ɗan juyo ya kalli TV'n sabida ganin program ɗin da Jannart tayi dashi ake haskawa.
Idanunshi ya zubawa rubutun dake tafiya kasan hotonsu mai motsin da yake fuskar TV'n.
*Daya daga cikin ma'aikatan wannan ma'aikata Mai gabatar da shirin Baƙon mako mai suna Jannart idi Saleh Dakata ta bata tun daren jumma'a, kana har yau babu ita babu lbrin ta, a madadin tashar Arewa 24 TV muna cekinta Tata ga duk wanda Allah yasa ya ganta ko yaji lbrinta, ya taimaka ya nemi ɗaya daga cikin wadannan numbers din... akwai tukuici mai girma ga duk wanda ya kawo ta ko lbrinta kimanin Naira million 5. Muna addu'a Allah ya baiyana ta ya kuma bawa mahaifinta lfyar jikinsa wanda sanadin batanta ya tada masa ciwonsa*
Wani irin numfashin ya fesar a hankali tare da mai-maita karanta rubutun a karo na barkatai.
Can cikin zuciyarsa yake nazari.
“Tabbas akwai gadar zaren da ake sakawa, wanda ake neman mai ruftawa a ciki.
Dole suna da manufa a kaina.
Amman manufar Barrister Kabir tafi ta kowa girmama a kaina, tabbas ba haka kawai ya zaɓeni ya lika min wannan mayataccen aurenba, nasani haƙƙun nasan akwai wata boyeyyiyar manufa da niyarsa ta liƙamin auren ya kawo diyarsu ya ajiye mana a cikin gida.”
Idonshi ya lumshe tare da buɗe kana yaci gaba da nazari.
“Wani wasane suke son bugawa dani, yarsu ta zamo yar leken asirinsu kenan itace zata basu duk wata damar cimma nasarar turani kan gadar zaren da suke saƙamin ko meye.
Itace mai iya buɗe musu kofa ta su shigo rayuwata.
Meyasa Abba na bai gane hakabanba ya akayi Abba na yayi saurin yarda dasu?”.
Numfashi mai nauyi yaja ya sauƙe tare da yin kwaffa.
Wanda sanadin hakane su Ramadan suka gane ya shigo.
Kallonsu kawai yayi tare da amsa sannu da dawowan da sukeyi masa.
Idonshi ya kuma maida kan TV inda ake haska fuskarsa data Jannart.
Batare daya ce musu komai ba, ya wuce zuwa dakinsa.
Yana shiga ya soma rage kayan jikinsa, tare ci gaba da nazari.
“Me Barrister Kabir yake nufi dani? Alhaji idi Saleh Dakata dai ɗan uwansa ne uwa ɗaya uba ɗaya.
Kana ita kuma wannan Jalila ne ko jalilu ne, yarsa ce ta cikinsa.
Haƙƙun Barrister Kabir medani tsanin hawa yake son yi!.”
A hankali ya tura ƙofar shiga toilet.
A fili yace.
“Me yasa Abbana ya yarda dashi, ya akayi yayi saurin gamsuwa dashi.
Bayan kuma shine ya dauramu kan turbar kebanta kai da mutane da gudunsu da rashin yarda dasu.
Sanadin haka muka taso ba abokai ba kawaye bama sakin jiki da kowa, daga ni har Ramadan, sabida horaswar Abbanmu ta gudun mu'amala da mutane,
Yasha cemin.
Rayyern ɗan adam abin tsorone kada ka yarda da kowa, mutun duhun darene Allah kadai ke saninsa!
To ya akayi yayi saurin yarda da Barrister Kabir?
Tabbas shima Abba na akwai manufar yardar sa”.
A hankali ya ɗago ƙafarsa ta hagu ya sa cikin Bathroom din.
Hannunshi duka biyu yasa ya matse kanshi da ƙarfi.
Dan yadda yakejin kansa na jujjuyawa nazarurrukansu na hautsinewa suna haɗe zaren suna curkudeshi.
Duk da azabebben sanyin da akeyi.
Ruwan sanyin ya sakarwa kansa.
Sabida jin kan nashi ya fara sarawar.
Bayan ya fito ne kuma, ya shirya kansa cikin wasu tattausun kayan bacci.
Wondon iya guiwa rigar irin mai hular nan.
Fridge d’insa dake cike da kayan ciye ciye ya bud’e, Apple goran swan water da kuma ledan diary milk ya d’auko.
Tare da komawa kan gadonsa ya zauna cikin sanyi yace.
“Ta yaya zan yarda da ita, a wani sashin ma zan ajiyeta bayan nasan ita ɗin makamin magautanane sun turora cikin rayuwata ne dan cin nasarar kansu a kaina.
Meyasa Abba na bai fahimci hakaba.
Itama da mugun nufinta a ranta fa, iyayenta zatayiwa aiki”.
Yayi mgnar yana mai ajiye Jannart a sashin da yake ajiye magautansa a cikin zuciyarsa da rayuwarsa da waɗanda yake zargi.
A hankali ya jujjuya kansa.
Kana ya ɗan gatsi apple din ya soma ci bayan ya gama ne kuma, ya daura chocolate d’insa da ruwa akai.
Numfashi ya ɗan fesar
Kana ya kwanta yana mai nazari.
A nan asibitin Dr Lukman kuwa.
Barrister Kabir ne da Mom ke zaune gaban table ɗin Dr Lukman.
“BP'nsa ne ya hau sama sosai, sabida tashin hankali rashin yarsa.
Kana kuma rashin baccin da baya samun yi, sai nazari da damuwa yasa zuciyarsa ta kumbura.”
Dr Lukman ya ƙare mgnar yana mai yin ƙasa da idonshi sabida wani irin tsareshi da ido da Barrister Kabir yayi.
Cikin zubda hawaye Mom tace.
“Innallahi wa innailaihi rajiun, zuciyarsa kuma ta kumbura?”.
Cikin murje ido yace.
“Hakkun kuwa, sabida damuwa tayi mishi yawa, Jannart ta bata kana shima Junaid yana hannun hukuma, wanda kuma ƙaninsa uwa ɗaya uba ɗaya yasa aka kama ɗan nashi da wanne abu ɗaya zaiji?”.
Cikin haɗe fuska Barrister Kabir yace.
“Shine yace ma ni na kai Junaid hannun hukuma?”.
Da sauri ya girgiza kai alamun a'a
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
“Toh ka tsaya iya matsayinka, ka tabbatar da abu kafin kayi mgn”.
Yana faɗin haka ya mike ya fita.
Dakin da aka kwantar da Daddy ya nufa a bakin ƙofar shigowa yayi kiciɓis da Dr Sajo.
Hannunshi Dr Sajo yaja kana suka juya suka nufi parking lot.
Cikin motar Dr Sajo suka shiga.
Wani dogon numfashi Dr Sajo ya sauƙe kana a nitse yace.
“Dr Mina da Dr Lukman yayi aikin duba Alhaji tare da ita, ƙanwatace cousin sister na.
Na samu duk bayanin komai a wurinta”.
Da sauri Barrister Kabir yace.
“Dan Allah menene gskyan abun dake damun Yayana?”.
Kai Dr Sajo ya jinjina tare da yiwa Barrister Kabir duk abinda Dr Mina ta sanar masa...
A nan Office din din Dr Lukman Kuma Barrister Kabir na fita, itama Mom ta fita.
Ta koma wurin mijin nata.
Ba ji mawa Barrister Kabir ya dawo akan dole a sallami yayanshi zasu sauya asibiti.
Kuma dole haka akayi.
Aka medashi asibitin Dr Sajo.
Washegari.
Kamar dai jiya yaudinma Jannart ce ta-taya Mamy duk wasu aikace-aikacen gida, bayan sun kammala ne kuma suka zauna suna dan tab’a hira.
Kasan cewar yau Monday ne tushen aiki.
Yasa tuni Ramadan ya tafi.
Riyyam-nsra kuma Ahmad yazo sun tafi gidan Malam Mai-nasara.
Takwas saura kwata. Ya sauko falon.
Cikin shigar Suit red color masu masifar kyau.
Hannunsa riƙe da wayarsa yana mgn.
Cikin sauri ya kalli Mamy tare da cewa.
“Mamy na tafi”.
Kafin ma tace wani abu tuni ya nufi hanyar fita.
Kawai sai ta bishi da ido.
Har ya fita kuma sai ya juyo ya leƙe fuska ya kwaɓe tare da cewa.
“Mamy na tafi”.
Murmushi tayi dan dama tasan tabbas zai juyo muddin batace mishi.
Allah ya bada sa'a yayi muku al'baka.
Cikin sauri ya kuma cewa.
“Mamy zan tafi”.
Fuska ta tsuke tare da cewa.
“Ka dawo kayi breakfast”.
Cikin kwaɓe fuska yace.
“Mamy sai na dawo, kinga Ramadan keta kirana, wai akwai matar da aka kawo haihuwa yaƙi kuma dole sai anyi mata CS, dan Allah Mamy ce Allah ya bani Sa'a yayi min al'barka Please Mamy say something".
Ta sani in dai yace bazai ciba ko ta matsa mishi bazaici yadda take sonba.
Hakane yasa tace.
“Toh Babana Allah ya bada sa'a ayi aiki lfy rabbil yayi maka al'barka”.
Da sauri ya juya yana mai cewa.
“Yessss Mamy Amin Amin”.
Da ido ta bishi tana murmushi tana tuno wasu abubuwa masu tarin yawa.
Jannart kuwa dake cikin Kitchen tana wonke-wonke rumtse idanunta tayi tana mai jin yadda bugun zuciyarta ke harba a duk sanda sautin muryarshi ya sauka kan kunneta.
Duk da bata hangoshi ba, ita robonta da shima tun jiya da safe zuwan Barrister Kabir nanma bataga fuskarsa ba, kuma haka yanzuma.
Sai dai yanayin alaƙarsa da mahaifiyarsa yasata jin maraicin rashin tata mahaifiyar da jin bege.
Domin a gidansu babu irin wannan tarbiyar shaukin mahaifa da Kekkyawar shaƙuwar.
Haka dai taci gaba da aiki ita da Mammynsu.
Alhamdulillah komai yana tafiya dai-dai, domin Jannart ta samu nutsuwa acikin gidan.
Kasancewar yau tsawon kwananta biyar kenan da zuwan ta gidan.
Akullum kuma sabonsu k’ara-k’arfi yake, da Mamy, Ramadan da kuma Riyyam, harma kuma Abba da take samun kulawa awajensa sosai ta kuma take jin daɗin zama dasu.
Takan kalli Mamy matsayin Mom da Aunty Dijat dan duka biyu ta meye mata gurbinsu.
Abba a matsayin Daddy kana Riyyam-nsra ya meye mata gurbin Abdul Ramadan kuma gurbin Yah Azeez yayinda tasa a ranta cewa wato duk inda kake a duniya sai ka samu kalubalen makiyin dan gashi nanma Rayyern ya zame mata gurbin Yah Junaid a cewarta kenan.
Acikin kuma way’annan kwanki biyar din, sau biyu tak kawai Jannart da Rayyern din suka ga juna.
Tun gaisuwar da tayi masa ranan farko kuwa, wata magana bata sake hadata dashi ba tunda bazai amsa mataba a zatonta bazata kara gaidashi ba Dan matsalar kunneta yasa bataji amsawar da yayinba.
Rayyern kuwa kasancewar yau laraba, tun sassafe ya fita, saboda akwai wasu patients da suke da appointment din ganinsa.
Bashi ne ya dawo gidan ba kuwa sai 2:00 pm, inda ya tsaya yayi sallan azahar d’insa a Darul Hadith Masque.
Yanzun kuwa Shigowarsa Cikin gidan kenan, hannunsa rike da suit dinsa, ya murda handle din kofar falon ya shiga bakinsa dauke da sallama.
Mamy dake zaune ne ta amsa masa.
Ganin kuma yanda yake da'alaman gajiya atattare dashi ne yasa ta zuba masa ido.
Shikuwa k’arasowa cikin falon yayi, tare da zama akan kujera, idanunsa ya lumshe, kana cikin sigar shagwab’a da bayyanar tarin gajiya da yunwar dake cinsa yace.
“Mamy nagaji, kuma yunwa nakeji sosai.”
Ya ƙare mgnar yana juya kwayar idanunshi da sukayi jazir.
Ido Mamy ta dan zuba mishi cikin tausayawa tace.
“Badole kaji yunwa ba Babana, kwata-kwata bakason cin abinci, saika wuni ka kwana batare da kasa abincin kirki acikin ka ba sai kayan zaki da Fruits.”
Mamyn ta fad’i haka tana me K’are masa kallo, saboda har wani dan rama taga yayi, saboda rashin cin abincin da bayayi akai akai dan abin nashi ya karune tun zuwan Jannart gidan.
“Kazo kaci abinci.”
Mamyn ta fad’a cikin kulawa.
Shikuwa Rayyern idanunsa ya d’an bud’e akasalance yace.
“Mamy me aka dafa.”
“Coconut rice, with onion sauce, gas meat, and salad cream, sai kuma milk shake, and plaintain da kuma fish.”
Mamyn ta bashi amsa atakaice.
Fuskarsa ya d’an kwab’e, tare da rausayar da kansa gefe, cikin sanyi yace.
“Shike nan Mamy ku kullum abu ɗaya.
Kwananfa naga shi kukayi kukayi taci ba sauki”.
Da sauri tace.
“Yoh ya mana daɗi Ramadan da Riyyam-nsra sukace a sake yinshi, nima kuma naji daɗinsa”.
Cikin tarin gajiya yace.
“Mutane ayi ta sasu tsatsagar shinkafa ba sauki kamar tsuntsaye.
Gsky ni bazan ciba,
abu mai dan ruwa ruwa nakeso, banason abinci mai nauyi.”
Jujjuya kai Mamy tayi tare da cewa.
“To Bari ayi maka.”
ta fad’a tana me mikewa tsaye.
Shikuwa mikewa yayi, tare da cewa.
“Mamy bari naje nayi wanka, Please a gama da wuri.”
“To.” Mamyn tace masa, Yayinda shikuwa kaitsaye ya haura sama.
Mamy kuwa direct falon Jannart ta nufa.
Cikin sa’a kuwa anan cikin falon ta sameta tana game a wayarta.
Ganin Mamyn ne kuma yasa ta tsaida Game din, tare da sakin murmushi tace.
“Mamy sannu da shigowa.”
“Yauwa Jannart Sannu, game kikeyi ne.”
Mamyn ta tambaya cikin kulawa.
Jannart kuwa murmushi tayi, tare da ajiye wayan, cikin girmamwa tace.
“Eh Mamy, akwai abunda zanyi miki ne?”
“Kwarai kuwa Jannart, mijinki ne ya dawo wai, yunwa yakeji kuma abu mai dan romo-romo yakeso, Dan Allah ko zaki dan shiga kitchine kisama masa abu mai sauki.”
Mamyn ta fad’i haka cikin tausasa murya.
Jannart kuwa jin ance mijinta ne yasa ta sunkuyar da kanta k’asa, cikin wasa da y’an yatsun hannunta tace.
“To Mamy bari na dafa masa.”
“Yauwa Jannart Allah dai ya miki albarka.”
Mamyn ta fad’i hakan, tare da juyawa ta fice daga cikin dakin.
Ita kuwa Jannart a hankali ta miƙe cikin nitsuwa
ta rufa mata baya.
Koda suka fito falon kitchine Jannart din ta wuce, tare da soma kokarin had’a masa abunda xaici.
Hearty Chicken Gnocchi soup ta had’a masa, wanda yaji kayan had’i da milk.
Bayan ta kammala ne kuma ta juyesa, acikin wani Dan madaidaicin glass bowl maikyau.
Tare kuma da had’a masa spearmint tea ta juyesa acikin wani cup mai kyau.
Wani tray na glass ta dauka tare da jere masa abincin akansu.
Anutse ta fito daga cikin kitchine.
Din tare da ajiye tray din akan dining.
Dai-dai Ta juya zata sauka akan dining table din ne, shi kuma sai gashi ya na sauk’owa, Inda ya sanja shigarsa cikin wani riga da wando masu masifar taushi farare kala-kala.
Ganinsa ne kuma yasa Mamy dake zaune afalon tace.
“Babana harka fito.”
Kansa ya jinjina tare da shafa cikinsa, ashagwabe yace.
“Eh Mamy abinci.”
Murmushi Mamyn tayi, tare da cewa.
“Abincinka is ready Jannart sa masa abinci yaci.”
Dan tasan ba karamar yunwa ke azalzakarsaba tunda yaketa damunta da yunwa-yunwa.
Ita kuwa Jannart dake kokarin komawa dakinta
Jin abunda Mamyn ta fadane yasa ta tsaya.
Shikuwa Rayyern batare ma daya kalli Inda Jannart din take ba, yaja daya daga cikin kujerun dining din ya zauna.
Jannart kuwa Kanta ta sunkuyar, tare da juyowa a hankali ta fara ta kowa atsanake ta nufi dining table din.
Isowarta kan dining dinne kuma yasa, tayi kasa da kanta kana cikin sanyin murya tace.
“Sannu da dawowa.”
“Uhum.”
Ya amsa mata atakaice tare da kawar da kansa gefe, acikin zuciyarsa kuwa cewa yayi.
“Kowa yayimin sannu da dawowa, amma ita sai yanzu zata wani yimin iyayi munafuka yar leken asiri.”
Jannart kuwa plate ta d’auka, atsanake ta zuba masa.
Hearty chicken Gnocchi soup din, wanda tana bude bowl din kamshin nama da milk din ya daki hancinsa.
Zuba masa tayi tare da tura masa plate din gabansa, kana ta ajiye masa cup na Spearmint tea din agefensa.
Juyawa tayi atsanake ta bar wajen.
Shikuwa Rayyern numfashin ya ɗan shaƙar spoon ya dauka, ya ɗan jujjuya sabida yadda yake ta tururi alamun yanzu aka gamashi.
Yasan da zafi amman yunwar dake zakularshi barata barshi ya kira ya huceba.
Sa spoon din yayi tare dayin bismillah ya soma Kai gudan Tsokan Kazan bakinsa.
aloman farko kuwa dadin abincin ya ratsa sa, wanda hakan yasa shi sauƙe numfashi tare da bude cikinsa ya fara ci duk loman da zaiyi kuwa saiya had’a da ruwan cikin hearty chicken din.
Kana kuma time to time
Yake zukan spearmint tea din, wanda yaji kayan kamshi, spearmint, and Lemongrass leaves, pinch of cloves and masoro, A piece of ginger, sai kuma sugar da ta saka mai dan dama aciki.
Sosai spearmint Tea din yayi masa dadi.
Hakan kuwa shiyasa yaci abincin sosai, irin cin daya jima baiyi ba, bayan ya kammala cin na plate din ne ya jawo yar kular da nufin ƙarawa sabida.
Bai gama jin ya kai dai-dai gejiba.
Wani ɗan guntun tsaki yaja tare da ture kular.
Baki ya ɗan tura tare da cewa.
“Mamy”.
Dariyar dake son tsubuce matane ta danne tare da cewa.
“Na'am”.
Cikin hararan hanyar kofar dakin Jannart ɗin yace.
“Mamy ni ban koshi ba”.
Cikin dariyar yadda yake hararar hanyar da Jannart ɗin tabi Mamy tace.
“To kaine ai Babana sai kayi ta tara yunwa in ka tashi ci in ba mutun yasan yadda kakeba sai yace kai ɗan boll ne ko pollo dan sune masu yawan cin abinci”.
Fuska a kwaɓe ya mike ya tashi ya tafi wajen Abba.
Cikin danne dariyar dai Mamy tace.
“Yauwa to in kaje wurin Abbanku watakil ka samu wani abu dan na mishi gashi ɗazu”.
Shi dai baice komaiba ya tafi yana tura baki har ga Allah bai koshin ba
Koda yaje a falo ya samu Abba.
Yana cin gashin gargajiya na jan nama.
Zubawa a plate Abban yayi tare dasa mishi yajin.
Kana ya miƙo mishi.
Amsa yayi tare da gyara zamanshi.
Da kallon flaks haka yasa Abba ya gane abin da yakeso.
A cup din da yasha tea ya haɗa mishi.
Sokan naman ya kai bakinshi kana a hankali ya tauna tare da kiransa da ruwan tea din.
Shi kuwa Abba Qur'anin hannanshi yaci gaba da bita.
Sabida yasan idan yana cin abinci muddin ya tara yunwa to bai mgn kuma baya son kallo, dan cine zaiyi sauri-sauri sai ya kauda yunwarsa.
So haka yasa ya kauda kanshi daga gareshi.
Shi kuwa cikin 13mnt ya cinye naman da Abban ya saka mishi tare da shanye shayin.
A hankali yayi gyatsa tare da cewa.
“Alhamdulillah Abba na koshi”.
Kai Abban ya jinjina kana sai da yaje kan aya kana ya datse tare da shafa addu'a ya rufe Kur'ani.
Sai lokacin yace.
“Abba Barka da dare”.
Murmushi Abba yayi kana yace.
“Barka dai ka dawo lfy”.
Bayan sun gaisane kuma ya gyara zamansa, tare da fuskantar Abban kana a nitse yace.
“Abba daya daga cikin ingines dinmu fa yayi kadan, dole sai ansanja ankawo babba, To yanzu dai munyi magana, da wanda nasaya kayan awajensa, akwai wani babban ingine, amman dole zanje China na sayo".
Cikin gamsuwa Abba ya jinjina kai.
Dan shima da yaje Engineer Bello ya mishi bayanin komai.
Shi kuwa Rayyern a nitse yaci gaba da cewa.
“Ina tunanin zuwana China kwanan nan in sha Allah, dan shine babban abinda zai hana a fara aikin.”
Kai Abba ya jinjina, kana cikin gamsuwa yace.
“Masha Allah to yaushe ne zakaje china’n?”
Sake gyara zamansa yayi tare da tankwashe kafafunsa, cikin nutsuwa yace.
“Maybe next month Insha Allah, saboda Idan na tashi booking flight, kawai Zanyi kasancewar dama akwai sauran visa na.”
Kai Abban ya jinjina kana cikin gamsuwa yace.
“Masha Allah Allah Ya taimaka.”
“Ameen.” Rayyern din ya amsa nan dai sukaci gaba da hiransu, kafun daga bisani ya tashi ya tafi.
Alhamdulillah Alhaji idi Saleh Dakata kuwa jiki da dan sauki tuni ma an sallameshi ya dawo gida.
Sai dai yana cikin tashin hankali.
Junaid kuwa yana hannun hukuma.
Akwana atashi ba wuya, domin yau satin Jannart biyu, agidansu Rayyern din.
Abubuwa suna tafiya yadda ya kamata akan shirin kowa.
Zuwa yanzu Jannart ta dan saki jiki sosai dasu Mamy da Riyyam-nsra da Ramadan.
Yanzu ma zaune suke ita da Mamy acikin falon.
Yayinda Jannart ɗin ke zaune akan kujera 3seater.
Don lokacin ta gama sawa Mamy lallen gargajiya a ƙafarta.
Mamy kuwa tana Dan nesa da ita kan 2 seater.
Hira suke dan tab’awa kadan kadan.
“Yau kuma har yanzu su Ramadan basu dawo ba.
Su dai sun suka samu ba aiki to sai yawo kamar ababen hawa”.
Kai ta dan dago ta kalli Mamy tare da yin ɗan murmushi kana tace.
“Uhum ai dama tun jiya suke cewa yau jumma'a, tun daga masallaci kai tsaye min jibir zasu wuce”.
Kwaffa Mamy tayi tare da buɗe baki zatayi mgn sai kuma tayi shiru tare da zubawa ƙofar shigowa falon ido.
Ahankali ya turo k’ofar falon, tare da jefo k’afafunsa, dake wani irin b’ari.
Ganin alamun bude kofar falonne kuma yasa, Mamy saurin juyawa da kai saboda bataji anyi sallama ba.
Idanunta ta dan zazzaro waje, Cikin yanayin mamaki da kuma tsoron, yanayin da taga Rayyern din aciki wani irin yanayin dake nuna ba lfy ba.
Rayyern kuwa, da gaba daya yakejiin duniyar na juya masa, Yayinda da hannunsa duka biyu ke dafe da mararsa.
A hankali cikin tsananin wahala yake daga ƙafarsa.
Gaba