Showing 105001 words to 108000 words out of 132995 words

Chapter 36 - TUBALI Book 1 Complete Document by GARKUWA

22 Aug 2025

142

sai munyi.
Dan sanin duk wani abu daya shafesa, dole zamu kashe sa.
Domin barinsa araye hadari ne.”


“K’warai kuwa ai dole ne ma sai ya mutu, batun nemo gidansu kuwa, ku barshi a hannuna da kaina zanyi wannan, Domin ni na mafi bukatar mutuwarsa ayanzu fiye da komai, gaba daya duk ya tottosheni, acikin kaso 100 na daga mutanen da suke zuwa hospital dina, yanzu kaso 80 sun koma masa, kullum da bakin cikin abun nan nake kwana.”


Cewar Dr Lukman.


Dukansu kwafa sukayi, Yayinda kowannensu ya soma tsara irin bak’ar nufin dake cikin zuciyarsa.


Acan gidan su Rayyern kuwa, da matsanancin farinciki, Mamy take Kallon Abba wanda ya gaya mata batun d’aurin auren Rayyern din.


“Alhamdulillah, Alhamdulillah Allah mungode ma, Lallai Tabbas komai nada lokaci, Yau RAYYERN dina ya zama ango, Allah ya basu zaman lafiya, ya kuma saka al'khairi da al'barka acikin auren, ya kade musu duk wata fitina.”


Da.
“Ameen.” Abba ya amsa.


Batare kuma daya jima awajen Mamyn ba, ya tashi kaitsaye ya tafi wajen Baba Maud’o.


Mamy kuwa cikin tsananin farinciki ta fito falo ta zauna, dai-dai lokacinne kuma Ramadan da Riyyam-nsra suma suka sauk’o k’asa.


Riyyam-nsra ne ya karaso wajen Mamyn da sauri, cikin farincikin da yake ciki ne kuma yace.


“Mamy yaufa Auren Hamma Rayyern, gaskiya ya kamata ace mun d’an shashe, duk da ma auren sirrine amma ai dai mukam ya kamata, mu Dan shana ko Mamy.”


Murmushi Mamyn tayi, tare da dan jinjina masa Kai alaman eh.
Saboda tana cikin farin ciki itama yau din.


Riyyam kuwa waka ya kunna awayarsa, tare dayi musu connecting da tv, nan take kuwa sautin wakan Davido Maisuna Jowo ya soma tashi.


Nanfa Yayi starting video awayartasa, tare da soma rawa wayar na shooting d’insa, Mamy kuwa dake zaune gudun kada ya shooting da ita ne yasa ta tashi ta koma daki.


Tana tafiya kuwa Ramadan shima ya mik’e yana taya Riyyam-nsra din dancewa dan shi farin cikinsa biyu ne auren Hammansa da kuma samun damar nasa.


Adai-dai lokacinne kuma Rayyern ya bud’e murfin kofar dakinsa ya fito, jikinsa dauke da danshin ruwan alwala, kasancewar adai-dai lokacin ana ta kiraye kirayen sallan la’asar.


Tun kafun ya gama saukowa akan steps din falon, kuwa yake jin kida na tashi.


Da sauri ya dan karaso cikin falon.
Abunda ya ganine kuma ya sashi tsayawa, tare da dakawa su Riyyam din tsawa, fuska a murtuke yace.


“Mekukeyi haka, wannan wanni irin haukan banzane, ya zaku mayar mana da gida kaman filin gala ko club? Akan meye zaku cika mana gida da kide-kide, saboda meye akan wani dalili??”


Cikin fada sosai ya kare maganar.


Wanda hakan yasa Zakariyya Dan langwabar da kansa.


“Eyyah Hamma Rayyern Dan Allah ka barmu, yau fa ranar farinciki ne ranar auren babban yaya.”


Harara Rayyern din ya watsa masa, kana cikin takaici yace.


“Nabaku nanda 1mn ku tsaida kidannan, sannan lokacin sallah yayi, kuje kuyi alwala ku wuce masallaci.”


Baki Riyyam-nsra din ya dan turo gaba, dai-dai lokacin kuma Mamy ta fito daga cikin dakinta.


Kallon Mamyn Rayyern yayi, tare da d’an narkar da fuska yace.


“Mamy yaran nan basa ji, wai kida suke kunna mana acikin gida, kuma Mamy kinajinsu amma kika kyalesu.”


Murmushi Mamyn tayi tare da cewa.


“To Rayyern me kakeso nayi musu, na hanasu nishadi? Bayan ni kaina yau din farin cikin dake zuciyata bazai misaltu ba, yaufa aka daura maka aure, kaga Aikuwa ya zama dole muyi farinciki.”


Fuskarsa yadan narke, kaman zaice wani abu kuma saiya fasa kaitsaye ya fita tare da wucewa zuwa masallaci.


Yayinda su Riyyam-nsra da Ramadan kuwa suka haura sama dan gabatar da nasu alwalan.


Rayyern kuwa Koda yaje masallacin, bayan an idar da sallah, kaitsaye company d’insa ya sake komawa, yayi hakanne kuma saboda kwata kwata bayason zama haka har wani tunani ya dameshi.


Yayinda su Ramadan kuwa bayan sun idar da nasu sallan, suka shiga gari, musamman kuma suka yada zango a Green park, nanfa Riyyam-nsra ya shiga aikin yi musu Video, yana sending direct to Tiktok, daga karshe ma live ya fara yi.
Daga nan masaukinsa Ramadan ya wuce dole yasa Riyyam-nsra kwatso kwamutsansa suka taho gida.


Basu ne suka dawo gidan ba kuma, saida akayi sallan magriba.


Bayan sun dawo dinne kuma suka shirya kayan Riyyam-nsra sukayi al'wala kana suka wuce masallaci.


Rayyern kuwa har saida aka idar da sallan Isha kafun yake dawowa gida.


Anan falo ya samesu dukansu suna dinner.


Shigowarsa ne kuma yasa Mamy sakin murmushi, cike da kulawa tace.


“Yauwa Babana ka dawo ko, yanzu nake zancenka araina, zo kaci abinci.”


Kansa ya dan langwabar tare da Karasowa dining table din,


“Na nakoshi.”


Ya fad’a akasalance.


Wanda hakan yasa duk suka tsura masa ido, musamman Abba.


Shikuwa Rayyern still sake kwab’e Fuskarsa yayi, tare da dubansu yace.


“Ni baccima nakeji saida safe.”


Yana gama fadin hakan kuwa, baijirayi me waninsu zaice ba kaitsaye ya haura Sama.


Da Kallo Abba ya bisa, Yayinda acikin ransa yake mamakin halin Rayyern din, daga daura masa aure kawai lokaci daya harya sanja, sai kace wani mai aljanu.


Da haka dai suka ci gaba da cin abincinsu, bayan sun kammala ne kuma Abba ya koma dakinsa, Yayinda Ramadan Riyyam da Mamy kuwa suka zauna afalo, suna yar tab’a hira.




11:30 pm.


Gaba d’aya ko ina dake Cikin gidan, yayi shiru babu wani alaman kwakkwaran motsi dake tashi, wanda kuma hakan alamace dake nuna cewar duk wasu mutannen dake zirga-zirga acikin gidan sunyi bacci.

Haka ma compound din gidan babu kowa, ko ina shiru.
Daga can gefe kuwa, gaba daya guards din da suke gadin Jannart ne kwance, kowannesu ya sake katon baki da ciki, suna bacci kamar matattu.


Ind daga gefensu kuwa Baba Ado ne zaune, yana rik’e dayar radion sa.


Sai kuma Ashiru dake bakin gate, yana ta faman lellek’awa tako ta Ina, gudun kada su aikata kifi na ganinka mai jarkoma.




Acan cikin gidan kuwa, Momy ce ta fito daga cikin dakinta, cikin shirin kayan bacci, kaitsaye kuma dakin Daddy ta nufa.


Jannart dake tsaye acikin dakinta kuwa, Idanunta dake zubar da hawaye ta lumshe.


Wani iri takeji, Yayinda acikin ranta kuwa take cewa.


Inama da zata iya bijirewa umarnin Abba Kabir din, da zatace itakam ta fasa, da zata zauna agidansu da dadi ko ba dadi, tayarda kaddarar ta ce tazo a haka.
To amma ya zatayi? Bata da wani zabi ako da yaushe, tasani zatayi kewar gidansu sosai, zatayi kewar dakinta da kuma yan uwanta.


“Zanyi kewarka Daddy na, zanyi kewar Momy da Abdull, nasani zanyi kewar duk wani abu daya shafeni, Daddyna baya tab’a takuramin, bayayimin komai, kawai dai baya daukan mataki akan duk wani cin zarafi da Yah Junaid zaimin.”


Ta fadi hakan hawaye na ci gaba da zubowa akan fuskar ta.
Cikin sanyi da mutuwar jiki kuma ta d’auki yar jakar da ya hade komai nata na amfani aciki.


Drawernta ta bud’e tare da zaro, wani hijab mai kyau hadi da tsananin taushi ta zura akan, Daguwar rigar, Arabian gown dake jikinta.


Juyawa tayi Ahankali ta nufi kofar fita daga dakin, Yayinda tabar wayarta da goro da kuma sweets din da Abba Kabir ya bata atsakiyar gadon dakin.


Harta Kai bakin kofar fita ne kuma ta juyo, ta sake Kallon cikin dakin nata.


Lokaci daya kuma hawaye ya cigaba da sauka akan fuskarta.


Saidai kuma babu yanda ta iya, haka ta murda handle din kofar, cikin sand’a ta fice.


Fitowar nata ne kuma yayi dai-dai da wulgawan Momy, wanda ta wuce dakin Daddy.


Saurin komawa baya tayi ta labe.


Harsaida ta tabbatar da wucewan Momyn kafun ta fito, cikin tsananin sand’a take tafiya.
Harta karaso Cikin falon da Kwata Kwata babu yalwan haske acikinsa.


Handle din kofar falon ta murda Ahankali, bayan ta fito ne kuma ta maida kofar ta rufe.


Dai-dai lokacinne kuma Abdull wanda ya fito daukar ruwa, yaji kaman karan rufe kofa, saurin maida kallonsa ga kofar yayi, saidai ko alaman motsi baiga kofar tana yiba, gashi kuma babu kowa acikin falon, hakan yasa yayi tunanin ko kunnuwansa ne basu jiye masa dai-dai ba, kasancewar yana gigin bacci, bayan ya d’auki ruwanne kuma ya juya ya koma dakinsa.




Jannart kuwa Koda ta fito compound din gidan, cikin sand’a take tafiya, wanda hakan yasa Baba Ado dake tsaye yi mata alama akan tayi sauri.
Yayinda shikuwa Ashiru ya fita ya lellak’a musu waje, ganin babu kowa a arean wajenne kuma, yasa Ashirun daga mata hannu akan tazo ta wuce.


Aikuwa cikin sauri, da kuma tarin fargaban da takeji ta zo ta fice daga cikin gidan.


Yayinda Baba Ado shima ya rufa mata baya.


Ganin ficewar nasu ne kuma yasa Baba Ashiru maida kofar ahankali ya rufe.


Jannart kuwa tafiya suke ita da Baba Ado, wanda ya riga da yayi gaba, ita take biye dashi abaya.


Tafiya kuwa sukayi mai dan tsawo.


Kamar kuma yanda Abba Kabir din ya fad’a, kwana Uku suka shiga, ata ukunne kuma suka hango motarsa.


K’arasawa sukayi da sauri, inda Baba Adon kuma da kansa, ya budewa Jannart din gidan baya ta shiga ta zauna.


Kallon Abba Kabir din yayi, kana yace.


“Barrister Allah Yatsare ya kuma, taimaka akan duk wani abu da kukasa gaba, Allah Ya tono gaskiyar da ake boyewa.”


Da Ameen Barrister Kabir din ya amsa, Yayinda shi kuwa, Baba Ado ya juya Cikin sauri ya nufi hanyar komawa gidan, yana isa gidan kuwa, Baba Ashiru ya bud’e masa kofa.


Sa d’ab sad’ab haka ya shiga cikin mayan guard dinnan ya kwanta.




Barrister Kabir kuwa tada motar tasa yayi suka bar wajen.
Kaitsaye kuma Nassarawa G.R.A suka nufa.


Ita dai Jannart tunda ta shiga motar, ta kwantar da kanta ajikin kujera, hakanan takejin kanta wani iri.


Tafiyar mintuna kadan sukayi, suka shigo Cikin unguwar.


Adai-dai gaban babban gate din gidan, kuma Abba Kabir ya tsaya tare da dan danna horn.


Ari dake zaune ne ya taso ya bude musu, kasancewar Baba Maud’o karatun Qur’ani yakeyi shiyasa, Arin bai katseshi ba kuma dama Abba da Rayyern sun hanashi ziryar buɗe gate.


Ana bud’e gate din kuwa, Barrister Kabir ya tura hancin motar tasa ciki.


Bayan ya gama dai-dai-ta parking din motar ne, kuma ya bud’e b’angaren da yake ya fito.


Karasowa wajen su Baba Maud’on da yanzu ya shafa addu'a.
Isa garesa yayi, cikin girmamawa da kuma sakin fuska, ya bawa Baba Maud’on hannu suka gaisa.


kana yace.


“Dan Allah Baba Maud’o ko zaka iya nemamin iso zuwa cikin gidan.”


Murmushi Baba Maud’o yayi, tare da mikewa tsaye yace.


“Babu komai, Barrister bari nayiwa Alhajin magana.”


Kai Barrister Kabir ya jinjina, Yayinda shikuwa Baba Maud’o kaitsaye ya nufi cikin gidan, Koda ya karasa jikin kofar, kwankwasawa yayi tare dayin sallama.


Abba dake zaune afalo kuwa, Jin muryar Baba Maud’o ne, yasashi mikewa tsaye.


Tare da tasowa yazo ya bude kofar.

“A’a Baba Maud’o kaine.”
Abban ya fada.


Inda Baba Maud’o kuwa gyara tsayuwarsa yayi, tare da cewa.


”Ni ne Alhaji dama Barrister Kabir ne yace na nemama masa iso.”


Murmushi Abban ya fadada, tare da cewa.


“Masha Allah kace masa ya shigo.”


Da To Baba Maud’o ya amsa, kafun ya juya kaitsaye ya nufi wajen da Barrister din ke tsaye.


“Yace ka isa.”


“To To masha Allah Nagode sosai.”
Barrister Kabir din ya fad’a, yana me bud’e murfin motar, nan b’angaren baya inda Jannart din take.


Wanda kuma tad’an rufe gefen fuskarta, da tattausan hijabin dake jikinta.


Hannunta Abba Kabir din ya kamo, tare da cewa.


“Jannart fito, amma ki fito da kafar dama sannan ki rike addu’a a bakinki.”


Kanta ta Dan jinjina, cikin kuma sheshshekan kukan da yaso kwace mata ta fito daga cikin motar.


Sosai takejin kirjinta na wani irin bugawa, ga kuma wani nauyi da takeji acikin zuciyarta.


Yayinda hawayen dake cikin idanunta kuwa har yanzu suka kasa tsayuwa, shin wanni irin kulline acikin rayuwarta da har yasa akayi mata irin wannan auren?




“Masha Allah mu isa To.”


Baba Maud’o ya fad’a, yana me shigewa gaba, shikuwa Abba dake rike da hannun Jannart ya rufa masa baya.


Koda suka isa bakin kofar falon kuwa, Abba da kansa ya taso ya bud’e musu.


Tare da yi musu iso, cikin tsananin farinciki da jin dadi.


Karasowa cikin falon sukayi, Inda Abba Kabir din ya Zaunar da Jannart akan lallausan carfet din dake cikin falon.
Kana ya zauna asaman kujeran dake gefenta.


Abba kuwa Kallon Ramadan yayi, kana fuska asake yace.


“Ramadan jeka kiramin Rayyern.”


To Ramadan ya amsa, tare kuma da mikewa cikin sauri ya haura sama dan kiran Rayyern.


Rayyern dake kwance yana latsa system d’insa, jin muryar Ramadan dake knocking yasashi bada izinin shigowa.
Bud’e kofar Ramadan yayi ya shigo.


Cikin girmamawa, yace.


“Hamma Rayyern Abba na kiranka.”


Kai Rayyern din ya jinjina, Yayinda Ramadan kuwa ya juya ya tafi.


Koda ya dawo falon, cewa Abban yayi Rayyern din yana zuwa.


Kai Abba Ya jinjina, tare da cewa.


“Masha Allah to kaida Riyyam kudan bamu waje.”


Babu musu kuwa, duk suka Mike suka nufi steps din sama.


Suna haurawa kan steps din kuma Rayyern yana sauk’owa.


Kallonsa Ramadan yayi, tare da d’an gumtse dariyar farin cikin dake cinsa na sanin yanzu shine a layi.


Shikuwa Rayyern wani irin masifeffen kallon ya watsawa Ramadan, musamman alokacin daya sauke idanunsa akan Barrister Kabir da yake Zaune acikin falon.


Hakan yaji wani irin takaici ya cika masa zuciya sabida anfa dameshi matuka an hanashi salama.


Su kuwa Ramadan da Riyyam-nsra neman waje sukayi suka tsaya, Acan saman stairs din.


Yayinda shikuwa Rayyern jiki asanyaye ya karasa saukowa cikin falon.


Inda Barrister Kabir ke zaune agaban Abba, still kuma har yanzu yana rik’e da hannun Jannart wanda ta sunkuyar da kanta k’asa.


Abba kuwa Kallon Barrister Kabir din yayi, cikin tausasa Murya yace.


“Barrister daka koma sama ka zauna, Domin aduk sanda kazo gabana ka zauna akasa sai naji abun yamin nauyi.”


Murmushi Barrister Kabir din yayi, kana cikin mutum tawa yace.


“Babu komai Alhaji, zamana a k’asan bawai gazawa bace, kuma hakan yana da dalili.”


Kai Abban ya jinjina.


Tare kuma da kai dubansa ga Rayyern wanda ya karasa shigowa cikin falon.


“Zoka zauna anan Rayyern.”
Abban ya fada yana me nunawa Rayyern gefensa, kuma kusa da Mamy dake zaune.


Yayinda Jannart kuwa hawayen Idanunta, kwata-kwata sun kasa tsayawa, saboda yanda kukan ke neman cin karfinta ne kuma yasa har shashshekan kukan nata ya Dan soma fitowa.


Idanu duk suka zubawa Jannart din da kanta ke k’asa, Yayinda tsananin tausayin yarinyar ke sake lullub’e zuciyarsu, musamman ma Mamy da taji son yarinyar acikin zuciyarta, duk da cewar bata ga fuskar yarinyar ba, amma taji ta kwanta mata.


Rayyern kuwa yanda ya dauke kansa gefe, tamkar ma baisan da wata mai sakin sheshshekan kuka acikin falon ba.


Abba Kabir kuwa gyara zamansa yayi, tare da sake rike hannun Jannart kam, cikin muryarsa da tayi rauni sosai yace.


“Alhamdulillahi.
Yau gani na agabanka Alhaji Bashir, ga y’ata nan Jannart na kawota gareku”.
Sai kuma ya ɗan numfasa kana a hankali yaci gaba da cewa.
“Bansanku ba baku sanni ba, amma musulumci ya had’a mu kamar yanda manzon Allah yace, Almuslimu ak’ul muslim, musulmi d’an uwan musulmi ne, na nemi taimako kunyi mini, har lau kuma Ina sake neman taimakonku, akan kulawa da y’ata Jannart, da kuma rik’emin amanarta, Jannart amanace awajena numa kuma nima yau zan baku amana, arikemin Jannart Amana marainiya ce, Dan Allah ku rikemin amanarta, Jannart bata da laifi, jarrabawar rayuwace tazo mata ahaka.
Kana bata da tashin hankali, Jannart yarinyace mai tsananin biyayya, haka kuma mai tausasshiyar zuciya, Jannart yarinyace mai rauni, yarinyar da maraici ya cika gaba daya rayuwarta, Ina da tabbaci akan biyayyar Jannart.
Domin yarinya ce da take gudun bacin ran wanda ke kusa da ita, Idan tayi muku ba dai-dai ba ku hukuntata kamar yanda zaku hukunta y’ay’an cikinku.”


Dan tsagaitawa da maganan nasa yayi, saboda yanda Hawaye ke sauka akan fuskarsa.


Juyowa da kallonsa yayi ya kalli Mamy, cikin sanyin jiki yace.


“Hajiya ga Jannart nan na kawo muku Amana, Dan Allah ki rikemin ita, ki dauketa tamkar yar da kika haifa acikin cikinki, Dan Allah ku killacemin Jannart, banason ko k’ofar gida ta l’eka, Idan kuma akwai buk’atar fitar ta wanda ya kama da dalili a gayamin, saboda banason idanun wasu su sauk’a akanta.
Domin fataucin rayuwarta sukeyi, tamkar wanda yaje farauta yagaji bai samu komai ba, haka suke ayanzu, da zaran lokaci ya cika akanta zasu dire, suna son su kasheta, suna tsananin son ganin bayanta,
Alhamdulillah yau inajin na sauke wani nauyi akaina...”


Kasa karasa maganan nasa yayi, saboda kukan da yakeji na tasar masa.


Yayinda Jannart kuwa tuni kuka yaci karfinta, ba abunda ke tashi kuwa face sautin kukan ta.


Wanda hakan yasa gaba daya su Abba, Mamy, da Baba Maud’o duk jikinsu yayi sanyi.


Shikuwa Rayyern zuwa yanzu ya tankwashe kafafunsa, tare kuma dayin shiru, ya sunkuyar da kansa k’asa.
Haka kuma yakejin kansa na.
Dan sarawa, Yayinda yakejin jijiyon dake cikin kannsa nayi masa ciwo.
Badon komai ba kuma saidan saboda yanda yakejin kukan yarinyar na hawa kanshi.


Barrister Kabir kuwa Hannun Rayyern din ya kamo.
Da sauri Rayyern ya ɗago kansa ya kalleshi.
Sai kuma yayi ƙasa da ida nunshi ganin yadda mutumin mai girma yana kuka.
Shi kuwa Barrister Kabir.
cikin sanyin da jikinsa yayi yace.
“Rayyern ga amanar diyata matarka”.
Ya ƙare mgnar yana mai ɗago hannun Jannart ya saka acikin tattausan tafin hannun Rayyern din tare dasa nashi hannun ya rumtse tafin hannun Rayyern dake riƙe dana Jannart ya rumtse ya haɗe su...!




*Littafin TUBALI na kuɗine special Group 1k ne ƙaramin group 500 yawan posting ne banbanci su, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in baki da halin turawa ta banki to ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp na*








By
*GARKUWAR FULANI*










Wani irin raunataccen kuka ne ya kwabcewa Jannart cike da rauni shessheƙan kukan yake fitowa, yana ratsa kunnuwansu.
Banda kukan Jannart dake tashi, shiru gaba d’aya falon ya d’auka.


Yayinda Rayyern kuwa ya sunkuyar da kansa k’asa, tare kuma da rumtse idanunsa gam dan jin fatan saman idonsa nata karkarwa.
Domin kuwa adai-dai lokacin da hannun Jannart din ya sauk’a acikin nasa hannun, wani irin harbawa zuciyarshi tayi tare da buɗewa da azaban ƙarfi.


Duk da cewar kuwa ba wannan bane first time nasa daya fara tab’a jikin mace, musamman Idan akayi duba da irin yanayin aikinsa, saidai kuma a iya tsawon rayuwarsa, bai tab’a rik’e jikin mace, da sunan wai dan yaji wani abu ajikinsa ba, yana rikewa ne kawai idan takama dole, enfact ma shi baicika son duba mata ba, sai idan abun yayi worst ya kuma zama lallai dole shidin ake da buk’atar ya duba su.
Sam bai tab’ajin wani abu makamancin haka ba.


Tamkar kuma yanda

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login