Showing 87001 words to 90000 words out of 132995 words
wai nayi aure! Kai ubana ne!? ko yayana!? kama fini sanin abinda ya dace kenan?.”
Rayyern din ya k’are maganan cikin fad’a.
Wanda hakan yasa Ramadan Dan sunkuyar da kansa, cikin yanayin sanyi kuma yace.
“Ayyah Hamma Rayyern kayi hakuri Insha Allah bazan sake ba kaji kayi haƙuri.”
Kai Rayyern din ya kawar, Yayinda Abba da Mamy kuwa suka kalli junansu.
Ramadan kuma mik’ewa tsaye yayi, tare da kama hannun Riyyam-nsra suka fice daga cikin falon.
Fitansu daga cikin falonne kuma yasa Abba d’ago Kai ya kalli Rayyern din.
Yayinda su Ramadan kuwa suna fita, kaitsaye wajen Baba Maud’o dake zaune abakin gate suka nufa.
Ganin su dinne kuma yasa Baba Maud’o sakin murmushi.
Bayan sun zauna akan dogon bencin da Baba Maud’on ke kaine kuma.
Baba Maud’on Ya kalli Riyyam-nsra tare cewa.
“Riyyam ya mutanen can k’asar taku, da su Mammyn ka da Zaiton.”
Murmushi Riyyam-nsra yayi, tare da gyara zamansa ya kalli Baba Maud’on cikin kuma jin dadi yace.
“Munyi waya dasu dazu kowa da kowa yana nan lafiya, sunma ce na gaishe da kai, saboda na tura musu hotonka, har Zaiton tana cewa wai itama zata zo ka nad’a mata irin abunda kake sawa afuskarka, wai zatana boye fuskarta saboda Samarin dake damunta.”
Yar dariya Baba Maud’o yayi, tare da jinjina kansa.
Cikin jin dadi yace.
“To shikenan Idan tazo zan koya mata yanda ake na dawa, ai rawani ne ba komai ba, nadashi kuma ba wahala.”
“To Baba Maud’o nima dai ai watarana zaka koya min ko, sai naje na koya mata.”
Kai Baba Maud’on ya jinjina alaman.
“Eh.” Daga haka kuma suka ci gaba da hiransu.
Ethiopian.
Adai-dai lokacin ne kuma Mammy dake zaune akan sallaya ta kurawa, hoton dake kan screen din wayar nata idanu, wanda kuma hoton Baba Maud’o ne da Riyyam ya turo mata.
Azahirin gaskia ba kuma tana Kallon hoton da wata manufa ko tunani bane.
Kawai dai tana mamamkin irin shigar da taga mutumin yayi ne, saboda su anan basu tab’a Ganin irin shigar ba.
Ajiye wayar nata tayi tare kuma da watsar da duk wani tunani dake ranta, kaitsaye ta mike daga kan sallayan ta shige kitchine.
Acan falo kuwa Abba dake Kallon Rayyern d’an gyara zamansa yayi.
Tare da fuskantar shi kana cikin yanayi masifa faɗa da kuma umarni yace.
“Uhmmm RAYYERN kenan.
Saboda kawai yace maka kayi aure shine kake daka masa irin wannan tsawan? Da ɗaga jijiyoyin wuya.
To shi meyene laifinsa, saboda kawai yace ka cika martabarka, ka kuma raya sunnar Annabi Muhammad SAW shine, yayi laifi?”.
Ya ƙare mgnar tare da tsareshi da idanun
Da dole yasa RAYYERN yayi ƙasa da kansa.
Shi kuwa Abba kwaffa yayi tare daci gaba da cewa.
“Yoh wai kai azatonka da tunaninka haka zaka ta zama babu aure ne, saboda kawai kaga na zuba maka ido tsawon shekaru, kayi tunani da hankalin ka fa Rayyern, ayanzu Kai ba yaro bane, Domin kuwa kabawa shekaru 30 baya, shin kana tunanin banason yin aurenka ne? Ko atunaninka bana da buk’atar Ganin aurenka ne? To kasani duk da cewar nasan tabbas na sakar maka ragaamar komai, na tara maka ayyukan da sukafi karfinka, bawai Ina nufin ka zauna haka babu aure bane ba wurin aiki kawai nake son ganin kamalarka ba harda aure, Tabbas banajin dadi aduk sanda ka nuna cewar babu maganar aure kwata-kwata agabanka, kaine babba akan Ramadan, ya kuma zama dole kayi aure, Domin duk wani Namiji mutumcinsa da Darajarsa bata cika ko a idanun mutane, har sai in yana da aure, komin dukiya da mulkinsa kuwa, aure shine abunda ke maida Rabi ya dawo Guda, ka d’aga mutumci da darajarka ta hanyar yin aure, Allah dakansa zai dubi al’amuranka, amma ace akoda yaushe Kai baka da zance sai na cewar bakason aure...”
*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*
NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.
Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.
Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.
Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.
🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*
By
*GARKUWAR FULANI*
Shi kuwa Rayyern.
Kansa ya d’an langwabar gefe, tare da dagowa ya kalli Abban nasa cikin sanyi kuma yace.
“To Abba ni ta yaya zan kawo batun aure atsarina.
Abba ni bani da wacce nake ko mgnar so bare aure.
Kuma ma nida kullum Ina busy Abba, yaushe naji da kaina ma, balle har na kula da wata da zata zauna akarkashi na ta yaya zata samu kulawar da zata bukata daga gareni tunda Ni da kaina bani da lokacin kaina ma.”
Hannu Abban ya d’aga masa, cikin kuma dan had’e fuska yace.
“Ni ka rufemin baki, kullum baka da aiki sai maimaita abu d’aya kai baka da lokaci ita matar in ka aurota ta zama kamar wayarka ina kanada lokacin waya to zaka ware lokacin matarma.”
Jin abunda Abban ya fad’ane kuma yasa shi sunkuyar da kansa k’asa.
Yayinda Abban kuwa yaci gaba da cewa.
“Dole zakayi Aure Rayyern, Aure kuma irin na Jahadi da taimako, Lallai zakayi Aure anan kusa Insha Allah.
Yarinya yar gidan mutumci, iyayen ta manyan mutane, mutum yaga darajarka da mutumcinka ya yaba da tarbiyarka da gskyarka, sannan ya yaba da mutuncinka ya kuma dauki yarsa, yar da take da mutumci da daraja hadi da kyakkyawan tarbiya, yace zai baka aurenta, har kana da bakin cewa a’a, ko kunya baka jiba kyautar raifa akace an baka.
Rayyern karkamin haka fa, na dauraka akan turban yin taimako, da kuma jin kai, wannan mutumin daya zo ya Nemi taimakon ka, ya shaida maka yarsa tana da buk’atar taimako ya haɗaka da Allah da Manzonsa, shin Meyasa zaka ki amince musu, (bana son ka koyi kafurin zuciya da baya jin roko dan Allah da Manzonsa kamar irin muguwar zukatan barayin littafin TUBALI) Meyasa bazaka amincewa hakan ba Rayyern? shida bakinsa yake cewa, idan ma baka amincewa auren ba, ko ajiya ne ya amince zai kawota aboye masa ita, To amma ninaga ko a Shari’ance hakan baidace ba, muba y’an uwanta muharramanta bane, tayaya zamu iya ajiyeta, saboda haka ninafi yarda da a baka auren ta, kuma Insha Allah zaka aureta nan bada jimawa ba.”
Saurin dago kansa yayi ya kalli Abban nasa, cikin kuma nuna rashin son Auren yace.
“Abba ka amince musu, batare da ka sansu da sanin kosu su waye ba, Abba nifa...”
“Dakata Rayyern, ai ba dole Lallai saina sansu ba, da yawan mutane kuma dama baka sansu ba amma aurene dai ke had’aku ku zama yan uwa, auren ne kuma kesa kasan komai akan mutum, ka kuma San ance matar mutum kabarinsa, aduk inda matarka take Koda abirnin sin ne kuma sai kaje ka nemota ka aureta.
Yanzu Kai Rayyern baka son kayi aure ka hayayyafa kamar yanda muka haifeku? Komai na Allah Ne Rayyern haka kuma komai dayake faruwa ko zai faru tsararrene awajen Ubangiji, saboda haka kada Kayiwa Allah shishshigi acikin al’amuransa.”
Shiru Rayyen din yayi, lokaci daya kuma yaji duk jikinsa yayi sanyi.
Abba kuwa kallonsa yayi tare da cewa.
“Tashi ka bamu waje.”
Mikewa yayi jiki asalube ya nufi sama, koda yake tafiyan duk jin zuciyarsa ajagule yake, Domin Allah ya sani kwata kwata shi ayanzu babu tsarin aure acikin rayuwarsa, amma Meyasa dole sai an tursasa masa, shi haka yake son yin rayuwarsa batare da wata ta shigo masa tsarinsa ba yafi jin dadin rayuwa shi ɗaya ya sake yayi yadda yake so a side nashi ba mai kallonsa.
“Ni mezanyi ma da mace? Ni Wallahi bana buƙatar mace.
chocolates dina ma yafi min zama da wata mace, Domin Idan Ina da chocolates dina mace bazata tab’a damuna ba, saboda chocolate yana samin jin daɗin da macen bazata saminba.
Ya fad’i hakan acikin. Zuciyarsa,
Dai-dai lokacin ne kuma ya iso dakinsa.
Ransa duk ajagule dai haka yayi wanka, tare da dauro alwalan sallan magriba.
Koda ya fito atare sukaje masallacin dukansu, basu dawo ba kuma saida akayi sallan isha.
Ko dinner baiyi ba yaudin haka yaje ya kwanta, Yayinda Riyyam-nsra kuwa bayan sun gama cin abinci, Ramadan ya maidashi masaukinsa.
Ko awajen bacci haka dai Rayyern yayi ta sake sake har bacci ya daukesa.
Washegari.
7:30 am dai-dai ya gama shirya kansa, cikin shigarsa ta yau da kullum wato Suit.
Inda ya saka wasu tsadaddun takalma akafarsa.
Koda ya sauko kasa, ya samu Abba Mamy da kuma Ramadan akan dining table.
Bayan sun sake gaisawane kuma ya Zauna, inda Mamy ta hada masa tea da pepper chicken yaci, nan ma baiwani ci sosai ba ya mike tsaye tare dayi musu sallama, kusan atare suka fito shida Ramadan.
Kaitsaye kuma Mainasara Hospital suka nufa.
Suna isa kuwa Rayyern din ya wuce duba wasu patients, saboda dama kusan one week kenan yanzu da suke da appointment dashi.
Bayan ya duba sune kuma ya dawo Office d’insa, inda ya soma cike wasu files, kasancewar kuma saida yamma ne zaije Tv station na Arewa24 din, kamar yanda yayi al'kawari tunda sun gaya mishi lokacin shirin nasu.
Acan gidan Alhaji Idi Saleh dakata kuwa, yau Jannart ce da kanta a kitchine, kasancewar bada wuri ta shiryawa zuwa office yau dinba.
A kuma safiyar yau dinne Abba Kabir yazo gidan.
Inda ya samu Momy da kuma Yayan nasa zaune afalo, Koda suka gaisa hira suka Dan tab’a, kadan har ya mike zai tafine kuma ya kalli Momy dake zaune.
Tare da cewa.
“Hajiya baku dafa wani abu bane, yunwa nakeji Dan bansamu nayi breakfast agida ba.”
Murmushi Momy tayi tare da cewa.
“Mundafa yau mutumiyar taka cema a kitchine, Gata can ta ishemu da kanshi bansan ma abunda take dafawa ba, amma bari na duba Idan ta gama saina zubo maka.”
Momyn ta fada tana me mikewa tsaye, kaitsaye ta nufi kitchine.
Abba Kabir kuwa jin ance Jannart dince da kanta ke girkin, yasa shi marawa Momyn baya, cikin dan sigan tsokana kuma yake cewa.
“Ah Lallai su Jannart angirma, har an iya jagwalgwalon girki.”
Jannart dake staye a kitchine tana karasa had’a faten irish mai roman da ta keyi ne ta juyo, saboda Jin muryar Abban nata murmushi ta saki cikin jin daɗi.
Ganinsa din da tayine kuma ya sa ta fadada murmushi, tare da cewa.
“Oyoyo Abbana, yau dai da girkina zaki break.”
Dariya Abba Kabir da Momy sukayi,
Dai-dai lokacin kuwa Momyn ta soma jiyo karar wayarta dake daki, alamun kuma kiranta akeyi.
Cikin sauri kuwa tatafi Dan dauko wayar.
Jannart kuwa Kallon Abban nata tayi, tare da cewa.
“Yauwa Abba bakace jagwalgwalo na iya ba, To yanzu bari na zuba maka abincina kaci kaji.”
Ta fadi maganan tana me daukan plate ta zuba masa gasashshen kifi roasted wanda ta gasashi da kayan kamshi, agefen katon kifin kuma ta zuba masa faten Irish patatoe din mai romo, wanda yaji kayan hadi, da kuma vegetables.
Spoon ta saka masa acikin plate din, tare da karasawa ta ajiye masa akan wani Dan table mai kujeru biyu dake cikin kitchine din.
“To ai shikenan kinga yanzu zanji irin dandanon girkin naki duk da ma nasan Mom ba wasa a girki kuma ta koyar dake.”
Abba Kabir din ya fada, yana me jan daya daga cikin kujerun ya zauna.
Saidai kuma Batare dayasaka abincin acikin bakinsa ba, ya Dan dago ya kalli Kofar shigowa Kitchine din.
Wanda kuma hakan alamane dake nuna cewa akwai magana abakinsa.
Gane hakan kuwa shiyasa Jannart Dan matsowa, cikin yin kasa da murya tace.
“Abba ya maganan aikina kuma Idan har abunda kake shiryawan ya tabbata, hakura zanyi da aikin nawa kenan?”
Kai Abba Kabir din ya girgiza mata, cikin tausasawa kuma yace.
“Karki damu Jannart, komai zai tafi dai-dai, Domin zanje na samu MD’n ku, duk wani abu daya dace nayi zanyi, tayanda aikinki bazai bar hannunki ba, koda kuwa bakyanan, kada kiji komai aranki Jannart, Insha Allah sauyi ne yake zuwawa rayuwarki.”
Ajiyar zuciya ta sauke saboda sai yanzu ne taji sanyi acikin zuciyarta.
Yayinda Abban kuwa abincin ya soma ci, tun aloman farko kuwa ya soma yin santi.
Tas kuwa ya cinye abincin, bayan ya kammala ne kuma ya yi musu sallaama ya tafi
Yana fita kai tsaye Mai-nasara Hospital ya nufa...
Jannart kuwa bayan ta kammala komai, jere musu abincin tayi akan dining table.
Koda sukayi breakfast din kuma daki ta koma ta kwanta, zuciyarta cike da sake sake kala kala, musamman yau din takejin bugun zuciya da faduwar gaba.
Saboda tsoro da takeyi na kada yamma tayi kuma mutumin da sukayi dashi akan zai kawo musu Dr. Rayyern Mai-nasara yaki zuwa.
Haka dai ta wuni cikin fargaba.
A hankali ya ɗago kanshi ya kalli ƙofar shigowa Office din nasa.
Wanda ake neman izinin shiga.
Idonshi ya ɗan lumshe tare da bada izinin shigowa.
Dr Sulaiman a gaba sai Barrister Kabir dake bayansa da alama jagora yayi masa.
Da sauri ya ida buɗe idansa.
Tare da gyara zamanshi.
Ido ya zuwa Dr Sulaiman dake nuna Barrister Kabir kujerar zama tare da ce mishi.
“Bismillah Barrister ga wurin zama.
Gaka ga Dr Rayyern Mai-nasara, ni bari in koma bakin aiki”.
Cikin jin daɗi Barrister Kabir ya zauna tare da cewa.
“Docta ngd matuƙa”.
Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara wani irin kallon tuhuma yakeyiwa Dr Sulaiman shi kuwa Sulaiman murmushi yayi tare da cewa.
“Toh na tafi”.
Ya ƙare mgnar yana fita.
Wani nannauyan numfashin ya fesar kana a hankali ya kalli Barrister Kabir dake zaune cikin kamala da mutuntaka.
Cikin nitsuwa yace.
"Barka da zuwa”.
“Barka dai Rayyern, ya gida yasu Abbanka?”.
Barrister Kabir yayi mgnar cikin kulawa da mutuntakar da tasa jikin Rayyern yin sanyi, cikin girmamawa yace.
“Alhamdulillah. Ya mai jiki?”.
Ya ida mgnar a matuƙar gajarce.
Wanda mgnar kamar subutar bakine.
Cike da jin daɗin yace.
“Alhamdullih jiki da sauƙi”.
Uhum yace tare da gyara zamanshi.
Shima Abba gyara zamanshi yayi cikin nitsuwa yace.
“Yanzuma mgnar tane ya kawoni gareka in ba matsala dan Allah da Manzonsa mu tattauna!”.
Ya ƙare mgnar yana zubawa Dr Rayyern Mai-nasara idanu.
Shi kuwa Rayyern a hankali ya meda bayanshi ya jingine da jikin kujerar tasa.
Wani sassanyan numfashi ya fesar.
Tabbas Barrister yana karya mishi duk wani logonshi da yake haɗashi da Allah da Manzonsa.
Cikin yin ƙasa da murya yace.
“Bismillah”.
Jin hakane yasa Abba gyara zamanshi da kyau fuska cike da tsantsar gsky ya fara mgn a sanyaye.
Yayinda shi kuwa Dr Rayyern