Showing 117001 words to 120000 words out of 132995 words
sai kije kiyi mata duk wata sayayya da ta dace.”
Kai Mamy ta jinjina, cikin kuma yin kasa da murya da alaman ladabi tace.
“Mijinta kuwa?”
“K’warai kuwa shid’in dai, ai yanzu duk wani nauyinta ya rataya ne akan wuyansa ne.
Hakkinsa ne dole kuma shi zai sauke dan haka ya fara da wurima.”
Kai Mamyn ta jinjina, kana a gamsashe tace.
“To shikenan Insha Allah zanyi masa magana.”
Daga haka kuwa babu wanda ya sake cewa komai, suka ci gaba da cin abincinsu.
Bayan sun kammala ne cin abincinnasu ne kuma suka dawo cikin falon.
Mamy kuwa Ganin lokaci ya danja sosai ne, yasa ta kalli Ramadan, kana cikin kulawa tace.
“Ramadan jeka kiramin Hammanku, gashi har kusan goma ko breakfast bai sauk’o yayi ba.”
“To.” Ramadan yace tare kuma da mik’ewa ya haura sama, Koda ya k’arasa d’akin Rayyern d’in, samunsa yayi acikin blanket yana ta bacci.
Batare daya tashesa ba kuma ya juyo, tare da dawowa falon.
Tun kafun ya zauna kuma ya kalli Mamyn tare da cewa.
“Mamy Hamma Rayyern fa bacci yakeyi, ni kuma gaskiya tsoron tashinsa nake kada na tashesa kuma ya hauni da fad’a.”
D’an Jim Mamyn tayi, tare da mik’ewa tsaye tace.
“Shikenan badamuwa bari na fad’awa Abban ku.”
Kaitsaye falon Abban ta wuce.
Koda taje zaune tasa meshi, zama tayi ad’an gefensa kana cikin tausasa Murya tace.
“Natura Ramadan ya kira Rayyern, amma yace bacci yake har yanzu bai tashi ba, ka kumasan Rayyern kwata kwata baya so atashesa Idan yana bacci kasan matsalar ciwon kansa.”
Kai Abban ya girgiza bayan ya tankwashe kafafunsa ne kuma ya d’ago da kansa ya kalli Mamyn, cikin bada umarni kuma yace.
“Yau dai kam atashesa daga baccin da yakeyi, saboda yana da kyau yasan cewar yanzu bawai lokacin kansa kawai yake dashi ba.
Yana da lokaci wata, maza ki tura Ramadan ya taso sa.”
Kai Mamyn ta jinjina, cikin Dan ladabtar da murya tace.
“Ramadan yace yana jin tsoron tashin sa, kada Yayi masa fad’a”
“To ke kije ki tasosa.”
Abban ya fad’a kaitsaye.
Jin hakanne kuma yasa Mamy yin shiru, saboda tasani Sam Rayyern bayaso Idan yana bacci azo atashesa any how, musamman kuma kasancewar yana da matsalan ciwon Kai, shiyasa Mamyn ma take gudun yin duk wani abu dazai takurasa, domin tun yana karaminsa, Idan yana bacci bata cika son tashinsa, saidai idan ya gaji ya tashi dan kansa.
Fahimtar hakanne kuma yasa Abba mik’ewa tsaye, tare da cewa.
“To ni bari naje na tasosa da kaina.”
Hakan kuwa akayi inda kaitsaye ya nufi sama, nan sashin Rayyern din.
Yana zuwa kuwa ya tura kofar dakin ya shiga.
Still Rayyern din bacci yake.
Yayinda ya lullub’e duka jikinsa da blanket.
Karasa shigowa dakin Abba yayi,
Idanu ya ɗan zuwa fuskar Rayyern ɗin yana mai tuno wata kamanceceniya.
Numfashi ya ɗan fesar tare kuma da matsowa ya daura hannunsa dai-dai kan wuyan Rayyern din, Jin da yayi jikin Rayyern d’in babu alaman zafi ne, yasa shi soma kiran sunansa a nitse.
“Rayyern! Rayyern!! Rayyern!!!.”
Abban ya kira sunansa sau uku cikin kuma yanayin Dan daga murya.
Take kuma sauti da Amon muryar Abban ya ratsa kunnuwansa, wanda hakan ya sashi soma bud’e lumsasssun idanunsa ahankali, lokaci daya kuma jijiyoyin kansa suka amsa.
Saidai Ganin Abban nasa da yayi atsaye ne yasashi karasa bude idanunsa.
Abba kuwa gyara tsayuwarsa yayi, tare da cewa.
“Katashi daga wannan baccin da kakeyi kaje kaci abinci, sam baka karya ba, sannan kuma ka kawo kudi za’aje a iyawa matarka sayayya.”
Jin an ambaci mata ne kuma yasa shi shagwab’e fuska, tare da karyar da wuyansa gefe, cikin zallar yanayin shagwab’a yace.
“Abba kudi kuma, ni fa banida kudi.”
Tsareshi da ido Abban yayi, kana cikin tsare gida yace.
“Ka kawo kudi za’ayiwa matarka sayayya nace, ko kamanta cewar yanzu duk wani ci da sha da tufatarwar ta yana wuyanka ne?”
Bakinsa ya d’an tura gaba, kana cikin lumshe ido, ya mirgina gefe tare da saka hannunsa akan bedside drawer, ya d’auko Atm card d’insa, mikawa Abban atm card din yayi, still yana ta tura baki tamkar wani karamin yaro.
Abba kuwa karb’an atm card din yayi, batare daya sake cewa Rayyern din komai ba ya juya ya fice sabida yasan Ramadan yasan pin number sa.
Yana fita kuwa Rayyern ya sake langwab’ar da kansa, cikin wani irin takaicin yarinyar da aka tashesa daga baccin da yakeyi ta sanadiyarta, kwana daya kawai tak da tayi agidannasu, yau gashi har an fara takura rayuwarsa da shiga sabgar sa a kanta.
Abba kuwa Koda ya sauko kasa, atm card din ya bawa Mamy tare da cewa.
“Kisaya mata duk wani abu da kikasan zata buk’ata, maganan suturun sawa kuma ki saya mata isassu, komai da komai ahada a saya mata.”
“To Insha Allah, zan saya mata duk wani abu daya dace.”
Ramadan dake gefe ne kuma yace.
“Mamy nida Riyyam zamuyi miki rakiya, ko Riyyam.”
Ya ƙare mgnar yana kallon Riyyam-nsra.
Kai Riyyam ya jinjina cikin sauri, hade da cewa.
“Eh Mamy zamu rakaki, Ado Bayero Mall zamuje ko Jifatu, ko kuma Mudassir and Brothers?”
Murmushi Mamy tayi, tare da cewa.
“Shoprite dindai zamu fara zuwa, saboda nasan akwai komai da komai, Idan akazo b’angaren dogin riguna kuma, sai muje Jifatu, yanzu dai bari naje na shirya saina zo mutafi.”
“To.”
Suka amsa mata.
Ramadan kuma juyowa yayi ya kalli Riyyam-nsra tare da cewa.
“Wai ni kam yaushe kasan Kano haka!?.”
Kai ya shafa tare da cewa.
“Nida jihata ƙasata!”.
Kiran wayarshi da akayi ne yasa baibi ta kan furucin Riyyam-nsra ba.
Yayinda ita kuwa Mamy kaitsaye bedroom dinta ta wuce, bayan tayi wankane kuma ta shirya kanta acikin, wani tsadadden leshi, tare da yafa mayafinta cikin kamala ta fito.
Kaitsaye kuma d’akin Jannart din ta nufa.
Koda ta shiga falon, yanzun ma bata iske Jannart dinba shiyasa kaitsaye ta wuce cikin d’akin.
A dai-dai lokacin kuwa Jannart din, zaune take abakin gado, hannunta rike da wani dan littafi na turanci tana karantawa, wanda kuma yana daya daga cikin, yan abubuwan da ta taho dashi.
Ganin Mamy da tayi ne kuma, yasa tayi saurin sunkuyar da kanta k’asa, Mamy kuwa murmushi tayi, kana cikin kulawa tace.
“Jannart nida Ramadan da Riyyam zamuje kasuwa, sannan Abbanku ma zasu fita yanzu saboda naji dazu suna magana da Baba Maud’o akan cewar zasuje wani waje.”
Cikin girmama tace.
“Toh Mamy sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya”.
Amin Mamy kana ta daura da cewa.
“Yanzu ki fad’amin me dame kikeso asayo miki Idan munje.”
Kai Jannart din ta dan sunkuyar k’asa, cikin sanyin murya, had’i da tsantsar ladabinta ga Mamyn tace.
“Mamy duk abunda kika sayamin yayi.”
Kai Mamyn ta jinjina cike da gamsuwa kuma tace.
“Masha Allah! To bari muje saimun dawo ko. Idan zaman dakin ya isheki, zaki iya fitowa falonki kisha iska, ko kallo kiyi nasan zai d’ebe miki kewa kafin mu dawo”.
“To Mamy, amman sai yaushe zaku dawo ne?”.
Jannart din ta tambaya, cikin tausasa murya.
Murmushi Mamyn tayi, again kuma itama cikin kulawa tace.
“Jannart kinsan yanayin kasuwa, Idan ka shigesa sai abunda Allah yayi, kana lisssafin zaka dawo da wurwuri, kuma sai kaga ba haka abun yake ba.”
Kai Jannart din ta jinjina, inda Mamy kuwa ta cigaba da cewa.
“Ni kaina bansan yaushe zamu dawo ba, saboda iya yanayin cikowan jama’a,n da muka samu, iya jimawan mu, amma dai Ina da yakinin bazamu wuce azahar ba.”
“Mamy har azahar.”
Jannart din ta tambaya fuska a karye.
“Eh mana Jannart, domin ya danganta da irin abubuwan da zamu saya, kuma kinga yanzu ma ana neman wajen karfe sha d’aya bamu tafiba.”
Kai Jannart din ta jinjina tare da gyara zamanta, tace.
“To Mamy saikun dawo Allah ya tsare.”
Da “Ameen.”
Mamyn ta amsa, harta juya zata fitane kuma idanunta suka Sauk’a, akan breakfast din da ta kawowa Jannart din, wanda ko tab’ashi batayi ba.
Kallonta Mamyn tayi, kana cikin kulawa tace.
“Jannart Meyasa baki ci abincin dana kawo miki ba?.”
Kai Jannart din ta dan sunkuyar kasa, kana murya asanyaye tace.
“Mamy banajin yunwa sosai ne, amma zanci zuwa anjima.”
“A’akam, banyarda da hakan ba, sam ban lamunci zama da yunwa ba sauk’o maza kici abinci kinji.”
Mamyn ta fad’a tana me kamo hannunta, ta zaunar da ita akan sofa, tare da matso mata kwanon abincin gabanta, cikin kulawa kuma tace.
“Kici abinci kinji, kada ki zauna da yunwa, domin yunwa tana illatar da lafiya, ko ke dinma irin Mijin naki ne, baku damu da abinci ba sai kayan kwalama.”
Shiru Jannart din tayi, kana Cikin matukar kunya, ta sadda kanta kasa, domin aduk sanda taji ance mijinta, wani irin abu ne takeji mai nauyi ya tsaya akan kirjinta to waye mijin? Ya yake? Me halinsa?.
Wadanan sune tambayoyin da takewa kanta tun jiya.
Mamy kuwa zuba mata abincin acikin plate tayi, tare da cewa.
“Idan kina buk’atar wani abu kafun mudawo, akwai kitchine anan cikin falon mu.
Taso ma muje na nuna miki.”
Mamyn ta fad’a tana me kamo, hannunta babu musu kuwa Jannart din ta mik’e, tare dabin bayan Mamyn suka fito, har cikin babban falon.
“Kinga wannan shine kitchine dinmu, wacccan kofan kuma anan part dina dana Abbansu Rayyern yake akwai kofar shiga da fita ta cikin falonmu wanda ba sai anbi ta nan ba.”
Mamyn ta fad’a tana meyi mata nuni da kitchine da kuma sashin su ita da Abba.
Kai Jannart din ta jinjina cike da gamsuwa.
“Can kuma dakunan k’asane irin Part ɗin dake sama ne. sai kuma sama inda anan bedroom na Rayyern, da kuma Ramadan suke, sai kuma extra part guda d’aya da yake can ta woje.
Sai nasu Baba Mauɗo, sai wanda kike ciki.
A can saman Mai gidanki yake.”
Mamyn ta k’are maganan tana meyi mata nuni da saman.
Jannart kuwa, kanta tad’an sadda k’asa, tare kuma da soma wasa da y’an yatsun hannunta, kana cikin sanyin murya tace.
“Mamy To meza’a girka yau d’in, kafun kudawo zan girka tunda dama ina zaune ne kawai babu abunda nakeyi.”
Murmushi Mamy tayi, tare da girgiza Kanta, kana cikin tsananin kulawa tace.
“A'a ki huta kinji Januart, bana son ki shiga kitchine daga yanzu.
Idan na dawo, zan girka abincin karki damu, ai bazamu wani jima sosai ba”
Dan juya kanta, tayi, saboda zuwan su Ramadan da kuma Riyyam kallonsu ta ɗanyi kana ta juyo ta kalli Mamy, atsanake cikin yanayin dake nuna biyayyarta tace.
“Da gaske Allah Mamy zanyi girkin, kinga zaku dawo a gajiye.”
Riyyam-nsra da yake karasowa wajennasu ne yayi saurin cab’e zancen da cewa.
“Please mana Mamy kibar My Aunty tayi mana girki yau, nasan abincinta dole zaiyi dadi.”
Jin muryar Riyyam-nsra dinne kuma yasa Jannart ɗin.
Dan dago da kanta, ta kallesu dai dai lokacinne kuma Ramadan ma
Ya karaso wajen.
Fuskarsa dauke da murmushi kuma yake Kallon matar Hamman nasa.
Cikin sakin fuska da kuma walwala yace.
“Good morning my beautiful Aunty, ya kwanan bak’unta.”
Murmushi ta ɗanyi kana ta ɗan kalleshi.
Tare da cewa tace.
“Morning.”
Riyyam ne yayi saurin matsowa kusa da ita, tare da danyin kasa da muryarsa, cikin kulawa yace.
“Aha My Aunty kin tunani ko?”.
cikin ɗan sakin fuska ta gyaɗa mishi kai, alamun ta tunoshi haduwarsu a airport,
Cikin yanayin rawan kansa yace.
“Aunty Jannart ni sunana Riyyam-nsra, tiktokers nasan kinsani ko?”.
Murmushi tayi tare da gyaɗa kai, ganin yadda ya tsareta da ido.
Kuma tabbas ta tunoshi haɗuwarsu a airport.
Shima murmushi yayi tare da cewa.
“Yauwa shi kuma wannan Hamma Ramadan sunansa, kuma yaya nane, akwai kuma babban yayanmu Hamma Rayyern.”
“Please kiyi mana abinci maidadi kinji, wanda zaisa kunnuwanmu su motsa.”
Ba iya Mamy da Ramadan ba harta ita saida ta saki murmushi mai hade da dan dariya.
Mamy kuwa Ganin lokaci na k’ure musu ne yasa, tace.
“Jannart rabu da shirmen Riyyam, koma daki kije kici abincinki.
Maganan girki kuma tunda kin dage sai kinyi, ki dafa mana abu mai sauki kawai.”
Kai Jannart din ta jinjina, sannan cikin zazzakar muryarta tace.
“Mamy ku dawo lafiya.”
Da “Ameen” duk sauka amsa, inda Mamy ta had’a kan Ramadan da Riyyam sukayi waje.
Itakuwa Jannart d’akinta ta koma, duk da cewar bata wani jin yunwa amma haka ta zauna ta d’an ci abincin, bayan ta kammala ne kuma ta d’aura da, lemon strawberry da Mamyn ta had’o mata dashi.
Gyatsa mai sanyi tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
Kana ta yunƙura
A nitse ta mik’e tsaye tare da d’aukan plates din da taci abincin ta fita dashi.
A hankali ta buɗe ƙofar falon nata.
Kana ta sako kanta.
Cikin Babban falon.
Numfashi ta dan fesar sabida wani irin masifeffen sanyin AC'n da suke busowa duka biyu.
A hankali take takowa har ta iso tsakiyar falon.
“Masha Allah, Mamy ba dai tsabta ba”.
Ta faɗi haka tana jujjuya kai tana kallon komai doke cikin falon.
Tsab-tsab sai ƙamshi da sanyi daya wadaci falon.
A hankali ta juyo ta nufi Dinning area.
Tray'n dake hannunta ta ajiye kam table ɗin.
Kana ta juya a nitse.
Ta dawo tsakiyar falon.
Gaban tv ta nufa.
Sabida shiru da gidan yayi sai taji kamar tana tsoron gidan.
TV'n ta kunna cikin sa'a kuma kan tashar Sunnan TV yake.
Inda aka saka sautin muryar Malam Sulaiman.
Rage sautin tayi dai-dai misali.
Kana a hankali ta juya ta nufi Dinning area.
Tray'n data ajiye ta ɗauka a hankali ta nufi Kitchen kaitsaye.
“Wow. Masha Allah”.
Ta kuma faɗa tana mai bin tsarin Kitchen da kallo komai tsab-tsab.
Kai tsabta rahmace.
Ta kuma cewa tana mai
nannad’e hannun rigarta.
Tare kuma da k’arasawa gaban sink, plates din da taci abincin ta wanke, bayan ta kammala wanke wanken ne kuma.
Ta ɗan tsaya jim a tsakiyar Kitchen din.
Cikin sanyin murya tace.
“Toh me zan dafa?”.
Tayi mgnar alamun tambayar kai da kai.
Kanta ta ɗan jinjina kana matso gaban Fridge guda biyu dake cikin Kitchen din.
A hankali ta bud’e babban deep freezer
Kai ta jinjina tare da ƙara matsowa.
Gaba daya cikinsa shak’e yake da kayan Miya, hadi da kuma naman, Rago, Saniya, da kuma naman kaji, sai kifayen da tuni sun daskare ma acikin fridgen.
Naman kaza ta d’ebo d’an da-dai.
bayan ta wanke naman ne kuma ta zubashi acikin tukunya tare da kunna gas ta d’aurashi akai, al'basa ta ɗauka wanda ta gani a jere cikin wani da karfe.
Mai yawa ta yanka kana ta watsa a cikin naman.
Kana ta ɗan kalli gefenta inda wasu robobi farare masu marafe pink color ke jere, da kayan bukatu kamarsu. k’amshi, da dandano.
garlic, kanumfari da kuma maggi Corry ta saka.
Kana ta meda marfin ta rufe.
Sai kuma taja kujera ɗaya dake gaban ɗan ƙaramin table ɗin dake tsakiyar Kitchen din ta zauna tana mai tunanin to me zata dafa musu.
Lokaci ɗaya.
Gidan ya cika da ƙamshin tafashen.
A hankali ta ɗan juyo ta kalli tukunyar daketa fidda tururi mai masifar ƙamshi.
Ganin naman na dahuwa ne kuma yasa ta mike ta sake bud’e fridge din, inda ta ibo.
Pease, green beans, carrot, green pepper, red chilies, cabbage, cucumber, onion, and liver, tsayuwa tayi na musamman inda ta yanka kowannensu, awaje na musamman, saidai Banda carrot wanda tayi greeting d’insa.
Bayan ta kammala duk wayannan dinne kuma, kazan na gama dahuwa.
Ta sauƙeshi kana ta ɗauki kaskon suya ta doro tare da zuba mai.
Kana ta fara soya shi sama sama.
Tana gama ta ajiyeshi gefe.
Kana ta ɗauko kayan miyanta duk abin buƙata
tare fara aikinta a nitse ta hada masa pepper onion chicken soup.
Gaba ɗaya kwamshin ya ƙara de ko ina.
Tana kammala had’a kazartata kuwa ta d’aura shinkafa kasancewar, fried rice and coleslaw takeson yi.
Da ɗan hanzarin taci gaba da aikinta yanayi tana ɗan jujjuyawa da waige-wauge na bakunta da kaɗaici.
Cikin abunda bai wuce awa ɗaya da rabi ba kuwa ta kammala, had’a abincin acikin babban food flask.
Bayan ta gama da abincinne kuma ta dawo b’angaren drinks.
Shaka mai dadin gaske ta had’a musu, sai kuma pineapple and orange juice.
Cikin abunda bai wuce 50mn ba ta gama haɗa abubuwan shan, gidansu Rayyern din gaba d’aya ya kacame da k’amshin daddad’an girkinta.
Ganin akwai sauran lokaci ne kuma yasa ta, had’a fan cake ta somayi.
Acan b’angaren Rayyern kuwa, sai yanzu yake tashi daga kwanciyar da yayi, ahankali ya zuro da k’afafunsa k’asa, tare kuma da mik’ewa, kaitsaye ya nufi bathroom saboda yanason sakarwa kansa ruwa.
Ajiyar zuciya ya sauk’e a dai-dai lokacin da yaji saukar ruwan shower ajikinsa, lokaci daya kuma ya lumshe idanunsa, tare da soma gogawa jikinsa sabulu.
Cikin nutsuwa yayi wankasa, tare da d’auro alwala.
Yana fitowa daga cikin toilet din kuwa, k’arar fitar motar Abba, wanda suka fita da Baba Maud’o ya daki kunnensa.
Wanda ya fita da Baba Mauɗo.
D’an langawab’ar da kansa gefe yayi, tare dasa hannu ya shafa lafaffen cikinsa, kasancewar sai ayanzu ne ma yake tuna cewar rabonsa da abinci tun daren jiya, sosai kuma zuwa yanzu yakejin yunwa na k’wak’ulan cikinsa.
Anutse ya shafawa jikinsa mai, bayan ya kammala shafa mai dinne kuma, ya karasa gaban Sif din kayansa.
Wani had’add’en rika da wando, masu masifar taushi pink color masu digon fari-fari.
ya ciro tare da sakawa ajikinsa, kasancewar kuma rigar irin mai aninaye a gaban nanne, yasa faffadan chest d’insa bayyana.
Body spray ya shafa ajikinsa, tare kuma da d’aukan watch d’insa ya makala.
Masha Allah bak’aramin kyau shigar riga da wandon tayi masa ba, musamman ma yanda kawataccen sajensa keta shining ya kwanta lib.
Wayarsa ya d’auka, tare da k’arasawa, jikin dan karamin fridgen dake cikin dakin nasa ya bud’e, fuskarsa ya d’an ya mutsa, saboda yanda yaga fridge din babu komai naci acikinsa, chocolates dinsa duk sun kare, sai drinks kawai da sukayi saura.
Maida murfin fridgen yayi ya rufe, kaitsaye kuma ya nufi cikin falon nasu dake sama, saidai still shima babu komai acikinsa, sai kayan shaye shaye.
Kansa ya d’an girgiza saboda yunwa sosai yakeji.
Batare da tunanin wani abu ba kuwa, ya nufi falon k’asa, inda ahankali yake sauk’owa daga kan matattakalan falon, Yayinda k’amshin sa ke dada mamaye ko ina.
Saidai kuma jin da yayi ko ina shiru babu motsin mutanene yasashi soma rarraba idanunsa ba amun kowa a gidan.
Sai wani ɗan karen kamshin da yake shige masa hanci.
K’arasa sauk’owa daga kan steps din yayi, tare da k’arasowa tsakiyan falon ya tsaya, hannayensa duka biyu ya d’aura akan k’ugunsa, tare kuma da karyar da wuya ya d’an langwab’ar da kansa gefe, cike da alamun shagwab’a.
Acan cikin kitchine kuwa Jannart ce tsaye, tana k’arasa had’a fan cake din da takeyi.
Tana aikinta a sake.
sabida doguwar rigarta ne ajikinta, sai kuma dan kwalin rigar da ta daura akanta, wanda hakanne kuma yasa dogon gashinta ya baje akan gadon bayanta kuma a zatonta babu kowa a gidan sai masu gadi.
Aikinta take cike da nutsuwa, Yayinda karatun al’q’uranin da ta kunna acikin falon ke kawowa kunnuwanta ziyara har Cikin Kitchen din shiyasa tsoronta ya kau.
Rayyern kuwa daya gama k’arewa falon kallo, Ganin babu motsin kowa acikinsa ne, yasa kaitsaye ya nufi dining table, inda