Showing 102001 words to 105000 words out of 132995 words
yasa kuma wani matakin nasara ne.”
“Ameen.” Ya fad’a, Ganin fitowar Ramadan daga cikin toilet ne kuma, yasa shi katse kiran, inda yacewa Mammyn nasa zai kirata anjima.
Acan falon Abba kuwa tafiyar su Rayyern dinne, yasa Usman P.A, Hadi da kuma Ari mikewa duk suka fice daga cikin falon, suna mai fadin Allah ya sanya alkhairi acikin auren.
Baba Maud’o kuwa Kallon su Barrister Kabir yayi, cikin muryar dake bayyana farin cikinsa, yace.
“Barrister mun gode da kyauta mai daraja.
Yanzu yaushe ne za’a je d’auko mana diyar tamu.”
Gyara zama Barrister Kabir din yayi, kana cikin mutumtawa yace.
“Insha Allah ni dakaina zan kawo muku diyar ku, bama sai kunje d’auko ta ba.
Domin kamar yanda aka daura auren nan, asirrance haka kawo amaryar ma zai kasance asirrance, saboda nima acikin hikima zan samu na fita da ita daga cikin gidan da yake gab da zame mata kabari, bisa taimakon maigadin gidan, da kuma driver’nta, saboda mun shirya akan da misalin k’arfe sha d’aya zata fito daga gidan, Idan ta fito ni kuma zan dauketa na kawota.”
Kai duk suka jinjina, Yayinda Baba Maud’o kuwa yayi murmushi, tare da cewa.
“Masha Allah hakan ma yayi, Allah Ubangiji ya taimaka.” Da “Ameen” duk suka amsa.
Batare daya sake cewa komai ba, kuma ya tashi ya tafi.
Acan b’angaren Rayyern kuwa, yana haurawa sama, babbar rigar dake jikinsa ya zare, tare da hayewa saman gadonsa ya kwanta.
Idanunsa da sukayi ja, ya rumtse da karfi tare kuma da soma fitar da wani irin numfashi mai zafi ta bakinsa.
Shikam acikin rai da zuciyarsa ya rasa wannan wanni irin fitinannen aure ne da aka lik’a masa, gaba daya suna neman dagula masa rayuwarsa, wanda bai kuma San dalilin yin hakan ba, dududu acikin kwanaki goma da dawowarsa daga Ethiopia, acikin kwanaki takwas na cikin gomanne kuma, abubuwa mabanbanta suka faru dashi, aciki kuwa harda babban abu daya kasance Aure.
Auren da bai shirya masa ba, auren da yazo da wani irin k’ulli.
Sam arayuwarsa shi bai tab’a kawo tunani ko maganar aure cikin k’wak’walwarsa ba.
Fact Shi baima tab’aji ajikinsa cewar zaiyi aure ba.
But why yanzu suke son sanja masa rayuwa?
Yar karamar tsuka yaja, tare da gyara kwanciyarsa, cikin takaici kuma abayyane yace.
“Koma meye nidai bazan sanja tsarin rayuwata daga yanda na saba ba, babu wata mace agabana, haka kuma babu wata wanda zan tsaya kulawa da ita ehe inji da kaina ma mana.”
Ya kare maganan yana me jawo murfin bedside drawer’nsa, inda ya d’auko ledan chocolate d’insa na kinder bueno, bayan ya bare ledanne kuma yasa chocolate din abakinsa yana sha.
Acan falon kasa kuwa, su Abban suna gama tattaunawa ne, Barrister Kabir da kuma Dr. Sajo suka mik’e Daniyar tafiya, har bakin mota kuwa Abba ya rakasu.
Bayan yaga tafiyarsu ne kuma ya dawo gida, kaitsaye kuma dakin Mamy ya nufa, Dan sanar da ita abunda ke wakana.
*Jannart*
Zaune take akan lallausan carpet dake, cikin falon nasu, Yayinda ta duk’ar da kanta k’asa, nail cutter ne hannunta, tana gyara yan fara tun yatsun kafarta, Yayinda Momy da kuma Abdull ke zaune agefe.
Azahirance Idan ka kalleta zakayi tunanin, cewa hankalinta ya tafi ne Izuwa kan nails dinta da take gyarawa, saidai kuma awajenta sam ba hakan bane.
Domin tunaninta ya tafine izuwa wani waje na daban, wani abu takeji na musamman yau din, Domin kuwa abubuwa uku ne suka hade acikin rai da zuciyarta, Wanda kuma batasan dalilin jin hakan da takeyi ba.
Idanunta tad’an lumshe ahankali, saboda yanda takejin kirjinta na bugawa time to time, kuma zuciyarta na tsinkewa, Yayinda wani abu mai kama da fargaba ke yawan tasan mata.
Acan kasan zuciyarta kuwa, ji take tamkar ana zare mata wani babban kaso na daga cikin damuwarta.
Jin kanta take tamkar awata duniya sabuwa.
Bud’e kofar falon da akayi ne kuma yasa ta saurin d’ago kanta.
Inda idanunta sukayi mata tozali da Daddy.
Har zata dauke Idanunta daga kan Daddy’n ne kuma, Idanunta suka sauka akan Junaid dake bayan Dadyn, wani irin matsanancin fad’uwar gaba taji, lokaci daya kuma duk jikinta ya d’auki tsuma.
Wani irin matsanancin tsoro ne ya shigeta, wanda hakan yasa tayi saurin mik’ewa tsaye.
Ido biyu da sukayi da Junaid dinne kuma, yasa ta soma girgiza kanta, tare da jan jikinta baya baya.
Kamar wanda aka tsikara kuma, haka ta juya Cikin sauri, har k’afafunta na hard’ewa ta nufi sama.
Idanu Junaid ya zazzaro cike da haushi hadi da takaici.
Yace.
“Ke Jannart, Ki dawo nan dan Uwarki mahaukaci kika ganine da zaki gudu, ki dawo nan na fad’a miki.”
Ya k’are maganan cikin d’aga murya da tsananin b’acin rai.
Jannart kuwa duk da taji kiran da yakeyi mata din, amma Sam batajin zata tsaya ko ta juyo ta sauraresa.
Domin sosai ganin nasa ya haifar mata da tsoro, hadi da kuma tsananin fargaba, kasancewar. Ganin nasa da tayi ayanzu, ya dawo mata da duk wata bakar izaya daya gana mata.
Daddy dake tsaye kuwa, Ganin hakan bai wani dameshi ba, hasali ko damuwa baiyi ba, saima juyawa da yayi ya fice daga cikin falon, yana me amsa kiran wayan da akayi masa.
Momy da Abdull kuwa tsit sukayi, domin sunsan suna magana zai sauke abunda ke tsakiyar kanshi anasu kan.
Kwata kwata Junaid ba mutumci ne dashi ba, baya ganin darajar kowa acikin gidan, musamman ma Momy da ko kadan baya mutumtata, amatsayinta na matar Babansa.
K’wafa yaja tare da fesar da hucin sauran hayakin taban dake bakinsa, cikin haushi da kufula kuma ya zaro wayarsa tare da dannawa numbern Jannart din kira.
Jannart kuwa da bata zame ko ina ba sai cikin dakinta, tana shiga kuma ta dannawa kofar key.
Numfarfashi ta soma fitarwa, tare dasa hannunta ta dafe kirjinta dake bugawa, dai-dai lokacinne kuma kiran Junaid din ya shigo cikin wayarta.
Arazane takai dubanta ga screen din wayar, ganin sunan Junaid din dake yawo akan screen din wayar nata ne kuma, yasa tayi saurin karasawa jikin gadonta, ayunkurinta na rejecting call dinne kuma, tayi picking batare da ta sani ba, still batare kuma da ta.
Ankara da hakan ba, ta cilla wayartata kan gado, tare da daura pillow akanta ta kwanta.
Junaid dake tsaye afalo kuwa jin Jannart din ta d’aga wayarne yasa, amatukar hasale yace.
“Yau zakici uwarki wallahi, wancan karon Sumar dake kawai nayi, amma yanzu kasheki ma zanyi kawai kowa ya huta, wallahil azim kuma nayi rantsuwa, adaren yau basai gobe ba saina cika burina akanki, yar iskar yarinya kawai me zubin munafukai.”
Yana gama fad’an hakan ya kashe kiran, sai faman zuba huci yake tamkar mayunwacin zaki.
Dab da zaifita ne kuma ya juyo, ya bankawa Mom da kuma Abdull Harara, cikin halinsa na y’an shaye shaye daya saba yace.
“Mchewww munafukai kawai.”
Yana gama fadin haka yasa kai ya fice daga cikin falon.
Momy kuwa Kai ta girgiza, cike da takaicin halin Junaid din kuma tace.
“Insha Allah babu wani burinka dazai cika akan Jannart, bazaka tab’a samun nasara akants ba kowanni mugun nufinka, in banda ma halin dabbanci da hauka, ace yarinya uwarku daya ubanku daya amma baka da aiki sai musgunawa, da son b’ata rayuwarta, hmmm Allah Ya kyauta.”
Abdull dai dake zaune shiru yayi, saidai kuma har acikin zuciyarsa yana matuk’ar takaicin irin rayuwar da akeyi acikin gidan nasu, wanda kwata-kwata babu girmamawa ko tarbiya acikinsa, kiri-kiri ana zalunci amma babu wani wanda zaiyi magana.
Acan b’angaren su Abba Kabir kuwa, Koda suka baro gidansu Dr. Rayyern, abakin titi Dr Sajo ya sauk’e Abba Kabir, inda kaitsaye Abban ya Tari taxi ya nufo gidansu Jannart.
Koda ya iso cikin unguwar daga nesa, yasa mai taxi din ya sauk’eshi, bayan ya biyasa kudinsa ne kuma kaitsaye ya nufi katafaren gidan Yayan nasa.
Tura k’aramar k’ofar dake jikin gate din yayi ya shiga, bayan sun gaisa dasu Ashiru dake bakin gate dinne kuma kaitsaye, ya nufi cikin gidan.
Koda ya shigo ya samu su Momyn, bayan sun gaisa ne kuma Momyn tasa Abdull ya cika masa Dan table din dake gabansa da kayan drinks hadi da fruits.
Lemun exotic ya dan kurb’a, tare da duban Momyn.
“Yaya Baya nan ne?”
Ya tambaya da kulawa.
“Eh dazun nan ya fita babu jimawa, amma munyi waya dashi, wai wani meeting ne aka kirasa na gaggawa.” Momyn ta bashi amsa.
Shikuwa kansa ya jinjina, alaman gamsuwa, kamar zaiyi shiru kuma sai ya sake duban Mamy, tare da cewa.
“Jannart fa, kodai ta tafi wajen aiki ne? Duk da shigowa na ma naga guard dinta awaje.”
Ajiyar zuciya Momy ta sauke, cikin Dan yanayin sanyi kuma tace.
“A’a Jannart tana sama, batama jima da haurawa ba, dazu dukanmu mu nan azaune, dawowan Junaid ne yasa duk ta tsorita.”
D’an Jim Barrister Kabir din yayi, na y’an wasu daƙiƙu kafun daga bisani, ya mik’e tsaye, yana me cewa.
“Badamuwa To bari na haura saman na duba ta.”
Da “To.” Momyn ta amsa, Yayinda shikuwa kaitsaye ya wuce saman.
Koda ya karasa jikin kofar nata tsayawa yayi, tare da kwankwasawa.
Jannart dake kwance akan gadonta, Jin ana knocking kofar nata ne yasa ta zaro Idanunta da sauri tare da tashi zaune.
Kana cikin yanayi na tsoro, saboda duk atunaninta Ya Junaid dinne ya biyota.
“Jannart! Jannart ki bude nine Abba ne.”
Barrister Kabir ya fad’a, cikin dan daga murya yanda zata jiyosa.
Jin muryar Abba Kabir dinne kuma ya sata, sauke Wata irin wawiyar Ajiyar zuciya, tare da tashi cikin sauri ta nufi kofar.
Murza key din tayi ta bud’e k’ofar, wanda hakan ya bashi daman shigowa, murmushi tayi kana cikin jin wani abu na daban, acikin zuciyarta da ganin nasa ya haifar mata tace.
“Good morning Abba.”
“Morning Jannart, fatan kina lafiya.”
“Lafiya na kalau Abba.”
Ta fad’a tana me komawa kan gado ta zauna.
Shikuwa Abba Kabir din karasawa cikin dakin yayi, tare da zama akan daya daga cikin bedside carbinate dinta.
Bayan ya zauna dinne kuma, ya zura Hannunsa acikin aljihun rigarsa, tare da zaro rapper’n kud’i.
“Jannart.”
Ya kira sunanta cikin tausasawa.
“Na’am Abba.” Jannart din ta amsa tana me juyowa izuwa gareshi.
Shikuwa Abban Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauk’e, tare da d’an muskutawa ya kamo hannayenta, rappern kudin dake hannunsa ya dank’a mata acikin nata hannun.
Cikin muryar da yake fatan zata gamsar da ita yace.
“Ga sadakin ki Jannart, an d’aura miki Aure yau, bayan an idar da sallan Jumma’a.”
Amatuk’ar razane da kuma wani irin bugun zuciya ta d’ago Idanunta da suka firfito ta kalleshi, hakanan taji maganan Abban nata wata iri, duk da kuwa tasan da plan d’insa nayi mata aure, amma sam kwata-kwata bata tab’a kawowa aranta cewar, arana irin tayau za’a daura mata aure ba kana taji kalmar tayi mata nauyi.
Ganin Abba Kabir din na kallonta ne kuma yasa Ahankali ta janye Idanunta kasa, tare da kama y’an yatsun hannunta ta soma motsawa.
“Jannart.”
Again Barrister Kabir din ya sake kiran sunanta.
Idanunta da sukayi raurau ta d’ago ta kallesa, dai-dai lokacin kuwa hawayen dake cikin idanun nata suka gangaro zuwa kan k’uncinta.
Cikin sanyi da kuma raunin dake kwance acikin zuciyarta tace.
“Abba Karik’e su awajenka.”
Kai Abba Kabir din ya girgiza, tare kuma da dan gyara zamansa yace.
“Bazan karb’a ba Jannart, sadakin kine kuma halal dinki, sabida haka ki rik’e awajenki.”
Yana gama fad’in haka ya kuma saka hannayensa acikin aljihun rigarsa, sweets da kuma chewing gums ya fito dashi, tare da Mika mata Cikin kulawa yace.
“Ga goro da kuma sweets din daurin aurenki.
Alhamdulillah kin tabbata matar aure yanzu Jannart, babu wani wanda zai sake kokarin keta haddinki, ayanzu kin tabbata mai y’anci, zan kaiki inda zaki samu kariya, zan kaiki wajen way’anda nake da tabbacin cewa ko bayan ba raina, zasu zame miki Garkuwa, har abada ina al'fahari da wannan Auren naki Jannart, kuma Insha Allah yau da dare zan kaiki d’akinki, na dank’aki ga Mijinki, sannan karki damu da batun su Baba Ado da Baba Ashiru maigadi, akoda yaushe Idan kika fito zaki samesu abakin gate, sannan na sashi yasa maganin bacci acikin abincin bodyguard dinki, ta yanda za ki fita ba tare da sunsan da hakan ba, Baba Ashiru ma yasan duk wani shirin mu, sannan ki tabbatar idan zaki fita babu wanda ya ganki, ciki kuwa harda Momyn ki, Abdull da Junaid, meyene Junaid din ya miki dazu har yasa kika hawo sama.”
Ya jero mata jawabin a tare.
Idanunta ta d’an marairaice, kana asanyaye tace.
“Ni tsoronsa nakeji Abba, daya shigo nagansa shine na gudu, amma kuma ina shigo daki saida ya kirani awaya.”
Kai Abban Ya jinjina, cikin gamsuwa da samun wata sabuwar dama yace.
“Alhamdulillah dama me kyau, to kidai kiyaye idan zaki fita, Idan ba Baba Ashiru da Baba Ado ba, banason kowa ya ganki Jannart, sannan kina fita kibi layin bayan kunnan, ki tsallake layi uku ana gefe zaki sameni Ina tsaye ina jiranki, please Jannart kiyi komai da takatsantsan.
Dan inason na mikaki ga mijinki cikin aminci, wanda nake da yakini akan zamanki acan zai kawar da duk wani damuwarki.”
Kanta ta d’an jinjina, kana cikin muryarta dake rawa tace.
“Insha Allah zanyi abunda kace Abba, amma inajin wani irin acikin zuciya da gangar jikina, inajin cewa zanyi kewar Daddy Momy, da kuma Abdull, yanzu idan na tafi kuma sai yaushe zanzo na gansu?”
Tak’are maganan Idanunta suna zubda da k’walla.
Ajiyar zuciya Abban ya sauke, tare da kamo hannunta Cikin kulawa yace.
“Kada ki damu Jannart, Insha Allah Watan-warana zaki zo ki gansu, komai zai dai-dai-ta.”
Kai ta d’an jinjina, still kuma da muryar kuka tace.
“Abba kayi hakuri kawai dai inajin ba dadi ne, Ina son gidanmu sosai, inajin banason barinsa, matsalata kawai.
Yah Junaid ne, shine wanda ako da yaushe baya son farinciki na, asanadinsa ne kuma yau gashi, zan bar gidan zantafi wajen way’anda, basu sanni ba.”
Hannayenta Abban ya kama, tare da girgiza mata Kai.
“Kada kiyi kuka Jannart, gidan da zan kaiki zai samar miki da ingantaccen farinciki, mutanen cikinsa masu karamci ne kuma zasu zame miki yan uwa da yardar Allah, kinsani Jannart bazan tab’a cutar dake ko na kaiki inda za’a cutar dake ba.”
Kai Jannart din ta jinjina, alaman gamsuwa da kalamansa.
“Yauwa Jannart, Allah ya sanyawa rayuwar aurenki al'barka, sannan idan zaki fita, ki tattare duk wani abu naki mai amfani, kama daga kan laptop da kuma certificates, and duk wasu takardunki masu amfani, ki sasu ajaka ki kuma taho dasu, wayoyinki kuma ki barsu a nan a tsakiyar gadonki. Maganan kaya kuma banda kayan jikinki kada ki d’auki kaya ko kala d’aya, ni da kaina zanje na saya miki kayayyakin da zakina sawa.”
Kanta ta jinjina tana mai son tsaida hawayenta, Yayinda shi kuwa Abba Kabir din, ya mik’e ya fice daga cikin dakin.
Yana fita kuwa Jannart din ta mik’e, jiki asanyaye ta soma harhad’a takardun ta dama yan kananan abubuwan ta masu amfani.
Ab’angaren Abba Kabir kuwa yana fita daga cikin gidan, kaitsaye gidansa ya nufa.
Koda yaje ya samu Aunty Dijat zaune afalo, anan yake shaida mata cewar yau an daura Auren Jannart.
Farinciki ne ya lullub’e zuciyar Aunty Dijat, cikin jin dadi tace.
“Masha Allah, gaskiya naji dadi Allah Ya basu zaman lafiya, yaushe za’a kaita gidan Mijin?”
“Adaren yau zan kaita, amma Dijat karki manta, wannan maganan sirrine atsakaninmu, muddin ta fita daga bakinki, kada kiyi tunanin soyayyar dake tsakaninmu, da kuma irin zaman lafiyar da mukeyi, hadi da al’amarin yaya, zan watsar da ita, zan gurfanar dake agaban hukuma, ke kanki zan iya daura ayar zargi akanki.”
Kai Aunty Dijat din ta jinjina, cikin yin imani da abunda zata fad’a tace.
“Insha Allah Abban Hafeez, zaka sameni me matuk’ar sirrinta sirrinka, da izinin Ubangiji, wannan magana ba zata tab’a fita daga bakina ba.”
Kansa ya jinjina, alaman gamsuwa da bayanan nata.
By
*GARKUWAR FULANI*
https://chat.whatsapp.com/K6m92SSD10n24Jc3FDLxMp
Samun zafafan saukakan kayayyakin zamani na mata tun daga kan leshi, shadda, atamfa, material, jaka da takalmi, hijab..... da dai sauransu akan farashi mai sauki da rahusa sai a kamfanin Garkuwa collection. Bama wannan kadai ba akwai kayan order da muke yi shi ma duk a cikin rahusan da saukin kudi. Ba mu tsaya nan ba ina kuke yan kasar *NIGER* albishirinku kuma kuna iya siyan kayanmu ya isa gareku cikin aminci ba tare da bata lokaci ba. maza yan’uwa ku garzayo ku gane wa kanku wannan rahusar da kuke jin labari. Kayanmu ko a kasuwa ba zaka samu farashinsu ba. gidanmu gidan duniyar leshi, atamfa shadda, material da sauransu. Sai kun zo. Muna maraba da kai a kowanne gari kake.
GARKUWA COLLECTION! Siyan nagari mayar da kudi gida!
Acan B’angaren Daddy kuwa, shida Dr Lukman, da kuma Alhaji Abdu Tababa ne ke zaune, ad’aya daga cikin hall, na Tababa Company.
Wanda kuma gama meeting dinsu kenan, bayan kowa ya watse ne kuma suka d’auko zance akan Rayyern.
K’wafa Alhaji Idi Sale Dakata’n. Yayi, tare da d’agowa ya kalli abokanan makircin nasa.
“Yaron nan Dr. Rayyern ya tsayamin aka, kullum da zancen kawar dashi nake kwana nake tashi, amma Dan iskan yaro har yau ko gidansu na kasa ganewa, yaron yana nan kamar Maye, duk wani motsin da kayi yakan zama tamkar a tsakiyar tafin hannunsa yake, narasa wanni irin yaro ne, nasa abibiyeshi amma ya gane, binciken da yayi akaina kuma saida ya ninka wanda nayi akansa, yanzu shi babu abunda bai sani ha akaina, yasan gidana yasan komai akan al’amurana, ni kuma har yau bansan inane, gidansu ba, nadaisan acikin Nassarawa G.R.A suke, amma bansan Ina ne taka maimai gidansu ba acikin unguwar, duk iya bincikena na gaza ganewa, karfi da yaji.
D’an karamin tsako yana nema ya zamarmin ciwon ido, ya kuma zama dole na kawar dashi dole na b’atar dashi adoron kasa, dole yabar numfasawa nan bada jimawa ba, Domin Idan ba haka ba zai jawo babban b’arakar da dinketa zaiyi mana matuk’ar wahala.”
Gyara zama Alhaji Abdu Tababa yayi, cikin son kwantarwa da Alhaji Idi’n hankali yace.
“Karka damu Insha Allah, duk yanda zamuyi