Showing 42001 words to 45000 words out of 132995 words
Mamyna.”
Abba daya kafe Rayyern din da ido kuwa baya ko k’yaftawa, fuskarsa cike da mamaki yace.
“Rayyern wannan shigar fa yaushe ka fara ta? sannan a ina ka samo alkyabba mai tsananin kyau haka?”
D’an sunkuyar da kansa k’asa yayi, tare da kama y’an yatsun hannunsa ya soma murzawa.
Sam arayuwarsa shi bai iya k’arya ba, impact ma arayuwarsa babu abunda yafi tsana kamar k’arya, bayayin k’arya bakuma yaso ayi masa.
Duk da kuwa yasan Abban nasu bazai so abunba so gskyar da zai fada ba, amma ya zama dole ya gaya masa gaskiya, saboda karya ba d’abi’arsa bace.
“Kayi hakuri Abba Malam Mai-nasara ne ya bani kyautan Alkyabbu guda bakwai.”
Idanu Abba ya kankance cikin kuma nuna rashin jin dadin hakan ya kawar da kansa gefe.
Ganin hakanne kuma yasa Rayyern d’in, ya d’an rank’wafar da kansa.
Kana cikin sigar ban baki yace.
“Kayi hakuri Abba, idan bakason shigartawa sainaje na cire.”
Ajiyar zuciya Abban ya sauk’e kana ahankali yace.
“A’a ni Bance Banason shigarka ba, kayi kyau Tabbas kuma shigar alkyabba shigace da take da matuk’ar mutumci, gashi kuma ta bayyana tsananin haiba da kwarjininka, saidai amma ka kiyaye nan gaba bafa na son wata alaƙa a tsakaninku.”
Kai Rayyern din ya jinjina kana cikin girmama zancen Abban nasu yace.
“Nagode Abba kuma Insha Allah zan kiyaye.”
“Shikenan.” Abban ya fad’a atakaice.
Riyyam-nsra kuwa cikin kasa kosawa da Kallon yanda Hamadan nasu yayi kyau yace.
“Please Hamma Rayyern Ina zakaje.”
“Polo.”
Ya bawa Riyyam din amsa a taƙaice kuma dai-dai lokacin da yake kokarin fita daga falon.
Da sauri Riyyam din ya tashi yabi bayansa, yana me fad’in.
“To Hamma Rayyern tsaya muyi video dan Allah.”
Ramadan dake zaune ma mik’ewa tsaye yayi yabi bayansu.
A compound din gidan suka tsaya, inda Riyyam sarkin tiktok ya saita wayarsa ya soma yi musu video dukansu uku.
Harda sa musu wata y’ar wak’a, shidai Rayyern Kallon Yaron kawai yakeyi, domin a wuni biyu kawai da sukayi da yaron, ya fahimci wani abu, da kuma irin d’abi’a da yaron yayi shura akai.
Saidai kuma baisan Meyasa ba yakejin yaron acikin zuciyarsa hakan yasa yake kasa yakiceshi.
Gama k’arasowarsu compound din gidan kuwa, yayi dai-dai da fitowan Baba Maud’o daga cikin d’an madaidacin Part ɗinsa dake gefen gate.
Yana fitowa dinne kuma ya sauk’e idanunsa akan Rayyern, dake sanye cikin al-kyabba.
Wani irin tsayuwa Baba Maud’on yaji zuciyarsa tayi, take kuma wasu irin abubuwa suka shiga dawowa cikin tunaninsa.
Saidai kuma Ina ayanzu kwakwalwarsa bata da wani buk’atar amsar kowani irin sak’o, wannan dalilin yasa zuciyarsa ke cigaba da bugawa da harbawa a hankali.
D’an matsowa kusa dasu Baba Maud’on yayi, tare kuma da sauk’e idanunsa akan Riyyam wanda keta faman bin wak’ar Justin Bieber me suna (Peaches) dake tashi awayarsa.
Idanu Baba Maud’o ya tsurawa yaron baya ko k’iftawa, Yayinda zuciyarsa ke cike da zallan mamakin, kamannin Rayyern dake kwance akan fuskar yaron.
“Baba Maud’o barka da yammaci.”
Cewar Rayyern.
Wanda maganan nasa ne kuma yasa Baba Maud’o dawowa cikin tunaninsa.
Murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa, duk da kuwa cewar rabin fuskartasa arufe take, amma hakan bai hana Rayyern din gane cewar Baba Maud’on murmushi yayi ba.
“Yauwa Barka dai Rayyern, yau kuma inazaka je haka naga kayi shigar da ta bayyana kyau da cikar haibarka.”
Murmushi Rayyern din yayi, tare da dan matsowa kusa da Baba Maud’on kana yace.
“Wurin wasan polo zanje Baba Maud’o".
Kai ya jinjina alamun gamsuwa.
"Shin ko akwai wasu abubuwan buk’ata naka da suka k’are, idan nazo dawowa saina sayo maka.”
Rayyern ya tambayeshi cikin mutunta ma'aikatan gidan nasu.
Again Murmushi Baba Maud’o yayi, cikin kuma Jin dadin kulawan da su Rayyern din sukeyi dashi yace.
“A’a Alhamdulillah ayanzu kam bana buk’atar komai, saidai nace kayi kyau sosai cikin wannan shigar, amma baka daura hiramin naka dai-dai ba, Bari na gyarama irin yanda samarin makka suke saka nasu.”
Murmushi Rayyern din yayi, kana ya matso Baba Maud’o d’in ya gyara masa sakun hiramin.
Riyyam-nsra kuwa da d’an mamaki ya kalli Hamma Rayyern dinnasu, tare da cewa.
“Hamma Rayyern waye wannan mutumin, naga jiya da nazo banganshi ba.”
“Sunansa Baba Maud’o.”
Ramadam ya bashi amsa.
Saurin jinjina Kai Riyyam yayi, kana ahankali ya matso kusa da Baba Maud’o din.
Fuskarsa dauke da murmushi yace.
“Rawanin da kasa akanka zuwa fuskarka yayi kyau sosai Baba Maud’o, Dan Allah Hamma Rayyern kuzo mu d’auki hoton selfie tare dashi, saboda Idan na koma Ethiopia zan nunawa Mammyna, na kuma bata labarin yanda wasu daga cikin yan Nigeria sukeyin shigarsu.”
Ya fad’i hakan saboda baisan cewa Baba Maud’o’n shigar buzayen Niger 🇳🇪 yayi ba.
Kamar yanda ya buk’ata kuwa matsowa Rayyern da Ramadan sukayi, inda suka saka Baba Maud’o da Riyyam din atsakiya.
Hakanne kuwa yasa Baba Maud’o da Riyyam din ke iya jiyo sautin bugun zuciyar kowannensu, saboda yanayin yanda sukayi kusan ci sosai da juna, domin Riyyam dan sarkin son jiki, har rungume Baba Maud’on yayi ajikinsa.
Yayinda Ramadan ya karb’i wayar Riyyam d’in, yayi musu hoton selfie har kala biyu.
Bayan ya mikawa Riyyam din wayarsa ne kuma,
Rayyern ya juya ya shiga motarsa, driver’nsa yaja suka fice daga cikin gidan.
Ramadan da Riyyam kuwa zama sukayi dab’as Akan wani dan dogon Bencin da Baba Maud’o ke zama, haka kuwa suka sa Baba Maud’on agaba sunata hira, musamman Riyyam daya bud’e baki ya dinga shararawa Baba Maud’on labarai kala-kala, wanda duk rabinsu na abun dariya ne.
*Arewa 24 TV*
Jannart ne da Salman ke tafe acikin babban corridor din, da zai sadasu da compound din gidan tv'n nasu.
Anutse Jannart take takunta, Yayinda time to time take Kallon fuskar wayarta dake rike ahannunta.
Salman dake biye da ita kuwa, idan hankalinsa yakai dubu to duk akanta yake.
Baisan meyasaba hardai idan Jannart tana waje, baya tab’a iya dauke kansa daga gareta, koda kuwa yaya baya iya gajiya da Kallon tafiyarta mai kama data hawainiya.
Yayi Imani azuciyarsa cewa Jannart macece ta gasken gaske, ko acikin mata irinta basu da yawa.
Isowarsu jikin motarsa ne kuma yasa Jannart fakon idanun guard dinta ta shige cikin motar, kana cikin sauri tace.
“Please Salman kayi sauri mubar nan, Domin idan wayannan kattin suka ganni dakai ina mai tabbatar maka cewar akwai matsala.”
“Nikuwa nasan da cewar akwai matsala ai Jannart, abu mai sauki ne ma su samin bindiga akaina su harbeni, tsoron da ake baki agidanku ko Gwamna iyakaci.”
Salman din ya fada adaidai lokacin da yake ta da motar suka bar wajen.
Suna hawa titi kuwa Jannart ta sauk’e ajiyar zuciya tare da fad’in.
“Allah Yasa dai mudace mu samu ganinsa yau, amma mutum dan ya zama richest man shikenan kuma ganinsa saiya zama wahala.”
Shidai Salman murmushi kawai yayi kaman zaice wani abu kuma saiya fasa.
Kaitsaye suka nufi Mai-nasara Hospital.
Tafiyar mintuna kad’anne ya kawosu bakin kofar katafaren asibitin.
Kasancewar kuma ba ashiga can Cikin hospital din da mota, matuk’ar ba emergency bane, yasa Salman parking motar anan babban parking lot na asibitin, wanda shi kansa ya kusan kwatan wata karamar unguwa.
Bud’e murfin motar Jannart tayi ta fito, tana me k’arewa kyau da had’uwar asibitin kallo.
Lallai privet Hospital ne daya amsa sunansa, saboda daga ginin asibitin ma kasan ba kananan billions aka kashe masa ba.
“Mai-nasara Hospital! Lallai asibitin ya had’u.”
Jannart din ta fad’a tana me Kallon Salman.
Shima Salman din kallonta yayi, tare da cewa.
“To Kema da bakinki kin fad’a, yanzu kiyi imagine tayaya za ace kinsamu ganin mamallakin wannan wajen acikin sauki? karki manta kuma bawai iya Hospital dinnan ya mallaka ba, yana da companies, bama a iya Nigeria ba, wallahi Jannart wannan mutumin *Richest Man* ne na k’arshe.”
Kai Jannart d’in ta jinjina, domin ita kanta ayanzu ta yarda da hakan.
Kaitsaye kuma suka kutsa cikin asibitin.
Acan b’angaren Rayyern kuwa kaitsaye Wajen buga wasan polo suka nufa.
Koda suka isa wajen da haduwarsa da kuma kyawunsa ya darawa kwatance.
A parking lot driver’nsa yayi parking.
Bayan ya fito daga motar nasa ne kuma kaitsaye ya nufi cikin wajen.
Da kwata-kwata babu mutane acikinsa.
Duk da tsananin girman wajen kuwa, amma bakajin motsin komai saina tarin dawakai da kuma tsirarun masu kula dasu.
Wanda kuma hakan ya faru ne saboda zuwan Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, kasancewar idan har zaizo wajen To yakan biya mak’udan kud’ad’e ne, ta yanda ranar baza'a amshi kuɗin wasuba, harsai yayi wasansa ya gama ak’alla na tsawon awa 2, bayan ya tafi ne kuma sauran jama’a zasu dawo su cigaba da harkokinsu bawai kuma yana haka dan isa bane, sai dan sosai hayani kan iya sa mishi ciwon kai, yana kuma jin daɗi wasan polo a jikinsa.
Shigarsa cikin babban wajen wasan buga Polo dinne kuma yasashi, zare alkyabban dake jikinsa ya ajiye, tare da wayoyinsa harma da y’ar bag din da yasaka bottle water mai sanyi aciki.
K’arasawa yayi wajen tarin dokunan da akeyin wasan dasu, tare da zab’o wani farin doki, wanda mafi yawanci idan yazo shi yake hawa.
Batare da wani bata lokaci ba kuma ya dale saman dokin tare da rik’e Sandar buga k’wallon nasa ya soma sukuwa, tare da gabatar da wasan.
Mai-nasara hospital.
Salman da kuma Jannart dake tsaye abakin k’ofar office d’inne suka tsaya suna Kallon juna.
Salman ne ya gyara tsayuwarsa tare da cewa.
“Please Jananrt mushiga mana, kinfi kowa sanin irin wahalan da muka sha, kafun mu samu aka nuna mana wannan office din, wannan ita kadaice daman mu ta karshe, kada muyi wasa da ita.”
Kai Jannart ta jinjina kana asanyaye tace.
“To.”
Knocking kofar Salman yayi, inda Dr Sulaiman dake zaune akan wata hamshakiyar kujera ya bada izinin shigowa.
Hakanne kuwa yasa suka kutsa Kai suka shiga bakinsu d’auke da sallama.
Amsa musu sallaman Sulaiman yayi, tare da dago kansa ya kallesu.
D’an Kallon juna suka tsayayi na tsawon sakanni, kafun daga bisani Dr.Sulaiman din yace.
“Bismillah’nku.”
Ya kare maganan yana meyi musu nuni da wasu kujeru guda biyu dake gabansa.
Yayinda kuma acikin mintuna kadan na Kallon daya musu, ya fahimci cewar sudin ba marassa lafiya bane.
Zama sukayi akan kujerun daya nuna musu d’in, Salman ne ya mik’awa Sulaiman din hannu suka gaisa, Yayinda ita kuma Jannart ta gaidashi da sassanyar muryarta, wanda har hakan yasa shi kasa jurewa saida ya dago ya sake Kallon ta, Yayinda azuciyarsa yake mamakin jin ta gaishe shi da Hausa, domin sam baiyi mata Kallon y’ar Nigeria kuma maijin Hausa ba, kasancewar yanayin kamannin ta da kuma shigarta da tsarinta dabanne, bawai irin normal mata da kowa ya sani bane, ita din akwai abu na musamman atattare da ita, wanda kowanni irin Namiji idan ya kalleta saiya gane hakan.
“Meke tafe daku? Ko kuma patient kuka kawo?.”
Salaiman ya tambaya.
Jin hakan ne yasa Salman d’an gyara zama, tare da fuskarta Sulaiman d’in, kana atausashe yace.
“Sunana Salman Aliyu, wannan kuma abokiyar aikina ce sunanta Jannart Idi Sale Dakata, Mu y’an Jarida ne, ma’aikata Tashar Arewa24.”
ID Card d’insu suka zaro tare da nunawa Salaiman daya zuba musu ido.
Salman ne ya cigaba da cewa.
“Munzo nanne bisa dogaro da kuma fatan, dacewar samun ganin Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, Dan Allah Dr. Idan akwai taimakon da zakayi mana, ka taimaka muganshi, wallahi ganin nasa nada matuk’ar muhimmmanci, musamman ga Jannart.”
Ajiyar zuciya Sulaiman ya sauke, tare da maida hankalinsa ga Jannart, domin kuwa idan har abunda tunaninsa ya basa gaskiya ne, to Lallai ya kamata ace ya taimaka musu.
Domin ya raya aransa cewa aiki aka basu domin su tattauna da Dr.Rayyern d’in.
Zamansa ya gyara kana anutse yace.
“Babu damuwa tunda dai harkunzo nan Insha Allah zaku gansa, duk da cewar ayanzu baya cikin hospital d’in, amma Ina da tabbacin inda zaku sameshi, saidai kuma ganin nasa ba shine ba, dan Ina da tabbacin ba lallaine Dr. Rayyern ya amince kuyi hira dashi ba, saboda aduk k’asarnan babu wani gidan Jarida daya tab’a amincewa sukayi hira dashi.”
Idanu Jannart ta d’an lumshe ahankali, Yayinda ajikinta takejin Wannan shine last chance dinta, akasin haka kuwa zata iya rasa aikinta, wanda kuma shine ke sata acikin farinciki.
D’an cije labb’an bakinta tayi, kana cikin siririyar muryarta tace.
“Please Dr. I need your help please!! Banason nayi losing job d’ina!!!”
Takai k’arshen maganan muryarta araunane.
Wanda hakan yasa Dr.Sulaiman Jin tausayin yarinyar, saidai kuma har acikin zuciyarsa yayi mamakin, Jin tace bataso ta rasa aikinta.
Domin yasan kamarta dinnan ba ace daga gidan talakawa ta fito ba, Sam Kwata-kwata ma batayi kama da hakan ba bare kuma waye bai san sunan mahaifintaba Alhaji idi Saleh Dakata.
Sake gyara zamansa yayi, tare da cewa.
“Badamuwa zan taimaka muku Insha Allah, yau Wednessday kuma duk ranan wednessday at this time Dr. Rayyern yakan je wajen wasan Polo, ba kuma ya barin wajen sai 5 na yamma, saboda haka zan baku Andreas din wajen, zakuma ku iya zuwa kusa meshi.
Wani irin sanyi Jannart taji acikin zuciyarta, Yayinda Salman kuwa yayiwa Dr.Sulaiman din Godiya.
Shikuwa Dr. Sulaiman a paper ya rubuta musu adress din wajen, tare kuma da yi musu fatan nasara.
Godiya sosai sukayi masa kafun sukayi masa sallama, cikin hanzari suka fito daga cikin asibitin.
Direct wajen da motar Salman din ke fake suka nufa.
Suna shiga kuwa ya tada motar suka nufi wajen buga wasan Polo’n kaitsaye.
Tafiyar da bata wuce ta 20mn sukayi ba, sai gasu abakin kofar babban mashigar wajen wasan Polo’n da yake duka a unguwa ɗaya ce.
Bayan kuma Salman yayi parking motar ne suka fito, direct mashigan wajen suka nufa.
Amma sai guard din dake tsaron wajen suka dakatar dasu, had’e da cewa bazasu shiga ba, anyi clossing wajen na two hours, suje anjima su dawo.
Rau-rau Jannart tayi da ido, Yayinda Salman kuwa ya zaro ID card d’insa ya nuna musu, cikin sanin makamar aikinsa kuma yace.
“Mu y’an Jarida ne, ankuma tabbatar mana da cewar mutumin da muke nema yana cikin wajen nan, please dan Allah kubari mugansa, abune na gaggawa.”
Dan Kallon juna guard din sukayi, kaman zasu hanasu kuma sai suka matsa musu alaman su shige.
Aikuwa wani irin sanyi Jannart taji zuciyarta tayi, cikin sauri kuwa suka sakai suka wuce cikin wajen.
Y’an tsirarun mutanen dake wajen suka soma wuce wa, ganin kuma kamar babu alaman yalwan mutane awajenne yasa sukayi tsaya, saboda su kansu basu San ta Ina zasu fara nemansa ba.
Jannart dinne ta kalli Salman kana zuciyarta akarye tace.
“Anya kuwa Salman kana ga zamu sameshi anan wajen?”
Shiru Salman din yayi, alamun nazari dai-dai lokacin kuwa wani ma’aikacin wajen yazo gilmawa ta gabansu.
Salman dinne ya tare mutumin, tare da cewa.
“Dan Allah Malam muna tambaya ne,".
"Allah yasa na sani."
Ya basu amsa yana kallon Jannart.
Numfashin gajiya Salman ya sauƙe tare da cewa.
"Please Dr. Rayyern Basheer Mainasara muke nema.”
Idanu sauran ma’aikatan wajen da sukaji abunda Salman din ya fada suka zuba musu.
Shikuwa wanda Salman din ya tambaya, kansa ya girgiza cike da mamaki kuma yace.
“Dr. Rayyern Bashir Mai-nasara kuma anan wajen? gaskiya bana tunanin hakan, saboda muma bamu sanshi ba, sunansa kawai dai mukeji, amma dama yana zuwa nan dinne.”
Baki Jannart ta cije tare da sanya hannayenta ta kama waist dinta.
Cike da takaici tace.
“Again na sake rasa damata.”
“Calm down Jannart, mu k’arasa can cikin wajen mu duba ko zamu dace.”
Salman ya ce mata.
Fuskarta ta kwab’e saboda zuwa yanzu ta fara gajiya da gantalin neman mutumin tunda shi ba kuɗi bane.
Amma da yake ta San wannan din shine last hope dinta, hakan yasa tabi bayan Salman suka shige cikin inda ake gudanar da asalin wasan Polo din.
A dai-dai lokacin kuwa Rayyern yayi nisa acikin wasan nasa, sai sukuwa yakeyi akan doki cike da k’warewa da jin daɗin yanayin wurin shiru ba hayani ba mai takura mishi.
Yayinda kuma ya kasance shi kad’ai ne awajen yake sashi karsashi.
D’an shigowa su Jannart da Salman sukayi Cikin wajen, Saidai kuma ganin da sukayi babu kowa awajenne yasa Jannart jingina bayanta da jikin wani k’arfe.
Akasalance tace.
“Salman zuwa yanzu Tabbas inaji ajikina cewar na kusa rasa aikina, wannan ɗan is ɗin mutumin ba saukin ganine dashi ba, kalli wajen nan fa babu kowa sai wancan mutumin daya bamu baya yana ta sukuwa akan doki shima ɗaya kamar mara aikin yi.”
Takai karshen maganan nata tana me Kallon bayan Dr Rayyern, da yake nesa dasu sosai.
Dan kallonta Salman yayi cikin kuma son k’arfafa mata guiwa yace.
“Karki damu Jannart Insha Allah zamu hadu dashi, Yanzu dai mukarasa wajen wancan mutumin sai mu tambayeshi koya San wani abu dangane da wanda muke nema.”
Still fuskarta ta kwab’e tare da cewa.
“shikenan muje.”
Hakan kuwa akayi inda suka k’arasa shiga can cikin wajen wasan dake malale da koriyar ciyawa mai cike da damshi.
Suna kara kusantan cikin wurin wasanne kuwa Rayyern din ya juyo da akalar dokinsa.
Sai-dai kuma Sam baisauke idanunsa akansu ba.
Idanu gaba dayansu suka zazzaro, Yayinda Jannart kuwa cike da mamaki tadan matsa bayan Salman.
Tana fadin
“Laaa Salman wannan mutumin nefa da na fasawa waya a airport, wayyo Allah Salman nikam kazo mu gudu, tun kafun ma ya ganmu.”
Kai Salman din ya girgiza tare da cewa.
“Mu gudu kuma Jannart? saikace marasa gskiya muje dai ki bashi hakuri dama ai aranar baki bashi hakuri ba, daga ganinsa ma Babban mutum ne watakila ma zai iya taimaka mana muga Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din.”
Fiki-fiki tayi da idanunta, kana adan tsorace tace.
“Shikenan muje.”
Nanfa suka nufi wajen Rayyern d’in.
Dai-dai lokacin kuwa Rayyern dayake matuk’ar gudu akan doki, batare daya d’ago ko waiwaye ba ya taho aguje.
Kaitsaye kuma direct inda su Jannart d’in ke tsaye ya nufa.
Gadan gadan.
Su Jannart din kuwa kansu basu ankar ba, saida dokin ya kusan zuwa gab dasu.
Wani irin k’ara mai cike da tsoro da firgici Jannart ta saka da karfi, tare kuma da daura hannayenta akanta ta rumtse Idanunta k’am, domin ta gama sadak’arwa akan cewar dokin ya nuk’urk’usheta ma angama lokaci ɗaya numfashin ta ya fara fizgan firgici.
Domin hatta Salman dake gefenta shima yayi surrender.
Rayyern kuwa Sam bai Ankara ba saida ihun Jannart din ya shiga dodon kunnensa, wanda hakan yasa cikin sauri ya dago kansa.
Ganin yana gab da bi ta kansu ne, yasashi saurin.
Damƙe igiyar linzamin dokin da ƙarfi ya tsayar dashi cak.
Saboda ganin macen da yayi agabansa ne kuma ya sashi dirowa daga saman dokin.
Bayan ya juyashi.
Wani irin dogon tsaki yaja.
Tare da Kallon Salman wanda keta sauk’e ajiyar zuciya, kana ya watsawa Jannart din dake gabansa wani kallon da yasa cikinta ya murda ya haɗe da numfashin