Showing 90001 words to 93000 words out of 132995 words
ya tsareshi da idanu dan son gano gskyr zuciyarsa.
A nitse ya fara mgn.
“Kayi haƙuri Dr Rayyern Mai-nasara, nasan dole kaga batun da nazo muku dashi a matsayin tatsuniya ko shirme.
Ko kuma zance mara dalili.”
Numfashi ya dan ja sai ga wasu irin hawaye masu zafi suka kwaranyo mishi wanda sukayi masifar karya zuciyar Dr Rayyern Mai-nasara da take mai tausayi.
Cikin raunin murya yaci gaba da cewa.
“Jannart yarinya ce mai rauni, da son taimako da samun tsayayyen jigon da zai zame mata GARKUWA'N da zai iya killaceta, sabida akwai masu bibiyar rayuwarta suna son kasheta!!!.”
Sosai Dr Rayyern ya rumtse idanunshi sabida hawayen mutumin na karya mishi zuciya.
A raunace yaci gaba da cewa.
“Haka yasa nake neman inda zan sata ta tsira da rayuwarta, ID card ɗinshi ya miƙa mishi tare da cewa.
“Ka gani ni Lawyer ne mai kare haƙin ɗan adam bisa umarnin kotu nake neman inda zan adanata ba wai haka nan gaba gad’i nakeyi ba.
Rayyern Jannart macece da takeda cikar sura, ba rashin mijin nema bane yasa na baka ita sai dai bisa dalilin gamayyar TUBALIn matsalar.
Please ka amince da auren Jannart bisa Kekkyawar niya, ita marainiyace, mahaifiyarta ta barmin amanarta da wasiyyar in aura mata miji na gari da zai riƙeta da amana”.
Wani irin taune lips ɗinshi yayi duka biyu.
Tare da jin wani irin masifeffen tausayi rauni da kuma shiga rud’un kalaman Barrister.
Cikin murya mai cike da kamala da yanayinsa na rashin iya ƙarya yace.
“Bana sonta batayi min ba ko kaɗan, sam bafa na sonta cikin raina. Koda dai-dai da kwayar zarra a haka zamuyi zaman auren?”.
Da sauri Barrister Kabir yace.
“Zaka sota Rayyern in ka zauna da Jannart zaka sota.
Sabida ita macece mai biyayya da amsar umarni tanada haƙuri”.
Da sauri ya girgiza kansa tare da cewa.
“Bazan sotaba wlh bazan sotaba har gaban abadan sabida in na tsani abu bani dawowa in soshi daga baya”.
Cikin tsananta hawaye Barrister Kabir ya mai-maita kalmar tsana a ransa.
A fili kuwa cewa yayi.
"Ya ilahi ya mujibadda'awati, ya Allah ka kawo min mafita, Allah ka gani ina son kare rai da lfy da martabar Jannart bani da nufin haɗata da wanda ya tsaneta”.
Sai kuma ga sabbin hawaye.
Hannunshi yasa ya kamo hannun Dr Rayyern cikin sanyi yace.
“Toh amman zaka iya riƙe min amanar kula da tsaronta da lfyarta da cinta da shanta bisa ƙarƙashin inuwar auren na wani ɗan lokacin da gsky zatayi halinta sai ka sakar min ita in bata mai sonta? Dan Allah da Manzonsa kamin wannan alfmafar”.
Wani irin nannauyan numfashin ya fesar jin yadda murmuyar Abba ke rawan kuka
Cikin rauni da tausayin mutumin yace.
“Har zuwa wannne lokacin kenan?”.
Da sauri Barrister Kabir yace.
“Wata takwas zuwa shekara ɗaya dan Allah”.
Cikin sanyi yace.
“Ba komai na amince zan kula da ita dai-dai iyawa ta.
Abba na yayi saurin aminta da kai, ya kuma nuna min dole in auri ɗiyarka, bayan kuma Bani da isasshen lokacin.
Toh zamuyi yarjejeniyar shekara ɗaya tana cika kacewa Abba in sakar maka ƴarka sabida bani da isasshen lokacin kainama bare na kula da ƴarka.
Kaga daga nan in na saketa Abba bazai sake min mgnar aureba tunda yaga rashin lokacin ya shafi auren”.
Cikin wani irin kallo Barrister Kabir yace.
“Zan amince da haka sai dai cikin yarjejeniyar tamu, ya zama Jannart ta tsira da budurcibta kada ka meda min ƴaƴan ƙaramar bazawara tunda har kasan baka sonta, ka tabbatar ta dawo hannuna a budurwa”.
Fuskarshi ya ɗan yamutsa tare da tura baki kana yace.
“Nayima al'ƙari, ni kuma mema haɗina da ita nifa RAYYERN babu mace a idanuna”.
Da sauri ya kalli Barrister Kabir da yace.
“Kada ka manta wannan tattaunawar tamu fa”.
Cikin yarda da kai yace.
“Ban cika mantuwa ba, kuma in nayi al'ƙawari nakan yi iya iyawa ta inga na cikashi”.
Cikin jan numfashi Barrister Kabir ya miƙa tare da cewa.
“Ngd matuka ni dai fatana. Ci da sha jinya muhalli nitsuwa nake buƙatar Jannart ta samu masu sata farin ciki”.
Hannu ya bashi ganin yana miƙa mishi hannu busaha sukayi kana yace.
“Uhum”.
Daga nan Barrister Kabir ya sallameshi ya tafi.
Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara gyara zamanshi yayi yana mai cewa.
“Wai kada in taɓa masa ƴa jifa, sai kace ance masa ni irin jarabbun nanne marasa haƙuri da rashin iya sarrafa kai, ko zato yake ni mayen matane!?”
Chocolate ɗin dake gefenshi ya ɓare ya afa a baki.
Ya tauna ido ya lumshe tare da cewa.
“Ni ko kalloma wannan uwar ƙwaƙƙwazon ta isheni nema, me ma zai kaini kusa da ita tunda nafi kowa sanin karo da ita ba dama kamar anyi karo da doki.
Tana ƙasa ina sama”.
Ya ida mgnar yana shan Chocolate ɗinsa da yasa yaketa lumshe ido.
Shi kuwa Abba daga Mai-nasara Hospital kai tsaye gidansu Dr Rayyern ɗin yaje.
Suka tattauna da Abba kana ya koma gida bayan ya biya wurin Dr Sajo ma.
Ita kuwa Jannart 4:00 pm dai dai ta fito daga wanka, bayan ta gama tsane ruwan dake jikinta ne kuma, ta shafawa lallausan fatar jikinta body lotion, tare da fesawa kowani lungu dake jikinta turare mai dadin kamshi.
Kamar kullum kuma bata wani yi kwalliya akan fuskarta ba, powder ce kawai sai lipstick da kuma mascara da ta shafa.
Amma duk da hakan kuwa tayi kyau sosai.
Musamman kajol din da tasa sun kara bayyana hasken idanunta.
Wata had’add’iyar Turkish Abaya mai kalan Dark greeen ta ciro daga cikin drawer’nta, abayace mai tsananin kyaun gaske, da kuma tsada Domin kuwa ko adon duwatsun da aka kawata jikinsa dashi abun kallone.
Kimtsa cikin jikinta tayi, Domin kuwa yaudin harda bra ta saka domin sosai takejin nauyin da ƙirjinta keyi ya ragun mata tunda ta fara shan magungunan da aka bata a Mai-nasara Hospital, bayan ta kammala ne kuma ta Zura doguwar rigar ajikinta, tare da daukan mayafin rigar, bayan tayi parking dogon gashin kanta ne, kuma ta yafa vail din abayan, wanda ya rufe mata kai zuwa wuyanta.
Bayan ta saka wani dankunnen gold mai kalan dark green akunnenta ne kuma,
Anutse ta zura wani had’add’en hill shoe mai kalan dark green ak’afarta.
Yah Allah bak’aramin kyau Jannart din tayi yau ba, musamman yanda doguwar rigar yabi hadaddiyar Surar jikinta ya kwanta.
Koda ta kalli kanta amadubi murmushi tayi, Domin ita kanta tasan cewa rigar tayi masifar mata kyau sosai, musamman da dark green color din ya bayyana hasken fatarta.
Bayan ta sake shafa parfumed ajikinta ne kuma, ta d’auki Waya hadi da dan maidaidaicin dark green handbag dinta, wanda adon duwatsun jikinsa ke shige da na jikin rigarta.
Kyau iya kyau kam tasha shi.
Koda ta fito daga cikin dakinnata kuwa, haka take takawa Ahankali harta sauko kasa inda Momy ke zaune.
Idanu Momyn ta zuba mata, tare da bud’e baki tace.
“Masha Allah Kai gaskiya Jannart kinyi kyau kinganki kuwa saikace irin matan Egypt dinnan.”
Murmushin Jin dadi Jannart din tayi, tare kuma da yiwa Momyn godiya.
Kana cikin dan hanzari tace.
“Momy natafi saina dawo.”
Adawo lafiya Momyn tayi mata, Yayinda ita kuma kaitsaye ta fice daga cikin falon.
Koda ta fito compound din gidan, ta samu Baba Ado da guards dinta na jiranta.
Ad’an k’agauce haka ta shiga cikin mota suka bar gidan.
Koda suka hau titi haka takejin zuciyarta, na wani irin bugawa, Yayinda aduk bayan kowanni minti fargaba ke sake lullubeta.
Ahaka dai suka isa cikin tv station din nasu.
Koda ta fito daga cikin mota, gaba daya kallon jama’ar dake waje Kanta ya dawo, Domin sosai kwalliyar tata ta dauki hankalinsu.
Itakuwa Jannart kaitsaye cikin wajen da zasu gudanar da program dinnasu ta nufa.
Wanda kuma tuntuni Salman, Aisha Lawal. Aunty Fauziya D Sulaiman da kuma Aunty Rabi da wasu sauran abokan aiki ke jiran zuwan ta.
Shigowarta cikin wajen ne kuwa yasa duk suka dago suka kalleta.
Yayinda Salman dake gefe kuwa, kyawun da yaga tayi yaudin ya kusan kashesa azaune.
Karasowa tayi, cikin kuma danne tarin fargaban dake zuciyarta, ta fadada Murmushin dake kan fuskarta, kana tabi kowannensu suka gaisa daya bayan daya.
Dai dai lokacin ne kuma MD yazo wucewa, ganinsu da yayi a zaune a harabar wurin ne kuma yasa shi, cewa.
“Yadai naganku duk waje ɗaya harda Shugabar marubuta.
haka, lafiya kuwa?”
Ya kare mgnar yana kallon Aunty Fauziyya X Sulaiman
“Sir Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara muke jira.”
Salman ya fad’a yana me Dan satan Kallon Jannart din.
Yayinda Aunty Fauziyya D Sulaiman kuwa take ɗan murmushin sunan da MD ya kirata dashi.
MD kuwa kansa yadan jinjina cike da yaba kwazonsu yace.
“To Allah Ya kawosa lafiya, amma Idan har bai samu zuwaba Jannart kada ki tashi hankalin ki, saboda akwai wani sauran chance da kike dashi.”
Kai Jannart din ta jinjina, kana asanyaye tace.
“Nagode Sir, amma anyi mana al'k’awarin cewa zaizo yaudin, shiyasa nasa hope dina akan zuwan nasa yau.”
“To shikenan Jannart badamuwa, nima bari Nafasa fitan da zanyi, Idan dai zaizo da gaske, zan zauna saboda nima kaina inason na sake ganinsa bare kuma a wurin aikinmu.”
Idanu Jannart tadan zaro cikin yanayin mamaki kuma tace.
“Laa Sir dama kasanshi ne?”
“Kwarai kuwa na tab’a haduwa dashi acikin jirgi, lokacin zanje France, amma abun ya Dan kwan biyu, duk da haka kuma Idan na ganshi na tabbata zan ganeshi to kwanaki naki ce muku na taɓa ganinshi kada kuyi ta damuna da ya kamanninsa yake.
Ajiyar zuciya duk mutanen wajen suka sauk’e, musamman Jannart da ayanzu zuciyarta ke dukan uku uku.
Saidai kuma wani abun daya kara rugurguza zuciyar Jannart din shine Ganin har 4:30 pm tayi amma babu alaman bak’on nasu zaizo.
Lokaci daya taji wani irin karyewar zuciya, wanda hakan yasa dole ta d’an janye jikinta gefe, tare da matsawa gefen had’add’un shuke shuken flowers din dake wajen.
Duk abunda takeyi kuwa Salman na lure da ita.
Yayinda Asiya kuwa taketa murmushi jin daɗi tunda itama ta rasa dama suna Allah yasa su rasa.
Wato irin a mutu har liman din nan
Suna tsaitsaye awajenne kuma.
Suka hango shigowar wata masifeffiyar mota had’add’iyar BMW bak’a mai matukar kyaun gaske da tsada.
Wani irin bugawa Jannart taji zuciyarta tayi, lokaci daya kuma duk suka kakkafe motor da ido hardai aka gama dai-dai-ta parking.
Bayan motor ta tsayane kuma, wani mai bakaken kaya ya fito cikin hanzari, inda ya zagaya ya bud’e murfin motar Usman P.A Kenan wanda shine yaja motar ma.
Ahankali ya zuro da k’afafunsa wanda sukasha tsadaddun bakaken takalma waje, lokaci daya kuma shima ya fito waje.
Yayinda ajikinsa yake sanye da royal blue suit masu masifar kyau.
Idanu Jannart ta zazzaro waje, Yayinda takejin tsanantawan da bugun zuciyarta yayi.
Amatuk’ar rud’e take binshi da kallo, lokaci daya kuma ta kwab’e fuska kaman zatayi kuka.
Cikin hanzari kuma ta nufi inda yake tsaye.
Matsowa tayi gab dashi, batare kuma dako lura da hakan da tayi ba, tace.
“Kai kuma, ya haka?
Toh ina yake Ina Dr. din? Bakace zaka zo dashi ba, Meyasa To zaka zo Kai daya kuma me zakayi mana? Kai me zanyi da kai”
Idanunsa yadan zuba mata.
Dai-dai lokacin ne kuma MD yakaraso wajen da matukar sauri.
Yace.
“Masha Allah sannu da zuwa.
Sir Sannu da zuwa, Mara ba da zuwa gidan tv’n mu, Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara!!”
Dammmmmm haka zuciyar Jannart ta buga, alokacin da taji abunda MD din nasu ya fad’a.
Idanunta ta zazzaro waje tana me Kallon mutumin da taji ankira da Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.
Shikuwa Rayyern hannu ya mikawa MD n suka gaisa cike da mutuntaka.
Ganin hakanne kuma yasa duk sauran ma’aikatan dake wajen suka karaso, fuskarsu dauke da matsanancin farinciki sukeyi mishi sannu da zuwa cikin iya aikinsu da karrama manyan baƙinsu na musamman ne.
8Kusan irin karramar da za'ayiwa Dr Rayyern Mai-nasara.
In AYSHA ALIYU GARKUWA taje ba irinshi za'ayimata ba. Kunsan ace tuwon girma miyansa nama)
Da matukar girmamawa kuwa MD'n Yayi masa iso zuwa, cikin wani babban dakin tarban baki dake sashin.
Salman da Jannart kuwa kasa Koda motsawa sukayi, saboda tsananin mamakin da suke ciki.
Kallon Salman Jannart din tayi, cike da tsananin mamaki tace.
“Wai gizo idanuna keyi ne Salman ko kuwa gaskiya ne?”
Salman da shima ya shiga shock sosai, Kai ya Dan girgiza tare da cewa.
“Ko d’aya Jannart ba gizo idanunki keyi miki ba, shidinne dai, amma muje saboda mu sake tabbatarwa.”
Saurin jinjina masa Kai Jannart din tayi, tare da bin bayan Salman din suka shiga ciki.
Yayinda acan cikin kuwa, gaba daya MD ya rude da tsananin farincikin ganin Dr. Rayyern din mutumin da duk kafafen sada lbaran kasar Nigeria'n ke nema ganawa dashi basu samu. Sai su a yau ai yana cikin farin ciki.
Hakan yasa da kansa ya shiga debo masa drinks yana Jerawa akan babban table din dake tsakiyar dakin cike da mutuntaka.
Still kuma har yanzu bakinsa baiyi shiru ba, sannu da zuwa kawai yaketa Jerowa su Rayyern d’in.
Yayinda shikuwa Rayyern ke dan sakin murmushi, saboda yawan magana ba al’adarsa bace.
MD kuwa saida ya cika gaban su Rayyern din da kayan ciye ciyen fruit kala kala.
Cikin kuma sakin fuskan, dake bayyan tsananin jin dadinsa yace.
“Bismillah Dr ka sha ruwa, Domin yanzu saura mintuna 5 a fara shirin, kasamu kadan taba wani abu.”
Kai Rayyern din yadan girgiza, Cikin kuma muryarsa dake bayyana ajinsa akoda yaushe aji irin na mutunta kai ba girman kai.
A mutunce yace.
“Alhamdulillah Nagode, saidai kuma bani da ishashshen time, Ko zamu iya wucewa inda za’a haska shirin kaitsaye?”
Kai MD ya jinjina da sauri, cikin jin dadi da murna yace.
“Mezai hana ai muje kawai, mu zuwanka ayanzu ya fiye mana komai.”
Mikewa sukayi inda MD din ya shige gaba da sassarfa dan nunawa Rayyern din dakin da za’a haska shirin.
Inda tuntuni Jannart ta shiga cikin babban hall din ta zauna, gaba daya hall din cike yake da cameras, da kuma abubuwan daukan sauti da sauran na'urorin daukar hoto da sauti kai tsaye.
Yayinda aka shirya camera's sukayi layi, Yayinda duk suka zaku da son Ganin bakonna su.
Ba kuma ga iyasuba harda sauran ma’aikatan dake gidan TV, da kuma mutanen cikin ƙasar mu Nigeria kasancewar Tashar Arewa 24 TV tashece mai inkantattun kayan aiki da haziƙan mahaikata.
Kasancewar shirin live ne kaitsaye za’a haska shi wa duniya alokacin da ake tsaka da daukanshi.
Jannart kuwa da take zaune akan kujerar dake tsakiyan wajen.
Yayinda can gefe kuwa kujerune a jere.
Inda wasu daga cikin ma'aikatan ke zazzaune
Jannart kuwa.
Shiru tayi tana me mamakin yanda al’amarin ke shirin kasancewa.
Yayinda Salman dake can gefe shidinma zallar mamakin faruwar hakan yake.
Shigowar Dr. Rayyern da kuma MD wajen yayi dai-dai da cikar lokacin da za’a fara shirin.
Wannan yasa tun kafun Dr. Rayyern din ya karaso kan babban stage din da mazauninsa yake suka fara dauka.
Yayinda Rayyern kuwa ganin wace zatayi masa tambayoyin, yasa ya d’an hade rai.
Acikin zuciyarsa kuwa cewa yayi.
“Kenan karya sukamin itace zata gudanar da shirin, bawai wancan namijin ba.”
Azahiri kuwa karasowa kan stage din yayi, tare da zama akan kujerar dake fuskantar na Jannart din.
Yayinda Jannart kuwa ta danne duk wani tunani dake ranta, juyawa tayi ta kalli camera hade da cewa.
“B....!
*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*
NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.
Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.
Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya