Showing 21001 words to 24000 words out of 68854 words

Chapter 8 - AHALINA Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

284

ta juya tana Mai ɗago musu hannu alamun bye bye,

Kallan Anisa dake faman yaƙe Mami tayi tace"kar ki biye Nadiya haka nan take ,kar ki ɗauki komai nata har zuci"

    Cikin yanayi na yan duniya Anisa tace"La mami wallahi babu komai,Ai duk Yan gidan nan babu wadda nake so sama da Nadiya ,she's caring',"

Murmushi mami tayi wanda kamar ana mata dole tace,so bazaki bimu asibita ba saboda kaɗaici ko kibi Nameer kiga company ɗinsa ?

Cikin saurin katse Anisa Nameer yace"A'a mami sai dai ta biku amma nikam yau meeting ne dani har six,banda lokacin entertaining kowa.

    Kafun mami tace wani Abu Anisa tace "wallahi babu komai mami dama nima ina san zuwa gurin Wata Aunty na ne ."

Kada kai mami tayi cikin rashin san cigaba da sauraran Anisa ,dan wani irin mugun ɗacinta take ji a maƙoshi,

Abdallah ne Ya fara tashi yana mai fadin mu mun Ta tafi taron Malaman Adamawa,mami kisa ɗanki a addua yau nine zan fa'tawa,

Durƙusawa yayi dai dai iyayen nasu,

Kallan juna Mami da Papa sukayi suka murmusa a tare suka ɗora hannunsu a kansa 'dan sun gane abunda yake nufi ,Addua suka masa yayi musu sallama inda Nameer shima Ya tashi yana mai musu sallama,

Saurin tashi Anisa tayi tana Mai cewa "Baby bari na taka maka, "

Jiyowa yayi yamata wani irin kallo kana yace "bana san kafafunki su sha wahala ,kiyi zamanki,"

Zata yi magana Papa Ya katseta ta hanyar fadin "rabu dashi kiyi zamanki,."

    Badan taso ɗinba ta zauna yayin da shi da Abdallah suka taka,

Kunshe dariya Abdallah yayi lokacin da Ya hango Nadiya na fitowa a ɗakin Anisa kamar b'arauniya,

Dan mintsino Nameer yayi wanda shima yana ganinta suka saka dariya a tare,

Kaɗa kai Papa yayi dan yasan yaran nan nashi are of to something 'dan yana kallan giftawar Nadiya shi yasa ya hana Anisa binsu,

A parking space suka haɗu ,kowa matsa keynsa yayi motarsu tayi tsiwa,

Motar Nadiya ce a tsakiya,kowa a bakin motarsa Ya tsaya,

Kallansu tayi ta kuma saka wata dariyar tace "im sure this time around game ɗin Anisa Ya kare,"

Cos wayanta yanzu haka an fara bincike mun,

And yarda nayi tempering bata isa ta gane ba insha Allahu yau sai mun kamata da wani abun,

Ɗanewa tayi saman range rover ɗinta ta ɗaga Hannayenta dukka biyu suka sako nasu suka tafa,

Cikin murna tace success ,faɗawa tayi cikin motarta tace sai anjimanku.

    Kiss Abdallah yayiwa Nameer blowing yace "ina sanka Hamma chop kisses,kafun Nameer yace wani abu shima Ya shiga motansa dan barin gidan,

Kada kai Nameer yayi yana Mai murmusawa ,tabbas yayi dacen yan uwa na gari masu sanshi.


CHUCHUJAY ✍🏽
[3/6, 5:13 PM] Chuchujay✍️: AHALINA

    (Siblings of different fathers )

Book 2 'in Aure uku series

        By

CHUCHUJAY

EPISODE2⃣1⃣➡2⃣2⃣

   بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

    Cikin wani matsanancin fushi Anisa  ta shiga ɗakinta tana mai tunanin Abinda zatayi ta kawo karshen dukkan su kar ma ace Nadiya wadda a kullum ita ke shigar mata hanci da kudundune,

Wayarta ta ciro ta danna Numbern Hajiyarta ,

Tana ɗagawa tace"uwar ɗakina ina buƙatar die detro,"

Cikin mamaki hajiyar tata tace "Mai kuma zakiyi da die detro , tell me ba abunda nake tunani bane ke cikin zuciyar ki. "

    Yar ƙaramar dariya tayi da ta fahimci inda maganar tata ta nufa tace "trust me ,bazan tab'a commiting suicide ba , but ina san datse numfashin wasu ne,yau za'ayi babbar mutuwa a gidan Paki,ina san ayi masu mutuwar da zasu tarwatse su daidace ,shi yasa nake neman wannan killer poison ɗin a hannunki wanda zanyi amfani dashi na datse numfashin Umaimah paki,saboda itace mutum mafi girma a cikin waɗanda suka bawa mahaifiyata Gudunmuwar baƙin ciki,dan haka Dole nayi amfani da ita wajen bawa iyalanta dafin da suka bani tit for tat,Sannan bayan haka ,a hankali kuma ina jikinsu bayan ukunta Zan kunna masu wuta cikin dare kowa na gidan ya mutu,yana ɗaya daga cikin babban dalilan da suka saka naƙi yarda ya Kaini gidan sa ,dan Allah kiyi mun delivery nashi ,dan shiru uwar ɗakin nata tayi kana tace shikenan Anisa indai kinji zuciyarki ta gamsu da hakan just Do it ,finish everything ki dawo ,the house need you around ,

Murmushi tayi bayan ta gama wayar ta kalli mahmood tace "im Sorry amma bana tunanin kaima zakayi escaping wannan fate ɗin domin a gurina amfaninka Ya ƙare so lokacin da gidan nan zaici wuta kayi hakuri dan kana ɗaya daga cikin abincinta ,

Kamar yaran yasan Mai take faɗi Ya saka kuka ,sai da yayi Mai isarsa kana ta ɗaukesa ta fara basa nono tana Mai faɗin "sadaqa. "

    Ko minti talatin Anisa bata gamayi da yin wayar da take ba saseen police guy ɗin da Nadiya ta bawa aikin a boye ya tura mata da Recording ɗin yana Mai fadin"Nady wannan enough evidence ne da zai kaita prison,ɗan murmushi tayi tace "saseen My guy calm down ,zamu Kama Anisa and kaima nasan you're eager amma kasan Mai nake so?

So nake Ya zamana mun kamata a act ɗin yarda bazata tab'a escaping ba , kai dai ka cigaba da mun monitoring wayanta nagode sosai ,im glad to have a frnd like you. "

    Bayan sun gama wayan ta saka sauraran wayan da Anisa ɗin tayi tana Mai jinjina rashin Imani irin na Anisa da bata da niyar tunani na biyu wajen hallaka yan gidan da jaririn da ta haifa da cikin ta,lallai rashin imaninta ya kai wani matakin da babu Mai sakata ta bari,

Amma wani abu da ta rasa mai bata amsa shine yarda Anisa ke ikirarin zata kashe mami kamar yarda taji suma suji,

Shin wanne abu ne sukayi mata har haka da har take neman rayuwar kowa a gidan ?

Tasan babu mai bata wannan amsar indai ba taje ta tunkari iyayensu ba domin yarda ta fahimci abun wani abu da ya shiga tsakanin mahaifiyarta ne da iyayensu,

Wayarta ta ciro tana mai ƙara kiran guy ɗin dake mata bincike ,yana dauka tace "about Anisa inason kayi mun bincike sosai akan mahaifiyarta Sameera,

Daga ɗaya bangaren yace "abunda nake san kiranki akai kenan,binciken da mukayi mahaifiyarta Sameera tana da tsohowar alaƙa da parents ɗinki wanda a binciken da mukayi ma har mun gano a baya ita mahaifiyar Anisa taso Dr Imam paki Wanda akwai wani scandal da ya tab'a faruwa wanda a da kamar da ita but im not sure ,amma dai main abunda yake kawai shine mun samu babban labari akan shigar Anisa gidan wanda fansa ce ta mutuwar mahaifiyarta wanda ta dangantasa da dalilin Dr Imam da Umaimah ne."

Dan shiru tayi tana Mai san tuna wannan sameerah wadda duk inda hankalinta Ya tafi ta kasa tunawa amma tasan tabbas a bakin iyayanta zataji wanda Ya kamata ace tuntuni sun san Mai ke faruwa.

Lokacin lunch nayi kamar yarda tayiwa Papa alƙwari kai tsaye restaurant ɗin da tasaba ordering tayi ordering sushi.

    Kai tsaye asibitin nasu ta tafi tana mai jin wani irin daɗi cos jikinta Ya bata lallai ƙarshen Anisa yazo a gidansu ,ita ta fara zuwa, kai tsaye bayan an shaida mata Dr paki na last floor ta danna floor ɗin bayan shigarta Elevator wanda shine zai kaita inda asibitin Ya mallaki falo da ɗaki,

Soyayyar iyayenta na burge ta Wanda sau da dama take kwaɗayin samun masoyi kamar Papa wanda yake mutuwar san Maminsu,duk da Akan samu sab'ani tsakanin ma'aurata amma nasu bashi da yawa saboda sun fahimci junansu sosai,Evans ne ya faɗo mata tun sakon da Ya tura mata bai sake kiranta ba ko tura mata wani saƙon wanda wani lokacin takanji abun a ranta amma sai ta danne tana Addu'ar Allah yasa Its for the best.

    Knocking tayi a bakin kofa bayan isarta ,izini aka bata ta shigo,

Zaune ta tarar da Papa kan couch da system a cinyansa yana ganinta Ya faɗaɗa murmushin sa yace "Ashe dai princess ɗin Papa da gaske Take zata kawo masa sushi,"

Zama tayi kusa dashi tace"Papa is my Bae "

Before anyone else dole na bar komai na kawo masa sushi and remember nace maka yau akwai surprise party a asibitin nan buɗe masa Take away ɗin tayi tana Mai sake faɗin yes Papa maza kaci kar mami tazo ta saka maka rani ita ma ga nata Ai amma idan tazo naka zata sawa ido,

    Dariya yayi yace "wannan haka yake princess ɗin Papa bismillah,yana kai ɗaya bakinsa mami na buɗe kofar tana Mai fadin"Honey its lunch time and na maka fave ɗin ka,"

Ɗago kai tayi dan kallansa amma idanunta Ya sauka kan Nadiya sannan goganta wanda ke fama aika sushi baki,

Ƙaramar dariya tayi tace "a'h bazakaci fave ba tunda dai favorite daughter ɗinka ta kawo maka favorite sushi ɗinka ,"

Zama tayi kan couch na mutum ɗaya tace "what's the occasion?"

Kafun Nadiya tayi magana sukaji knocking bakin door ɗin,

Ɗan kallan Papa mami tayi ko shi ake nema amma kuma no worker is allowed here tafi tunanin na gida ne dan haka tace yes?

Come in,

Nameer da Abdallah ne suka shigo suma hannun su dauke da take away ,kallansu mami tayi tace "menene wai babban occasion ɗin yau da dukkanku kuka baro aikinku kukazo nan,"

Zama sukayi inda Nameer ke faɗin ,"Mami yaushe rabon da muyi having lunch tare ,so we just decided yau mu baku surprise sannan At the Same time na sake tabbatar maku da cewa banyi disappointing ɗinku ba,"

Ƙaramar envelop Ya aje kan center table ɗin dake kusa da Mami,

Kallan envelop ɗin mami tayi tana Mai ɗauka idanta na kallansu ,babu wanda Ya san me Take ɗauke dashi cikin ɗakin dan ko su Nadiya bai sanar ma maganar takardarba,

Da Mamaki mami ta karanta result ɗin DNA ɗin wanda ke ɗauke da sunan Nameer dana Mahmood sannan a result d'in da take kallo yana Mai shaida mata cewa babu wani abu na jini da NAMEER da MAHMOOD suka haɗa,

Aje result d'in tayi tana Mai murmusawa tace "Papa wai mu Nameer zai maida Kananun yara a wannan stage ɗin,

Miƙa masa takardar tayi wanda yana gama dubawa taga wa Washe haƙoransa cike da farin ciki yana Mai faɗin "Alhamdulillah Kina kalla Mami dama kinsan ance Allah ba azzalimun bawansa bane,"

    Ɗan karamin murmushi Mami tayi tace "Papa ban yarda wannan result ɗin gaske bane cos result ɗin farko da akayi bana tunanin akwai wani mistake saboda a cikin asibitin nan akayi sa and bana tunanin akwai Mai guts ɗin da zai sake result ɗin which im sure yaje yayi faking nasane ,so Nameer munsan kayi mana ba dai dai ba and bamuyi alfahari da hakan ba but please ka daina ƙokarin danne wannan laifin naka it wont work".

    Idan kuma nace miki mami ba ƙarya yake ba sannan na baki hujojina fa?

Nasan nima zakice na haɗane ,bansan Hamma yaje sake wani DNA d'in ba amma nayi imani da Allah ba ƙarya sakamakonsa yake ba saboda Mami Anisa is not who we thought she was,yarinyar nan is an assassin tazo gidan mu ne dan ɗaukar fansa ,Anisa tana using Hamma ne dan ci mako ke da Papa.

    Da mamaki Papa yace "mu kuma?"

Kaɗa kai Nadiya tayi tace "Eh Papa,Anisa yarinyar wata sameerah ce wadda a binciken da nayi nake sanin cewa kuna da alaƙa da ita tsohuwa ,sannan Anisa tazo gidan mu ne dan ɗaukar fansan mutuwar mahaifiyarta sameerah d'in,and yarinyar nan is a snake ,tana ƙarkashin wata kungiya dake bada kwangilar kisa wanda a maganar da nake maku ta kashe wajen 25 people on a mission sannan she was a stripper a newyork and a drug dealer,taje gidan yari bama na kasar nan kaɗai ba ,duk yarda Zan faɗa maku Ya wuce nan,tana da haɗari sosai"

    Badan na tsaneta bane Ya saka nake making up zancena nasan Mami zata iya cewa haka,inada evidence Mai kyau sannan maganar da nake maku a yanzu yau da dare tana da mission na kashe mami wanda a wayarta da nasa ake bibiya tayi mentioning wani poison wanda ke kisa nan Take ,shes going to use it on Mami,sannan bayan nan zata sakawa gidanmu wuta ta ƙona kowa har da Mahmood.

     A zabure Papa yace "kinaso kice mun tazo ne dan kashe mun mata?"

Shine Take using iyalina ?

Tabbas tayi babban ganganci wanda sai taji dama batayi ba,

Wayarsa Ya ɗauka yana Mai faɗin"yaya ma za'ayi mukasa fahimtar wani abu har tazo gidan mu karkashin roof ɗina tana san kashe iyalina,ban tab'a tunanin rashin ɗa'a irin na sameera zai tab'a Ahalina a yanzu ba,How on earth zaka sama yaranka mentality na daukar fansa wanda nasan itace sila,Mai ma akayi na daukar fansa?

    ,Kama hannun Papa Nadiya tayi tace "Papa duk yarda Zan faɗa maka wannan sheɗaniyar yarinyar Ya wuce nan cos akwai manya dake goya masu baya,babban damuwarmu kuma anan shine tayarda zamu cire ta a rayuwarmu babu wanda Ya ji koda ciwo,yarda tayi using dinmu kamata yayi mu cimmata tabazata itama muyi amfani da ita wajen kamata dumu dumu,and na riga nayi involving SWAT nasan kuma dole zata shiga hannu muna jira kawai tayi mistake ne wanda im sure zatayi yau da dare .  ,"

    Nikam Papa wacece wannan sameerah ɗin?

Sannan Mai ne Ya saka Take san ɗaukar fansa Akan AHALINMU

Abdallah Ya tambaya da ƙaguwa.

    Ajiya zuciya Papa yayi yace"tare mukayi secondary school har zuwa jami'a da Uncle ɗinku KB mijin ƙanwata Afnan,ni dashi mun kasance aminanine inda Sameera ta shiga cikin muka dawo abu ɗaya bansan sona Take ba bayan kuma na sani na tabbatar mata babu wannan batu tsakanina da ita,i thought ta hakura muka cigaba da zumunci dan har gidanmu tana zuwa tayi kwanaki,

Lokacin da na hadu da Maminku a city hospital na nuna ina santa cos babu wata ɗiya mace da nake ji araina bayan ita har yanzu kuwa,

Murmushi dukkanninsu sukayi,

Cigabawa yayi yace "lokacin da sameerah ta bayyana it wasn't a nice thing dan haɗuwar farko saida sukayi Faɗa da Maminku,kasancewar Maminku boss lady Ya saka ta sa sameera a gurinta inda dalilin da yasa ta tsaneta kenan,so bayan ta koma gidan mu ta samu karbuwa gurin Nana kakata wadda take ganin babu yarda za'ayi Na Auri Maminku saboda kawai tayi AURE UKU yara uku,wannan damar sameerah ta samu ta ɗinga yin amfani da Nana wanda ta bamu ciwan kai bayan Aure,

Da taimakon Allah dana Maminku Wadda tayi playing role ɗin da bansan ta iya ba ta saka sameera confessing wanda sai bayan shekaru masu yasa take faɗa mun,a process ɗin kuma Nana ta juya baya ga sameerah wadda dalilin hakan Ya saka sameera shaƙe Nana ta faffasa mata baki,

Afan Ya saka aka kulleta daga karshe kuma akayi freeing ɗinta wanda bana cire ɗayan biyu shine dalilin da Ya saka yarinyarta tazo wanda na tabbata tayi poisoning mata zuciya ne ,ni ban ma sake jin wani labarinta ba sai daga baya KB ke Faɗa mun tayi Aure .

    Shiru sukayi kafun Nameer yace yanzu Ai anzo dai dai gurin sannan yakamata ace kamar yarda Nadiya ta faɗa muyi mata lamb'o mu kamata Cikin ruwan sanyi,

Nadiya Zamu samu SWAT ɗin suyi surrounding gida a kamata a act ɗin,

    Tafa hannu Abdallah yayi yace "So mission on ,yau Anisa zata gane cewa ba ko wanne AHALI zaka shiga kaci galabarsu kai tsaye ba muddin suna tare da juna ,mu ɗin bata sani ba tsintsiyane maɗaurin mu ɗaya."

    Kallan Mami da tayi shiru Nadiya tayi tace "Mami menene?"

Wata kwalla dake shirin zubo mata ta goge tace "kawai ina farin cikin yarda kuke tsaye ma juna ne a lokaci dani mahaifiyarku idanuna suka rufe ,Allah ya sani dama ina da doubts Akan Anisa domin ban tab'a jin santa ba koda sau ɗaya ba ,amma dannewa nake gudu kar na Zab'i nawa na cutar da ɗan wani ne,Bani da abunda zance illa Allah ubangiji Ya saka maku albarka Ya kula da bayanku da gabanku,

Duk da iyayenku maza ba ƊAYA ba amma kuna masu Kara tabbatar mun da cikinku ɗaya,haka nake san ku cigaba tsakaninku da kannenku domin kune madubin dubawarsu.

    Matsowa kusa da ita Nadiya tayi ta Rungumeta inda Abdallah na Ganin haka shima ya rungume ta,murmushi Papa yayi yana Mai kallan Nameer yace kai bazaka je bane?

Ƙasa Nameer yayi da kansa yayi murmushi kafin Ya rungume Papa yace"Ni kai Zan bawa hug Papa it been a l'ong time i really miss it,"

Tapping bayansa Papa yayi yace Allah yayi maka Albarka.

    A tare suka fito kowa da zuciya fes cos it been a l'ong time da sukayi having lunch tare haka,a zaman har skyping sukayi da yan uku wanda suke ji kamar su fito ta screen ɗin,

Daga nan kowa Ya Kama hanya dan komawa kan aikinsa .

************

    Iyayen  nasu suka fara shiga gida,a falo suka tarar da Anisa wadda ke zaune kamar tana zaman jiransu,

Suna Shigowa ta taso da farin cikinta hannunta ɗauke da mahmood tana masu sannu da zuwa,

Murmushin yake mami tayi lokacin da taga dining table a cike da kololi,

Kallan Anisa wadda ke bin idanta da kallo tayi kana tace "naga dining dinnan a cike wanne irin abinci ne cook yayi,"

Cike da ladabin ƙarya Anisa tace "wallahi Mami nice ina fatan ban laifi ba ,nace ne bari nayi abinci yau ganin dukkanku baku gida ,da ƙyar mahmood Ya barni nagama yana ta kukan missing grannies ɗinsa,"

ƙarasa maganar tayi tana Mai miƙawa Mami Mahmood ,

Cike da tausayin yaran Mami ke kallansa inda gefe guda kuma da ta juya ta ga Papa yana takawa zuwa sashen sa,

Ɗan wasa tayi masa kana ta miƙa mata shine tace "bari na shiga na watsa ruwa nasan kafin nan Yaran sun dawo sai mu haɗu a ci abincin baki daya."

    Faɗaɗa murmushi Anisa tayi lokaci da Mami tabar gurin tace "Allah sarki ,yau zakici abincin surukarki wanda zai kai ki kushewa ,bama ke kaɗai ba har da iyalinki."

    Tana wannan zaune su Nadiya suka shigo su uku suna labari wanda Ya basu dariya,

Kallansu Anisa tayi tana Mai jin kamar ta harbesu a take ta huta,gyara yanayin fuskarta tayi lokacin da suka shigo ciki,

Da yaukinta ta nufi gurinsu tana Mai faɗin oyoyo Baby,

Hannunsa Ya ɗaga alamun dakatar da ita yace "kar ki fara wannan dani abeg,"

Kafun tace wani abu Ya Kama hanyar da zata sadashi da ɗakinsa,Abdallah na Ganin haka shima Ya kama gabansa,

Nadiya ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login