Showing 27001 words to 30000 words out of 68854 words
wanda hakan yana nufin ka rike mun alƙwari ,menene abun boyewa yan gidan ku, tho nima na boyewa mahaifina maimartaba Rais amma mahaifiyata babbar gimbiya tasan da maganar ,magana ake tayi min aure nikuma bana san wanda za'a Aura mun,infact bani da niyar bautawa ko wanne lamido da sunan sarauniya wadda ta basa mulki bugu da ƙari kuma bana san aikata laifin Aure Akan aure tunda dai niɗin matar Aure ce kuma ina san mijina so na hakika 'dan haka na yanke shawarar barin kowa da komai Nazo gareku,"
Kallan mami da Papa tayi waɗanda suke speechless tace"ina fatan zakuyi haƙuri dani ku ƙarb'eni a yarda nake ta bangarena kuma nayi alƙwarin zanyi iya bakin kokarina wajen ganin na ƙwantar da kaina gareku a matsayin ku na surukaina duk da abune wanda ban iya ba,"
Gyara zamanta ta sake tace "kuyi haƙuri ban samu damar gabatar maku da kaina ba,sunana Jamaimah Rais ,yar asalin garin cameroon haifafiyar masarautar Dilah,"
Ni kaɗai nake gurin iyayena sannan nice ke da hakkin nada lamido Ta hanyar Aure,haka al'adarmu yake ,ni kuma ina san ɗanku shi yasa Na bar komai domin sa.
Hannunta NAMEER yakama yace "tashi kibar gidan nan Jamaimah kafun raina yayi mutukar baci naki Kema Ya b'aci,kizo ki koma inda kika fito."
Tsawar da Mami ta daka masa itace ta saka Ya saketa ,
Kallansa tayi ranta a mutuƙar bace tace"samu guri ka zauna ,Bana san iskanci yanzu Zan b'ata maka sosai da sosai."
Kallan su Nadiya tayi waɗanda a kallo ɗaya zakayi masu kasan cewa sun san da maganar Jamaima,ƙaramar dariya tayi tace "so its true,fuskar kannenka ma Ya faɗa Sun san komai so nida Papanku ne yan iska waɗanda bamu da darajar da zamu san abunda kayi ko,"
Katab'a zuwa kace kana san Aure munce baza muyi maka ba?
Shine har zakayi Aure a wani guri NAMEER bamu sani ba?
Yaushe zamu samu peace sau ɗaya a gidan nan ne,jiya da daren nan muka fita daga wata fitinar gashi wata ta mana sallama,
Tashi tayi idanunta cike da ƙwalla ,
Cike da tashin hankali NAMEER ya bita yana Mai faɗin"mami i can explain please,"
Da fitina cikin idanunta ta juyo tana kallansa tace"idan ka sake taku ɗaya ka biyoni sai na sab'a maka ,Zan maka abunda zakayi dana sani nima nayi,sannan bana san na fito naganka kai da yarinya Chan a cikin gidan nan ,ka ɗauke ta tunda Allah yayi kana da naka gidan ka kaita,Ai kaine ka haifi kanka baka neman shawarar kowa kaje kayi abinda kaga dama da rayuwarka."
Durƙusawa yayi a gurin yana kuka saboda irin tsananin bacin ran da Ya gani a cikin idanun Mami,yana wannan kukan Papa ya gifta ta gefensa ba Tare da yace masa komai ba yabi bayan matarsa ,
Tasowa Nadiya tayi ta Dafasa tace "Hamma wannan kukan bashine solution ba,Ka tashi yanzu kamar yarda Mami tace zamu san yarda za'ayi ,"
Tasowa Abdallah yayi shima yana Mai faɗin"hamma we will sort everything out insha Allah."
Tashi yayi yana Mai kallan inda mami tayi kana Ya share hawayensa Ya maida kallansa kan Jamaima wadda take mamaki zaman da yayi yana kuka,
Tasowa tayi tace "ni Bansan menene abun tashin hankali ba Akan maganar Auren nan,naji ba'a kyauta ba amma Ai the damage has been done maine abun kuka ,"
Cikin wani yanayi na b'acin rai Nadiya Tace"na tabbata baki san menene girman abunda kika aikata ba ko nace baki san menene ake kira da mutunci family ba shi yasa zaki tambaya menen abun kuka."
Barin gurin tayi 'dan idan ta cigaba da Zama a anan gurin zata yiwa Jamaimah wulaƙancin da har abada bazata manta ba,
Da wani iri yanayi NAMEER Ya kaleta yace "kisan inda dare yayi maki domin bana tunanin darenki yana tattare dani,"
Cikin nutsuwa Abdallah yace"hamma idan har Auranka kai da ita kaima kasan Aurene maganar ta Kama gabanta bai taso ba,"
Yarda mami ta faɗa ka ɗauketa ku tafi gidan ka 'in yaso daga baya komai zai gyaru.
Cikin ido Nameer ya kallesa inda shi kuma Ya bashi assurance da ido,
Bai ce da ita komai ba ya shiga ɗakinsa ɗan ɗauko mukullin motansa dana gidan.
Zama abdallah yayi kujerar dake kusa da ita yace"ni tabbata ba kisan wanene hamma ba,ta iyu kin Aure sa amma bana tunanin kinsan menene ma'anar Aure ,nuna lollipop ɗin da Take sha yayi yace "na farko wannan alawar da kike tsotsa gaban su Mami kina magana cikin kalamai marasa da'a Shine abu na farko da zai fara baki matsala,'dan a iya zuwanki yau na tabbatar ladabinki da sauki,
Ta iyu a inda kika fito kowa yana duƙa maki amma annan kuwa Babu Mai duƙa maki muddin baki sauke girman kai da yake damun ki ba dan akwai sa,
Anyi kuskure kuma ba wai ance ke kikayi ba,dukkaninku kunyi amma ki sani abunda kike taƙama dashi na Aurensa to Allah da Ya halicci Auren Ya halicci rabuwarsa ,idan kuma Kina san ƙarkonsa a dole kisan wanene Nameer da abunda Ahalinsa suka ƙunsa."
Bai jira jin ta bakinta ba Ya bar gurin.
B'in sa Jamaimah take da kallo hannunta riƙe da sweet ɗin da bataga wani aibu ba dan tasha a gaban ko wane,wannan Shine karo na farko da wani Ya zauna Ya daddara mata,
Tabbas Family ɗin Nameer is interesting,tana san sabo da baƙon yanayi 'dan haka tana maraba da wannan.
Tana wannan tunanin taga gilmawar Nameer Ya nufi ƙofa,
Kallan akwatinta tayi da kit ɗinta cikin wata irin shagwababiyar murya tace "baby bazan iya ɗaukan abunnan ba is heavy babu wasu maids ne around here?,"
Jin babu motsin kowa sannan yafita a Falon ya sakata yarfe hannu tana Mai jan akwatin da kit din tabi bayansa.
CHUCHUJAY ✍🏽
[3/6, 5:15 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different father's)
Book two 'in AURE uku series
By
CHUCHUJAY✍🏽
Episode 2⃣7⃣➡2⃣8⃣
*'
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
ACCRA GHANA.
Kallo ɗaya zakayiwa dattijuwar matar dake zaune kan katafariyar couch ɗin dake cikin katafaren mansion zaka gane inyamura ce saboda irin yanayi na hasken fatarta wanda yawancin inyamurai suka da akwai ,yar gayu ce wadda a kallonta ma ba sai wani Ya faɗa maka hakan ba,MRS Ella Hans kenan mahaifiya gurin Evans,
Cikin wani irin yanayi take kallansa yayin da shi koma yake durƙushe kan gwiwowinsa a gabanta kansa a ƙasa,da harshenta na igbo tayi masa yare a yayin da take cewa"Evan ka fara magana,ban fahimci maganar kana san converting ba for what?
Saboda yarinya ?kana san yarinyar musulmai shine zaka yi converting ,you are a born christian and kasani barinka addinin mu is An abomination,ka cire yarinyar nan a ranka zaifi maka sauki,muna da kyawawan yaran igbo kamar sune sukayi Kansu ,you choose one,ga Amarachi cousin dinka ,yarinyar nan ba karamin sanka take ba amma kana nuna wa kamar baka san tanayi ba,just dare me i wont tolerate this. "
Zama yayi Ya kamo hannunta yace "Mommy please ba ina san converting bane saboda Nadiya ,i Had to go through My bible again over and over again,jesus said i am a man(john 8:40)
And mommy a musulunci ma shi mutum ne,
And mom yace "i am a son of man(mathew,11:19)"
And God is not a man Mom,haka a musulunci shi ɗan mutum ne bana Allah ba ,
Yace "God sent me only To the lost sheep of israel (mathew15:24,mathew 10:5-6)"
Yace Allah yafisa girma a (john14:28).
Ya aikosane dan yayi ba a matsayin Allah ,bai aikosa dan a bauta masa ba amma dan ayi masa bauta shi kaɗai(matthew 20:28).
"He said i never claim tO be God because i have God To whom i cried and prayed to (matthew 27:46 and Matthew 26:39).
"He said i cant do anything on My Own i Do only what God commands me to Do(john 5:19,30).
Sake riƙe hannunta yayi gam gam yace "Mommy mun sani but we still Call him Son of God"
Ƙwace hannunta tayi tace "bansan mene yake san juya maka tunanin ba,im sure muslim girl d'in Chan ce,and komene zakace a cikin bible da ka karanta yesu ɗan Allah ne haka muka yarda dashi dukkan Kaka da kakani,so kar ka nemi ka chanza "
Marairaice fuska yayi yace"Mommy abunda na lissafa miki wanda bible Ya faɗa is islam,saboda cikin ɗan abunda na sani a musulunci duk ya kunsa,and Trust me mommy Nadiya na ɗaya daga cikin hujja ta na ƙarban musulunci amma badan soyayyarta kawai ba saidan gamsuwa da naji hankalina da zuciyata yayi da islam,i sense peace there."
Da wani irin kallo da uwa takewa ɗanta idan Ya faɗa wata harka da ta yarda da zuciyarta da hankalinta akancewa ba dai dai bace tace "Oge ,islam addini ne na yan ta'adda they are all terrorist ,bana san ka ƙare a hell fire,kullum idan kaji an'a kashe kashe sune,duk wani kungiya na kashe mutane sune ,"
Licking lips ɗinsa yayi 'dan yasan yana da l'ong way kafun Ya shawo kan ta Mommynsa duk da kuwa ita macene Mai saukin kai,
"Mommy dan wasu na ta'addancin da sunan musulmaine ba shine yake nuna duk wani musulmi terrorist ne ba,wasu sunayi ne dan bata addinin da kuma bacewa da sukayi ko kuma wata akida da manyansu suka saka masu a zuciya ,yana nufin kenan christians dake kashe kashe suma kowa Ya zama ɗan ta'adda kenan muddin yana cikin addinin? "
Akwai Good muslims out there da idan kikace su kashe maki goat ma bazasu iya ba ballantana ɗan adam,bai kamata muna yiwa juna kallo mara amfani ba bayan munsan akwai innocent one's out there,and masu kashekashen Chan suna kiran Kansu musulmaine amma basu san menene ma musuluncin ba,
Kamar yarda na faɗa maki it means peace and a ciki nake hango peace ɗina da naki dana Dad dana sister na mercy ,
Saurin ɗaga masa hannu tayi tace babu peace ɗinmu a ciki ,kai dai da kagano naka kaje kayi tayi.
Tasowa yayi Ya zauna a kusa da ita yana Mai sake kama hannunta yace "Mom wallahi idan Ban Auri Nadiya ba Zan mutu ,idan kuma ban mutu ba zan haukace ,idan ban haukace ba kuma bazan kuma moruwa ba,sannan musuluncina Shine babban abunda zai sa na samu Nadiya da Peace."
Da sauri tasa hannu ta toshe bakinsa tana Mai kaɗa masa kai tace "God forbid ,babu wanda zai faru da yarona ,indai kuma Nadiya ne na shirya zuwa Nigeria magana da mutanenta,and na yarda bazan maka dole Akan ka zauna kan addinin mu ba,idan ka Aureta im sure a hankali zaka gane gaskiya har Ita ka dawo da ita hanyar dai dai,amma for now kayi abinda kake so Evans Mommy na tare da kai and zan baka dukkanin goyan baya ."
Rungumeta yayi ƙam ƙam yana Mai jin wani irin dadi yana ratsa dukkan wani jikinsa,yadarta yake nema amma Ya riga yayi converting sannan ko bata yarda ba bazai hakura ba a hankali zaina cusa mata ra'ayinsa,
Raba jikin sa yayi da nata yana Mai gano yar karamar kwallar dake gefe idanunta ,hannunsa ya saka daidai inda ƙwallar take Ya goge yace "Mommy wata rana da zatazo ki yarda dani kice gwanda danayi converting cos im sure ranar zaizo."
" Wanene yayi converting ,hope ba gizo kunnena kamun ba?
Mahaifin Evans, MR craig Hans Ya faɗa a yayin da Ya tsinci maganarsa ta karshe da Ya shigo gidan,
Saurin goge hawaye mahaifiyar Evans tayi tace "don't start it craig,Evans yayi converting and bana tunanin Laifi ne cos kaima daga wani addinin ka biyuni nan kar ka manta you were a jew and My love turned you a Christian "
Zama yayi yana Mai shafa gemunsa yace "bazan damu ba sai naji idan Naji ba Islam Ya koma ba."
Cikin haɗe rai tace "kafaɗa dai dai,He's a muslim now ,"
Yana ƙokarin fara kunfar baki Ta dakatar dashi saboda ita ɗin a tsaye take ta fannin magana dan 'in ta faɗi ɗaya baya ƙaucewa .
Tashi yayi ransa a mutuƙar bace yace"kar ki manta Ella muslims suka kashe kakana and muslims sune manyan maƙiyan Family ɗinmu dan haka kafin yaranki yaje yayi abunda zai dame shi Ya dame mu kisan ta inda zaki gyara cos curse ɗin da kakata ta aje ma duk wani danginmu da Ya koma musulmi zai kamasa sai dai idan har Kina so yaranki Ya talauce yakuma rayu babu jininsa ko ɗaya."
Yana gama maganarsa Ya bar Falon.
Dukan kirjinta tayi a hankali tana Mai jin wani abu yana Mai tsaya mata a kirjinta tace "God ,God have mercy on me"
Kama hannunta Evans ya kuma yi yace "mommy kinsan ban tab'a yarda da superstitions ba and bazan fara yarda dasu yanzu ba,babu abunda zai faru dani,Na yarda da Addinin dana ƙarb'a zai kareni daga dukkan wani curse da yake akwai ,Ballata na ma ban yarda da wani curse ba,
Duba agogonsa yayi yace mommy lokacin sallah yayi let me Go and pray zamuyi magana more idan na dawo ,
Har yakai baki kofa tace"Evans you're walking on the wrong path My child."
Murmushi kawai yayi mata baice komai ba Ya bar ɗakin yana Mai jin kamar an sauke masa wani irin nauyi a ƙirjinsa ,
Bayan yaje yayi sallan Azahar a masallacin da Ya karbi shahada Ya biya gurin wani abokinsa GodFavourite wanda shine Ya fara saka masa interest nayin Tattoo a gefen cikinsa da bayansa wanda da fari yayi ta cewa ayi masa Permanent amma Ya kafe Akan A'a saboda any time zai iya gogewa saboda dama bawai dan yana masifar so bane yayi,sannan gashi a ranar daya karbi musulunci Imam ɗin sai da yayi masa maganar Tattoo Ya faɗa masa da wuta za'a Goge masa Ranar gobe ƙiyaman,dama ba Mai zama har abada yayi ba ,menene yayi zafi,ba ƙaramin tsoro wutar da ake ta faɗa masa take basa ba,dan haka Dole yayi ƙokari wajen ganin ko yayane Ya kauce mata.
A bar ɗin da suka saba haɗuwa Ya tarar dashi ,Cup ɗin Whiskey ɗin da yake sha Ya basa yana faɗin "Man where have you been"
Kallan wine d'in Evans yayi kana yasa hannu guda Ya tura masa yace "i don't do alcohol anymore And nazo gurin ka ne kazo ka raka ni".
Yar dariya favour yayi yace"Man don't tell me that What i heard was true"
Kaɗa kai Evans yayi yace"its beyond tunda gani gabanka ina san ka tashi yanzu muje gurin tekashi Ya goge mun wannan Tattoo ɗin na jikina My religion is against it."
Kaɗa kofin giyar Favour yayi ƙanƙarar ciki na motsi yace "that's sad man,tho i wont Judge you ,but Bro you gonna deprive yourself duk wani enjoyment na rayuwa cos muslims na living boring life ne,no Alcohol,no clubs ,no Amazing sex Before marriage ,Zero 1 night stands Bro ko masturbation ɗinan fa i heard that islamically is haram,you and your body again ,You wont even have the space to steam out your seed your self,juyowa yayi yana Mai kallan Evans da kyau yace "ina ƙokarin suggesting maka Dick pierce da nayi ,omo Bro i had sex With juju this morning and it was hell because she oath not to leave me saboda yarda ring ɗin ke kara mata pleasure,its so sad that you're still a virgin and more ka shiga addinin takura.
"Murmushi Evans yayi yace "ban san inda Bible yace maka duk abun nan da ka lissafa a musulunci Ya hallarta a Christianity,a good Christian yana avoiding duk wani abu da ka lissafa a yanzu , "
Shiru favour yayi kana yace "zaka iya zama a addininka sai ka kare duk abun da na lissafa why do you convert."
Dafasa Evans yayi yace "babu abunda zan faɗa maka ka fahimta dan haka kawai ka tashi muje ka Kaini inda za'a cire mun abunnan Ya dameni already."
Dariya favour yasa yana Mai ƙarasa shanye wine ɗinsa Kana yace"lets go man you're My gee for life ,be an idol worshiper and imma love you equally ."
Yana tunani kiran Nadiya amma ya hana kansa cos yana san yaje mata ne a mutum as pure as honey ,
Dan suna ma ita yake so ta bashi.
A/N:
A page ɗinan wanda yaji kamar cin fuska Ya yafe mun sannan Note im not trying to say this religion is better than this,akwai christians readers hello im not saying ku juya cos addininku ba dai dai bane i have no place, i just state' the fact .
Allah yasan dai dai ,sannan ya yafe mana baki ɗaya.
Chuchujay✍🏽
[3/6, 5:16 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different father's)
Book 2 'in AURE UKU series
By
CHUCHUJAY ✍🏽
Episode 2⃣9⃣➡3⃣0⃣
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
Cikin Yauƙi Jamaimah ke takawa dan zuwa motar da Nameer Ya shiga ,ganin Ya wa motar key tasan tabbas idan bata hanzarta ba zai tafi yabarta Ya saka ta ja akwatinta gudu gudu sauri sauri ta nufi motan tana Mai faɗin "Baby mana wai menene hakan?"
Buɗe bayan motar tayi ta saka akwatinta dan kit din kana ta koma passenger seat ta zauna,
Tun kan ta rufe ƙofar da kyau Ya fafareta dan har sai da ta saka ƙara saboda yarda ta tsorata,
Tunda suka fara tafiyar har suka isa gidan bai ce mata komai ba hakazalika itama dan ganin yarda Ya haɗe rai kamar an aiko masa da saƙon mutuwa,
Bakin katafaren gidansa dake cikin GRA ya tsaya yana Mai yin horn,sau ɗaya yayi Mai gadin gidan yazo da gudunsa Ya buɗe masa dan yasan motar Nameer sarai,
Bai tsaya kula gate man ɗin ba Ya nufi ma'adanar aje mota Ya aje,
Shi Ya fara fita Kana ita ,
Get man d'in da Ya tako garesu ta kalla da wani yauƙin wulaƙanci tace "kai zo ɗauki min akwatina ka shiga dashi ciki sannan kabi mun shi a hankali dan yayi costing salary dinka sau goma."
Da mamaki Nameer Ya juyo yana kallanta dan a haife Mai gadin Ya haifeta,
Hannayensa Ya saka a kugu yayin da Mai gadin Ya nufi akwatin dan dauka amma Ya tsaya a lokacin da Nameer yace "Baba sulaiman bari mata akwainta ka koma kan aikinka dan aikinka yafi ɗaukan akwatin nan."
Babu musu Baba sulaiman Ya juya yana Mai faɗin Angama ranka shi daɗe.
Buɗe baki tayi tawani shagwab'e fuska tace "yanzu dan Allah Baby mene hakan,Mai zaisa kayi humbling ɗina gaban Mai gadi kaskantacce,wannan ai salan kaja mun raini ne ina matar gida.
Karamin murmushi yayi Ya Kalleta a kyau yace "Jamaimah kenan,kina bani mamaki,ke gani kikeyi kamar ke kinfi