Showing 45001 words to 48000 words out of 68854 words
yanzu im 29 ba?"
Sannan nayi achieving komai da yakamata mutum a shekaruna yayi ko?
Kallanta da kyau Mami tayi tana Mai san fahimtar inda maganar Nadiya kesan tafiya kafin tace"kin samu mijin aure kenan,to kice Ya turo".
Yar karamar dariya Nadiya tayi cike da jin kunya tace "Kai Mami "
"Ehen ai idan kaji budurwar yarinyan ka ta fara magana haka to Aure take so ,yanzu haka nima tawa budurwar dake gabana Aure take so,juyowa Mami tayi tana Mai faɗaɗa fara'ar da Rabon da tayi ta kwana biyu ,daga mata gira ɗaya tayi tace "uhum ina sauraranki wanene lucky guy din".
Ƙasa tayi da idanunta tace "Mami na ta kaina you got me,sunansa Ahmed and ghanian ne mahaifiyarsa kuma yar Nageria ce amma inyamura ce".
Ɗan shiru mami tayi na wani lokaci cikin fuskar da zakace abun Ya daki mutum tace"Mai ya faru da dukkan Hausawa da fulanin Nigerian da sai Kinje har ghana kin zaƙulo mana ɗan ghana irin inyamurai ni Umaimah ,"
Cije lebe Nadiya tayi tace "Ai mami bama wannan ba ,he was a Christian amma Ya musulunta sannan yanzu haka suna nan Nigeria da mahaifiyarsa akan tana san ganin iyayena"
Gyara zama Mami tayi tace "interesting,yanzu maganar da kuke yazo da Mamansa nan dan taga iyayenki ,ita ma musulmarce sannan a danginsu mace ke zuwa ganawa da iyayan mace ,bani nasha".
Sosa ƙeyarta tayi tace "ita ba musulma bace 'infact dukkan iyayensa ma babu musulmai shi kaɗai ne musulmi shima kuma haɗuwa dani Ya saka Ya musulunta".
"Uhum ,kice saboda ke Ya musulunta,abun gwanin dadi na kwana biyu banji labari Mai ban dariya da daɗin wannan ba,na kasa yarda Nadiyata ta faɗa tarkon mayaudara,dama da popcorn munayi munaci cos this is hilarious, "
Ganin da gaske Mami bata ɗauki abun gaske ba Ya saka Nadiya saka serious face tace "mami da gaske nake ba wasa ba Allah,Bana boye miki komai 'dan baki koya mun yi miki boye boye ba shiyasa a wannan karan bazan fara ba,na amince da shi Mami sannan na gamsu da cewa musuluncinsa ba domin Ya yaudareni bane Allah ne Ya kirasa Ya zabesa And Sanin wacece ni yasaka ban tab'a bashi dama ko na nuna masa amincewata da soyayyarsa ba har saida na tabbatar da cewa ni dashi akwai hallarci,
Bugu da ƙari kuma nasan AHALINA ba mutane bane masu duba banbanci na Al'ada muddin kuwa addinin mu abu ɗaya ne dashi kawai nayi amfani wajen zuwa sanar dake kai tsaye ba tare da Naji wani abu ba Mami.
Shiru Mami tayi tana kallan ta Kana tace"daɗina dake akwai iya tsara zance muddin kuwa Kina san abu,Naji dai yanzu gobe idan Papanku Ya dawo tunda bazani asibiti ba zamu zauna mu tattauna akan maganar sannan mu samu Daddy muyi magana dashi bayan haka sai su zo mu gansu nan da kwana biyu nasan dole Papanku bazai taba bada goyan bayansa ba ɗari bisa ɗari muddin baiyyi bincike sosai akansa ba da kuma danginsa".
Rungume ta Nadiya tayi tace "Allah Ya saka maki da gidan Aljanna Mamina uwa ta gari,"
Shafa bayanta mami tayi tace "uhum uchenna "
Dariya suka saka a tare inda Mami ta daɗe tana nazarin wannan baban al'amarin da Nadiya tazo dashi.
Kamar yarda tace sai tayi magana da Papa bayan dawowarsa kuwa ta zauna tana Mai zayyana masa abunda ke a aƙasa ,ɗan jim yayi kafun yace"kuma tace tana san yaran?"
Kaɗa kai mami tayi tace "haka nan tace sannan a idanunta ma na gano hakan ,kawai dai ina jin tsoron Abunda zaije Ya dawo ne wanda Ya shafi banbancin al'ada da kuma addini wanda kaga 'fa yaran nan shi kaɗai ne musulmi a danginsu wanda kuma sanadiyar ita Nadiya ɗin Ya musulunta".
Tabbas yasan maganarta da ƙamshin gaskiya,amma komai a rayuwa idan zaka duba ka duba positive side ɗinsa,
Cikin Hikima ya ƙwantar mata da hankali inda ya sake kwantar mata hankali akan zai yi bincke Mai kyau akansa 'dan haka suka bawa Nadiya dama akan yazo ɗin kafun su kai maganar gurin su Daddy,
Ille kuwa kamar yarda Papa ya bukaci ganin Evans haka yazo cikin shiga ta mutunci da kammala,a hirarsu da sukayi mai tsiya Papa da Mami suka nuna gamsuwatsu da Shi 'dan haka babu bata lokaci suka kai maganar gurinsu Daddy waɗanda suma bayan ganawa da mahaifiyarsa suka gane ita ɗin babbar mutum ce Mai fadin zuciya 'dan haka suka rufe babi na ƙabilanci da banbance Ra'ayoyi da Al'ada suka ƙarbi Evans da zummar zasu fadaɗa bincike sannan zasu nemesu domin tsayar da magana ɗaya.
Chuchujay✍🏽
[3/6, 5:20 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different father's)
Book two in Aure uku series
By
CHUCHUJAY ✍🏽
EPISODE 4⃣3⃣➡4⃣4⃣
GARABASA GARABASA BONANZA
2024 Shin kuna sane da ban bada garabasa ba?
To ku kwantar da hankalinku ga chuchu dai tazo maku da garabasar sabuwar shekara,
Shin kin fara kin fara karanta YAR AREWA labarin captain Jasmine Bilal shareef da captain Shuraym Sadauki,
Ta tashi da mafarkin zama pilot a yayinda shi da yake kan aikin yake kusheta Akan tayaya ɗiya mace Yar Arewa zata zama matuƙiyar jirgin sama?
Soyayyar da ta shiga tsakaninsu ba tsammani wadda take ƙokarin danne kiyayya .
Ko kuwa kin fara karanta littafin ABLA ADNAN ne labari na matashiyar budurwa wadda bata barin taƙwana ,budurwar da tazamarwa masu kuɗin gaske barazana ,
Shin baki fara karantashi ba ko kin fara kin tsaya saboda kuɗin Ya maki yawa?
Maza zo na maki sauki ki ji yarda soyayyar ABLA take farawa da PRINCE WASEEMUDDIN,kowa na kiranta karuwa harda shima Shin ita ɗin karuwarce?
Maza garzayo gareni ka samu amsa,
Normal price na YAR Arewa book 1&2 N700
ABLA ADNAN N700 complete amma a wanann lokaci na garabasa kuzo na baku ,Yar arewa 1&2 da ABLA adnan Akan farashin naira N600 dukka biyun ɗari shida kacal 🥱ragin N800?
Kamar yayi yawa amma a haka dai Zan baku wannan garabasar ,masu cemun sati yayi kaɗa ga shi kanan sai 1st February 2024
maza kar ayi baku.
0264267657
Gt bank
Amina jamil adam.
09058191213
Dm me
Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga masu comment na wannan littafi wanda ina mutuƙar jin dadin sharhin ku,kuyi yarda kuka ga dama dashi.❤
Ina mutuƙar kyaunarku.
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
Adda wai maganar me kikeyi cos wallahi bana fahimta
Kina nufin Hamma Ya Auri Mai Aikin Aunty shatuh fa kike magana ,
Abdallah Ya faɗa da mamaki yana Mai kallan Nameer da Nadiya da Aunty shatuh ,
Dafa sa Nadiya tayi tace "kana san tane sai kayi magana ,beside maganar da ake ba Auranta Hamma zaiyyi ba illa za'ayi pretending ne akan Ya Aureta d'in amma ba Auren nata zaiyyi ba ka ƙwantar da hankalinka."
Wani kallo Abdallah ya bata cike da gardamar kalmarta na yana san Hafsa yace"ba wai maganar ina santa ake ba amma magana ce ta Menene dai dai gudun kar a shiga hakkin Addini sannan ita hafsan ta amince baza'a shiga hakkinta ba "
Dariya Nameer yasa yace "ka kwantar da hankalinka yallabai ,babu wanda zai shiga hakkin Addini insha Allahu,"
Shiru yayi bai sake cewa komai ba amma tabbas zuciyar sa bata kwanta da wannan tsarin da Nadiya ta tsiro ba,
Aunty shatuh wadda ta kula da rashin nutsuwar Abdallah wanda tun tuni tasan yana san hafsa tace "Nameer wannan abun Ya zamana business ne straight ,ka samu abunda kake bukata ga matarka ka bama yarinya kuɗinta ta dawo nan cos kasan da kyar na samu ta amince it took me great effort "
Kaɗa kai yayi yana Mai faɗada murmushinsa yace "na baki assurance ɗina Aunty nasan yarda Jamaimah bata san kishiya bazai dauke mu lokaci Mai tsayi ba zata dawo gurin ki cos naga alamar ke kanki baki san rabuwa da ita ,ni nama ƙosa naganta yarda Aunty ta gama kafa mun shariɗai akanta.
Suna wannan maganar sallamar Hafsa ta katse su,
Wani irin yanayi Abdallah Ya tsinci kansa ciki lokacin da Ya saka idanunsa akanta domin ganin yarda ta sake yi masa wani irin kyau Mai ɗaukar hankali ,."
"Masha Allah "
Cewan Nameer wanda shima hafsa ɗin yake kalla wadda keda wani irin sassanyan kyau,
Da sauri Abdallah ya kalle sa ganin yana kallanta,haka kawai yaji wani irin kulu a wuyansa Ya tsaya cos shi kansa bai san yana san Hafsa har haka ba sai yanzu da aka kawo wannan maganar ta zuwan Hafsa gidan Nameer ,
Zama tayi kasa bayan shigowarta tana Mai gaida kowa cikin jin nauyinsu,
Kallanta Aunty shatuh tayi tace "yarinyata taso kizo kusa dani ki zauna,"
Cike da jin kunya tace "Aunty nan ma yayi".
Sanin bazata dawo ɗin bane Ya saka Aunty shatuh cewa,zan baki kuɗi kuje ke da Nadiya ki zabi kayan da kike so saboda wannan aikin yana bukatar chanjin wardrobe kinga a matsayin Mata zakije gidan,kar ki ɗauke shi matsayin kayanki basuyi ba ,kinga Ai amarya da sabon kaya aka santa,
Sannan zaku tsaya ku siya waya domin naga ta hannunki karamace dama tun tuni ina da niyyar siyan maki waya,Mai ne kuma kike buƙata?
Dan shiru Hafsa tayi ba tare da ta gamsu da maganar kuɗin da zasu kashe mata ba tace"Aunty nagode da komai Allah Ya saka da Alheri,amma Aunty bana san kashe kudin da zakuyi akaina ,iya kulawarku ma kawai ta wadatar sannan ni zanyi aikin nan ne badan abiyani ba Ai alherinki gareni yafi kudi duk yawansa,siyan kayan kuma tunda kince dole ne ni 'ina gani ba sai na bita ba komene aka siya dai dai ne,sannan ina san kafun naje gidan naje gurin inna na gansu tunda kince kar na faɗa mata wanda nima nasan baza taji daɗi ba."
Cikin ƙwantar mata da Hankali Aunty shatuh tace"shikenan Nadiya zata je idan yaso sai Nameer Ya kaiki gida daga chan ki wuce."
Charaf kamar Abdallah na jira yace"Ya bari Aunty zan kaita idan yaso sai na aje ma Nadiya ita sai ta wuce da ita gidan Hamma cos kinsan baiyyi ace shi Ya tafi da ita gida ba"
Sanin hankalin Abdallah ba kwance yake ba da wannan tsarin yasa Aunty shatuh cewa"kaga shikenan ma hakan ma dabara ce".
Nameer ne Ya fara tashi yana Mai faɗin"dama kuwa ina da wani Aiki Mai muhimmanci tare da Fadil bari na fara wucewa,kallan hafsa yayi cike da sigar tsokanarta yace "sai mun hadu a gida amaryata sannan kisa 'fa aranki matata lioness ce Allah yasa kin shirya"
Dariya Aunty shatuh da Nadiya suka saka banda Abdallah wanda maganar Nameer ta tsaya masa a wuya duk da kuwa Yasan maganar gaibu ce,
Sallama Nadiya ma tayi musu inda Abdallah Ya tashi yana Mai cewa Hafsa ta samesa a mota,
Ya daɗe yana shawara a zuciyarsa akan ya faɗa mata yana santa wata zuciyar kuma na faɗa masa Ya jira ta gama aikinta gidan Nameer,
Yana wannan shawarar Ya hangota cikin milk hijab ɗinta wanda yasha guga duk da kuwa ya sha jiki,tafiya take cikin nutsuwa wadda ke ɗaukar hankali Mai kallo,
Fitowa yayi da sauri Ya buɗe mata kofa,cike da kunya ta shiga tana Mai faɗin "na gode."
Rufewa yayi Ya zagaya Ya shiga seat ɗinsa Ya zauna,rufe idanunsa a hankali yayi kana yayiwa motar key Ya tashe ta suka fita a cikin gidan.
Tunda suka fita titi babu wanda yayi magana ,a karo na farko ya Kalleta yace ina zamuje hajiya,
Murmushi tayi a karo na farko tace "da naga ka ɗauki hanya nazata kasan unguwan namu Ai,tudun wada ne,"
Shafa sajensa yayi yace "kinga kuma na dauki hanya dai dai wanda zuciyata ta bani hakan,Mai kike tunani akan zuwa gidan Hamma? "
Ya jefa mata tambayar cikin maganar.
Kallan waje tayi tace "to gani nan dai ,babu abunda Aunty zata nema gurina na kasa yi mata domin a iya zamana gidan ta babu cuta sai Alheri,shi yasa da ta mun magana na yarda tunda nasan bazata cutar dani ba.
Kaɗa kai yayi yace "Yayi,nasan dai baki da saurayi,Mai zai hana ni nazama saurayinki tunda kinga ni Abdallah na kamu da sanki mara misaltuwa,ina sanki da yawa hafsa sannan san da nake miki soyyayace wadda nake so muzama guda ta hanyar Auren sunna'ar ma'aiki,banyi niyyar faɗa miki ba amma ganin yanzu zaki wani gurin da babu damar naje kar na b'atawa hamma na plan dinsa Ya saka nake sanar dake mene ke cikin zuciyata ,sannan ban ce dole ki amsa mini yanzu ba ,kije kiyi tunani koda kuwa zuwa lokacin da zaki bar gidan Hamma ne,ina san ki je gidan ne da sanin ina fitinar sanki Hafsat ".
Wani irin maƙwat ɗin yawo ta haɗiya da ya kai Ayar maganar domin jinta take kamar a mafarkin da idan akace ta tashi zata firgita ta miƙe,wai ita Abdallah Hafiz ke furtawa kalmar so,baki ɗaya jinta tayi kamar a saman ruwa ,
Dan leko fuskarta yayi,da sauri ta Juyar da kanta tana Mai yin ƙaramun murmushi,
Murmushin shima yayi yace "gamu dai mun shiga tudun wada ina zamuyi,"?
Cikin kwatance suka isa gidan nasu,tana ƙokarin buɗe kofar ta ɗago ta kallesa tace"bazaka shiga ba?"
Girgiza mata kai yayi yace "Inajin kunyane ,zan shiga amma ba yanzu ba sai ranar da kika amsa mun soyayya ta kinga sai na shiga kaina a sama Ina da soyayyar Hafsa na."
Saurin bude kofar tayi cike da jin kunyarsa ta shiga gidan.
Girgiza kai yayi yana Mai binta da kallo yana jin wani nishaɗi yana ratsasa,ko ba'a faɗa masa ba yasan cewa shi Mai sa'a ne gurin hafsa .
Baya wasu mintuna ta fito da Muhammad yana rike da yar karamar Jakarta wadda ta karba kafun su karaso bakin motar tana Mai dagaa masa hannu,
Koda ta iso motan Ya kunna sautin qur'ani yana saurare,da sallama a bakinta ta shiga,
Ido Ya ƙura mata,dauke kanta tayi cikin wata irin murya da ta tafi dashi tace "ni kadai na kallo na haka bana so".
Daga hannunsa yayi cikin surrender yace na bari gimbiya,key yayiwa motar suka bar gurin,
Kai tsaye gurin siyan waya suka nufa Ya siya mata tsaleliyan waya da sim card wanda a take akayi register,
Da kyar ta karbi wayar shima sai da Ya haɗa da dabara,bayan sun gama Ya kaita office d'in Nadiya ,kamar kar Ya wuce Ya barta ,amma hakan nan gudin kar Nadiya ta gano wani abun Ya wuce.
****************************
Kai tsaye Nadiya da Hafsa suka nufi gidan Nameer wanda kafun suje ta kirasa ta sanar masa da zuwansu,
Dama kafun su wuce sai da ta kaita aka gyarata tasha lalle sannan tasa wani mayyar TURKISH abaya Mai shegen kyau
Already dama ko wanne daki a gida a gyare yake 'dan haka yace ta kaita dakin dake gefen nasa ,
Suna isa kuwa bata tsaya wani knocking ba ta buɗe gidan suka shiga ,babu wani sallama ko magana ta ja akwatin Hafsa ta buɗe dakin da Nameer yace ta zauna ta shiga da kayan,
Biye da ita hafsa take zuciyarta na ɗari ɗari domin tana tsoran haɗuwa da Jamaimah 'dan taji ance yar sarkice,
Kama hannunta Nadiya tayi ta zaunar da ita tace"Hafsa kalli nan,jikinki 'fa Zaki saki idan ba haka ba Jamaimah zata raina ki sosai cos yar rainin wayauce na fitina ,nasan Abun da wuya ,amma a yanayin Jamaimah tana da gasa ,nasan ganinki a nan zai saka tayi duk abunda zatayi domin ganin ta samo kan Nameer."
Kaɗa kai Hafsa tayi tace "Aunty ina jin kawai gabana na faɗuwane amma insha Allahu zan ƙokari ,amma zakina zuwa ko?"
Murmushi Nadiya tayi tana Mai jin san hafsa cikin ranta,she's just another word of simplicity,kaɗa mata kai tayi tace"insha Allahu zan rinka zuwa,amma dole fa kizama jajirtatta wannan sanyin ki ajesa saboda idan kikace sanyi zakiyi zaki sha wahala."
Ajiyar zuciya tayi tace zan ƙokari.
Suna cikin aje kaya jamaimah ta shigo ɗakin kamar wata barauniyya,
Turus tayi tace "to lafiya?"
Tashi Nadiya tayi tace"lafiya uwar gidan Hamma ,nayi tunanin kar nayi knocking ne ki kasa tashi ki buɗe gudun kar na baki wahala ya saka na ƙarbo key hannun Hamma cos zuwan nan bana san bata lokaci.
Ɗaga hannu Jamaimah tayi tace "gyara zan maki ,bana san kirarin uwargidan Nameer ,saboda ni Uwargida ce kuma amarya ,daga ni babu ƙari,kallanta ta mayar kan Hafsa tace "wannan kuma 'fa,sannan Mai kukeyi ɗakin nan?"
Yar ƙaramar dariya Nadiya tayi tace "Allah sarki,shi yasa nace uwargidan Hamma saboda yanzu yayi amarya,"
Nuna Hafsa wadda gabanta yayi mugun faɗuwar ganin haɗuwar Jamaima tayi tace "gata nan ,amaryar Hamma kenan wadda aka ɗaura Aurenta da Hamma a yau sannan iyayanmu sun shaida,sannan abun daɗin shine yar danginmu ce wadda tasan darajar iyayanmu da kuma mijinta da yan uwansa,Abu Mai daɗin kuma shine ta iya girki chef ce ,sannan tazo da niyyar girkawa mijinta da kulawa dashi wanda shine ibadar Aure.,"
😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂
Tofa ....
CHUCHUJAY ✍🏽
[3/6, 5:21 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different fathers)
Book two 'in Aure uki series
By
CHUCHUJAY ✍🏽
EPISODE4⃣5⃣➡4⃣6⃣
Lokaci guda ji da fahimtar Jamaimah Ya dauke domin maganar tazo mata ne a bazata sannan kamar ƙanzan kurege wanda tama san shine ,
Dariya tasa Mai sauti tana Mai Nuna Nadiya ,sai da tayi Mai isarta sannan tace "kalli Nadiya nasan muna da differences namu tsakanina dake ,and nasan abunda nayi miki ranar da kikazo bai kamata ba,sannan Kema wanda kika mun bai kamata ba,Ya wuce lets bygones be bygones ,muyi moving on ,amma wannan kam ba Wasa bane ,idan kuma wasane Ya bani dariya ba sosai ba,so please mudaina kalar wasan nan,im sure sabuwar yar Aiki ce Mami ta bani ko? "
Zama tayi tana Mai crossing Kafarta tace "kin iya zaba mata daki kuwa ba sai nasha wahalar ƙawala mata kira ba ko ita ta b'ata min lokaci,ni dama nasan Mami zata ji dani,dole gobe na shirya naje nayi mata godia,"
Wani irin Kallo Nadiya ta bita dashi Kana ta ɗora yatsunta guda biyu gefen kunnen ta tace"are you nuts"?
Ko kuma wani abu akanki yana miki yumm yumm da yake hana ki gane lissafi?
To bari kiji na faɗa miki,maganar da kike ɗauka kanzan kurege gaskiya ce wadda babu ƙarya ko wani wasa a cikin ta a yanzu wata daya kenan da Auren su kamar yarda akayi naki babu wanda Ya sani,to suma haka akayi nasu wanda ita a wannan karan iyayanmu sun sani kuma sun amince maganar da nake miki a yanzu ma cikin ne a jikinta ,wata guda kinga kuwa tana shiga tayi tuntube dashi, idan baki fahimta ba bari na fasa miki baƙi ,ita da Hamma Nameer sun san juna sun zama abu ɗaya,sunyi consummating Auren su wanda a process ɗin aka samu rabo Mai amfani