Showing 15001 words to 18000 words out of 68854 words

Chapter 6 - AHALINA Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

282

New york ba.

    Cije leben tayi tace "send me evidence ɗin ta Email ɗina sannan kaja bakinka kayi shiru,and make sure a sauran yininka gida kayi avoiding ɗinta and be careful."

Dan shiru yayi yana kallanta kafun yace"abun is serious haka".

Kamar jira take Ya tambaya ta amsa tace "ƙwarai ,'dan haka be careful ,Tashi yayi yana Mai saka hannunsa Aljihu kafin yace "nasan ko mene tazo dashi Family ɗinmu yafi karfinta cos kan mu a haɗe yake babu wanda zai iya rabamu ,saboda wanann ƙaunar ma nake so yanzu kasaka mun 20k zan ɗan fita,kuma banda mai"

    Dariya tayi tace"naughty boy,ko wacce mota a gida cike take,kai dai kace mun zaka je yawo and its okay zan tura maka 50k"

Da murnarsa Ya fita office ɗin nata,

Bayan ta gama ayyukanta itama wurin lunch time Abdallah Ya kirata Akan su haɗu zai zo da Fadil,

    Ita ta rigasu zuwa restaurant ɗin kana suka zo,

Kallanta Fadil yayi kafun Ya zauna yace "Nadiya right" .

Ƙaramun murmushi tayi tace "yes Nadiya,naji daɗin haduwa da kai fuska da fuska,"

Bismillah zauna .

    Babu musu ya zauna,waiter ne yazo sukayi ordering abinci,

Kallan Fadil tayi kafun tace"kai Abokin Hamma Nameer ne ko kuma Abokin Salis"?,

Ba wani ƙwana ƙwana ya kawoni ba saboda abubuwan da na bari kafin nazo nan suna da yawa,

    Da mamaki Fadil Ya Kalleta yace "ina kika san Salis,sannan wannan tambayan na ji ƙamshin trouble cikin ta hope im safe,

Ruwan ta ɗauka ta ƙurba kana tace"Eh kamar kana cikin gaskiya a hangena,kamar yarda nace maka im a busy woman to ba wasa nake ba,let me cut to the chase,"

Wayarta ta ɗauko ta kunna recording  ɗin hirarta da Salis tace"ka saurara da kyau".

    Nutsuwa yayi dan saurara yana Mai sake kallanta cos yarda yake ganinta a hoto ta taka haka a fili sannan duk wani abu da take a yanzun ji yake tana wani sake burgesa,Amma Nameer shegene,yana da Zan ƙaɗeɗiyar ƙanwa tun fil azal yayi masu shiru Ai Da tun tana da ƙananun shekarunta zai gina mata soyayyarsa dan shifa Ya kamu,

Ɗago kai yayi yana Mai kallanta lokacin da sautin Ya hau kan muryarsa ,

Ɗaga masa gira ɗaya tayi tace "Ba sai ka tambayeni ba ,lokacin da kuke waya ina zaune a office ɗinsa ,"

Jan wayarta tayi da ta tabbatar ankai inda Ya kamata yaji,

Mayarwa tayi handbag ɗinta tace "ka fara magana,ka dai saurari abunda abokin ku yace ,sannan da wanda ka faɗa a yayin da Ya kira ka,menene gaskiya a ciki sannan idan kamun ƙarya bazan ƙasa a gwiwa ba wajen sanarwa da Hamma Nameer da irin micijin da yake tare,

Hannu Abdallah Ya saka a ƙafarta jin yarda take wa Fadil ɗin magana yace Adda mana.

    Murmushi Mai sauti Fadil yayi yace "kar ka damu Abdallah,Ai duk wanda yake hot seat bai kamata Ayi masa sauki ba sannan nima yanzu Akansa nake Its okay,"Wato ainayin magana fisabilillahi duk abunda Salis Ya faɗa maki ƙaryane ,

Nameer mutum ne wanda ko drugs kake yana tare dakai zai rabu da kai,shi Salis ɗin da yake wani maganar An Kama Nameer da Drugs ƙarya yake yi,maganar da yake shine aka Kama da Drugs masu haɗarin gaske ,mu muka fara ganinsa dashi so we asked him yayi turning kansa in amma yaƙi so mukayi reporting ɗin sa wanda shine babban Abunda Ya saka muka yanke alaƙa dashi,

Sannan magana da yake na Nameer na bin mata ,ƙarya yakeyi,nayi imani da Allah da kikaje gurin sa Ya nuna miki ɗaya daga Cikin halayyarsa na dabbobi im sure,

Amma kirana da yayi akan maganar Jamaimah tunda ya fara miki maganar bari na Faɗa maki Ya abun ya faru,

Cikin kwanciyar hankali yayi mata Narrating yarda Auren Jamaimah da Nameer Ya kasance.

Dukan table ɗin Nadiya tayi tace "a cikin zancen nan Fadil kaine ummul abaisin komai da Ya faru "

Kamo hannunta Abdallah yayi yace "Adda Hamma is equal responsible ko nace miki ma yafi kowa laifi cos Aurensa muke magana akai wanda Am sure a lokacin yana da isashen ilimin addinin da yasan cewa Auren da yayi Ya ɗauro,the damage has been done kawai yanzu solution' zamu nemo ,amma tukunna Ya maganar Anisa,

    Kallan Fadil tayi "tace Thank you,Zan iya samun numbern Jamaimah gurinka ko kuma wata hanya da Zan sameta?

Murmushi yayi yace "you're welcome and wallahi tun gama makarantar mu bani da wani contact da ita ,amma dai yar kamaru ce ,sannan kuma ɗiyar sarkice shi kaɗai na sani.

Abincin da sukayi order aka kawo musu, bayan sun gama ci Fadil Ya kalli Nadiya yana Mai shirin barinsu yace "Zan iya samun numbern ki?"

Murmushi tayi ta buɗe jakarta ta ciro office card ɗinta ta miƙa masa tace "gashi ,kana da jiki mai kyau ,sai dai kana da bukatar motsa jiki sosai,

Duk lokacin da kaji aiki a company ɗin yayana Ya isheka kazo muna da gurin aje ka  .

    Dariya yayi wadda ta bayyana hakoransa yace "nine da godia Hajiya Nadiya sannan kamar yarda kika Bani wannan tayin Zan ƙoƙari naga nayi amfani dashi,"

Yana bari gurin Nadiya ta kalli Abdallah tace "kake wani tambayana maganar Anisa gabansa ,ba wani hurumi da yake dashi na jin wacece ita,amafaninsa na muji tabbacin Auren Hamma ne kuma munji cos Anisa da kake gani serial killer ce ,Assassin sannan she's dangerous fiye da Tunanin ka,  "

Abunda ta samo na dangane da ita ta nuna masa,da mamaki yace kamata yayi Info ɗin nan yanzu yana gurin police 'fa,

    Karbar wayar Nadiya tayi tace"as if,"

Kana tunanin police zasu wani ɗauki Wani hukunci kanta?

Idan zasu dauka Mai takeyi har yanzu a waje,

Bro abun wannan yarinyar is beyond tunanin ka ,babu ruwan mu da kisanta da dalilin rashin kamata da ba'ayi ba,yanzu mu babban damuwar mu shine tayaya zamu gano dalilin zuwanta gidan mu,sannan mu sakata tayi wani fuck up ko sau ɗayane mu bada hujjar da zaisaka ta zuwa gidan yari,shikenan,

We need her out of our home and our lives.

Sannan Maganar Jamaimah dole muyi confronting Hamma ,wannan ba abu bane na boyewa cos idan Ya bar abun nan a boye nan gaba Outcome ɗinsa babu kyau,

Kaɗa kai yayi cikin gamsuwa da shawararta ,bayan sun gama cin abinci kowa Ya koma kan aikinsa Akan idan suka koma gida zasuyi magana da Nameer.


**************

CAMEROON DILAH PALACE  .

     Jamaimah bazan gaji da faɗa miki ba kinyi girman da masarauta ke buƙatar kiyi Aure ,sannan kinfi kowa sanin Al'adar mu babu wani namiji da zaki Aura bayan wanda muka zab'a miki shima ɗan AHALINMU,Saboda shi kaɗai ne wanda zamu ɗora kan kujerarmu saboda kinsan dai mazan Mata ke sarauta ba gado ba,shi yasa muke zaban na jikinmu,masarautar nan baki ɗaya kece mace wanda mijinki zai gajeni.

Tun Kina yarinya muke miki abunda kike so kika zaba ,kama da abunda zakici zuwa sutura ,zuwa zabin karatu,wanda ke Kina kallo yarda akayi tataburza zuwanki China,

Yanzu kuma Lokacine da magabata suka zab'a maki mijin Aure HARITH bana san azo an'a wayace Jamaimah,

Mahaifinta Sarki Rais Ya faɗa ciki harshensu na Fulanin cameroon fuskarsa fal dumuwa.

    Gyara zamanta tayi tana mai kallan girman faɗar mahaifinata wanda Ya gada guri mahaifin Mamanta ,kamar yarda baban nata Ya faɗa dukkansu idan kabi zagayen masarautar da tarihin mulkinta maza da matansu AHALI ɗaya ne,shi yasa Aurensu mace ɗaya wanda a haka aladarsu ta tafi muddin zakayi mulki macen nan guda ɗaya,

Kallan mahaifinta tayi cike da fitsara cikin yaren nasu da kuma salo na amfani da soyayyar da mahaifin nata yake nata tace "Lamiɗo ,kafi gane nayi Aure cikin wannan masarautar nazama baiwar wani wanda saboda ni yake mulki badan Ya kai yayi ba,,

Kamar 'fa kaine Lamiɗo, yarda Dada na ta ɗoraka kan kujerar nan amma kana kallo abinci nan bata ci sai ka gama tukunna taci sauranka indai Kana gurin wai da sunan al'ada,alada a mey?

Ni gaskiya Lamiɗo ka yafe ni ,dan babu wani da Zan Aura wanda kuka zab'a 'dan kawai na maidashi Lamiɗo,sai dai sarautar nan tabar ɗakinmu ta koma wani ɗakin tunda Ai masarautar nan akwai yaƴan mata da kakannin akwai yarda zakuyi ku ɗora harith d'in idan shi kuke so,ga yan mata a gidan,amma banda Jamaimah 'dan yarda nake zab'an duk wani abu da nake so a bisa yarda kuka lalatani da zab'ar abinda nake So haka nan yanzu ma zaku barni da wannan lalatar na zab'i wanda nake san Aura dan har nama zab'a .

    Da fuskar lallashi lamido Ya Kalleta yace "idan kin sakko zamu sake magana yar Albarka ,naga alamun yanzu bazaki fahimci Mai nake nufi ba,"

Tashi tayi tana Mai sake basa girmansa kana Ya fita a fadar wadda dama daga ita sai shi ,

Tana ƙokarin fitowa wani bafaɗe yana koƙarin shiga inda bai Aune ba sukayi gware,

Ɗago kai da yayi yaga itace ba ƙaramun rawar jiki Ya fara ba 'dan yasan rashin mutuncin Gimbiya Jamaimah yau zai hau kansa,

Ille kuwa bai Aune ba ta ɗauke fuskarsa da wani irin tafi wanda yayi bala'in gigitasa,

Alƙabarta da Ya goga ta cire ta cilla masa kana ta miƙa hannunta wanda ƙuyangunta sarai sun fahimci Mai take nufi,

Da gudu ɗaya ta ƙaraso da ƙwarya a hannu ɗaya kuma da ruwa a wani tulu ta fara zuba Mata tana ɗauraye hannun data mari bafaden dashi,

Alamu tayi da hannu zuwa ga bafaɗen wanda sarai Kungarta ta hannun dama ta fahimta ,kai tsaye gurin Bafaden tayi da ƙokan da ta wanke hannu ta kama kanta ta kafa masa ruwan sai da Ya shanye tasa kana tace "a ɗauke mun shi akaisa gidan gyaran hali ,ruwan nan da yasha shi kaɗai nake san Ya riƙesa har gobe ."

Take kamar jira suke kar suyi wani laifin suka kama dakarin wanda yake ta ihun bata haƙuri amma taƙi koda sauraransa,

Kai tsaye sashen mahaifiyarta ta nufa wanda yaji kayan Alatu na sarauta,a kishingiɗe ta tarar da ita,

Kuyangun na ganinta suka fita dan basu guri 'dan yanzu Gimbiya Jamaimah zata maka wulaƙancin da zakaji baki ɗaya ka tsani kanka,

Zama tayi kusa da ita tana Mai ɗora kanta Akan cinyarta kana ta shagwabe fuska tace "Dada wai shi kam lamido bai gajiya da magana ɗaya?"

Ki samu lokaci fa ki faɗa masa nikam ina da miji a Nijeriya sannan ban Aura ba sai da na dirje,sannan nayi hakuri dada da har Yanzu banbi mijina ba abisa umarninki na 'in sake hakuri ,yakusa karewa fa Dada kifaɗa musu.

"Shafa yalwataccen gashinta mai santsin gaske Da Ya fito ta baya dadan nata ta fara tana Mai cewa"Jamaimah na faɗa miki Aurenki da yaran chan na Nigeria ba Aure bane ba,kaddararki itace ki maida Harith Lamiɗo wanda dole zakiyi,'dan haka gudun karmu sab'awa mahalicci muyi Aure kan Aure Ya kamata aje Nigeria a kamo yaran nan ko kuyi magana tunda akwai hanyoyi na zamani a kashe auren kizo ki bawa Harith Lamiɗo kiyi addua ke ki haifi diya kamar ki ta bawa wani Lamiɗo cikin Ahalimu bana san rigima surbajona,."

    Tashi Jamaimah tayi a cinyar Dadan nata ba tare da tace komai ba dan idan tayi magana rashin ɗa'ane zai fito sannan a rayuwarta duk da fitsara da izza irinta mulki jininta take bata so koda yayane tab'atawa mahaifiyarta ,amma 'fa itama bazata bari a b'ata mata ba ,

Tana mutuwar san Nameer wanda shine babban dalili da yasa ta Auresa sannan tayi imani da Allah koshi bai isa Ya raba kansa da ita ba sai dai Allah Ya rabasu ,saboda a yarda take jinta babu wani namiji da zai kalleta yace wai yau baya santa zai rabu da ita ,tabbas 'dan kuwa duk inda kake jin kyau Jamaimah takai,

Takanas ta miƙe tana Mai faɗin ma Dadan nata "na barki lafiya sarauniya babba",

Sanin maganar ce bata so a ja yasaka mahaifiyar tata rabuwa da ita tunda duk guje gujenta tasan sai ta Auri harith,

    Tunda ta fito 'dan nufa sashen ta take neman mai rabon shan wulaƙanci bata samu ba har ta shiga sashenta,

Zaune ta tarar da Harith a dining ɗinta yana Mai shafawa wata kuyangata ɗuwawu,

Ƙaramar dariya tayi lokacin da idanunta suka sauka Akan wanga al'amari,

Da sauri yarinyar ta matsa daga gefensa jikinta na ƙarma inda shikuma Ya lashe leb'ensa na ƙasa yana Mai kallan JAMAIMA da maita.


Ya kukaji character ɗin Jamaimah?

Shine mene ra'ayoyinku bisa rayuwarta?

Shin Mai kuke tunanin kan Fadil?

CHUCHUJAY

Tbc
[3/6, 5:11 PM] Chuchujay✍️: AHALINA

(Siblings of different father's)

Book two 'in Aure Uku series

        By

chuchujay

Episode 1⃣7⃣➡1⃣8⃣

  Tasowa Harith yayi yana Takowa ga Jamaima kamar babu abunda ta kamasa ya nayi,

Yana ɗaya daga cikin abunda Ya saka ta tsanesa ,a kullum idan zai ganta sai Ya nuna a fili jikinta yake so.

Kallan kuyangar dake ƙarma tayi tace "idan ma nace zan miki wani abu maine zan miki,kije kanki kike cuta saboda shi Yarima Harith ɗin da kike biyewa babu inda zai kaiki sai dai Ya baroki,sannan wani abu Mai daɗi da nake so ki sani,kinyi babbar sa'a da Ya zamana ba nawa bane kuma bazai zama nawa ba,'dan haka ki bace mun a guri sannan idan kika kuskura na sake ganinki sashe na sai na yagaki ,Alƙwarin gimbiya jamaima kenan,kinsan zanyi fiye da haka,"

Bace mun a guri stinky whore .

    Da gudu yarinyar ta fita har tana tuntube 'dan tagama sawa aranta ta mutu kawai a sanin halayyar jamaima ,amma ga mamakin ta sai taga akasin haka,

Daf da ita harith Ya matso ,bata matsa ba sannan batayi gizau ba ,jira kawai take taga ƙarshen iskancinsa ƙugunta Ya kamo ya jawota jikinsa yana Mai mata wani irin shafa a ƙugu,

Wani karamin dariya tayi tana mamakin ƙarfin guts ɗin Harith,tayi imani da Allah idan baiyyi wasa ba akan jikinta shi zata fara kashewa,

Kansa Ya sako dai dai saitin kunnenta yace "Ki daina wancan furucin na ni ba naki bane ba kuma Zan zamo naki ba,ƙaddarar mu a haɗe take gimbiyata,Nan da ƙwana uku ki shirya mayar dani lamiɗon ki domin hakan zai faru ko Kina so ko baki so,a yayin da nikuma nake kan murnar da bana tunanin da wani Lamiɗo da zai Kaini,saboda na farko Zan samu masarautar nan sannan na biyu Zan samu sarauniya Mai kyau da diri na jiki nayi yarda nake so da ita Akan gadon milkina,ina mutukar kwadayin jikin ki Gimbiya jamaima ,sannan kar ki damu 6 inch ne D*ck ɗina kinsan babban goro sai magogar ƙarfe., "

    Kafun yayi Aune tayi wani irin Hankaɗe sa ta ban mamaki da Kafarta inda Ya faɗi kasa wanwar,binsa tayi ta ɗora Kafarta kan kirjinsa ta taka da karfi kana tace "Abu na farko da nake so ka sani saboda yan iska irin ka koda naje china ba karatu kawai na tsaya ba sai da na samu Black belt a taekwondo ,idan na maka wani dukan sai  anyi tunanin hatsarin mota ne kayi,

Kana daukar kanka jarumi ba?

To kai da b'awan gyada a gurina baka da banbanci ,b'awan gyaɗa wanda zanyiwa b'ara ɗaya ya fashe ,gwanda da kasan cewa babban goro sai magogin ƙarfe domin jikina yafi karfin wannan abun dake gabanka da kake bin low life kuyangu dashi ,be guided Next time idan ka kuma tab'a mun jiki Zan saka takobi nasare dukkan hannun ka da Ya taba ni,

Stupid scumbag ,

Yawu ta tofa masa a fuskasa ta bar gurin,

Mikawa yayi yana binta da kallo yana tunanin hanyoyi da dama da zaibi Ya wulakantata ,tabbas da ace baya san zama sarkin garin da babu abunda Zai hanasa yi mata fyaɗe tuntuni 'dan shi jikinta yake so ba ita ba,

Amma yazama dole Ya ƙwantar da wuya muddin yana san cimma burinsa guda biyu,na samun jikinta da kuma zaman sarkin DILAH,."

Tashi yayi daga ƙasan da yake yabar sashen da Tunanin kala kala.

    Jamaima kuwa bayan ta shiga ɗakinta Gadonta ta hau ta ƙwanta ta jawo system ɗinta,

Maiyi mata tausace ta shigo,alamu tayi mata da ta tafi ,babu musu ta koma cikin girmamawa,

Page d'in Nameer na Instagram ta shiga,sababbin hotunan sa ta gani da Fadil,

Murmushi tayi tana Mai jin wani irin masifaffan sansa a cikin zuciyarta ,tayaya ma zata iya zama a raba ta da Nameer wanda take jinsa shine rayuwarta?

Tayaya?

Zumbur tayi ta miƙe da ta tuna maganar Harith na cewa nan da kwana uku zata zama tashi,

Dole tasan abunyi domin ta fahimci idan ta tsaya a gwiwowinta za'ayi mata shirme ne a masarautar,dan haka idea ɗin guduwa taje gurin Nameer shine kawai Ya faɗo mata,

Passport ɗinta ta nemo tare da ID cards ɗinta,

Take tayi Booking flight d'in da zai tashi Nigeria da yamma,

Aƙwatinta ƙarami ta haɗa da dukkan wani jewelry nata da kuɗaɗe masu yawa aje gefe tana tunanin ta yarda zata gudu,

Driver ɗinta ta kirawo,

Babu daɗewa yazo ,ƙaramun akwatinta ta bashi yayin da ta dauko kit din tabi bayan sa,

Kai tsaye Airport Ya kaita,suna zuwa ta wani haɗe rai ta kallesa tace "Zan kiraka anjima kazo ka ɗauke ni amma for now zaka iya tafiya,"Babu musu yace to cike da girmamawa,wani daɗi taji lokacin da Ya bar Airport d'in tana Mai jin wata iskar freedom na shigar ta ,atleast har ta bar kasar babu wanda zai san guduwa tayi,

Zama tayi dan jiran akirasu idan lokaci yayi,

A hankali ta rufe idanunta tana Mai fadin "Nameer gani  nan zuwa gareka."


*************************

    Tunda Hafsatu ta iso garin Adamawa taji hankalinta yayi wani irin ƙwanciya da bata iya misaltawa,bata tab'a zuwa garin ba amma a karo na farko ɗin nan taji baki daya komai nata Ya aminta da garin,

    Samun gidan innan mahaifinta bai mata wahala ba saboda tunda ta taso suke communicating da juna,

Ƙauna babu irin wadda Inna talle bata nunawa Hafsa ba ,ba sai ta faɗa ba Babanta yana ɗaya daga cikin abubuwa mafi soyuwa a gareta,abu ɗayane wanda ta kula Innar tata tana cikin shine hali irin na talauci sosai ,bata da kowa sai yaranta Muhammad shi ɗaya wanda yake sayar da rake a ƙofar gidan ,dukanin shekarun sa bazasu wuce Goma sha ɗaya ba,kamata yayi ace yana makaranta a wannan shekarun ba wai zama saida rake ba wanda ƙwataƙwata ribar tasa nawa Take,

Sawa tayi a ranta bazata bari ta zamar masu wani karin nauyi ba ,ko aiki ne zata nema tayi dan basu nata tallafin duk da kuwa itama tana da burin nata karatun ,bari tayi sai ta ɗan kwana biyu zata wa Innar tata maganar Aikin nata ,

Ille kuwa bayan ƙwanakinta Huɗu a gidan wata safiya bayan ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login