Showing 51001 words to 54000 words out of 68854 words
misimisi da ido kamar bazawarar jaba,to wallahi ki kiyayeni domin tsakanina dake yanzu muka fara cos wallahi sai na zamar miki damuwar da zata hanaki sukuni a gidan nan tunda kika zabi shigar mun hanci,
A tare suke kallan ta ,ƙaramar dariya Hafsa ta tsinci kanta dayi kafun tace "Allah sarki Adda ina ƙwana ,Kin tashi lafiya".
Cike da masifa tace "idan kika sake kirana Adda wallahi tallahi sai naci ubanki,Idan da ace ni Addarki ce bazaki taba Auran mijina har ki saka shi a ɗaki yayi miki ciki ba so cut the crap,"
Kallata da kyau Nameer yayi ko wanka batayi ba 'dan ga dukkan Alamu Ko gashinta da yake mess bata kula bata fito domin fitina ,murmushi Ya tsinci kansa dayi yayin da hafsa tace "Allah Ya huce zuciyarki Adda,Baby muje na haɗa maka favourite breakfast ɗinka ,gyara tsayuwarsa yayi yace "for real,OMG kunun gyaɗa da ƙosai?"
Ƙaɗa kai tayi tana Mai murmusawa tace "uhum kasan bazan manta abunda kafi so a rayuwarka ba Ko menene shi domin kaine first priority ɗina and you're the one that matter a komai Nawa."
Wani iri yake ji a ransa yana fatan dama ace hallayarta itace halayyar Jamaimah duk da kuwa acting ne amma Exactly kulawa da attention shi yake nema gurin matarsa ,alamu yayi mata da hannu yace "bismillah gimviyar zuciyar Nameer Habib,daga ke babu wata ,ke dai Allah yayi miki albarka,"
A tare suka taka har izuwa dining table ɗin da ta jera masa komai,cikin san Jamaimah taji tace"tunda na tashi ban koma bacci ba,bayan nayi addua na roƙa maka Allah Ya biya maka dukkan buƙatunka na Alheri then na fito domin biya maka buƙatarka ta cikinka cos nasan da yunwa zaka tashi"
Cikin fahimta taƙaitacciya na maganar tashinsa da yunwa Jamaimah ta kawo a ranta a yau ɗin ma bayan shigarsa ɗakinsa Ya dawo cikin dare Ya koma ɗakin Hafsa,abu guda ɗaya Ya saka ta rintsawa wanda shine rashin ganin shigarsa ɗakin hafsa wanda she was positive bai shiga ɗakin ba,amma sai take jin akasin haka a fahimtar da take so tayiwa hirar tasu,
Kanta ne Ya fara juyawa yayin da wani abu yazo dai dai saitin zuciyar ta yayi mata suka wanda kafun tayi Aune numfashinta Ya fara saƙewa ta fara kokawa dashi,take ganinta Ya ɗauke a yayin da ta fara ganin wani irin duhu Ya ziyarci ganinta,duk wani sunan Allah da ta sani ta kirasa inda a lokaci ɗaya kuma ta zube a ƙasa cikin fita hayyacinta,
Ƙarar faɗuwarta yayi dai dai da ɗagowarsu a tare,salati Nameer Ya saki Ya tashi da gudunsa yana Mai kiran sunan ta cikin tashin hankali ,haka zalika hafsa wadda taga abun kamar a mafarki,Allah yasa ba mutuwa tayi ba shine kawai abunda zuciyarta ke jadada mata domin kuwa muddin akace Jamaimah ta mutu bazata taba yafewa kanta ba ,
Cikin tashin hankali Nameer Ya ɗauketa yana Mai faɗin"shiga ɗakina kan bed side zaki ga car key ɗina ki dauko mu kaita asibiti,."
A kiɗime ta shiga ɗakin nasa ta ɗauko car key ɗin ,tana miƙa masa Ya nufi hanyar ɗakin ta ɗan ɗauko mata abunda zata rufe kanta Kana ta mara masa baya tana addua kala kala a ranta cos last abunda take So shine wani abu mara kyau Ya sameta,
Asibitin su suka nufa kai tsaye ,babu mami da Papa amma sanin su ɗin su wanene babu shiri aka shiga da ita domin bata taimakon gaggawa,
Safa da marwa Kawai Nameer keyi a gurin yana Addu'ar Allah Yasa babu abunda Ya sameta haka zalika Hafsa wadda tama rasa abunyi Domin hankali ta Ya tashi sosai wanda Take gani kamar ma itace silar komai domin da ace da suka kawo mata tayi abun duk yarda zasuyi da ita ta ƙi yarda,
Ganin yarda Nameer ke cikin tashin hankali ne Ya sata matsawa inda yake tace "hamma kayi hakuri ka zauna babu abunda zai sameta insha Allahu,"
Kallanta yayi da kyau kana yace"Allah yasa hafsa,Allah yasa bamuyi barna ba garin gyara ,im scared".
Ganin yarda rauninsa Ya bayyana Ta tabbatar da tabbas yana san matarsa sannan tayi alwashin taimaka mata ta duk wani bangare da ta gaza domin itama tana san mijinta cos san ya kaita inda ake a yanzu,ganin halin da yake ciki ya sata kira Nadiya ta faɗa mata halin da ake ciki,suna wannan tsaiwar na jiran tsammani likitan Ya fito,da mutuƙar kaguwa Nameer yace"mene damuwar Dr Na'im?"
Dafasa yayi yace"muje office muyi magana"
Babu musu Ya bisa yana Mai cewa "hafsa wait for me,ina zuwa"
Babu musu ta ce to kana ta samu guri ta zauna tana Addu'ar Allah yasa babu abunda Ya samu Jamaimah,
Tana wannan zaman taji an kira sunanta ,ɗaga kai tayi ta saukesu kan Abdallah wanda yake tare da Nadiya,wasu irin kwalla taji sun zubo mata a ido,kamar jira take a tambayeta Mai Ya faru tasa kuka,aikuwa ta fashe dashi tana Mai faɗin"Kawai 'fa da safen nan nayi ma hamma breakfast muna magana dan taji Shine ta faɗi gashi har yanzu ni bansan Mai yake damun ta ba,ina tsoro ace wani abune babba Ya zamana nice silar komai cos we provoked her ".
Durkusawa Nadiya tayi dai dai ita tace "kali nan Hafsa kar ma kisawa ranki wai kece kikayi causing komai ,duk abunda kikaga Ya faru ga ɗan Adam to ƙadararsa ce and you were only helping sannan komene akayi Ai domin ƙaruwarta ne,"
Kaɗa kai hafsa tayi,tana ƙokarin sake magana ta hango Nameer yana dosowa inda suke,da sauri hafsa ta je garesa tana Mai faɗin"Mai Ya faru Hamma Nameer ?"
Karamin murmushi yayi yace "babu wani abu serious kawai Blood pressure ɗinta yayi shooting cos ta sawa kanta fitina amma bayan nan babu wani serious abu,yanzu haka tana bacci ne and zata iya tashi any moment from now ,"Fitowar Nurse daga ɗakin da aka ƙwantar da ita ne Ya sakashi yin shiru cos yaga bakinta da magana,
Cike da fara'a tace "Ta tashi zaku iya zuwa dubata cos ban expecting ma alluran zai saketa da wuri haka ba,and tace tana san gani Nameer"
Godiya Nameer yayi mata kana Ya tashi yana Mai cewa "kuzo muje mana ,hafsa ke yakamata ma ace kin fara ganin Addan nan naki "
Ƴar dariya tasa tace "aikuwa dai kam amma yanzu tunda kalau take kaje dai nikam ina tsoro kar ta shakeni"
Dariya Nameer da Nadiya sukayi yayin da Abdallah Ya gagara ganin yarda a rana ɗaya sun sake da juna inaga ƙwana biyu,sati ɗaya ko wata?
Tabbas yana tsoran abunda zai je Ya dawo domin idan Ya rasa hafsa akwai matsala ,sannan a duk lokacin da Nameer Ya furta yana santa to tabbas bazai jayayya dashi ba domin kuwa babu abunda bazai iya sadaukarwa gareshi ba a rayuwa ko menene shi kuwa,to shi kuma menene tashi makomar,
Dafasa Nadiya tayi tace "Ya sayyadi tunanin menene kuma ake?"Dariya yayi yace rayuwa mana ,ni dai bari kiga ina da abunyi zan wuce idan kin shiga kice ina mata sannu,
Kallansa Ya maida kan hafsa yace "amaryar Hamma ni na wuce"Kafun tace wani abu ya juya yana Mai jin wani irin abu a zuciyarsa yana masa yawo,binsa da ido hafsa tayi tana Mai san gano wani abu a maganar sa ,domin ba sai anfaɗa mata ba akwai wani abu.
Kai tsaye Nameer na shiga ya nufa gareta ,tana kallansa wani hawaye Ya Ƙwace mata ,da saurinsa Ya zauna yana Mai kallanta yace "kukan kuma na menene ?"
Hannunta Ya kama yace "ban san me yasa ba kya jin magana ba Jamaimah,Simple magana dai nayi miki wadda zaki fahimta amma kika gagara har sai da kika saka na ɗauki step ɗin da bai yi miki daɗi ba ,yanzu kalli inda muke 'fa,Blood pressure ɗin 190 'fa,for What ,Kina san ki mutu ne? "
Cikin kuka tace "For you Nameer,saboda kai na kasan handling komai na kasa sanin inda zan saka tunanin na da hankali na da nutsuwa ta,na yarda da duk wani suna da zaka kirani dashi akan ka,na yarda im illiterate akan abunda Ya danganci Aure ,na yarda bani da tunani sannan bani da wani respect wanda za'ayi alfahari dani ,na yarda ni ba matar da zaka nunawa wani bace ,i lack in many ways,1 month Plus amma bani da wani amfani da zai nuna nayi worthing ka kirani matar ka ,amma still im hurt saboda cikin watan nan kaje ka Auri wata har da ciki,ba ƙorafi nake Anan ba amma abun Ya mun dafi sosai da na kasa handling ,a yau da najini a geji na mutuwa i got scared,naji tsoro ,da ace mutuwa nayi fa wanda nasan cikin ƙiftawar ido hakan zai faru a gama wannan moment ɗin Ya sani na fahimta,da na mutu na barma wata kai gwanda na rayu koda zan sharing naka ne ."
Sake damƙe hannunta yayi yace"kina nufin you're okay With hafsa matsayin matata "
Ajiyar zuciya tayi tace"ba wasa nake ba ,na aminci duk da kuwa abun da ciwo sosai da sosai,amma fa dole nima na samu gurina dake cikin zuciyarka wanda ka bata dukka ,cos i can't be a loser Akan ka,'duk wani abu da kake so matarka tayi nima zanyi,duk wani abu da hafsa ta maka ta kwace mun kai zanyi na ƙwato ka,sannan Family ɗinka daga yanzu suma Nawane ,baza ka sake samun wani gurbi na ƙorafi na akansu ba,AHALINKA nawa ne daga yanzu ,girman kai Da sarauta da kake ganina dashi a jinin AHALINA yake ,komai za'ayima mutum ko ina yaje za'a duƙa masa ayi masa fadanci,idan abu ja ne nace baƙine Ya zauna ,Ya kake gani girman kai bazai Kama mutum ba,amma kai na zaba da sarautata da mulkina da gata na,da izza ta, insha Allahu zan ƙokari na gyara halayyata da mu'amalata ,nayi maka Alƙwari . "
Narai Narai da ido tayi tace "im sorry about everything 'dan Allah ka yafe mun mijina sannan ka bani dama ,sannan zanje na bama Mami da Papa hakuri suma su yafe mun i was wrong"
Jin Kalmar hakurin nata yayi kamar mafarki domin idan bai manta ba tace bama ta iya bada haƙuri ba ,zaiyyi magana kenan muryar hafsa ta Katsesa inda take faɗin,Na taya ki murna Adda sannan ki gode Ma Allah wanda yaso Ya ɗoraki a hanyar dai dai saboda abune wanda yazo miki cikin sauki lokacin da kowa yake ɗaukar sa Mai wahala,
Kaɗa kai Nadiya tayi tana Mai murmusawa tace "gaskiya dai matar Hamma kin burgeni sannan a yau kamar yarda kike neman gurbinki cikin zuciyar hammana nima kin samu a nawa".
Kallansu Nameer yayi yace "ku zo nan,labe kuke mun ina magana da matata"
Dariya suka saka a tare yayin da suke ƙarasowa gurin Nadiya tace "mukam ba labe Mikewa masoyan nan ba ,kawai dai Allah yayi zamu tsinkayi hirar takuce a yayin da muke zuwa duba ta".
Shiru Jamaimah tayi batace komai ba domin kallan hafsa kawai a sunan matar mijinta yana bala'in bula mata zuciya sannan uwa uba ace tana Ma da cikinsa jikinta ita Ya riga saninsa kafun ita,ta fahimta idan ta cigaba da haukan kishinta da faɗanta hafsa zata ƙwace mata kowa a dangin Nameer bayan shi wanda tasan tabbas zata iya mutuwa baki ɗaya,'dan haka duk da bata san al'amarin haka nan zatayi hakuri ta gyara zamantakewarta wajen ganin ta bige hafsa a komai,gashi abunda ke ciza mata yarda take da wani irin sirrin kyau ɗin da Mai kallansa baya gajiya.
Ganin irin kallan da Take wa hafsa yasa cikin lokaci mara yawa ta gane Mai Ya kunsa,tabbas kallan kishine da rashin yarda zakayi,murmushi tayi tace "Adda jamaimah da farko dai hakuri zan fara baki saboda yau ganin halin da kika shiga ba karamin ɗimautani yayi ba sannan da ace wani abu Yau ya sameki har na koma ga ubangijina bazan daina jin abun na damuwa araina ba ,bazan taba mantawa ba ,ina so na sanar dake labari Mai daɗi da bakina ba da bakin wani ba "
Ni ɗin sojan haya ce !
Cikin confusion JAMAIMA tace "menene wannan kuma?"
Kalli ba sai kinyi confusing ɗina da wata hausa wadda ban fahimta ba,im ready to make peace amma fa sai kinyi alƙawarin bar mun Nameer na wata nima,har na samu ciki
A tare dukkansu suka saka dariya kafun Hafsa tace "Ai bama sai na baki ba ga hamma nan naki ne baki ɗaya ,ni ba matar sa bace Ya ɗaukeni ne domin wannan aikin"
"Bisa shawarata"
Nadiya ta faɗa tana Mai gyara zama kana ta ƙara da cewa,mun zauna ne munga hamma yana sanki amma halayyarki da dama bata da daɗi 'dan haka muka ƙirƙiri wannan wasan inda hafsa ta amince zatayi wanda Alhamdulillah cikin kwana ɗaya ba sai an ƙara wani ba an samu abunda ake so .
Kallan Nameer jamaimah tayi wanda Ya kaɗa mata kai alamun haka maganar yake,fashewa tayi da kuka tana Mai kai masa duka ,hannayenta duka biyu Ya riƙe yace "im sorry matar Nameer ayi mun afuwa, Kallan hafsa da Nadiya tayi tace "wannan ba wasa bane ,bana so gashi nan kun kusa kasheni"
Dariya suka saka inda Nadiya ke sake faɗin Ayi mana afuwa Addan mu sannan hafsa ki kwantar da Hankalinki babu wani abu da zai shiga tsakaninta da Hamma Nameer domin kuwa babban malamin gidan mu yariga kowa so she's off limit ,
Dariya Nameer yasa yace"'dan ƙaniya shine yake ta mun wani gani gani,ni dama nasan akwai wata a ƙasa ,"
Inyehh
Ƙasa hafsa tayi da kanta tana Mai jin kunya sosai ganin yarda suka koma zolayarta,
Hannunta jamaimah ta kama tace "koma ta yayane godiyar ke zanyiwa domin da ace ba dan wannan labarin da aka haɗa ba da bazan gane menene kuskurena ba na gyara,Allah Ya saka miki da alheri Ya barki da Abdallah har abada .
Ɗan sunkuyar da kai hafsa tayi ita dai batace komai ba amma a zuciya kuwa armee take faɗi yayin da kuma dukkan hankalinta Ya karkata gareshi domin kuwa a maganarsa ta Dazu akwai damuwa da magana a ciki wanda magana dashi ne kawai zaisaka ta gano bakin zaren.
Amma 'fa kun raina mun hankali sosai wallahi"jamaimah ta faɗa tana Mai binsu da ido tana tuna rainin wayan su,
A tare suka saka dariya ganin yarda yake binsu da kallo.
Kuyi mun afuwa kunjini shiru kwana biyu wallahi bana jin daɗi yanzu ma na ɗanji dai dai ne nace bari na tuna daku 'dan hakan na baku long chapter ,saura sati biyu na fara exams ina san gama muku kafin nan idan Allah Ya bani iko.
CHUCHUJAY ✍🏽
[3/6, 5:21 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different fathers)
Book two in Aure uku series
By
CHUCHUJAY ✍🏽
Episode 4⃣9⃣➡5⃣0⃣
Bayan barin hafsa Asibitin kai tsaye gidan su Nadiya suka wuce domin sama musu abincin da zata ci cos tana buƙatar kwana Biyu gaba a asibintin 'dan ta sake hutawa,
Kallanta Nadiya tayi tana tukasu tace "uhum ina saurarenki Hafsa Ya maganar ƙanina fa,ni dai ko Abdallah bai faɗamun ba ya faɗa sanki 'dan haka bari na fara Mana neman iri ,
Ƙasa da kai Hafsa tayi tace "kai Aunty nifa ba soyayya muke ba tukunna."
Dariya Nadiya tayi tace "na fahimta kenan dai za'ayi ne amma ba a fara ba,shikenan nayi shiru bari na bashi dama Ya dama da kansa.
Ita dai hafsa ƙasa tayi da kanta tana murmusawa tana Mai jin wata irin kunya kamar ƙasa ta buɗe ta shige,murmushi itama Nadiya tayi tana Mai Addu'ar Allah yasa Hafsa rabon Abdallah ce domin ta yaba da hankalinta mutuƙa.
Suna isa gida horn ɗaya tayi aka buɗe masu gate ,parking motar ta tayi tana Mai jiyo kamar hayaniya cikin gidan,bata kawo komai ba ta buɗe motar yayin da hafsa ma ta buɗe suka fara takawa a tare bisa jagorancin Nadiya,turus Nadiya tayi lokacin da ta cigaba da jin surutun na mutum ɗaya daga sashen baya Na baƙi yayin da gefe ɗaya kuma taji kukan Maminta tana faɗin"'dan Allah bilal kar ka fasa idan ka isa ka haifu,dama Ai imam na faɗa maka bani san magana dashi amma kayi masa jagora cikin gidan mu ,Kana tunanin ana wa ɗan iska hallaci ne".?
Kallan hafsa Nadiya tayi tace "kin buɗe kofar chan zata kaiki falo ,ki jirani anan ina zuwa babu daɗewa,"
Babu musu hafsa tace to yayin da itama kunnuwanta suka jiyo mata abunda na Nadiya suka jiyo amma tayi ƙokarin ɗauke jinta daga garesu domin daga gani magana ce babba ganin yarda idanun Nadiya suka kawo ruwa.
Cikin nutsuwa Nadiya ta fara takawa gurin tana ƙokarin saita kanta ,babu wani alert ko notice ta shiga ɗakin,zaune ta tarar da Mami gefenta kuma Papa Ya ɗora hannunsa kan kafaɗarta yayin da Mahaifinta Bilal ke tsaye wanda da alama tafiya zaiyyi amma bai daina surutai ba,a tare dukkaninsu suka Kalleta ,bilal ne yafara cewa "Alhamdulillah gama Nadiya ɗin nan Ai,ki kalli yarinyar nan fisabililahi yanayin shigar dake jikinta,kinyi duk ƙokarin da zakiyi umaimah kin mayar da yarinya Yar iska mai ciyar da kai da tallata jikinta ,sannan a yanzu Kina neman haɗata da tubbabe,wanda da banji bakin babana ba haka nan zaki cuceni, dama tana sana'ar modeling ina zata ɗauki hankalin musulmi?,dole sai arne to wallahi indai ina numfashi babu wanda Ya isa Ya Aurawa ɗiyata Kafuri wallahi,Dan haka ki shirya kamar yarda na faɗa miki sai kotu ta bani custody ɗinta , "
Tashi Papa yayi ransa na mutukar suya domin duk yarda yaso Ya danne fushin nasa Bilal na ƙokarin wajen ganin Ya turasa bango,cikin saita kansa yace "Alhaji Bilal kamar yarda na faɗa maka mun kai karshen zance zamu haɗu a court idan alƙalin sakarai ne Ya baka custody ɗin Nadiya "
Juyawa bilal yayi ga Nadiya yace "kar ki damu Nadiya nasan Kina cikin damuwa kuma zan cire ki daga ciki insha Allahu".
Danne duk wani abu dake zuciyarta tayi ,ta faɗa jikinsa tana Mai faɗin "Daddyyy,"
Petting bayanta Ya fara yace "karki damu Nadiya babu wanda Ya isa Ya Aura miki kafiri,"
Kaɗa kai tayi ,kafun Ya farga tasa hannunta a bayan gashinsa daga baya wanda Ya tasa taja gashin sa da ƙarfi wanda sai da Ya saka ƙaramar ƙara,
Murmushi tayi tace "da zafi kenan,abunda nake so kaji kenan,sannan wanene yace maka bana san kafirin da ka raɗa masa?"
Shi nake so fiye da kai sannan wannan da kake gani Shine mahaifina ita kuma kafi kowa sani itace mahaifiyata ,sannan zan zabesu sau dubu a kanka,kar ka manta ni