Showing 33001 words to 36000 words out of 68854 words
wanda Ko ni kaina ina tir amma a kullum ban gushe ba wajen nema masa sauki da rahmar ubangiji,sannan kaima na koya maka haka tun yarintarka sannan ina da yaƙinin kana masa Addu'ar neman rahma a kullum,"
Goge ƙwallar dake shirin zuba mata tayi tace "kafun Papanku mahaifinka shine mutum na farko da na Aura saboda soyayya inda shima na yarda kuma na yarda da soyayyarsa gareni gaskiya ce ,lokacin da na samu cikinka ,irin kulawa da Ya bani ba'a cewa komai duk da yana da yawan zafi ,tunda na haifeka kuma yake nuna maka soyayya Mai girma wadda a kullum idan Ya ɗaukeka sai tsoro Ya bayyana a idanunsa wanda bansan na menene ba tunda bani da idea ɗin abunda yake yi a boye,"
Tabbas samunka nayi imani da Allah ya haifarwa da Hafiz babbar nadama Akan abunda Ya tsunduma kansa wanda Danginsa suna da babbar gudunmawa wajen faɗawa halaka ,marayane wanda suka wofintar ,bashi da komai bashi da maiyyi masa sannan ko wacce hanyar samun sa ta toshe.
Katseta Abdallah yayi yana Mai kuka yace "amma mami Ai dan komai nasa Ya toshe Ai Allah baice ka bijirce masa ba ta hanyar aikata haram,Shin shi ba musulmi bane wanda yayi imani da ƙaddara Mai kyau da mara kyau".
Ƙaramun murmushi mami tayi tace "ita kanta wannan da kagani ƙaddararsa ce,ba wai ina karesa bane dan wani dalili,mutum duk rashin imaninsa bazai rasa wani hali Mai kyau ba ,sannan ina faɗa maka abunda baka sani ba,Nasan hakkin jinin mutum abune Mai girma amma mahaifinka kafun Ya koma ga ubangijinsa yayi nadama mafi girma ,yaji tsoran Allah wanda ada Baiji ba a lokacin da Ya tabbatar za'a kashesa ne sannan baya da aikin da zai kalli ubangijinsa bayan sallah da azumi,Abdallah amfaninka ma mahaifinka a yanzu shine ka kasance iya tsawan adadadin rayuwarka kana masa Addu'ar samun sauki,
Iya rayuwata da kai nayi ƙokari wajen ganin na maidaka mutumin kirki wanda yazamana kai a yanzu Malami ne Mai tunatar da mutane wanda babban mafarkine na mahaifinka,
Sannan kuɗin da na baka kaƙi tabawa na cikin dukiyar da Ya bar maka ,zan iya tsaya masa a ko ina kudin halak ne wanda Ya aje maka da gumin sa ,nasan kasan ta yarda zaka juyasa Ya amfani al'umma,haka na raini Abdallah na sannan ina alfahari dashi"
Kansa ya ɗora kan kafaɗarta yace "Mami Allah baya yafe hakkin wani."
Shafa kansa ta fara a hankali tace "nasani amma mucigaba da nema masa rahma bamusan ta inda Allah zai masa rahma ba,ka sani yawaitar adduarmu da aikin ladan da zamuyi danshi su biya masa hakkin rai sannan su rage Ya shiga Aljanna."
Tsintar kansa yayi da yin murmushi inda itama tayi ganin nasa murmushin kafun yace "Allah yasa mami ,bana san babana ya shiga wuta.
Kaɗa kai tayi tace insha Allahu baki ɗayanmu baza muga kalarta ba ma,
Shiru yayi yana Mai jin wai irin nutsuwa na ratsashi sannan Ya fara tuna irin ayyukan da yayi domin mahaifinsa,dan a garuruwan da Ya saka aka samu ruwa domin shi suna da yawa ,ga masallatai da yayi suma dan mahaifinsa sannan bazai goshe ba wajen cigaba da nema masa lada da sassauci har Ya koma ga ubangijinsa.
Tashi yayi yace "mami zanje na bawa masu buƙata amsar da suke san sani,ni bamai laifi bane babu wanda Ya isa yayi mun alƙalanci Akan abunda banda masaniya.
Kaɗa kai tayi tace "yanzu ne nake kallan Abdallah ɗin da na haifa a gabana."
Abu na technology kai tsaye study room ɗinsa Ya wuce domin yin live video .
Bayan ya gama wallafar da live vid ɗin inda Ya amsa dukkan wasu tambayoyi da suka kunshi abunda Ya gabata kana Ya sake jaddadawa mutane shi baici kuɗin jini ba haka zalika duk wani abun na mahaifinsa da suke jin kishin akai na arzikin da yake dashi ba gaskiya bane,
Sannan Ya sake sanarwa a ƙarshe akan shi muƙamin da ake san bashi baya da buƙata Ya godewa Allah indai yau zau fito Ya faɗi Allah wasu su rabauta Ya ishe sa.
Bayan gamawarsa Yana ɗago ido Ya sauke kan Mami wadda ta masa alamar jinjina da hannu kana ta ƙaraso ta zauna kan kujera tace wasu sun ɗauki addini siyasa irin mutanen da ake kira mutane masu ci da addini,bana so ko ɗaya ka kasance cikinsu,dan haka offer ɗinka na tafiya Macca yana nan har nan da shekara goma gaba ,bazan ce maka dole ba amma idan kaji zuciyarka ta aminta da zuwan just talk to me,sannan ka cire a ranka akan zaka tafi kabarmune ,bafa wai baka ganinmu bane har abada ,zaka zo gida muma zamuzo mu ganka,
Zanyi farinciki ace yau yarona yana macca a matsayin Malami ,abun Alfahari ne.
Yar Dariya yayi yace "Mami indai na samu mata a Nigeria insha Allahu ina Aurenta zan karbi offer din nan saboda bana san tafiya bani da iyali"
Murmushi tayi na jin daɗin maganar Auren da Ya fara tace "Allah ya kawo ta gari Abdallah,ina san nima na samu sirika ta gari kamar kowa."
Yasan maganar kan Hammansa ne dan haka yace "Mami shi yasa nace,Hamma na ma ki bashi dama sannan a bama matarsa dama duk da abunda sukayi bai kamata ba ,amma Allah ma yana yafe mana balle mu yan adam, "
Daga bakin kofar da shigowa Nadiya kenan tace"Dan Allah mami yarda Abdallah Ya faɗa ki bawa hamma dama da matarsa ."
Kallanta sukayi a tare mami tace "daga ina haka ke kuma."
Zama tayi tace "na dawo ɗaukar wani file ne sannan akwai labari mara daɗi domin Anisa tun kafin aje court ta mutu a police custody wanda saseen Ya tabbatar mun da cewa aj kashe ta saboda a ranar an kawo mace prison d'in itama za'a wuce da iya court amma sai tashi akayi da safe babu ita sai gawar Anisa wanda suka da yakinin an aikota ne ta kashe ta,Mafia ɗinsu i guess ,amma dai tana Chan ana bincke sannan naje na bada statement ɗina hamma ma haka saura Ku da papa ".
Cike da tausaya mata mami tace "to yanzu wa gari Ya waya fisabililahi ,.
"Allah Ya rufa asiri cewan Abdallah,kana ya ƙara da cewa yanzu mami maganar Hamma ɗinfa, "
Tashi tayi tace "zan basa dama amma sai yayi taming wannan mara tarbiyar matar tasa tasan darajar iyayensa da AHALINSA kafin Ya sake shigo mun gida,"
Har ta fara tafiya ta juyo tana Mai kallan Nadiya tace "ke kuma ki fito da miji success ɗin da kike nema yanzu kin samu saura Aure shine darajarki ."
Kafun Nadiya tace wani abu Mami ta fita,Ajiyar zuciya Nadiya tayi tana Mai murmusawa tace"Mami ta fara fa."
Dariya Abdallah yayi yace"Ai gaskiya Mami ke faɗa a fito da miji ayi Aure Adda na nasan Akwai manema ,ga Yaya fadil Nan dai yana fadanci."
Kafun tace wani abin Ya fita yana mata dariya .
CHUCHUJAY ✍🏽
[3/6, 5:17 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different fathers )
Book two in AURE UKU Series.
By
Chuchujay
Episode 3⃣3⃣➡3⃣4⃣
tsaya akan kafafunki?*
*Shin kingaji da tambayar komai se an Miki?
*Shin kunsan irin damar da muke yasarwa a harkar samun kudi ta yanar gizo 📱*
*Kunaso na nuna muku hanyar dazaku Rika samun 5k-10k da wayarku a kullum📱*
_*KU KASANCE DAMU TA WANNAN LINK👇 DAN NUNA MUKU YADDA ZAKUYI*_
https://chat.whatsapp.com/KQxACOQxahb9tDxzuyiKfI
Bayan fitar Nameer daga gida kai tsaye online help ta fara nema within inda take wanda cikin awanni Kaɗan za a haɗata dasu,
Ille kuwa ta sauka kan wani organisation wanda su aikinsu kenan raba yan aiki masu class wanda Ko wanne irin aiki kakeso za'ayi maka ,cikin kankanin lokaci ta samu contact da ogan masu aikin inda suna gama waya ta kira uber dan duk motocin da ke a gidan bata san inda zata fara neman mukullinsu ba,
Da location ta isa gurin,ƙaramin company ne wanda yake kamar ma'aikata inda anyisa ne domin masu aikin da cooks wanda Babu wanda ba professional ba a gurin,
Babu wani b'ata lokaci ta zab'i wata Arniya Mai ɗan gwabigwabi dan a ganinta zata fi jurar wahala,
Linda shine sunan yar aikin wadda suka tsadance akan duk wata zata na biyan ta dubu ɗari da hamsin ,komai na gidan ita zata nayi kama daga shara ,wanke wanke ,wanki,goga ,gyaran gida ,Girki ,tausa idan masu gida na buƙata san first salary na company ne dama haka tsarin yake,
Babu wani b'ata lokaci Jamaimah tayi masu wiring kuɗin ta ɗauko Linda,
Koda suka dawo gida yamma tayi ,tana faman Yatsine Yatsine ta kalli Linda da wani banzan kallo Kana tace"dafari dai ban dauko ki gidan nan bane dan ki zo Kina wa mijina karkaɗekarkaɗe ,na ɗaukoki ne domin kiyi min Aiki wanda shine zakiyi professionally idan kuma kika karya dokar aikinki tabbas zan kulleki inda baki tunani,"
Gyara tayuwa Linda tayi cikin ƙwarewa tace"bazaki samu matsala dani ba tunda a Service ɗinki babu bawa mijinki pleasure insha Allahu bazaki samu matsala dani ba,"
Da wani irin kallan banza JAMAIMA ta Kalleta kafin tace "ashe kamfanin naku har da karuwanci ake yi,to Nidai bashine ya kawoki gida na ba ,sannan inaso ido ma bana so ki haɗa da mijina muddin yana cikin gida nan sannan ɗakin da zaki zauna ki nemi BQ a gidanan dan nima ban sani ba kuma bana bukatar na sani ki zabi ɗaki ɗaya ciki ki saka ƙazamin jikinki ki rufe mana baki.
Amma yanzu kafun nan ina so ki wuce ki fara gyaro min ɗakin mijina,bayinsa yayi datti a wanke ,zan zo na baki bidding ki shifiɗa dan ban yarda da buɗe masa wardrobe ba ni zan wannan aikin duk da bana so.
Takawa Linda tayi a hankali zuwa inda aka umarceta da taje,Tsawar da aka daka mata itace ta dakatar da ita daga taka ƙafarta gaba.
Cikin fushi Nameer Ya tako cikin falan yana Mai faɗin,ashe ma ɗan iska kika mayar dani Jamaimah ban sani ba,wato yar aikin da nace baza'a kawo min gida ba itace saboda kin rainani kikaje kika ɗauko a inda ke kaɗai kika sani kika kawota gidana babu Ko kunya babu Tunani kike bata izini ta shigarmun ɗaki ta gyara sannan the guts har kike bata gurin zama a gurin da ba naki ba dan tsabar isa da takama ,ko Kina tunanin nan ɗin fadar kuce?
Cikin wata irin shagwab'e fuska ta tako garesa tana mai fadin"Haba Baby gaban wannan low life d'in kake faɗa mun magana hakan,?"Menene aibu idan na dauko wadda zata na taya mu aiki,kasan fa ni Allah Ya sani babu wani abu da na iya wanda Ya shafi zaman gida da wani kula da gida.
Haɗe ransa yayi sosai yace "Ai idan baki saka wannan ƙazamar ta fita mun a gida yanzu ba ,zan saka dake da ita ne nayi ta ƙwallo daku a compound d'in gidan nan har sai kawunan ku Ya farfashe,idan kuma kina ganin wasa nake dan Allah kar ta fita kigani ."
Jin furucin da yake Ya saka Linda kama hanyar fita tana fadin Sorry sir ,Ma sai munyi waya idan oga yayi sanyi zan dawo.
Kallanta Nameer yayi yace "dan Allah ki dawo gidan nan ki gani wallahi sai na kulleki ,sai na saka a chanza maki kamanni tukunna zakije prison na shiga gidana babu izinina,"
Jin inda maganar ta nufa Ya saka Linda kama hanya sif sif ta fita tana Mai jin Haushin Nameer da Ya kashe mata hanyar samu a ranar farkonta .
Mamaki ne Ya kamasa lokacin da Ya juyo yaga hawaye idanun jamaima,nuna kanta tayi da ɗan yatsa tace "nice kayiwa wanchan abun Ko Nameer ,saboda kawai Allah Ya dora mun soyayyarka shine kake amfani da ita kake wulakantani Ko?
What about sadaukarwata?
Menene gurbin sadaukarwar da nayi na komai nawa a rayuwa nazo gareka.
Cikin ɗumbin mamakin rainin wayau irin nata yace "'ina fatan kina sane da cewa lokacin da zakiyi wannan sadaukarwar baki ji ta bakina ba kika sadaukar da komai naki kika ƙwaso yan matan jikinki da rashin ɗa'arki kika zo har gidan iyayena kika nuna mana irin taki tashen Balagar,"
Karki manta ikirarine kike na ke matata ce kuma na amince na yarda haka zalika addini Ma Ya amince dan Hakka indai ina raye zaki cigaba da amsa sunan matata sannan dole ne Ki dafa mun naci ,kiyi mun biyyaya sannan kiyiwa iyayena sannan ba shawara nake baki ba umarni ne na dole saboda kin riga kin shiga nasa tarkon dan haka dolene kiyi abunda nake So.
Cikin kuka tace "Ai addini Ma cewa yayi ka ciyar dani "
Kaɗa kai yayi Yace Allahu Akbar malama Jamaimah ,ashe kin san wannan fanin,amma bana tunanin kin san cewa "ba dole sai na baki da dafaffe ba ,muddin na aje maki komai da kike buƙata hakkinki ne ki dafa nima ki bani naci idan kuma ba haka ba na ɗauko wadda zatana dafawa ta bani naci tunda dai ke ɗin yar sarkice da bata san wahala amma tana san soyayya,tawa kuwa ƙwalelanki wallahi muddin idan kikace a komai zaki zauna to zaki tashi a Zero,Dan haka yanzu za'a kawo maki food stuffs sai ki nutsu ko ta yanar gizo ne ki duba kiga mene kike bukata sai a kawo maki,sannan wallahi kika sake kawo mani wata ƙatuwar Arniya gida da zummar Aiki ban yafe ba,na dai san an sanar dake illar taka rashin yafiyar miji kayi abunda bayaso,babu abunda Ya shafeni idan yarinya ta shiga wuta
Yana kai ƙarshen maganarsa Ya wuce yana yan wakensa cikin naishaɗin ganin yarda ranta yayi ƙololuwa wajen b'aci,
Yana shigewa ɗakinsa ta duƙa a gurin ta fashe da wani irin kuka tana Mai jin zafi a ranta musamman da yayi mata magana kan kishiya da zaiyyi mata ,wannan itace kalma mafi girma da tafi muzanta mata a maganarsa kafun ta girkin,ta ina Ma zata fara,Allah Ya sani tana san Nameer wanda dalilin hakan Ya saka ta ɗauko yar aIkin a gurin na farko Dan ta gyara yaji daɗi amma sai gashi abun ma sake dagula mata yayi musamman da Ya kawo maganar kishiya a ciki.
Zama tayi ta sake fashewa da kuka tana Mai faɗin"Wallahi na rantse da Allah a gidan nan baka isa ka kawo wata ba a matsayin matarka muddi ina da rai,dan haka kamayi zagayenka ka gama wallahi ni da kai mutu karaba takalmin kaza,idan kuma kaga wasa nake dan Allah ka gwada yimun kishiya ka gani. "
Yana jinta a ɗakinsa tana surutanta yayi mata banza domin tabbas idan baiyyi da gaske ba akan ta yarda santa ke fizgarsa ɗinnan zata maidashi ƙatan sakarai.
Tun yana jiyo kukanta har tayi Mai isarta ta tashi ta shiga ɗakinta tana Mai faɗin Girkin kuma bazan yi ba sai kowa Ya ƙwana da yunwarsa,
Kaɗa kafaɗa yayi kamar tana kallansa yace"tafi nono fari yarinya."
Chuchujay ✍🏽
[3/6, 5:18 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different fathers )
Book two 'in Aure uku series
Episode 3⃣5⃣➡3⃣6⃣
GARABASA GARABASA BONANZA
2024 Shin kuna sane da ban bada garabasa ba?
To ku kwantar da hankalinku ga chuchu dai tazo maku da garabasar sabuwar shekara,
Shin kin fara kin fara karanta YAR AREWA labarin captain Jasmine Bilal shareef da captain Shuraym Sadauki,
Ta tashi da mafarkin zama pilot a yayinda shi da yake kan aikin yake kusheta Akan tayaya ɗiya mace Yar Arewa zata zama matuƙiyar jirgin sama?
Soyayyar da ta shiga tsakaninsu ba tsammani wadda take ƙokarin danne kiyayya .
Ko kuwa kin fara karanta littafin ABLA ADNAN ne labari na matashiyar budurwa wadda bata barin taƙwana ,budurwar da tazamarwa masu kuɗin gaske barazana ,
Shin baki fara karantashi ba ko kin fara kin tsaya saboda kuɗin Ya maki yawa?
Maza zo na maki sauki ki ji yarda soyayyar ABLA take farawa da PRINCE WASEEMUDDIN,kowa na kiranta karuwa harda shima Shin ita ɗin karuwarce?
Maza garzayo gareni ka samu amsa,
Normal price na YAR Arewa book 1&2 N700
ABLA ADNAN N700 complete amma a wanann lokaci na garabasa kuzo na baku ,Yar arewa 1&2 da ABLA adnan Akan farashin naira N600 dukka biyun ɗari shida kacal 🥱ragin N800?
Kamar yayi yawa amma a haka dai Ya zanyi na baku wannan garabasar ta sati,maza kar ayi baku.
0264267657
Gt bank
Amina jamil adam.
09058191213
Dm me
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
Kwana gidan Nameer ƙwana ne akayi na yunwa kar ma ace Jamaimah domin shi yaci abinci a waje ,
Kamar yarda Ya shaida mata za'a kawo kayan abinci haka akayi,komai saida aka kawo mata har kifi da naman da zata bukata amma taƙi soya koda ƙwai ne dan bama tasan ta inda zata fara ba,
Washe gari da safe tana tashi wanka ta ɗanɗasa ta shirya cikin ɗinkin doguwar riga Mai A shape na atampa,wani figeggen gyale ta jawo yayin da cikin ta ke mata faman ƙungi yunwa ,Atm card ɗinta ta take saving kudin da ita kanta bata san nawa bane ta ciro ta saka cikin Jakarta dan dole ta siyo junks,
Main Atm Card dinta ta kalla tasan a yanzu tabbas mahaifin ta yayi freezing mata Account ɗina cos duk lokacin da tayi wani rashin jin abunda yake mata kenan,
Sakashi tayi shima cikin jakar tace "kilan wannan karan naga akasin haka ,who knows ,"
Takalmi flat ta jawo ta saka tana Mai sake touching fuskarta kana ta ɗauki hanyar fita ,sai da taje tsakiyar falo ta kula dashi zaune hannunsa ɗauke da mug ɗin coffee yana sipping a hankali,
Turo baki tayi saboda fushin da take dashi,
Har ta juya zata cigaba da tafiyarta taji miryarsa yana faɗin"Ina zakije baki tambayeni ba?"
Ba tare da ta juyo ba tace"zan je neman abinci ne tunda Allah yasa ina da kuɗi ba mitsiyaciya ba"
Cigaba da tafiyarta tayi inda ta tsinci muryarsa yace "ina jin ba'a koya maki tambayar miji idan za'a fita ba a gidan ku ,amma nasan kinsa Menene hukuncin miji yace ma matarsa bai yafe ba ko?"
To idan kika fita gidannan bada izini na ba ban yafe miki ba,tunda ban rageki da komai ba
Kafun tace wani abu ya tashi Ya wuce kitchen dan samawa kansa abinda zaici,
Binsa tayi kamar zata fashe ta tsaya bakin kitchen ɗin tace"wai menene damuwarka ne Nameer ,Mai yasa kake san bamu wahala a zamantakewar Auren mu,ni ban tab'a jin inda akace wai dole mace sai tayi ma mijinta girki ba dole,beb we have money,dan me akayi guraren cin abinci?"
Anyisune domin mu masu kuɗi waɗanda basu san menene wahala ba,dan mene Allah Ya bamu sauƙi muce mu bama so bamu gode ba?
Murmushi yayi wanda Ya bayyana