Showing 30001 words to 33000 words out of 68854 words

Chapter 11 - AHALINA Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

272

kowa a duniya saboda kawai an haife ki gidan sarauta ko?

Ku gani kukeyi kowa ma banza ne saboda kuna da mulki ko?

Bari kiji da kyau ki kuma saurareni,abunda kikayiwa iyayena Yau yana daya daga cikin abunda zaisa bazan tab'a sakinki ba sannan bazaki tab'a samuna miji ba muddin ke wulakanci shine jigon rayuwarki,sannan zan nuna maki ke ba kowa bace face mutum wadda idan kika mutu kasar da za'a saka kaskantacen almajiri kema nan za'a sakaki ,kilanma nashi kabarin yafi naki idan yafiki aiki mai kyau domin abinda baki sani bs shine wulaƙanta dan adam kawai zai halaƙar dakai,.

Abu Mai muhimmanci kuma da nake san ki sani shine  a kasarki ne kike gimbiya amma a ƙasata a gida na a matsayin Matata ke bakowa bace sai wadda zata zauna tayi mun biyyaya tayi ibadar Aure,idan kina so fa kenan,amma duk ta inda kika bullo nima na iya bullawa ta gurin ni dake kuma shege Ya fasa,kina wannan wulƙancin kuma wallahi zanyi Aure har mata uku musha soyayya ke kuma ki sha wulaƙancinki ke kaɗai tunda shi kika zab'a 

    Yana kai ƙarshen zancen sa Ya juya dan shiga cikin gidan,binsa tayi da ido tana Mai jin zuciyarta na mata wani irin zafi musamman da Ya kawo mata maganar Aure,Cije leb'enta na ƙasa tayi tace "ina sanka Nameer sannan kai nawane ni kaɗai ,bakuma zaka chanza ni daga yarda nake ba ,haka nan zaka karb'eni domin wannan sarautar a jinina take babu wanda ya isa Ya cire mun wannan izzar ."

Da haka tabi bayansa da kayanta,

A falon dake ihun Naira ta tarar dashi tsaye hannunsa cikin aljihu ya juya mata baya wanda ya tabbatar mata da jiranta yake,

Aje akwatin tayi ta taka garesa ,cikin wani irin salo ta saka hannunta ta ƙugunsa ta rungumesa ta baya wanda sai da Ya saka shi ajiyar zuciya,idanunsa Ya rufe gam yana Mai jin jikinta kwance a nasa kamar dan shi akayi,

Lafar da kanta tayi a bayansa cikin wata irin shagwab'abbiyar murya tace"Baby ban iya faɗin im sorry ba da na fada maka koda zuciyarka zatayi sanyi,a jininmu yake faɗar Kalmar haƙuri tana bamu wahala,amma komene nayi maka bazaka iya barinsa Ya wuce ba idan ka tuna saboda kai na baro  komai nawa nazo gareka ,i love you very much Nameer sannan ni banyi tunanin zuwana gidanku zai jawo abunda Ya jawo ba da zan nemeka ne ko ta yayane na sanar da kai tunda address ɗinka  ma a company dinka na samu,kar ka saka na shiga wani Hali ,ka kalleni mana da kyau,nasan kaima kana jin abunda nake ji akanka gareni,cos ni macene da babu Mai ganina da tayin soyayya ya dauke ido,please Baby."

    Ƙaramun murmushi yayi Mai sauti da tagama maganarta ,tabbas yana san Jamaimah amma soyayya bata rufe masa ido ba Ya zauna yana kallan wanann rashin tarbiyar tata dan hatta a kalami bata da tarbiyya wanda dole Ya gyara mata zama tasan cewa mulki ba hauka bane,sannan sai Ya gasa masa aya cikin ruwan sanyin da bazata taba sanin lokacin da zata faɗa masa sorry ba mara iyaka,

Duk da yana jin kamar yayi ripping duk wani kaya da ke jikinta saboda irin rungumar da tayi masa amma ya danne lust dinsa Ya kama Hannayenta Ya b'anbare su daga jikinta Ya juyo yana kallanta yace "Gimbiya Jamaimah Rais,tashen ki yana burgeni,wato baki iya faɗar sorry ba sannan kike ikirarin Kina sona ,okay barka da zuwa rayuwar Nameer Babu gayyata , "

Ɗaki ɗaya Ya nuna mata cikin ɗakuna biyar d'in dake jere da juna yace "ga ɗaki Chan ki kai kayanki sannan kiyi amfani dashi,"

Cike da mamaki ta juyo ta kallesa tace"ni bazan zauna ni kaɗai ba a ɗaki idan Babu kai sannan naga gidan dagani sai kai ,ina yan aiki dan ni wallahi bazan iya aiki ba",

    Baice mata komai ba Ya juya dan shiga ɗakin dake nasa yace "idan bazaki iya aiki ba gimbiya JAMAIMA zaki iya komawa gidan ku ,amma ki sani da Aurena zakiyi ta yawo dan wanann karen nima yin kaina bazan sakeki ba.

Yana kai karshen maganarsa Ya shige ɗaki na huɗu dake daga Chan ƙarshen corridor Ya barta tsaye.

    Tab'e bakinta tayi taja kayanta tana mai faɗin"zaka biyu ne indai muna gida ɗaya".

    Bayan shigar Nameer shahararren ɗakinsa kan gadonsa Ya faɗa yana Mai duba lokaci ƙarfe Ɗaya da rabi na rana,wayarsa Ya ɗauko yayo ordering pizza dan bashi da komai na abinci gidan sannan pizza ɗin yake sha'awa amma yana fita zai siyo mata kayan abinci duk da kuwa yasan ba iya girkin tayi ba amma a hakan sai Ya gyara mata zama tasa ita ba kowa bace.

Wayarsace ta fara ruri,Nadiya ke kiransa, kira ɗaya Ya ɗaga,conference ne su uku,daga ɗayan bangaren Nadiya tace "Hamma are you okay?"

Ajiyar zuciya yayi yace "im Okay Nadiya and nasan yarda zanyi da Jamaimah Yes i was planning to talk about her da su mami idan komai Ya lafa cos ina santa ,we made mistake amma Aurenmu a ko ina Aure ne wanda ya ɗauro,amma yarda tazo wa su mami dole ne nayi da gaske wajen ganin na gyara mata zama."

Daga ɗayan bangaren Abdallah yace "Hamma ka dai kula kar ka shiga hakkin ta cos tun ranar da aka ɗaura maku Aure hakkinta ya hau kanka.

    Rufe idanunsa Yayi kamar yana gabansu yace"Insha Allahu bazan cutar da ita ba ,Ni dai alfarma ɗaya zakuyi mun wanda shine ku tayani wa mami magana da Papa dan Allah."

Assuring ɗinsa sukayi inda Abdallah Ya fara fita a wayan Akan zaije wani taro da aka gayyace,

Yar hira Kaɗan suka taba da Nadiya wadda duka akan lallashin junane kafun sukayi hanging Call ɗin .

    Pizza ɗinsa ce tazo ya fita ya shigo da ita,

A ƙaton dining table Ya zauna bayan Ya ɗauko holandia da cup,

Ya buɗe zai faraci ta fito a dakin nata cikin buguwar riga mara Nauyi baƙa wadda ta ɗauki farar fatarta sosai,

Saurin ɗauke idanunsa yayi akanta yana Mai gutsurar pizzan da Ya ɗauko,

Cikin wani irin Yanayin ta tako garesa tana Mai yarfe hannu tace"Baby pizza God abunda nake craving kenan."

Zama tayi tana Mai ɗauko cup d'in da Ya zuba hollandia ɗin tayi sipping,bai hana taba sanann shima bai hanata sha ba ,a haka suka fara cin abincin suna shan hollandia ɗin a cup ɗaya yana Kara masu,

Bayan sun gama Ya kalleta yace "anjima zan kawo Food stuffs zanki fara girki".

    Wata irin dariya ta saka har tana ƙwarewa tace"amma wasa kake ba?"

I mean hatta ruwan wankan kaimun ake a gidan mu ,ni ko ruwan zafi bansan Ya zan ɗaura ba.

Tashi yayi bayan ya goge bakinsa yace "Ai kin iya kunna data dan haka kiyi browsing,"

Wayarta dake gefenta Ya ɗauka yasa numbernsa yayi dialing tana shiga Ya kashe yana Mai aje mata yace "Ni zan fita ki kula mun da gida sannan bathroom ɗina yayi datti kije ki wanke mun,bana san na dawo nagansa haka nan."

    Kafun tace wani abu Ya fita a gidan,

Murmushi tayi bayan fitar sa tace "abu na technology ,kafun ka dawo na samo yar aikin da zata wanke maka bayin amma ni kam sai dai a soni a lallab'a ni. "


    CHUCHUJAY ✍🏽

*
[3/6, 5:17 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different fathers )
Book two 'in Aure uku series
       By chuchujay
Episode 3⃣1⃣➡3⃣2⃣.
   NASREE VENUE.
Cike Nasree Venue yake ,katafaren guri da aka ƙirkiresa saboda taro irin na manyan malamai da walima,
Taro ne ake a gurin na manyan malamai waɗanda kana kallansu kasan malamai ne na gaske da gaske ,
Duk cikin su malami ɗayane yaro wanda bazai wuce shekaru Talatin da tara ba da haihuwa,
Wani dattijan malami ne Ya tashi yana Mai gabatar wa ta buɗe seminar ɗin da suka taro domin ita,
Kiran babban baƙo aka fara wanda shine Abdallah amma bai ƙaraso ba.
    Tunda ya iso harabar gurin yake jinsa gashi nan dai amma hankalin sa ba kwance ba baki ɗaya,
Daliban da suka taru dan bawa ilimi a gefe Ya kalla bayan Shigarsa gurin bayan sa da masu basa tsaro,
Yana shiga Ya samu gurin da aka tanada dominsa ya zauna ,
Bayan wasu mintuna aka gayyacesa domin zuwa kan stage yayi jawabi,
Tafi guri Ya ɗauka inda shikuma ya taka yana Mai faɗaɗa fara'arsa ,
Bayan yayi sallama yafara jawabinsa cikin iyawa da sani,
Bayan wasu lokuta ya bada filin tambaya inda yake amsawa duk wani Mai tambaya cikin hikima da ilimi,
Daga chan baya guy d'in dake baya ne fuskarsa ɗauke da face mask Ya ɗaga hannu alamun zaiyyi tambaya inda aka basa dama yayi,
Daga zaune mic na hannunsa yace "akaramakallahu munajin labarai akanka wanda muke da yakinin gaskiya ne amma muna so ka sake sanar mana da gaskiyar akan maganar tunda mu nan kowa yanaso ne a ɗora ka a kujerar shugaban matasan malamai,"
Tambaya ta anan kuma itace"shin menene gaskiyar zama mahaifinka ɗan shan jini wanda Ya tara dukiya da kuɗin jinin mutanen da basuji ba basu gani ba,sannan mun tsinci labarin cewa ka gaji wani abu daga cikin dukiyarsa ta haram ,Shin menene gaskiyar Al'amarin?"
Shin ka zama babban malamine a yarda kake yanzu dan kawai ka boye tabon mahaifinka da baka san mutane su faɗa?
    Daga kusa dashi ɗayan yace "Haka maganar take dan Babu wanda bai sani ba dan hatta mahaifiyarsa ance kafun ta Auri mijinta na uku abu yayi ta yaɗuwa Akan suna zaman daduro ne ."
Daga nan sauran abokan da suka zo tare suka fara fadin "a faɗa mana gaskiyar Al'amari,"
Take jikin Abdallah Ya fara karkarwa dan a rayuwarsa ta duniya babu abunda bayaso kamar ace yau ana masa magana kan mahaifinsa ko Akan clip ɗin mahaifiyar sa da yayi yawo a baya wanda yake ƙanzan kurege ,
Haka nan yaji jikinsa Ya fara kyarma musamman da yaga kowa kallan sa yake yana jiran yaji ta bakinsa sannan ga yan jarida kowa na faman haska masa camera suna san ɗaukar zazzafan shayi ,wani irin jiri yake ɗibansa,cikin nutsuwa ba tare da yace komai ba Ya fita daga kan mambarin yana mai jin kamar zai faɗi,
Ɗaya daga cikin waɗanda suke basa tsaro ne yayi saurin zuwa Ya kamosa inda suka taimaka masa suka fitar dashi a gurin yayin da kowa ke ihu da ikirarin Ya dawo Ya fadi gaskiyar abinda ake faɗa ɗin yayin da shikuma yake jin muryoyi da yawa suna masa tsiwa a kunne ,
Yana zuwa bakin motarsa hannu Ya ɗagawa wanda Ya  kawosa inda Ya fahimta yaja baya,
Ya jima a motar shi kaɗai yana san kansa Ya dai daita kafun yaja motar yabar harabar gurin,
Shikadai yake bulayi a titi dan baya san zuwa gida a haka,so yake yayi kuka sannan yana so wani Ya ara masa kafaɗarsa yayi  ,bashi da kowa a wannan lokacin da Ya wuce yan uwansa biyu,Nameer da Nadiya waɗanda bazaiso takura masu da damuwarsa ba Ya ƙara masu ciwo Akan wanda yake damunsu,hakazalika iyayensu sunfi kowa shiga damuwa dan me zai ƙara masu da nashi,
    Duk cikin yan uwansa shine wanda Ya samu uba mafi muni wanda Ya barmasa tabo mafi muni,duk yarda yaso Ya nuna He's okay amma abun yaci tura He's not and yau Ya kara tabbatar da He's not,
Duk ƙokarin da yake wajen zama mutum nagari amma sai da aka samu waɗanda suka binciko bakin mumunan bayansa suka yab'a masa a wajen taro mafi muhimmanci gurinsa,a gurin taro da matasan dalibai ke dubansa a matsayin abun koyinsu manyan malamai suke ganinsa da daraja amma a yau magana ɗaya wadda take dole tana jikinsa ta zubar masa da dukkan wannan kimar ,
Yana wannan tunani tunannin ya juya kan sitiyarin motarsa ya nufi gidan Auntynsa shatuh wadda sau da dama takan basa shawara ga damuwarsa sannan yaji hankalinsa Ya kwanta da shawarar saboda iirin shakuwa da yayi da ita tun yarinta,sau tari idan komai yayi masa zafi gidanta yakanje yayi Clearing kansa na kwana biyu.
    Yana isa bakin gate ɗin yayi horn ,Mai gadin na lekowa yaga motarsa babu tambaya Ya buɗe masa,ganin bai kulasa ba Ya saka shi tabbatarwa da lallai yau Abdallah ba kalau ba.
Parking motarsa yayi yana Mai ajiyar zuciya kana ya fito yana Mai takunsa cikin nutsuwa kamar babu komai a cikin ransa amma ransa fal yake da baci da damuwa ,
Yana ƙokarin shiga sashen yaji yayi gware da mutum inda manjan dake riƙe a hannun Mai fitowar Ya zubar masa jikin farar shaddarsa ɗa tayi worthing kuɗi masu yawa,
Bama ta shaddar yake ba tukkuna, ɗaga kai yayi ransa a mutuƙar bace yana san ganin fuskar wanda Ya ƙara masa bacin rai cikin wanda yake ciki.
*
  GARABASA GARABASA BONANZA
    2024 Shin kuna sane da ban bada garabasa ba?
To ku kwantar da hankalinku ga chuchu dai tazo maku da garabasar sabuwar shekara,
Shin kin fara kin fara karanta YAR AREWA labarin captain Jasmine Bilal shareef da captain Shuraym Sadauki,
Ta tashi da mafarkin zama pilot a yayinda shi da yake kan aikin yake kusheta Akan tayaya ɗiya mace Yar Arewa zata zama matuƙiyar jirgin sama?
Soyayyar da ta shiga tsakaninsu ba tsammani wadda take ƙokarin danne kiyayya .
Ko kuwa kin fara karanta littafin ABLA ADNAN ne labari na matashiyar budurwa wadda bata barin taƙwana ,budurwar da tazamarwa masu kuɗin gaske barazana ,
Shin baki fara karantashi ba ko kin fara kin tsaya saboda kuɗin Ya maki yawa?
Maza zo na maki sauki ki ji yarda soyayyar ABLA take farawa da PRINCE WASEEMUDDIN,kowa na kiranta karuwa harda shima Shin ita ɗin karuwarce?
Maza garzayo gareni ka samu amsa,
Normal price na YAR Arewa book 1&2 N700
ABLA ADNAN N700 complete amma a wanann lokaci na garabasa kuzo na baku ,Yar arewa 1&2 da ABLA adnan Akan farashin naira N600 dukka biyun ɗari shida kacal 🥱ragin N800?
Kamar yayi yawa amma a haka dai Ya zanyi na baku wannan garabasar ta sati,maza kar ayi baku.
0264267657
Gt bank
Amina jamil adam.
09058191213
Dm me
*
    Wata irin karkarwa jikin HAFSA Ya fara ganin ta'asar da tayi,tana ƙokarin basa haƙuri bakinta Ya sarke sakamakon ganin mutumin da har ta mutu bata taba tunanin zata sakashi cikin ido ba,
Bakinta na rawa tace "Malam Abdallah?"
Cike da fushi yace"shine Kalmar haƙuri wadda aka koya maki a gidanku?"
Ke makauniyace ko kuma Hankalinki ne ba dai dai ba kina tafiya baki kalla gabanki saboda hauka ko menene?
Dame kuke so mutum yaji ne ,da abunda Ya damesa koda rashin nutsuwarku?
Shashanci banza kawai.
Wani dogon tsaki yaja bayan Ya kai karshen maganarsa yana Mai kallan rigarsa cike da takaici kafun Ya juya Ya koma motarsa,
Rigar Ya cire daga shi sai singlet Ya ninketa ya aje a gefe kana yayiwa motar key yabar harabar gidan kamar zai tashi sama.
    Wani irin zazzafan hawaye Hafsa taji yana mata zarya a kumatunta,tasan lafinta ne amma dan me zai kirata da mara hankali,mutumin da take mafarkin gani a rayuwarta ta bawa guri mafi girma a zuciyarta yau gamon su da zaginta Ya fara,
Shin mene Ma yazo yi gidan?
Jin muryar Aunty shatuh ne Ya saka tayi saurin goge hawayenta tana Mai tsugunnawa domin kwashe manjan da ya zube.
Tsaye Aunt shatuh tayi kanta tace "naji kamar muryar Abdallah ina sallah ina kuma yake?"
Kamar jira take a tambayeta wane Ya dake ki taji hawaye yana reto a idanunta kamar suna jira,ƙokarin gogewa ta fara amma Aunty shatuh ta riga da ta gani,
Kamota tayi tace "subhanallah hafsa mene Ya faru,"
Cikin karyayiyar zuciya tace "Aunty ban sani bane na zuba masa manja a jikinsa,Shine ransa ya baci. "
Da mamaki Aunty shatuh ta Kalleta tace"ran Abdallah ya baci?"
Abun da mamaki,amma dai ba wani abu yayi maki ko yace maki ba dai ko?
Kaɗai kai tayi tace "babu abunda yayi mun Aunty,"
Cikin nutsuwa ta Kalleta ,ta tabbatar wani abun yayi mata amma bata san faɗa dan haka tace "shikenan maza gyara gurin dan kansa zai dawo,"
Babu musu ta koma ciki dan gyara inda ta bata hankalinta kashe kan Abdallah tana tunanin menene alaƙarsa da masu gidan?
Tabbas ita ƙaddara a rubuce take babu yarda za'ayi ka chanza ta domin a rayuwarta ta gama yarda da babu yarda za'ayi ta ga Abdallah ko ta taka inda Ya taka,ashe a kaddararsu zasu haɗu a yanayin da bata taba tsammanin zasu haɗu ba domin a dukkan tunaninta Abdallah mutum ne da baya fushi ballantana har yakai ga faɗawa wani magana mara daɗi,
Amma Mai take tsammani ?
Shima d'in dan adam ne Mai zuciyar da idan aka daɗaɗa mata zata ji daɗi idan kuma aka b'ata mata zataji babu daɗi kamar ko wanne ɗan adam.
    Bangaren Abdallah kuwa tunda ya figi motarsa tunanin Hafsat da yanayin da fuskarta ta nuna mutuƙar tsoro ne kawai yake damunsa ,
Shi ba mutum bane Mai wulaƙanci amma muddin ransa ya b'aci kamar na yau zai faɗawa mutum maganar da zata damesa sai kuma shi daga baya Ya dawo yana dana sani,
Karamin tsaki yayi yana Mai shafa kansa cike da ɗumbin damuwa ,kai tsaye gida Ya wuce da zummar idan yaje yayi wanka zai koma gidan Aunty shatuh Ya bawa wanann baiwar Allah haƙuri idan Ya sameta ,idan kuma bai sameta ba Ya saka Aunty shatuh ta bata haƙuri a madadin sa,
Yana shiga gida sashen sa yayi kai tsaye hannunsa ɗauke de rigarsa da ta b'aci,
Bathroom Ya shige Ya sakarwa kana ruwan mai dumi ,bayan ya gama shirin sa cikin navy blue kaftan Ya fito domin komawa gidan Aunty shatuh ,yana ƙokarin fita ta kitchen muryar mami ta Katsesa ,
Sunansa ta kira ,juyowa yayi ya hangota a babban falo a zaune,
Shigowa yayi yana Mai buye damuwarsa sosai yace "Mami ina wuni ,"
Yar ƙaramar fara'a tayi tace zo nan zauna.
    Babu musu yazo Ya zauna a kujerar dake kusa da ita,
Hannunsa ta kamo tace "i saw everything on the live news,caressing hannunsa ta fara tace "ka yarda dani ko?"
Ƙaɗa mata kai yayi idanun sa na cikowa da Ƙwalla yace "mami na yarda dake fiye da yarda na yarda da kaina."
Kaɗa kai tayi tana Mai goge ƙwallar dake idanunsa yayin da take ƙokari wajen ganin ta boye tata karayar gabansa .
    Duk cikin yaranta babu wanda Take tausayawa irin Abdallah duk da kuwa shiɗin yarone Mai ƙwazo da sanin Ya kamata tun yarintarsa sannan uwa uba tausayi ,
Cikin sanyin murya tace "duk wata tambaya da wani zaiyyi maka Abdallah a kullum ka sa a ranka kuma ka sani Mamin ka ba mutuniyar banza bace ,sannan mahaifinka yayi zunubai mafi muni a duniya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login