Showing 36001 words to 39000 words out of 68854 words
ƙyawawan haƙoransa kafun Ya buɗe cikin crete ɗin kwai Ya ɗauki guda biyar Ya fasa cikin bowl Kana Ya dauko ledar sausage wanda yake a yayyanke Ya zuba a ciki Ya yanka albasansa yasa spices Ya fara whisking ,frying pan din da Ya zuba mata butter Ya juye kwan kana ya bisa da cheese yana soyuwa yana ƙarawa a haka har Ya bashi omelet ɗin da yake so,
Tana nan tsaye tana binsa da ido Ya gama abunda zaiyyi Ya juye a plate ɗaya yazo ta saitin ta zai wuce,
Ganin tayi bake bake a ƙofar yasashi kamo hannunta Ya maidata ciki Ya fito dan zuwa bawa cikinsa hakkinsa ,
Da mamaki ta bisa da kallo Kana ta mara masa baya tana Mai faɗin"Baby magana fa nake amma kayi kamar baka jini ba,sannan bana san Kana cemun baka yafe ba cos wata rana zan fita azo kuma ana wane yace wane Ya faɗa,please ka zauna muyi magana cos yanzu ma maganar da muke im mad hungry sannan naga omelet ɗinka na mutum guda na. "
Bai kula ta ba still Ya wuce Ya zauna kan dining table Ya fara yankan omlt ɗinsa yayi bismillah ya kai baki,
Zama tayi a kujera Mai kallansa amma Ko inda take bai kalla ba ballantana yace mata bismillah yayin da ita kuma zuciyarta ta gama ƙwaɗaituwa da abunda yake ci ga uwa uba yunwa na ƙwaƙwular mata ciki,
Wata irin ƙara cikin ta yayi na yunwa wadda taso saka shi dariya amma Ya maze sannan yaki kalanta,
Licking lips ɗinta na ƙasa tayi tace"Baby im hungry fa"
Bai kulata ba still har saida Ya tabbatar babu ko anini a plate ɗin kana Ya Kalleta yace "Baby yunwa kuma?"
Bai kamata ace Kina jin yunwa ba a cikin gidan nan bayan komai na abinci akwai,amma nafi tunanin Yunwar bata ciki ba da yawa ,ni kinga yau ina tashi da baƙar yunwa na tashi shi yasa kikaga babu shiri na nemawa kaina mafita.
Yana Mai kai ƙarshen maganarsa Ya tashi da plate ɗin ya kai kitchen Ya wanke Kana Ya wuce ɗakinsa dan shirin fita aiki,
Har Ya gama abunda zaiyyi Ya shirya tana zaune kan dining ɗin ranta a bace cikinta kuma na ihun chiroma,
Kamshinsa kawai Ya tabbatar mata Ya fito ,Takowa yayi inda take Ya ɗuka yayi kissing gefen kumatunta yace "to Baby ni zan wuce aiki and inaso kar ki manta abunda nace "muddin kika fita cikin gidan nan ban yafe miki ba Ko kaɗan idan kuma kin yarda kin shirya ƙarbar tsinuwar malaikun Allah to kije duk inda kike so,ni dai nace Allah ya isa,ki kula mun da kanki.
Yana kai aya Ya saka kai Ya wuce yana Mai juya Key ɗin motar sa,
Kukane Mai sauti Ya Ƙwace mata,ko giyar Wake tasha bazata fita ba saboda tasan girman Allah ya isar tasa ,amma wanne irin wulaƙanci ne Nameer ke san yi mata haka?
Kuka ta sake fashewa dashi saida tayi Mai isarta Kana ta jawo wayarta ,tama rasa uban da zatayi tunda dai ita kasar nan ba wasu frnds gareta ba,duk waɗanda suka gama makaranta tare ta ɗaukesu ne matsayin masu mata bauta da maula shi yasa koda aka gama makaranta babu wanda ta sake nema,dan kada kowa kuma Ya dameta Ko yasan ina take ta cire layinta na ƙasarsu ta karya ,koda ma tana dashi babu abunda zatayi da mutan cikin layin dan ta gama da cameroon kuma ,ba dai yanzu ba,dan da rayuwar da zataje tayi achan ta ƙwammace ta zauna da Nameer tunda tana mutuwar sansa kamar ranta yanayin life ɗinsa ne kawai damuwarta,
Data ɗinta ta kunna tayi searching yarda zata dafa indomie kana ta shiga kitchen ɗin da wayar a gefenta ta dafa indomie ɗin da ta chabe,
Tsaki tayi ta soya ƙwai kamar yarda taga yayi kana ta haɗa black tea shima according to recipe online,bata tunanin rayuwarta da gyara saboda mene aibun rayuwar hutu?
Itafa saboda mulki bata tab'a koda takawa kitchen ɗinta ba ballantana ta kai ga dafa wani abinci,
Kira ɗaya idan tayi za'a gama mata komai jiki na rawa,idan baiyyi mata ba ta saka a kulle mata mutum har Ya manta ma ta kullesa,amma wai yau itace tayi girki ma cikinta wanda duk ta hanyar dafawa ta kokone hannunta.
Fara cin indomie ɗin tayi ,wani rashin daɗi da Ya ziyarceta Ya saka tayi saurin firzarwa saboda tayi mata wani yum yum a baki,
Bata san abinci mara daɗi Ko yayane dan haka ta ƙi ci,shima ƙwan da ta fara ci yasha maggi a haka dai ita tutturasa badan yana mata daɗi ba saboda yunwa dai,
Bayan ta gama nan ta bar ƙwanikan ta koma kan kujera ta zauna tana tunanin yarda zata nema wa kanta mafita,
Tana wannan zaman taji ana knocking ,ɗan tsaki tayi cos itafa bata san wahala sannan takawa ta buɗe kofar gani take kamar taci baya ta kuma kaskantar da kanta,abune fa wanda bata taba ba,cigaba da latsa wayarta tayi yayinda knocking ɗin kuma yaƙi karewa ,
Nadiya dake tsaye tana faman bugu ce ta zagaya ta backyard ɗin gidan inda karamar ɗoor ɗin da zata sadaka da kitchen ta nufa tana Mai Murɗa handle d'in wanda cikin sa'a ya buɗe ,kai tsaye ta shiga tana tunanin ko lafiya cos tasan Jamaimah na gidan sannan adadin knocking ɗin da tayi ko me mutum yake yi zaiji sai dai idan ba lafiya ba wanda tunanin hakan Ya sakata shigowa ta ƙofar bayan,
Da mamaki ta kalli Jamaimah lokacin da tayi shigo Falon ,a ɗan razana Jamaimah ta Kalleta jin mutum babu zato babu tsammani kana tace"wallahi har kin ban tsoro nayi tunanin aljanace yarda kika shigo ɗin nan babu zato babu tsammani,dama kece ke ƙwanƙwasa kofa,"
Ƙaramun murmushi Nadiya tayi kana ta tako ta zauna kujerar dake kusa da ita tace "nice sannan nayi mamakin yarda na shigo na ganki zaune kamar bake ake ƙwanƙwasawa kofa ba,"
Gyara zama tayi tace "wallahi na tashi naje na buɗe ɗinne aiki,kinsan abunka da mutum bai saba ba"
Kaɗa kai Nadiya tayi tace"tabbas kuwa abunka da mutum bai saba ba dole ne ayi masa uziri,to Ya za'ayi an maki,
Tashi tayi tace nufi kan dining ɗin tayi ƙwashe komai ta kai kitchen kana ta zubar da indomie ɗin ta gyara kitchen kana ta ɗora sanwar jallof rice wanda dama shine babban abinda Ya kawota,lokacin da Nameer Ya kirata a waya sukayi magana tayi Alƙwarin taimakawa wajen koyawa Jamaimah hankali da sanin mutuncin ɗan adam ,
Kafun kace mene gidan Ya cika da kamshin party jallof ɗin da Nadiya ke dafawa,babu abunda Ya damu Jamaimah ko tace dan me zatazo mata gida ta kama girki ko makamancin haka illa ma daɗi da takeji yau zataci homemade Food dan ƙamshin abinci Ya fara dukar mata dukkan wata ƙofa dake cikin hancinta na shaƙar kamshi.
Abinci na cikin nuna ta dawo ta zauna Falon tace"Kina jin daɗi Addanmu matar hamma Nameer ,"
Murmushi Jamaimah tayi tace "bakiji yarda kika sake shiga raina ba dan wallahi a rayuwa zan iya bada komai akan Nameer domin soyyayar da nake masa ba ƙarya bace ba yin Allah ne kawai na yarda da hakan,zan iya sadaukar da komai nawa kan Nameer.
Crossing kafa Nadiya tayi tace"ba shakka,"
Cikin zaƙuwa Jamaimah tace "na ƙosa ki Gama girkin nan bakiji ƙamshin sa yarda yake saka yawona rushing ba".
Tashi Nadiya tayi cikin saurin tace kinga na ma manta ban gyara chicken ɗin da Nagani cikin fridge ba zan yi Pepper chicken da ita,
Cike da murmushi Jamaimah tace "yaji garlic please ,wallahi naji daɗin zuwanki,dan Allah ki dawo gidan nan"
Ba tare da Nadiya tace komai ba ta faɗa kitchen ɗin tana murmushi.
Bayan Nadiya ta gama komai na Abinci ta ɗauko warmer Mai kyau ta juye jallof rice ɗin Ya zama saura ƙanzo sannan shima chicken ɗin ta juye komai saura kaya miya da wuya ɗaya ,basket ta ɗauko ta juye sannan ta fito tana Mai faɗaɗa murmushinta ,gyalenta ta ɗauka da keyn motarta tace"to ni nayi gaba zanje na kaima hamma cos jiya matar sa da zata iya sadaukar da komai dominsa banda girman kanta da izzarta ta barsa da yunwa,shi yasa ƙanwarsa kuma Mai ƙaunarsa wadda zata kawo masa matar Aure nan kusa wadda zata na mashi girki da girmama yan uwansa ta zo domin yi masa girkin cikin gidansa matarsa tasan tana wasa babban ganganci domin idan tayi wasa ba ƙanwarsa ce zata shigo gobe ba matarsa ce.
Tana kai ƙarshen magana ta fara takun barin falan,har takai bakin ƙofa ta juyo tace"akwai ƙanzo da wuyan kaza na aje miki,kinsan ance ido guba sannan gashi kamshin Ya dakeki da yawa,iyawar kenan domin Mamina duk kuɗinmu sai da ta tabbatar nasan sirrin kitchen ,indai mijin da zan Aura yayi Aure to badan girki bane sai dai dan yana da ra'ayi,"
Bata jira mai JAMAIMA zata ce ba ta sa kai ta fice tana Mai barin ƙofar Falon a kulle wanda tasan dole Jamaimah ta taso ta kulle.
Wani irin abune ya tsayawa JAMAIMA a wuya bayan fitar Nadiya domin tunda take a rayuwata babu wanda Ya taba takata yayi mata wulaƙanci kaca kaca kamar Nadiya,
Tashi tayi ta nufi kofar Falon ta kulle kan ta shigo ciki tana Mai jin wasu hawaye na bin kuncinta ,ita Nadiya zata zo ta taka har cikin gidanta sannan dan ta mayar da ita mayya ta aje mata ƙanzo da wuyan kaza,ita gimbiya Jamaimah ,ɗiyar babban gidan sarauta da kowa ke shakka cikin ƙasarsu,
Ɗakinta ta faɗa tana Mai faɗin wallahi yau idan Nameer Ya dawo sai Ya faɗa mata dalilin da ya saka Nadiya tazo Ya zage ta cikin ruwan sanyi haka,sannan Ya faɗa mata ta ina ya gwadata a gadonsa yaga ta b
Kasa da zaiyyi mata kishiya wanda zancene dama na ƙanzan kurge dan wallahi babu wanda Ya isa,dama menene auren idan ba shi ba
**
Dan Allah kumun afuwa da rashin update da baku samu kullum nakoma makaranta inaso nayi adjusting amma insha Allah zan na maku ƙokari ,sai mun haɗu idan Allah Ya kaimu..
.
Chuchujay✍🏽
[3/6, 5:18 PM] Chuchujay✍️: AHALINA
(Siblings of different fathers)
Book two 'in Aure uku series.
By
Chuchujay✍🏽
GARABASA GARABASA BONANZA
2024 Shin kuna sane da ban bada garabasa ba?
To ku kwantar da hankalinku ga chuchu dai tazo maku da garabasar sabuwar shekara,
Shin kin fara kin fara karanta YAR AREWA labarin captain Jasmine Bilal shareef da captain Shuraym Sadauki,
Ta tashi da mafarkin zama pilot a yayinda shi da yake kan aikin yake kusheta Akan tayaya ɗiya mace Yar Arewa zata zama matuƙiyar jirgin sama?
Soyayyar da ta shiga tsakaninsu ba tsammani wadda take ƙokarin danne kiyayya .
Ko kuwa kin fara karanta littafin ABLA ADNAN ne labari na matashiyar budurwa wadda bata barin taƙwana ,budurwar da tazamarwa masu kuɗin gaske barazana ,
Shin baki fara karantashi ba ko kin fara kin tsaya saboda kuɗin Ya maki yawa?
Maza zo na maki sauki ki ji yarda soyayyar ABLA take farawa da PRINCE WASEEMUDDIN,kowa na kiranta karuwa harda shima Shin ita ɗin karuwarce?
Maza garzayo gareni ka samu amsa,
Normal price na YAR Arewa book 1&2 N700
ABLA ADNAN N700 complete amma a wanann lokaci na garabasa kuzo na baku ,Yar arewa 1&2 da ABLA adnan Akan farashin naira N600 dukka biyun ɗari shida kacal 🥱ragin N800?
Kamar yayi yawa amma a haka dai Ya zanyi na baku wannan garabasar ta sati,maza kar ayi baku.
0264267657
Gt bank
Amina jamil adam.
09058191213
Dm me
Episode 3⃣7⃣➡3⃣8⃣
kai tsaye bayan fitar Abdallah daga gidansu gidan Aunty shatuh ya nufa yana Mai Addu'ar Allah yasa yaga yarinyar da ya cima mutunci Ya bata hakuri,idan kuma bata nan Ya faɗawa Aunt ɗinsa ta bata hakuri ko ta bashi numbernta idan da hali,
Shi kaɗai yana saƙe zuci har Ya isa gidan Aunty shatuh,a babbar harabar gidan Ya hango Arifullah yana basket ball,
Da murmushinsa Ya isa musamman da ya kula bai gansa ba,
Aikuwa yana isa yana ƙokarin saka kwallon a raga Abdallah yayi tickling ɗinsa wanda Ya sakashi sakin ƙwallan yana Mai sakin ihu kafun Ya furta ,Hamma Abdallah,'dan koda bai ga fuskarsa ba yasan wanda yake masa irin wannann wasan,
Gabansa ya koma yace "big man yane".
Murmushi Abdallah yayi yana Mai mika masa hannu yace "an ƙwana biyu rabona da kai ,"Hannunsa Ya rike yan Mai fadin" yanzu Ai gani,hope Aunty na na gida,"
Kaɗa kai arif yayi yace "tana nan ita da Yaya hafsa cos shigowansu kenan daga kasuwa."
A tare suka fara takawa inda Abdallah ke tambayarsa "wacece kuma Aunty hafsa?"
Faɗaɗa murmushi Ariffullah yayi yace"sabuwar Help ɗin Mummy ce but she's so nice and amazing da bazan iya kiranta Hafsa ba,nasan kaima you will like her idan kaganta,she's so calm"
Ɗan shiru Abdallah yayi bai kuma cewa komai ba yana tunanin Wannan Hafsan wadda hankalinsa Yafi karkata akan ita yayiwa wulaƙanci Ranar.
Suna shiga kuwa Hafsa suka tarar a falo tana peeling bayan Apple domin Arifullah wanda baya ci da bayan,
Idanunsa kuwa na sauka Ya nufi gurin yana Mai dashe baki yace "kai Aunty hafsa Allah ubangiji Ya baki miji na gari Mai ƙaunarki,kamar kinsan Apple ɗin nan shi nake bukata yanzu haka,
Murmushi tayi inda zuciyarta ke wani irin lugude lokacin da ta dora idanunta kan Abdallah wanda ke kallanta kamar zai cinyeta,
Alamu da yagani akan she's not comfortable sannan shima yayi la'akari da Ya ƙure kallanta Ya saka yana Mai saurin ɗauke idanunsa a kanta zuciyarsa kuma ba tasbihi da istigfari,
Muryar Arifullah ce ta katsesa a yayin da yake faɗin"Hamma na manta kaima baka cin bayan Apple aikuwa kazo a sa'a Aunty hafsa ta peeling mun da yawa wanda bazan iya cinyewa ba."
Murmushi yayi yana Mai san basar da abinda ke masa lugude a zuciya Ya zauna kan kujera dake kusa dasu yayi bismillah Ya ɗauki ɗaya yana Mai fadin"aikuwa Arifullah Auntyn nan taka ta iya fere Apple 'dan banga koda bawo ɗaya ba,"
Kamar Arif na jira yana taunar Apple ɗin yace"Ai Hamma bama anan ba sai kaci abincinta ,wallahi kamar a 5star hotel 'dan ta iya girki sosai da sosai,kai duk wanda Ya Auri Aunty hafsa wallahi Ya more dama ni".
Ƙaniyar ka nace Arifullah ,Hafsan sa'arka ce da zaka ce dama kai ka Aureta dan tsaurin ido?
Wato 'dan tana wasa da kai ko?
Shine kake ganin kayi girman da zakace dama kai ko
Aunty shatuh ta faɗa a yayin da take takowa inda suke.
Dan murmushi Hafsa tayi tace "Aunty wasa ne kawai yake kin sani,kinsan Arif da tsokana,"
Kaɗa kai Arifullah yayi yace "Aunty hafsa ki rabu da mommy mana kike bata Amsa ,Ai fatane nayi ma kaina Mai kyau,idan na samu mata irinki 'fa ,mai kirki Mai tsafta ,Mai nutsuwa ga iya girki Ai baya ni,dama kinsanni akwai ci".
Ƙaramar dariya Hafsa tayi mara hayaniya kana ta tashi tana Mai fadin "Aunty Mai za'a ɗora ne,"
Allah Allah take ta faɗa mata ko zata bar gurin dan gujewa wani rashin mutuncin na Abdallah 'dan dalilin haka yasa ko gaidashi batayi ba bayan amsa masa sallama da tayi.
Fuskar Anty shatuh ɗauke da murmushi tace"ke kam Hafsa baki gajiya da Aiki yanzu 'fa muka dawo daga kasuwa".
Cikin ladabi tace 'Ai Aunty gara nayi na gama kinsan yau zani gida ,
Cikin tunawa tace "haka 'fa,gamu da babban baƙo ma wanda baya san zuwa gidan Auntynsa Mai ƙaunarsa,to sai ka faɗi mai kake san ci."
Ɗan Sosa ƙeyarsa yayi yace "Aunty na kenan,kome aka dafa zanci amma san samu na samu ɗanwake nan naki Mai daɗin gasken nan "
Murmushi tayi tace"kace dai ni kake so na shiga kitchen ɗinan 'dan bana tunanin hafsa ta iya irinsa".
Ɗan murmushi Hafsa tayi tace "A koya mun Aunty sai ki huta ni sai nayi nasan bazan gagara iyawa ba indai an faɗa mun Ya akeyi".
Aunty shatuh zatayi magana ,Abdallah yace 'Aunty a koya mata ɗin 'dan yanzu Arifullah Ya gama ƙoda girkin ta ,nima inasan naci naji wannan ƙodawar da yake gaskiya ce.
Arif dake gefe ne yace "Hamma nifa na faɗa maka ,wallahi indai girki ne Aunty hafsa kuma Ai sai godia".
Ita dai babu abunda take sai ƙananun murmushin maganar Arif yayin da saiti ɗaya na zuciyarta ke san ta bar gurin saboda Abdallah.
Kaɗa kai Aunty shatuh tayi tace "Hafsa wanann ɗanwaken kwabin normal ɗanwake ne amma 'fa shi kamar zakiyi jallof na shinkafa haka zaki tsaida ruwansa da maggi da kaya miya da komai sai ki saka ɗan waken,ruwan amma bada yawa ba sannan kar kuka tayi yawa ,"
Kafun Aunty shatuh ta ƙara wani jawabin Hafsa tace "Ai Aunty nama iya ".
Kiji Mai na faɗa maka ko Hamma?
Wallahi Aunty hafsa full option ce ,
Cewan Arif.
Murmushi Abdallah yayi yace "to kabari mana akaramakallahu tayi tukunna."
Hanyar kitchen ta nufa tana Mai jiyo muryar Aunty shatuh tana cewa"kisa ogu ɗinnan da hanta.
Har ta kure Abdallah yana kallanta,snapping masa fingers Aunty shatuh tayi tace "Ya dai".
Sosa kansa yayi yace "ina kika samu yarinya Mai nutsuwa Aunty."
Faɗaɗa fara'arta tayi tace"yar aiki na ce da na ɗauka kwanakin baya,yarinyar marainiyace bata da uwa ,yar jibia ce amma ni anan garin na dauke ta aiki daga gurin innarta,bata da matsala ina jin daɗin zama da ita sosai,"
Hala ma ba yau ka fara ganinta ba dan ranar da aka ce mun kazo na ganta tana kuka,
Cike da rashin jin dadi yace "har kuka tayi?"
Kallansa da kyau Aunty shatuh tayi tace "wani abun kayi mata kenan"
Tunawa da abunda ya fada mata kawai sai dai Ya saka shi babu daɗi sosai,
Sosa kansa yayi wanda Ya zamar masa jiki yace "wallahi Aunty na shigo gidan nan ne cikin tsananin damuwa da baccin rai ita kuma ta taka sahun barawo Ta watsa mun manja cikin rashin sani and i lose it na faɗa mata magana mara daɗi and nayi realizing What i did was wrong shiyasa nazo ban hakuri ,ban masan yar aikinki bace".
Dan murmushi Aunty shatuh tayi tace "Allah sarki nima dai nasan akwai abunda Ya faru tunda taƙi magana,amma Ai nasan Ya wuce ,kamar yarda na faɗa maka hafsa bata da damuwa,kilan ma ta manta"
A'a 'fa Mommy bata manta ba 'dan ina lura da yanayin zaman hamma anan Yake damunta sannan Ko gaidashi batayi ba,and i know abunda Ya fada mata ba ƙarami bane,
Arif Ya faɗa yana Mai folding hannusa.
Yar dariya Abdallah yayi yace "kumafa Arif kace wani abu,dole ne yau na bawa