Showing 39001 words to 42000 words out of 68854 words
Aunty hafsanka hakuri ta yafe mun"
A tare suka saka dariya baki ɗaya inda Arifullah Ya tashi yana Mai faɗin Ya manta da daddynsa Ya sa ya kai masa goga 'dan haka yayi saurin tashi 'dan kaiwa ɗin yayin da Aunty shatuh da Abdallah suka ɗan taba hira kafun itama tayi excusing kanta zata amsa waya,
Shiru Abdallah yayi yana kallan ƙofar kitchen ɗin zuciyarsa na faɗa masa yaje wata na gargadinsa,
Ture Mai gargaɗin nasa yayi Ya tunkari kofar 'dan yin magana da ita.
Ta nutsu sosai wajen jefa ɗan waken nata Ya shigo bakinsa da sallama ,
Da ɗan fargaba ta amsa 'dan sallamar tasa kawai taji sabida baya da ta juya masa ,kan Built in cabinet Ya zauna yana mai folding hannunsa yace "kinji ƙamshin girkin ki kuwa yarda yake ta dukan hancina a falo Auntynmu,".
Da rashin sakewa ta juyo ta kallesa tayi murmushi kana tace "wani abu kake so ".
Dan Sosa kansa yayi Kaɗan yace "ke nake so"
Kamar wadda aka doka guduma a tsakiyar kai haka taji sukar maganar 'dan haka cike da mamaki tace "mene kace?"
Licking lips ɗinsa na ƙasa yayi yace "cewa nayi so nake ki bani dama na baki haƙuri akan abunda na faɗa maki mara daɗi,ranar raina ne a bace amma ba halina bane batawa wani,'dan Allah kiyi hakuri ki yafe wa Abdallah ko zaiji daɗi.
Da inda inda tace "ni ba'abunda kamun ,n yafe maka sannan kayi hakuri manjan da na watsa maka cikin rashin sani ne wallahi bada gangan ba."
Accent ɗinta na magana ba ƙaramun burgesa yake ba,
Taba madaidaicin sajen Fuskarsa yayi yace "na yafe miki Hafsat and ni Ai a daɗi na ne na aje mistake ɗin Auntyn Arif da yaketa ƙodawa,kinga idan ina kallan rigar nan zan na tuna Auntynsa tayi mistake sau daya"
"Babu wanda baya mistake Ai a rayuwa,daukan mu yan adam ne ajizai"
Ta faɗa tana Mai zuba ganyen ogu cikin abincin a zuciyarta kuma tana Allah Allah yatashi Ya fita domin burgeta da yake kafin Ya zageta dawomata yake kamar an koro ruwa,
Wayarsa ya ciro ya miƙa mata,kallansa tayi alamun mene zatayi dashi,
Gira ɗaya ya ɗaga mata yace "ki ƙarba mana ki saka mun numbernki saboda muna gaisawa akai akai kinsan zumunci nada amfani sannan na ganki naji ina san kulla zumuci dake."
Murmushi ta tsinci kanta dayi kana ta ƙarbi wayan ta rubuta masa numbernta ta mika masa tace gashi.
Kina da saurayi?
Shine tambayar da yayi mata cikin rashin zato da tsammani.
Kaɗa kai tayi cike da kunya cos bata taba tunanin tambaya makamanciyar wannan zata shiga tsakaninsu ba.
Sai me za'ayi idan bata da saurayi Abdullahi,
A tare suka kalli kofar inda ya furta Adda Nadiya?
Cikin salo na tambaya,
Takowa ciki tayi tana mai boye dariyarta tace "ina sauraranka ,dama nan ka zo kenan ana ta neman layinka baya tafiya ,Grandpa Bulama ya kira meeting".
Kallan wayar tasa yayi yace "kuma wayata lafiya ƙalau fa saidai network".
Ganin hankalin Nadiya baya garesa yasa shi kallan Hafsa da ta ƙurawa ido,
Cikin yanayi na rashin sakewa hafsa tace "ina wuni"
da fara'a Nadiya ta amsa tana mai faɗin"yayi confessing soyayyarsa ko ni nayi masa?"
Saukowa Abdallah yayi daga kan cabinet ɗin ya kamo hannun Nadiya yace"Adda muje ya maganar zuwa Gidan Bulaman. "
Hafsa na jiyo dariyarsu ,haka nan ta tsinci kanta cikin wani yanayi da bazata iya fassarawa ba,sauke tukunyar abincinta da ya nuna tayi tana mai sake jadadawa kanta wasa ne sukeyi nasu amma babu yarda za'ayi Abdallah yaso yarinya kamar ta.
A cikin ƙaton kula ta juye abincin ta fita dashi ta aje kan dining,babu kowa a falon amma tana jiyo muryarsu daga falon Sama.
Komawa tayi kitchen ɗin ta ɗauko cocktail ɗin da Aunty shatuh ta haɗa jiya,ta dawo ta aje tayi arranging table ɗin kana ta koma kitchen ɗin ta gyara ta zuba nata abincin cikin yar ƙaramar roba dan kaima muhammadu,
Shirinta tagama fes kafun ta haura kamar barauniya ta sanar dasu abinci ya sauka,
Kamar kuwa tana jira suna amsawa ta sauko ta koma ɗakinta dake ƙasan..
********************************************
Kamar yarda Ahaji Bulama ya kira taron gaggawa lokacin da labarin Nameer ya iskesa haka suka bayyana domin amsa gagarumin kiran nasa,
Nameer ne na ƙarshen zuwa wanda baiyyi gigin zuwa da Jamaimah ba dan yasan mai zai jawowa kansa,
Dan idan batayi wasa ba babu shiri zata koma kamaru dan kakansa mutum ne mara daukar shashanci,
Kowa ya hallaci zaman wanda abun ya shafa ,
Koda Nameer ya gaida kowa Mami ƙin amsashi tayi dan ko da ta koresa yaci a ce a waya ya kirata ya sake bata hakuri koda bazata saurara ba Amma shiru kamar dama jira yake ta koresa.
Bayan addua na buɗe zaman kamar koda yaushe idan sunyi Grandpa ya fara magana kamar haka"Nameer shin maganar da naji daga bakin Maminka haka take ko kuwa zakayi mana karin bayani."
Kasa yayi da kansa cike da girmamawa yace "kuyi haƙuri grandpa ,kuskure ne na riga da nayisa wanda ban taba tsammanin zai dawo min ba a wannan lokacin da bamu daɗe da fita daga wata matsala ba,"
Amma dan Allah Amun hakuri bayanshi Babu abinda zan faɗa im guilty.
Shiru ɗakin yayi babu wanda yace komai kafun Grandpa ya katse shirun Yace"idan nace baka bamu kunya ba NAMEER na yaudareki domin ka bamu kunya mutuƙa,domin kayi wasa da irin ilimin addinin da muka baka har kake tunanin wai bakayi tsammanin kuskuren zai dawo maka ba,"Haba Nameer Aure fa Kayi dungurugum,mai kake Tunanin duniya zata faɗa akamu bayan kasan mu ɗin abun magana ne a duniya haba Nameer ,ka bani kunya mutuka.
Yaya Abubakar dake gefe ne yace "bai kyauta ba dan rashin kyautawa daddy amma dan Allah ayi masa hakuri sai afara tunanin ta hanyar da za'a gyara."
Wanne gyara kuma baya ya b'ata,Allah yasa bai santa ba tun tana waje ,dan wallahi ni ba laifinsa na ke gani ba na umaimah ne wannan laifin ,
Hajiya matar Alhji Bulama wadda tsanar umaimah da Ahalinta har a lokacin tana ranta ta fada tana mai ya mutsa baki.
Ayi hakuri Hajiya""Mami ta fada ranta a mutukar bace,
Nadiya dake jin haushin Hajiya sosai ce tace,idan bazaki gyara ba hajiya ba sai kin hura wutar ba,mene na maganar saninta a waje kuma.
Kamar hajiya Zata cinyeta ta hayyayƙo tace "naci ubanki wallahi sosai babu ƙaƙƙautawa ,ke idan ana magana ma zakiyi,nan ɗan zinar ubanki ma saida ya dawo maku amma kike nan zaki mun rashin kunya."
Cikin zaƙala Nadiya tace "dan ma dai kowa na da kashi a maƙale ."
Tsawar da Mami da Grandpa suka daka lokaci guda ne ya saka Nadiya hadiye abunda tayi niyar yi,
Cike da fushi mami tace "maza bata hakuri,ni zaki wulaƙanta kicima mahaifiyata mutunci har kina neman fada mata magana,to bari kiji wannan da kike gani zaune duk da ba ita tayi nakuda ta ba ni kallan uwa nake mata".
Dunƙule hannu Nadiya tayi tana mai tuno abubuwan da tayi masu suna yara ita da yaranta da matansu da jikokinta banda yaran uncle Abubakar dashi,tana sane sarai ta kasa manta wannan bangaren a yarintata,
Kiyi hakuri sannan nima ai bada rashin kunya nake mata magana ba ina maganane ta jika da kaka ,ai kakatace.
Cike da balai hajiya tace"ni ba kakar ki bace,kakar ki na chan kasa ni su sultana ne jikokina domin iskanci da ɗiban albarkar da kike mun su basu mun saboda sun san muhimmancina sun kuma san nice na haifi ubansu"
Dakatar da ita da Grandpa yayi ne ya saka Nadiya kin bata amsar da ta dace da ita ,
Kan Nameer ya koma yace"gareka Nameer yanzu dai maganar rabuwa da matarka bai taso ba tunda nasan tunda kukayi wanchan shakiyancin nasan da soyayya tsakaninku koda kuwa babu ita dole kacikaga ba da zama da ita,sannan naji ance yar kamaru ce sannann diyar sarki Rais ce dake dilah ,zamuje chan ayi maslaha tunda ko ina a cikin addini ita din matarkace kuma Aurenku ingantacce ne,hanyar da kukabice mara daɗi,dan haka kaje gida ku shirya."
Ƙasa Nameer ya kuma yi da kai yace "daddy ayi mun alfama dan Allah,da gaske ina san Jamaimah amma halayyarta ce bana so wanda a yanzu ina kan hanyar ganin ta gyara tukunna sai muje chan gurin iyayane nata,a yanzu kam duk wata halayya ta rashin girmama na gaba ta iya,so nake koda za'a je chan ɗin ya zamana ta koma a mace ta daban,wanda a wanann lokacinne Mami tace zata amsheta amma banda yanzu"
Grandpa zai nuna rashin lamuncewar sa papa ya shigar masa ya tayasa roƙo.
A haka aka yanke shawarar kamar yarda Nameer yaso,
Bayan tashinsu kai tsaye mami ta shige motarta dan bata san sauraran Nameer wanda ke da zuci zucin mata magana,
Nameer na ƙokarin shiga motarss muryar Ibrahim yaran Yaya usman yayan mami ya katsesa inda yake fadi"haji Nameer rayuwa,kai wai mene damuwarka daga mai mai cikin shege sai kuma Auren boye,"Wani
Banzan kallo Nameer ya basa domin dama tsakaninsa da Ib babu jituwa tun yarinta,
Motarsa ya bude ya fada ,yana kokarin mata key sultan ya shigo ɗayan seat ɗin yace "ɗan uwana muje mana ka aje ni a saint plaza wallahi motana ya lalace,"
wani kallan banza Nameer ya basa yace"idan na kaika wane zai daukoka?"
Sannan duk motocin gidanan baka da wadda zaka dauka ,ko zakace mun dukka motocinka uku ne suka lalace?
Murmushi sultan yayi yana mai shafa lafiyyane sajensa yace "nayi missing dinka ne kawai,kaga muje tare nasiya turare sai mu tab'a hirar yaushe gamo sai ka dawo dani gida,"
Dariya Nameer yasa dan ya kasa rike ta kana yaja motar yana mai fadi kaji haushi .
Yana jin muryar Ibi basu yayi gaba.
Murmushi Nadiya dake kallan duk abunda ya faru tayi ta taka inda yake tana mai kaɗa car key ɗinta tace "adai nemi sana'a."
Cike da balai yace"ki dai ji da kanki da abunda ke damunki ,shegiya figagiya,kina nan kina faman buɗe jiki da sunan sana'a mene amfanin taki sana'ar ba har gwanda kazauna babu ba,shegiya yar isa".
Dariya sultana dake bayansa ta saka tana mai fadin "Nadiya akwai vacancy ne a company dinki ,Laila matar Hamma ibi na san modeling"
A fasace ibrahim ya juya wanda tana ganinsa ta juya da gudu tana ƙwalawa hajiya kira.
Kaɗa kai Nadiya tayi a fili tace "bazaka taba chanzawa ba Ibi".
Da haka ta tashi motarta tana tunanin zuwa gidan Aunty shatuh domin magana akan Hafsa kan saban plan ɗinsu dan gane da jamaimah,
Message din Evans da ya shigo mata ne ya katse ta daga tukin da take wanda yake cewa
"Gani a Nigeria da mommy na akan maganar Aurenmu. "
Chuchujay ✍🏽
https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
[3/6, 5:19 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
AHALINA
(Siblings of different fathers)
Book 2 in Aure uki series
By chuchujay
Episode 3⃣9⃣➡4⃣0⃣
Bayan isar Nameer ya aje Sultan a gida kai tsaye gida ya nufa dan ya gaji so yake kawai ya huta dan haka ya barwa Fadil meeting ɗin da zasuyi yaje a maimakon sa,
Key yasa ya buɗe gidan ya shiga , a falo ya tarar da Jamaimah tana cin fried rice &chicken da coke a gefenta tana wani yumm kamar an bata duniya,sallama yayi bata amsa ba dan haka ya wuce
Ganin ya wuce ta ɗinne ya sakata ɗan daga murya tace "tunda ance idan na fita Allah ya isa kaga ai mai kuɗi da kuɗinsa sai abunda yayi niyyah idan kuma yin order tazo har gida itama haramun ne sai a faɗa mun naji ya sheik".
Tsintar kansa yayi da murmusawa ,yasani dama za'azo nan da zata fara online order shiyasa koda Nadiya ta faɗa masa plan ɗinta ya amince babu bata lokaci,
Yana ƙokarin kulle ƙofarsa ta sako ƙafa a bakin kofar,matsawa yayi da ya fahimci jidali take ji dashi.
Shiigowa tayI ciki tace "malam magana nake maka tun jiya amma ka kasa bani amsa,"mene ya saka Nadiya tazo tayi abunda tayi mun jiya,"
Walk in closet ɗinsa ya faɗa yana ignoring ɗinta,
Binsa tayi tana cewa "wai Nameer nikam mai ka ɗauki Aure ne ?"
Why are you treating me this way for crying out loud .
ba tare da ya juyoba ya fara cire rigarsa yace yarda kika ɗauki Aure haka na Ɗaukesa jamaimah,sannan duk yarda kika shirya tafiyar da rayuwar Auren mu haka zan tafiyar dake na tayaki ta yarda kike so,
Takawa tayi garesa a hankali ta saka hannunta tayi hugging ɗinsa ta baya,baki ɗaya yaji wani tunani nasa ya tsaya,
Lafar da kanta tayi a bayan nasa tace"Baby dan Allah mu daina azabtar da rayuwarmu, lets live a peaceful life style ,im hurting bana jin daɗin abunda ke faruwa tsakani na da kai,har wani na shiga,sannan Bazan boye maka ba banji dadin abunda Nadiya tazo tayi mun ba wanda na tabbata da sanenka domin idan babu ba yarda za'ayi tazo tayi girki a cikin gidana domin kai sannan wai tace ta aje mun ƙanzo da wuya,imagine babe,sannan har tana faɗa mun zakayi Aure which idan kayi Aure zan iya rasa rayuwata saboda tunanin haɗaka da wata ƴa mace kawai yana sani shiga tashin hankali,"
Cikin shesheƙar kuka tace"is it a crime dan ban iya giriki ba?
Mata nawa ne basu iya girki ba kuma suke zaune cikin gidajensu da mazajensu cikin soyayya da ƙauna,
Wallahi Nameer ina Mutuwar sanka ,ina maka sanda bana yiwa kaina shi why wont you give us a chance?"
A hankali yake jin kukan nata yana ratsa dukkan wani sashe na jikinsa,jikinsa da ta ƙwanta kuma ji yake kamar ana hura masa wuta a dukkanin jikinsa,tabbas yana san jamaima shima ya sani kuma ya yarda amma bazai iya dealing da yarda take tafiyar da rayuwarta cikin rashin biyayya ba da sanin ya kamata ga ɗan adam,
A barshi ace ya amince da rashin iya girkinta ,zasu dawama ne a cin abinci a waje domin bama ta da niyar koya ,ko kuwa zasu ƙare a yan aikine,
Shin yan aiki ne zasu na kula da ɗakinsa su gyara masa har abada?
A tunaninsa ɗakinsa sirrinsa ne wanda matarsa kawai ya hallartarwa,ko kuwa zasu zauna a haka ne bata ganin mutunci da girman danginsa duk a sunan ita ɗiyar sarautace shin ita sarautar hauka ce?
Kukan nata bai daina sauti ba ,ajiyar zuciya yayi ya juyota tana kallansa ya kamo hannunta a hankali ya zaunar da ita kan couch din dake cikin gurin ya ɗuka gabanta ,hannunsa yasa a hankali yana mai share yar ƙwallar dake idanun ta yace"menene na kukan kuma?"
Duk fa abunnan bai kai ga nayin kuka ba,look jamaima i want a romantic simple life with my wife,ni da kika kalleni a tsari na babu Auren mace biyu saboda babu yarda za'ayi na haɗa sansu guri daya nayi adalci saboda nasan kaina,so i choose you duk da Aurenmu was nothing close to okay amma a haka nake san ɗaukan responsibility ɗina na kula da dukka hakkinki da Allah ya dora mun amma baki san bani dama domin kuwa a hadurwaki ta farko da iyayena kin basu expression a kanki mara dadi wanda yayi leading da ni kaina aka koreni daga gida ke shaida ce,
Im a family man jamaimah AHALINA suna gaba min da komai sannan a shirye nake na bata da duk wani wanda zai kawo mun matsala cikinsu,
Ni dake ba soyayya mukayi a baya ba mun tsinci kanmu ne kawai a cikin san juna bayan wannan abun na Aure ya faru.
Cikin shagwaba ta katsesa tace "sai dai idan kai amma nikam i loved you since day one,idan ba haka ba taya zan involving kaina a komai so don't speak for me".
Murmushi yayi ganin yarda ta wani shagawabe fuska yace "to naji i wont speak for you, amma ki sani ina sanki sosai amma kina san bani matsala wajen nuna miki ina sanki,so na kike yi amma baki san ni wanene ba,AHALINA nada tarihi da history wanda bazaki taba tsammani ba,na tabbata a maganar da nake baki san ina da kanne yan uku a America ba sanann baki san cewa ni dasu da Nadiya da Abdallah dukkan mu Siblings ne daga different fathers amma same mother,amma still we fight for each other and love each other ,i love them da dukkan rayuwata,
Sannan aje kan Mami na ,itace komai Nawa,ita ta bani uba a lokacin da nake mutukar bukatar daya wanda shine Papa mijinta a yanzu,ya bamu rayuwa mai kyau sannan yabada babbar gudunmawa wajen ganin mun zama abunda muka zama yanzu ,badan kuɗi ba saboda muna dashi,dangin mahifiyarmu kuɗi ne haka zalika mahaifiyarmu kuɗice amma ya bamu gudunmawar da kuɗi bazasu bamu ba,
Ko kinsan mahaifina dana Nadiya suna nan a raye?
Amma mene amfanin rayuwarsu garemu bayan munada wanda yafiso sau dubu wanda a koda yaushe zai zabemu sau babu iyaka ya bamu gudunmawa rayuwa kamar yarda yake kan bamu,
Tayaya kike tunanin zan zauna na kalle ki kina disrespecting ɗinsu?
Abun da kikayi ranar was awful and very bad .
I can help you wejen ganin kin iya duk wani abu da baki iya ba amma fa sai kin taimakeni tukkuna kin taimaki kanki zan iya taimaka miki ,muyi rayuwa mai kyau da inganci abun sha'awa ga kowa.
Narai narai haka idanunta ke kallan nasa kana ta sake damƙe hannunsa tace "da gaske nake bazan iya rayuwa babu kai ba and tunanin wata mace tare da kai yana sani cikin mutuƙar tashin hankali domin duk ranar da ka kawo wata cikin gidan nan matsayin matarka to zan mutu ne,mai zai saka bazamuyi rayuwarmu daga ni sai kai,i left everything for you cant you do the same for me?
Bazaka iya mun hakan ba please honey,i will try and adjust naga na fara yi maka girki koda ba daɗi a haka har ya fara yin daɗi,rayuwata tunda aka haifeni bayan iyayena babu wanda nake ma kallan sama cos ina kallansa matsayin ƙasƙanci a haka aka raine ni wanda bana tunanin zan iya chanzawa zuwa wata daban,abu daya na sani shine ina mutuƙar maka soyayyar da zan iya saudaukar da kaina domin kai amma bazan iya chanza kaina ba ,kazo muyi rayuwarmu mu biyu please".
Bai san lokacin da wata dariya ta ƙwace masa ba ,sai da yayi mai isarsa ya dago yaga tana kallansa cike da confusion ,baki iya wa kowa kallan sama ba ,ni ma kenan bazaki taba iya mun kallan sama dake ba right?
Snipping