Showing 3001 words to 6000 words out of 68854 words

Chapter 2 - AHALINA Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

277

yaji ƙiyayyarsa ta tsananta a zuciyarsa ,shi yasa gudun nuna masa ƙiyayya Mai yawa yasakashi limiting ganinsa ,

Kallan Papa yayi da gajiyayyun idanunsa yace"Papa wallahi wannan yarinyar tun jiya nake faɗawa Mami ban santa ba ban tab'a ganinta ba,na yarda Akwai mistakes da dama da nayi cikin sani da rashin sani,amma nayi maku alƙwari fyaɗe baya cikinsa ,wallahi ban san ta ba ban kuma taba yiwa wata ɗiya mace fyaɗe ba,cikin sani da kuma rashin sa,Allah kaɗai yasan menene manufarta da kuma abinda ke tafe da ita .

    Shiru Papa yayi na wani lokaci kafin yace "Ai abun ma yazo da sauƙi cos yanzu maganace ta technology,a zamanin baya mahaifiya ita kaɗa ke da say akan ɗan da ta haifa na wanene amma banda yanzu ,'dan haka ta shirya anjima zamuje asibiti tare Ai DNA test."

    Tafa hannu Nadiya tayi tace "Papa you're always the best ,kaganmu nan dukkan mu babu wanda yayi tunanin yin wani DNA har DR Mami,"

Dariya suka saka baki ɗayansu banda Mami wadda jikinta ke bata wani irin baƙwan yanayi,ji take a jikinta koda anyi DNA ɗin result d'in zai fito akan yaran ɗan Nameer ne .

    Kamar yarda suka yanke shawara Bayan gama cin Abincin Anisa da Mami da Papa da Nameer suka nufi asibitin 'dan daukar jinin yaro a gwada,

Bayan fitarsu Nadiya ta koma ɗakinta cos boyayyen masoyinta a yau yake san bayyana mata kansa wanda take Zuci zucin ganinsa tana addu'an Allah yasa dream Man ɗinta ne cos duk da dumbin masoyanta hankalinta yakasa ƙwanciya koda da mutum ɗayane.

    Gyara fuskarta ta sakeyi kana ta shirya cikin highwaist silk maroon wando da off White long sleeve,

Cotton maroon veil ta yafa kana ta ɗora kimono a sama ,talakmin Dolce ta saka flat Mai kyau Fari kana ta ɗauki ƙaramar purse ɗinta da Car key ɗinta ta fita a ɗakin tana mai jin farin cikin cos abu biyu zasu faru,na ɗaya zata gana da EH ,na biyu kuma Anisa zata fita a rayuwarsu da so Call babyn ta,

    Tana ƙokarin fita ta jiyo muryar Abdallah yana Mai faɗin"Addy a haka za'a fita?"

Kallan Kanta tayi for a moment kana tace "mene abun banza a shiga ta?

Fauza check me out,"

Fauza dake zaune tana Mai kallanta ne tayi mata alamu da hannu tace"My fav super model Babu,Kin gama haɗewa sannan kin gama kashe ni,ke Mai kyauce wallahi, you look so innalillahi wainna ilaihir rajiun..

Jifarta da Abdallah yayi ne yasaka ta rugawa da gudu tana dariya,"

Kusa dashi Nadiya ta koma ta zauna tace "dear Malam Abdallah na faɗa maka Im pure and clean,tun farko kake ƙin career ta amma trust me im not doing wani abu da yake against addinina ,namaka Alƙwari ,sannan Kasani shi hijab a zuciya yake,

Tashi tayi tana Mai sake kallan kanta tace "kalleni 'fa Ba shigan banza nayi ba,wandona is baggy and nasaka kimono sanann ga veil ."

    Shiru yayi yana kallanta kana yace"ina zakije yanzu,"

Murmushi tayi da ta tuna inda zataje tana Mai ji a ranta da ace Abdallah yayan ta ne da ta gama ganin boni,

Dafasa tayi tace "zanje wani business ne da zai benefiting ɗina,Inajin kun kosa na kawo miji ba?"

Na kusa 30 fa so im not getting any younger shi yasa Zan bawa wani chance just wait idan na dawo akwai gist mai zafiiiii.

    Just be careful and ina nan ina jiran dawowarki im eager nima naji wannan gist ɗin sannan nasan wanene wannan da Addy na ke rawar jikin zuwa ta gansa"Ya faɗa yana mai murmusawa"

Bashi da hayaniya ,sannan shi mutum ne da baya san damuwa ,idan kaji hirarsa Mai yawa to da Nadiya ne wadda jininsu yayi mugun haɗuwa,duk da kuwa da ƙannensa ma sukan tab'awa,amma Nameer kuwa ba wai sun cika zaman hira bane tunda shima Nameer ɗin akwai nashi miskilancin,'dan nashi Ya taka na kowa a gidan.

    Kai tsaye bayan Nadiya ta bar gidan Location ɗin da boyayyen masoyinta Ya tura mata tabi,

Crescent Food &grills Shine inda ta nufa,babban gurin cin Abinci ne da sai wane da wane 'dan haka bai da hayaniya,

A gurin da aka tanada domin adana motocin baƙi ta aje tata kana ta fito tana Mai b'in saƙon sa 'dan zuwa inda yake .

Tsaye tayi a bakin VVIP na gurin tana tunanin ina zata gansa 'dan bata san fuskarsa ba,wanda hakan ke ƙara bata mamaki tana Mai mamakin kanta sosai,

Kalle kalle take ganin babu kowa a gurin,waiter namijine Ya zo gareta yace"Nadiya Belal right?"

Kaɗa masa kai tayi inda yayi mata jagora suka shiga gurin.

    Romantic theme dake gurin Shine abunda Ya Fara mata sallama,ganin babu kowa a gurin ne Ya tabbatar mata da cewa ya Kama gurin ne baki ɗaya,

Kujerar da waiter ɗin Ya nuna mata ta zauna akai tana Mai kalle kallan yarda gurin yayi kyau sosai mood na soyayya.

Ita kaɗai ta tsinci kanta da Blushing tana Mai san saka wanann bawan Allah a cikin idanunta,

A hankali silent kiɗa Ya fara tashi wanda yake da daɗi a kunnen mai saurare,

Gyara zamanta tayi lokacin da ta hango shadow ɗinsa,shigowarsa ce ta saka dukkan wani tunani nata tsayawa ,

Ƙyaƙyawan murmushi da Ya sakar mata shine abunda Ya dawo dan ita cikin nutsuwarta,

Tabbas ta gane sa cos bayan haɗuwarsu ta farko kuma around her take tajin suruntunsa wanda hakan yasaka har ta gansa a yanar gizo inda tanan ne take sanin shi ɗin model ne sannan kuma Actor na Nollywood,abunka da bawai ma'abociyar kalla bace ,

Saurin tashi tayi musamman da hankalinta Ya dawo mata ya bata cewa "He's Evan Hans sannan christian wanda ƙatuwar ice ɗin dake wuyansa ta cross ta Kara tabbatar mata da hakan,take hankalinta Ya bata tazo wrong guri ne 'dan haka ba tare da b'ata lokaci ba tayi saurin tashi tana Mai ɗaukar Jakarta tace "im Sorry i think i'm 'in the wrong room.

" Sorry " Ta sake faɗa tana Mai ɗanyin karamin murmushi .

Takowa yayi inda take yana Mai sake faɗaɗa murmushi kafun Ya sha gab'anta yace"My cupcake bana tunanin kinyi mistake na zuwa nan ."


Wata irin faɗuwa gabanta yayi lokacin da ƙwaƙwalwarta ke shirin tattori mata abinda ke shirin faruwa sannan of course a cikin abun bata cire mamakin accent ɗinsa na hausa ba,

Ƙaramin murmushi tayi lokacin da zuciyarta ke shaida mata wasa ne kawai yayi da ƙwaƙwalwar ta,

Mukullin motarta ta ɗauka kana ta kallesa tace"naji dadi da Ya zamana kanajin hausa yarda bazan azabtar da turanci na Wajen faɗa maka ka kiyayeni ba ,bana san wasan banza, Dont mess With me cos ka yarda dani im d last person da zakayi messing da,i will let This slide amma Next time Bani ba kar kasake wasa da emotion ɗin wani ,and dama nazo ne 'dan nayi maka kashedi sannan lastly ina fatan kasan cewa Nadiya da Evan bazasu taba haɗuwa ba incase Bakasani ni musulmace,

Juyawa tayi 'dan fita ,riƙe mata hannun da yayi ne yazo mata a bazata inda marin da ta ɗauke masa fuskarsa dashi shima yazo masa a bazata.

Dafe kuncinsa yayi ,bata tsaya bi takansa ko abunda zai faɗa ba ta fice a gurin.

    Komawa yayi Ya zauna yana me shafa inda ta maresa kana yayi wani irin murmushi yace"Nadiya you're mine and i know Kema kinzo nan ne domin Kina jin wani abu akaina ko yaya ƙanƙantarsa take,

Amma menene laifi 'dan ba addininmu ɗaya ba,a tunaninsa ba wani aibu bane ba dan sunyi Aure, yana ganin kowa zai iya yin nasa addinin daban amma soyayya Ai ba addini bace kuma babu ruwan ta da addini,

Cup ɗin dake aje gurin Ya jawo Ya buɗe wine ɗin da ke gurin Ya zuba Kaɗan yana Mai kurb'a ,murmushi yayi yace "She's cute and i know we are meant to be".




Chuchujay ✍🏽
[3/6, 4:54 PM] Chuchujay✍️: .https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK

AHALINA

    (Siblings of different Father's)

(Book two in Aure uku series)

            By

   CHUCHUJAY ✍🏽

Gamasu san a tallata masu hajarsu cikin farashi Mai rahusa 09058191213 .

EPISODE 5⃣➡6⃣

    A hankali Nameer yake tuki a yayin da motar ta ɗauki shiru cos tabbas idan yayi magana shi kansa yasan bazai iya mayar da ita bakinsa ba duba da yarda zuciyar sa ke tafarfasa ,

Murmushi Anisa dake gefen sa tayi tace"Baby tunda muka taho bakin ka shiru kaƙi magana amma wani abu da baka sani ba shine ,ni a kowanne yanayi naganka burgeni yake ,shafa kan jaririn hannunta tayi tace "bashi da suna fa har yanzu cos dama uba ke bawa yaran sa suna 'dan haka wannan lokacin ma akan yarona hakan ne zai faru ,ka bashi suna and trust me DNA test ɗin Chan da zai fito 99% positive ne ,ni banga menene amfanin wahalar da kai ba. "

    Wani irin wawan burki yayi Ya Kalleta cikin fushi mai mutuƙar yawa yace "fita a motar nan ,"

Kallan sa take tana wannan murmushin wanda yake ji kamar ya yagesa a fuskarta ,hannunta ta kai ta ɗora a nasa tace "Nameer Stop trying ,mene amfanin ƙokarin da kasan babu wani outcome Mai kyau da zai fito a cikinsa?"

Kazo mu rufawa juna asiri muyi Aure mu bawa yaranmu rayuwa Mai kyau da inganci,babu wanda Ya gani babu wanda yaji please,

    Hannunta da ta saka Akan nasa Ya yakice da ƙarfin gaske kana yace "ke duk wani guntun haukaki fa inaji dashi,kila ma yafi na kanki ,sannan nasan duk hanyar da zanbi naci maki mutunci wallahi fiye da yarda baki zato 'dan haka kafun na wulakantaki ki fitar mun a mota tunda bata ubaki bace."

Ƙaramun murmushi tayi Mai ci masa rai kana tace "Cool down Man,"Bude murfin motar tayi ta fita tana Mai faɗin ,mu haɗu a gida uban ƴaƴana,

Wani irin figar motar yayi wanda Ya sakata saurin ja da baya tana Mai darawa tana juya wayarta da tayi recording abunda ya faɗa yanzu nayi mata rashin mutunci kana ta danna numbern uwar ɗakinta,

Kira ɗaya ta ɗauka ,murmushi tayi kamar tana kallanta kafun tace "uwar ɗakina ina fatan kin gama da Asibiti?"

Licking lebenta na ƙasa tayi tace "Allah yabarmu tare ,sannan a yanzu maganar da nake maki na samu wata hujja da babu yarda iyayen Nameer zasuyi dole su yarda,

Lokacine da yakamata ace sun girbi abunda suka shuka musamman Imam paki da matarsa Umaimah Bulama,ina jin suna jin labarin kiyayya da fansa amma bana taba tunanin sun tab'a ganin irin tawa ƙiyayyar da fansar dake dumama acikin zuciyata da b'argona wadda nake ji kamar na soke dukkanin acting ɗin da nake na kashesu a zuwa ɗaya,kin san nayi training wajen yin kisa ko wacce irice ballantana kuma akai ga maƙirici,

Dariya tayi kana ta kashe wayan tana Mai faɗin"Wallahi da ni yarinya ce Mai hali na gari,amma dukkan wannan halayyar ta gari ta ƙare ne a lokacin da na rasa mahaifiyata kuma kash sai Ya zamana kafun ta tafi ta sanar min da waɗanda sukayi silar mutuwarta,dukkan godiya ta tafi gareta da ta barni da ƙyautar fansa da ƙiyayya,wadda na rantse da Ubangijin da na yarda dashi bazan tab'a gushewa ba sai na ƙarar da zuri'ar Paki da duk abunda suka mallaka. "

    Da haka ta nufi gidan 'dan shirya saban tuggunta.

******************************************** 

  Bayan Rabuwar Nadiya da Evan ta daɗe tana saka da warwara a cikin zuciyarta kafun ta nufi gida kai tsaye dan ko office bata san zuwa,

Abu guda ɗaya ya tsaya mata a zuciya wanda shine yarda Evan yasan Abubawa da dama akanta ciki kuwa har da inda take zama,

Babu abunda yake sake b'ata mata rai da damunta kamar idan ta binciki zuciyarta taji har a lokacin akwai wani Abu tattare dashi wanda bazata iya fassarawa da baki ba ,

Tana shiga gida Motar Nameer Ya tabbatar mata da sun dawo ,ajiyar zuciya tayi atleast idan nata matsalar baiyyi working out ba na Hammanta ta tabbatar da yayi,

Tana Mai koƙarin fita a motanta bayan ta fakata a mazauninta Anisa ta buɗe ta zauna a mazaunin Mai zaman banza,

Wani banzan kallo Aneesa ta bata musamman da taji yarda Annoying kukan babyn da bai ji bai gani ba yana tashi,

Baki ɗayanta a foul mood take wanda idan Anisa ba tayi wasa ba zata iya juyewa akanta ,ɗaukar Jakarta tayi tana Mai faɗin"Get out of My car".

    Wata irin dariya Anisa tayi tace"na daɗe da lura Alhalin gidan nan arrogance ɗinsu abu ɗayane kamar yarda suke abu ɗaya,kamar kuma an tsinkuleta ko irin ka faɗin abu ba dai dai ba tace"a'h Afuwan fa ashe dake da Nameer ɗina da Abdallah zaman agolanci kuke a gidan nan,'dan naji sirikina da Ya haifi Nameer har Porn clip ɗin mahaifiyarki da Mijin ta na yanzu ma'ana mahaifin su Fawzan Ya ɗora wanda kuɗi yasa aka kashe maganar aka ƙaryata alhalin babu wanda bai san iskancin da suke yi a city hospital ba,

    Dafe bakin ta tayi tana Mai Kallan Nadiya da murmushi rainin hankali tace"amma fa rumours ne nima' wai 'naji suna iskanci a 'da amma bana tunanin jita jita da ya tashi a lokacin baya na kama mahaifiyarki da Mahaifinki Bilal yayi da gardi Akan gadonsa ƙarya ne ,sannan naji ance yana ƙokwantan kasancewar ki ƴarsa,After All baya nemanki " .

Sake dafa baki tayi tace "a'h shima nafi yarda da jita jita ne 'dan mother 'in law na batayi kama da Mai rabawa maza Pun@ ɗinta  ba duk da kuwa ta raba ga maza iri huɗu da sunan Aure.

Family ɗinmu nada reputation gaskiya .


    Buɗe murfin motar Nadiya tayi ta fito kana ta zagaya inda Anisa ke zaune ta buɗe ta finciko ta,kafun Anisa tayi Aune ta sharara mata wani irin zazzafan mari yayin da babu abunda bakinta keyi sai karkarwa ,ƙokari sosai tayi wajen danne kukan da yake san zubo mata 'dan sosai maganganun Aneesa sukayi mata zafi,tana ƙokarin sake marin ta sakamakon dariyar da Anisa ke Mata taji an riƙe mata hannu,

Juyawa tayi 'dan ganin wanene,Papa ne tsaye gefensa Mami,kaɗa mata kai yayi yace"No My princess bana san ki Aikata mistake ɗin nan ,"

Hawayen da take ƙokarin zubo mata ne suka fara neman hanyarsu ,ba tare da ta boye ba tace "Papa kalli yarinyar nan na tabbata ko Abdallah ƙanina Ya girmeta and trust me idan kaji maganganun da ta faɗa mun kai zaka mareta Bani ba,amma tunda kace na Bari Zan bari,nuna Anisa tayi da hannu tace "ki sani i will be your downfall sannan lokacin da Zan wulaƙantaki a gidan nan na maki koran kare lokacinne Zan baki amsa dai dai da abunda kika faɗa mun ,Stupid freaking Gold digging bitch .

    Ta juya dan barin gurin ta tsinci muryar Mami na faɗin"stupid freaking Gold digging bitch ɗin nan ina san kisa aranki babu ranar da zaki koreta,ki wulaƙantata cos zaman ta da Ahalinku yanzu ta fara cos tana ɗauke da ɗan da yake jinin gidan nan,"

    Wata irin murmushi frustration Nadiya tayii jin Abunda mami tace sannan sarai ta fahimci abunda Mamin ke nufi ma'ana dai Dna Ya nuna yaran dan Nameer ne,

Juyowa tayi ta kalle su kana tace "ban san menene kuka yarda dashi ba amma ni abu ɗaya na sani na yarda dashi wanda bana tunanin kun fahimce sa wanda shine"wannan yarinyar is fake and a cheat cos ada kokwanto nake amma a yau maganar da ta faɗa mun bana koƙwanto sannan sai na kawo ƙarshen maƙiricin ta cos naga Alama ni ta zab'a a gidan nan na kawo mata ƙarshen ta"

Fuu ta wuce ciki inda Anisa ta wani langwab'e kai tana Mai faɗin"interesting a zuciyarta ,mami na kallanta ta marairaice fuska ,Hannu mami ta miƙamata alamun ta bata yaran ,babu musu ta b'ata ,kallansa sosai mami Take tana san gano da uban da yayi Kama a zuria'rsu amma babu,babban kuma abunda Ya kuma ɗaure mata kai shine yarda DNA ɗin yaran yayi matching dana Nameer, bata tunanin anyi tempering dan a asibitinsu akayi bata tunanin zasu back stabbing ɗinta haka.

    Papa ya fara barin gurin kafun ta mara masa baya Anisa na biye dasu tana Mai jin daɗin defeat d'in da ta gani a kan fuskokinsu ,

Kaɗan ma suka fara gani A cikin irin abubuwan da ta shirya masu indai itace.


***********************

    Nameer zaka Auri Anisa nan da sati ɗaya sannan a yanzu zaka raɗa ma yaranku suna dan nauyin ka ne,idan kuma ban isa ba ban kai nasaka ka ba dan Allah ka bijirce mun.

    A zabure Ya kalli mami yace "Mami wallahi tallahi wannan yaran banawa bane sannan wallahi ban tab'a ganin yarinyar nan ba ballantana har na bata cikin da zata haifa mun yaro shima kuma ta hanyar fyaɗe ,mami zaki yarda da wannan yarinyar sama dani da kika haifa ne?

Papa say something.

    Ɗauke kai Papa yayi cos duk yarda yaso Ya yarda da maganar Nameer gaskiyace sai yaji kamar baiyyiwa Anisa adalci ba sanann yaso kansa .

Jefa masa result d'in DNA ɗin mami tayi tace "Ba yarda nayi da ita sama da kai ba result ɗin da na tabbatar babu kuskure shi nayarda dashi,zaka faɗi wani abu bayan nan ne,?

Zubewa tayi a ƙasa duk juriyarta ta saka wani irin kuka Mai cin rai tace"kalle ni nan Nameer  ba sai na faɗa maka ba nasan kana da wayan sanin abubuwan da nayi facing through kafun Papanku,ko ban kai uwa enough ba wani cikinku Ya fada mu,im a not That Good enough da kuke san dole sai kun tona mun asiri,dame na rageka Nameer,i gave you a father ,gashi nan zaune wanda Ya ɗauke ku kamar nasa duk da abunda duniya ta ringa Faɗa bai damu ba,he gave you guys a Good life and d father's warmth ,bai isa ba?

Idan baku guje mun abun magana domin ni ba zaku guje dominshi,amma sai da kayi yarda kayi ka nuna mun ban isa na goge jinin Habib a jikin ka ba atleast ka gado wani abu nasa.

    Da sauri Papa Ya ƙarasa gareta yana mai hanata faɗan abunda zatayi dana sani,

Goge hawayenta tayi tana Mai Kallan Papa tace "im Sorry ,kayi haƙuri da abunda Nameer Ya jawo mana and yau bazaka shigar masa ba cos you've pampered him enough,

Goge hawayeta tayi ta mike ta nufi gurin Anisa ta karbo babyn ta ɗorasa kan cinyar Nameer wanda yayi saurin tallafesa gudun kar ya faɗi.

Nuna yaran tayi tace He's yours dan haka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login