Showing 1 words to 3000 words out of 68854 words
[3/6, 4:35 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
AHALINA
(Siblings of different Father's)
(Book two of Aure uku series)
CHUCHUJAY ✍🏽
Domin fahimtar littafin sosai zaifi kyau ka fara karanta Aure uku,amma idan wannan ɗin ma ka fara laha lau amma i suggest kafara karanta Aure uku.
Gamasu san a tallata masu hajarsu cikin farashi mai sauki 'a duk guri uku da ake posting 09058131213.
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
EPISODE 1⃣➡2⃣
INTRODUCTION
•NAMEER HABIB
Saurayi ɗan kimanin shekaru talatin da huɗu ,saurayi mai Kyau da ji da kuɗi da aji,
Architecture sannan business tycoon wanda ke da Construction company Mai zaman kansa,
C.e.o PIXEL CONSTRUCTION COMPANY.
Wanda Ya haɗu da tsaƙwakiya a rayuwar Auren sa.
NADIYA BELAL,
Budurwa yar kimanin shekaru ishirin da tara ,
Idan ka Kalleta kaji shekarunta take zaka ƙaryata shekarunta saboda baki ɗaya tayi ma shekarun kankanta,
Mai kyauce irin melanin ɗin nan wanda kana kallansu kaga Africans ,kalarta Mai kyauce sannan ga hutu da kulawa ta samu,
Model ce sannan Founder ta AFRICAN QUEEN(s) MODELING ROOM ,
Kungiya dake ɗaukar MODELs tayi managing nasu .
ABDALLAH HAFIZ.
Mutane na masa inkiya da young Sheik ,ƙaramun malami Mai fasaha da hazaƙa wanda kowa ke mamakin yarda yazama malami a shekarunsa ishirin da shida na haihuwa ,
Shahararsa da ƙokarinsa ba kowa bane illa mahaliccinsa da kuma maminsa da papansa waɗanda suka tsaya masa,
kowa da maganar Abdallah a bakinsa 'dan shi ɗin abun burgewa ne ,
Babban foundation yake dashi na taimakawa marayu da marasa karfi sannan a harkar kasuwanci shima ba'a barsa a baya ba yana tab'awa.
JAMAIMAH RAIS
Budurwa yar kimanin shekaru ishirin da shida,yar asalin garin CAMEROON ce sannan ɗiya a gurin sarki RAIS tilo 'dan haka Ya ɗauki dukkan soyayyar duniya Ya ɗora mata ,irin yaran nan ne da aka sangarta sannan suke gani babu abunda zasu nema su rasa,shagwababiyar gimbiya a masarautar DILAH sannan gimbiya mai taka dukkan wani talaka ,mutane kance wulaƙanci Shine ɗaya sunan ta amma ta faɗa soyayyar da take wahalar da ita .
EVAN HANS
Matashi ɗan shekara talatin da huɗu ,Ghanian ne wanda ke da rubi da Nigeria ,mahaifinsa 'dan ghana ne yayin da mahaifiyarsa Igbo ce asalin Nigeria cikin garin akwaibom ,
Christian ne sannan sana'arsa modeling bugu da ƙari shi ɗin actor ne ,
Soyayyar da ake kira da forbidding love a cikin danginsa itace tayi masa kamun kazar kuku
HAFSAT BALARABE
Ɗaliba a kwalejin fasaha da kimiya a cikin garin jibia dake garin katsina inda take karantar Computer science,budurwa yar kimanin shekaru sha tara ,
Iyayenta asalin Yan garin katsina ne sanann marainiya ce dake zaune gurin matar uba,
Bata da wani gata bayan na Allah 'dan mahaifinta Ya zama shanyayye a gurin matarsa ,
Sosai take ganin rayuwa amma hakan bai hana mahaifin nata bata ilimin gaba da sakandare ba duk da kuwa halin matarsa wanda ƙarshe saida Mai garin yasa baki yasaka ta samu damar shiga kwalejin .
FAWZAN IMAM PAKI
FAWHA IMAM PAKI
FAWZA IMAM PAKi
Yan uku masu shekaru 23,
Suna jami'ar shekarar farko.
NYC University ,united state of America
ANEESAH LUKMAN UBA
??
Wacece Anisa Lukman uba?.
********************************************
ADAMAWA LUGARD CRESCENT NIGERIA.
Zazzaune suke a cikin makeken falon dake faman ihun naira a yayin da ko wannen su yayi jugum jugum ,gefe guda wata budurwa ce zaune idanunta sun kaɗa sunyi jajur saboda tsabar kukan da tasha hannunta kuma riƙe da jaririn da bazai wuce 'dan wata ɗaya ba.
Dattijuwar dake zaune a falon kana kallanta zaka gane cikin bacin rai take sosai bama sai an faɗa maka ba,duk da girmanta kyawunta bazai boyewa Mai kallo ba,bata da jiki Mai girma 'dan haka bazaka ce itace ta haifi yara Shida dake Zazzaune a gurin ba,Doctor Umaimah Bulama Imam kenan ,diyar attajiri sannan likita da tayi ƙarkon suna wadda ta malaki asibitoci guda biyar wanda suke karkashin jagorancinta da maigidan ta Doctor Imam Mukthar Paki.
Sake kallan budurwar dake ta fama sharar kwalla tayi tace "kikace menene sunan ki again baiwar Allah?"
Cikin shesheƙar kuka budurwar tace "Aneesah Lukman uba,sannan ni yar asalin garin Kano ce ,ina zaune da mahaifina da mahaifiyata amma sakamakon abunda Ya gifta tsakanina da NAMEER Ya saka sukayi disowning ɗina suka koreni a gida,sannan wallahi hajiya kamar yarda na faɗa maki fayɗe yayi mun gashi nan a zaune Ai, kuma Allah yasa da rabo tsakanina dashi wanda Ya zama silar lalacewar dukkan gatana ,na ɗauki ƙaddarata sanann hajiya a labarin ki da nake ji na mace Mai adalci nasan zaki ƙwatarma wannan yaran haƙƙinsa ,ni bana buƙatar komai da ya wuce Ya ƙabi ɗansa Ya bashi sunansa kar yayi rayuwa lalatacciya."
Wata irin dariya NADIYA ƙanwar Nameer Mai bi masa tayi tace "Mami i hope wai wannan tale story ɗin bawai kina ɗaukar sa bane cos zan iya rantsuwa karya yarinyar nan take,i mean babu wanda bai san halin Hamma Nameer ba ,Last abunda zan yarda dashi ace yayi Shine fyade, haba this doesn't even sounds okay,ABDALLAH kasa baki mana".
Ajiyan zuciya ABDALLAH dake bi mata yayi yace"Mami abunda addyna ke faɗa fa gaskiya ne,ban yarda da yarinyar nan ba".
Fawzan dake faman tafarfasa yana ƙokarin saka baki Mamin nasu ta Katsesa ta hanyar faɗin"kun gama goyan bayan hamman naku?"
Ko akwai Mai ƙara wani magana akai,
Fawzan ,Fauza,Fawha mic ɗin Ya dawo gare ku,Mai kuma zaku ƙara akan abunda yayyunku suka ce ?
Hammanku is saint an masa karya babyn ba nasa bane,Anisa ta haɗa labarine kawai na ƙanzan kureƙe ta kawo tayi framing yayanku?
Is that not it?
You All should cut the bullshit.
Kallanta ta mayar kan Nameer wanda babu abunda yake sai kallan Anisa tace "nasani Ai you're out of words Nameer,so abunda yasaka kake kauce mun duk ranar da nayi maka maganar Aure kenan,kasan Mai kake aikatawa a bayan fage ,abunda zaka saka mun dashi kenan ba?
Duniya ta zageni kaji daɗi,goge yar karamar kwallar dake shirin zubo mata tayi kana ta kalli Fawha tace"ke nuna mata guest room ta zauna kafun musan abunyi cos trust me sai na ƙwata nata encin ta ,you will have to marry this girl Nameer babu yarda za'ayi kayi escaping ma mistake ɗinka da responsibilities ɗinka, "
Dafa fuskar sa yayi cike da damuwa yace"Mami wallahi tallahi kamar yarda na faɗa maki,Bansan yarinyar nan ba ,hasalima ni Ban tab'a ganin ta ba ,yarda kuka fara ganinta yau ,wallahi nima yau nafara ganinta,ni ba mazinanci bane tayaya ma zanyi raping mace a cikin hankali da nutsuwa ta,?
Mami ki yarda dani,zaki yarda da maganar barene sama da tawa?
Ke kika haifeni sannan kinsan abunda Zanyi da wanda bazanyi ba ,and raping baya cikinsu,wallahi tallahi sharri take mun ,bansan mene ribarta ba.
Yana kai ƙarshen maganar sa Aneesa ta fashe da kuka tace"wallahi hajiya ba ƙarya nake masa ba,Nameer kada kamun haka 'dan Allah,ni bana buƙatar komai kawai ka ƙarbi yaranka and namaka Alƙawari zan tafi,".
A fusace Ya tashi yayi kanta yana Mai faɗin "ke ive heard enough of your nonsense,zaki bar gurin nan ne ko sai na ballaki ,"
Ganin yarda yayi kanta ganga ganga yasa Abdallah saurin tashi Ya riƙesa ,
Maminsu dake zaune ce tace "ka tab'a ta Nameer kaga mai zan maka,idan yarinyar nan ƙarya take bazata yi ta bibiyar san samun ganina ba har na sati kenan something is fishy here so kar kayi ƙokarin displaying mana borin kunya ,idan kuma ba haka ba zan sab'a maka fiye da tunanin ka sosai,".
Juyowa yayi Ya kalli maminsa kafin yace "i just hope Papa Ya dawo yau cos nasan Shine kaɗai zai yarda dani".
Takawa yayi yabar gurin inda yake jiyo muryar mami na faɗin"Eh papan naku yana nan dawowa Ai yau ɗin ,sannan kasani idan baka da gaskiya dole kayi man up ka ƙarbi laifinka,".
Kallanta Nadiya tayi tace "seriously mami?".
Batare da ta kuma cewa komai ba ta tashi a falan tana mai jin kamar ta Kama Aneesa tayi ta duka har sai tayi confessing akan karya take.
Kamar yarda mami ta umarci Fawha haka tayi ma Aneesa jagora zuwa ɗakin baki ,bata jira jin Mai Aneesa d'in zata ce ba tafito tana mai jin haushinta.
Kowa Ya tashi Ya zamana daga Mamin nasu sai Abdallah wanda yabi Mamin nasu da ido yana kallanta,
Kallansa tayi itama tace "yadai zaka jamun aya ka fassara ne da kake kallona tunda ku babu wanda Ya isa yayi laifi a cikin ku, tunda ku saint ne Ai Ahalin saints,".
Bai ce mata komai ba Ya miƙe yana Mai faɗin "zani gidan Granpa Bulama ne cos yana Mai jirana yanzu haka zamuje wani taro ƙarfe huɗu,Amma idan na dawo zan tsaya gun Ummu ƙwana biyu ban samu na shiga ba tunda na dawo Nigeria. "
Ɗauke kai tayi tace "Allah Ya kiyaye,
Daga haka bata kuma cewa komai ba wanda ko ba'a faɗa masa ba yasan cewa tana cikin tsantsar damuwar da baki bazai iya faɗarta ba ".
Ɗakin Fawzan Ya nufa dan yi masa magana akan yazo su wuce cos tare zasu tafi.
******************************************
Bayan shigar Aneesa Guest room ɗin walk 'in closet ɗin dake ɗakin ta shiga bayan ta kwantar da babynta akan gado ,murmushi tayi lokacin da take fara jera kayanta ciki tana mai faɗin"soon mrs Nameer Habib,young and handsome rich bachelor ,dawowa tayi bayan ta gama jera kayanta ta kalli babyn ta shafa fuskarsa a hankali tace "a wani bangaren ina takaicin samunka saboda irin wahalar da zansha na kulawa dakai kawai,amma wani bangaren ina Mai farin ciki da murna zan samu nasarar tarwatsa dukkan wani mutum ɗaya dake cikin AHALIN nan,ta dalilinka zan samu na sakawa duk wani ɗan gidan nan dafi a zuciya wanda bazai taba gogewa ba,
Ƙwalar dake ƙokarin zubo mata ta goge tace "ba lokacin kuka bane aneey baby lokacin buga wasa ne wanda dole kece da nasara 'dan baki tab'a saka gaba a abu ba kin faɗi.
Ɗaukar wayarta da tayi ƙara tayi ta kara a kunne tace "Hello, uwar ɗakina ,ina fatan kin shirya komai a yarda muka tsara dan bana san fuck up,
Murmushi tayi a yayin da take sauraren ɗaya bangaren kafun tace "baki da imani uwar ɗakina ,shine babban Abunda ke burgeni dake ,ina yinki a kullum,sai na jikii".
Kashe wayan tayi tace "yanzu wasan Zai fara,"Yaran da yake kuka ta ɗauka ta fara bawa nono tana mai shafa masa kansa cikin kulawa tana mai jin ƙamshin nasarar ta.
Kwance Nadiya take tana Mai juya abunda ya faru a falan ƙasa,
Wayanta ne ya hau ruri alamun message Ya shigo,
Jawo wayan tayi tana Mai kallan unknown Number ɗin dake addaban ta da messages na soyayya iri iri,
Shekara guda kenan numbern ke damunta da sakonin da tun bata sa su gabanta har suka fara bata nishaɗi ,
Sau da dama tasha kiran layin amma baya shiga ,
Murmushi tayi lokacin da saƙon Ya shigo mata kamar haka
"Im 'in Nigeria rn ,hope i will get to see you,i will give you a Call later 'in the night!!
xx EH❤.
Murmushi tayi tana Mai jin wani irin nishaɗi nasan saka wannan boyayyan masoyin nata wanda Ya ɗauki shekara yana nuna mata soyayyar da tun bata mayar masa har tafara a ido,
Case ɗin Nameer na ne Ya dawo mata ,tashi tayi zuciyarta na ingiza ta ta Nufi ɗakin da Aneesa ke ,
Ba tare da tayi knocking ba ta faɗa ɗakin,
Zaune ta tarar da Aneesa tana bawa yaranta nono,
Zama tayi gefen Aneesa tana Mai kallan yaran kana tace "gaki dai mace har mace wadda yanzu idan kika fita zaki samu miji na gani na faɗa ,amma kin ƙwammace kizo kiyima hamma ƙazafi,gyara zaman ta tayi tace,state the price ko nawane zan baki cos nasan saboda kuɗi kike wannan abun so ki faɗa ,na baki zero ki ƙara ko nawane zan baki, in return' ki ɗauki Bastard Son ɗinki ɗinan ku bar gurin nan.
Dariya Anisa ta saka Mai kyakyatawa kafun kuma kamar mai iska ta kece da kuka ta riƙo hannun Nadiya wadda ta tsorata da reaction ɗinta tace "sister abu guda Ya bani dariya da baƙin ciki da na kalleki a matsayin mace wadda ke neman tona asirin yar uwarta mace saboda kawai ta kare ɗan uwanta,amma ki sani ,ba ƙarya nake ba ,wannan ɗan na Nameer ne koda kuwa sama da ƙasa zata kife,ke kuma a matsayin mahaifiyarsa kike Tunda ke Auntynsa ce."
Miƙewa Nadiya tayi tana Mai faɗin "kije chan ki nemo Auntynsa da ubansa amma ba anan gidan ba ,sannan tunda ke kina ganin cewa bazakiyi mubaya a ba ta hanyar karbar kuɗi ki bace ba,zakiyi idan kika sha kashi,"
Fita tayi a dakin tana Mai jin kamar ta shaƙe Aneesa,
Wata irin dariya Aneesa ta saka tace"zakuyi ku gama domin ni abunda ke zuciyata yafi karfin duk wani abu da kuke tunanin kun mallaka a duniya."
**********
Masoyana barkanku da kasancewa cikin koshin lafiya,
Ya kukejin tafiyar AHALINA?
Ina fatan zai samu daɗaɗan comments ɗinku da kuma reactions naku,
Nice taku a kullum.
CHUCHUJAY ✍🏽
[3/6, 4:53 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqKAHALINA
(Siblings of different Father's)
(Book two of Aure uku series)
BY
CHUCHUJAY ✍🏽
Gamasu san a tallata masu hajarsu cikin farashi mai sauki 'a duk guri uku da ake posting 09058131213
EPISODE 3⃣➡4⃣
Hafsatu Hafsatu,ina kuma zakije ?
Ashe dai yau uwarki laraba zata taso daga kabari a duk hasashe na ,saboda ba a haifi ɗiyar da zata fita gidan nan yau bata kai mun sauran dawo na ta siyar ba.
Tsaye Hafsa tayi tana kallanta kana tace mama laure 'dan girman Allah kimun haƙuri yau ɗinnan kawai ,wallahi malamin da zai mana karatu yau tsauri ne dashi idan nayi missing attendance ɗinsa zanji babu daɗi,
Hasiya taje a maimakona in yaso ina dawowa zan karb'e ta ,
"Sai dai idan uwar Hasiya Laure ce zata je maki tallan fura ba Hasiya ba,"
Hasiya ƙanwarta ɗiyar laure dake fitowa a ɗaki ta faɗa .
"Ke Hafsatu zo ki wuce ki tafi karatunki maza kar kiyi latti "
Mahaifinta Ya faɗa yana Mai ɗan daurewa.
"To baba "
Sum sum ta wuce tana Mai jiyo mitar mama laure har tabar kan gidan.
Koda taje makaranta ƙawarta Hauwa da suke zama tare ta rigada ta kama mata seat,
Zama tayi bayan sun gaisa tana Mai faɗaɗa murmushinta tace"har yanzu malam kabiru baizo ba kenan"
Hankalin hauwa na kan waya tace "wallahi bai zo ba ,zo kiga ina kallan sabon video ɗin Abdallah Hafiz ne ,ke wallahi guy ɗin nan Ƙawata yana kashe ni ,inaji a jikina bani da mijin da Ya fisa 'dan haka ,kuma ɗauke kanku akansa.
"Murmushi hafsa tayi tana Mai jin wani irin abu a zuciyarta dangane da maganar da Hauwa tayi,
Dama bata wani sakashi aranta ba,tunani ne na ko wanne ɗan adam wanda ba'a rasa shi da shi sannan cikin tunanin nata bata tab'a cewa tanaji ajikinta zai zama nata ba,ina ita ina shi?ita ɗiyar talakace wadda ke neman yarda Zatayi ta rayu inda shi kuma bayan shararsa iyayensa shahararru ne na gani na faɗa,
Kakan sa ma kansa a duniya faɗan sa akeyi ,
Kilan ma har ta mutu bazata taka inda Ya taka ba a duniya ballantana akai ga haɗuwa ,burgeta ne fa yanayi bana kaɗan ba,sannan a duk lokacin da take sauraran karatunsa ta kanji nishaɗi da nutsuwa suna ratsa ko ina nata,
Tana wannan tunanin nata lecturer ɗinsu Ya shigo domin basu karatu.
********************************************
Washe gari Papan su Nameer Ya dawo gida inda Ya tsinci maganar Aneesa wadda tayi mutukar girgizasa,Amma sai bai yanke hukunci ba kasancewar ya yarda da Nameer sannan shi yafi jiyo kamshin gaskiya a maganar Nameer yarda Maminsu ta faɗa masa akan ta Anisa,
Instinct Ɗin na faɗa masa akwai wani abu a tattare da Aneesa duk da kuwa basu gana ba one in one amma ya rasa gane menene wanann abun,
Kamar yarda suka saba idan suna gida dukkaninsu,
Baki ɗayan su sun hallarci karin safe banda Nameer ,
Kallan Abdallah dake ƙokarin zama Papa yayi yace "kai Abdallah maza je ka duba Mai Ya hana hamman ku fitowa maza yazo,kin yin karin kumallo da safe da wuri is not Good for health, " .
Abdallah na ƙokarin fita muryar Nameer ta karaɗe gurin yayin da yake faɗin"Good morning fam,"
Yana kallan Papansa kuma Ya sake dashe baki yana Mai fadin "Papa thank God ka dawo ,".
Zama yayi yana Mai gaida su kafun yace "Papa i miss you wallahi"
Murmushi Papan yayi yace "As if,shiyasa naga jiya Ai naga kowa banda kai".
Kare kansa Ya farayi duk da yasan Papan nasa yasan da dalili.
Bayan gama cin abincin su Mami ta kalli Nadiya tace "Nadiya Ɗauki breakfast ki kaiwa Anisa,"
Kallan mamin nasu tayi kamar Zatayi kuka wanda hakan yasa Papa cewa"hayatee ga Fawha ga Fauza wani Ya kai mata cikin su mana why Nadiya,"
Turo baki Nadiya tayi tace "ooo Papa kaima ka faɗa dai ,mami tunda yarinyan chan tazo take ta neman rigima da kowa bayan ni nasan cewa yarinyar Chan wallahi snake ce,ko me tazo dashi gidan nan ba Alheri bane sharri ne,"
"Fawha ne dake gefen Abdallah tace "nikam Papa sai dai fauza taje Allah ,nifa na kai ta ɗaki jiya,i hate her guts".
Tashi mamin su tayi tace "bari ni naje na kai mata tunda dukkanku babu wanda zai iya kai mata,"
Da sauri Fauza ta miƙe ta shiga kitchen tana Mai faɗin bari naje na kai mata ,Allah ma yasa Papa Ya dawo zamu yi getting rid of her.
Kafun Papa yace wani Abu Mami tace"koma menene dai ai yayanku gashi nan Shine Ya jawo maku sannan idan yayi creating mess Ai ba Papan ne zaibi ya gyara masa ba ,shi ɗin da Ya b'ata Shine zai bi Ya gyara ."
Kamo hannunta Papa yayi yace "sarauniyata Ya isa haka nan zo zauna ki daina wannan faɗan 'dan Allah ".
Zama tayi tana Mai karamin murmushi .
Gyaran murya yayi yace "kaga nan Nameer kowa yana making mistake a rayuwa wadda ta shafi zamantakewa,nima akwai abubuwa da dama da nayi mistake akai ,amma a kullum maminku nakusa dani kuma tana tare dani a duk mistake ɗin da nayi muna gyarawa a tare so Son talk to me duk wani mistake da zakayi a rayuwanka muna tare da kai sannan zamu gyarasa a tare cos babu ɗan adam ɗin da ya wuce aikata kuskure."
Ajiyar zuciya Nameer yayi yana Mai jin papan nasa a ransa cos duk da bashine Ya haifesa ba amma baya taba nuna masu wariya tsakaninsu da Fawha,Fauza da Fawzan ,
Yasan yarda yake fahimtar sa mahaifinsa da Ya haifesa ma bazai tab'a fahimtarsa ba duk da Mahaifin nasa yakan je Ya gansa wanda a yanzu bazai ma iya faɗin yaushe rabo ba ,
Sosai yake jin Haushin mahaifinsa musamman idan yana tuna abubuwan da yayi wa mahaifiyarsa lokacin yarintarsa sai