Showing 24001 words to 27000 words out of 76019 words

Chapter 9 - MUMMUNAR DABIA PDF BY ASMA BAFFA

22 Aug 2025

287

uhm ai kan yana kubucewa dole sai anyi hakuri da ku,Sai da suka yi wanka Sahil ya kwanta bacci Sohail ya fito wajen Maheera tana kitchen tana musu girki,yace kika ce kin rasa wanda yafi wani kyau a cikinmu? Maheera ta manta ma ta fada,tace ai kamar ku daya amma kace baka da kamarsa zaka iya bar masa ni ma,Sohail yace ae zan iya mana ance miki damuwa nayi dake ko sonki nake?
Maheera tayi shuru ya ja tsaki ya fice.


Sai bayan Sahil ya tafi da kwana daya Aunty ganin ba kowa a gidan ta kori Islaha tace tafi kisan inda dare ya miki,kije duk inda zaki a duniya na gaji da ke tunda baki da wani amfani a rayuwa,sabo da bakin hali anyi anyi a hadaki da mazan arziki kinki,ashe abinda kika yiwa Alhaji Umaru kenan? Na tura ki har hotel ki tayashi kwana ashe da maganin bacci kika tafi kika zuba masa a lemo sai da yayi sati bai farfado ba yana bacci,kin kusa kashe bawan Allah,sai yau ya kirani a waya ya fada min sai da aka kwantar da shi a asibiti.


Islaha tace to kawai ni sai naje yayi iskanci dani ni kuwa na zuba masa maganin bacci a lemo ya sheka bacci,nayi kwanciya ta na sha bacci na da safe na fito.
Aunty tace kinwa kanki hada kayanki ki kara gaba,Islaha ta dauki jakarta tace a bude taskira lafiya,watarana mazan zasu daina yayin ku duk tsafinku,Aunty da gudu ta bi Islaha har Islaha ta fice da gudu daga gidan.


Tasha ta wuce ta shiga motar Abuja da kudin asusunta da ta tara sunfi dubu hamsim,dake karamar mota ce zuwa dare sun sauka bayan sallar Isha,Direct gidan da Sahil ya bata address ta nufa ruwan sama ake tsulawa kamar da bakin kwarya haka me mota ya sauketa ta fito,tuni ta jike sharkaf sai rawar sanyi take,tanaturo karamar kofar gate din taji ta bude ai kuwa ta fado gidan.


A ranta tace gaskiya batan kai nayi ta ya Sahil zai kasance a irin wannan gida,duk da cewar komai kalarsa ta me kudi ce amma yanda taga yana fama da talauci ta ya za ace nan ne gidan,har kofa ta nufa tayi knocking ruwa na zaneta,Sahil ne a palo shi kadai yayi zugum ya zuba tagumi kasancewar yau yaci uban aikin da Ibrahim ya sa shi me wahala duka motocin su sai da ya wanke,ya share compound ko ina,ya gyara fulawowin da suke gidan ko ina har garden.


Tashi yayi cike da gajiya ya bude kofar, tsayawa yayi kamar gawa sabo da tsoro,idanuwansa ya murza sosai ya bude ya ga dai ita ce,kumatunsa ya buga yace ba ita bace Sahil dawo hayyacinka,ya ga dai tana nan,hannu ya mika a hankali tare da rike hannunta a tsorace yaji dai mutum ce,yace ah'ah lafiya?
Nice fa Islaha ai Aunty ce ta kore ni shine na taho nan.


Kuma ki rasa wajen wanda zaki taho sai wajena,Kizo ayi miki ciki ko wata matsala ta faru ace nine,Islaha tana rawar sanyi tace dan Allah ai da mace a gidan,Sahil matsawa yayi daga kofar yace wuce ciki,ta shige da sauri ya kulle kofar, Ibrahim ne ya fito ya bi Islaha da kallo yana gadara,yace ke me ya kawo ki nan? Sahil yace na santa kawata ce hanya ta biyo da ita zata tafi soon.


Sabo da mugunta Ibrahim a ransa yace Allah yasa kayi mata ciki tunda baku da hankali masifa ta afka muku a ja ku can a kulle a prison kowa ya huta da jaraba Allah yasa,Mamaki ya tsaya yi ina suke samo yan mata haka ne full option shi kuwa duk baya samu duk kudinsa da motar da yake hawa,a fili ya kalli Sahil yace kuke nan kawo mata gida wannan tazo wannan tazo bakwa gajiya da zinace zinace ne sabo da Allah yayi muku kyau sai ku dinga lalata yaran mutane an muku fada kunki ji,kuje duniya ce zata yi muku karatu da kanta,wai dan ya bata Sahil a gaban Islaha.


Zayna ce ta fito cikin kana nan kaya riga da wando 3qtr farare ta sha kyau sun mata kyau amma ba ruwanta da kannen miji na kallon surar ta haka take fitowa cikinsu suna kallo,


Tana zuwa ta kalli Islaha,ran Zayna ya kara baci tace a ranta a barni naji da wannan yar aikin Maheera ita kadai ga wata an kara kawo ta na rasa wacce tafi kyau ma a cikinsu.


Zayna a fili tace wannan fa? Sahil yace sabuwar yar aiki ce aka kawo miki zata dinga miki wanki da guga,Zayna tace kuma me yasa ake kawo min mata irin wannan munana,Maheera da kyar na karbe ta ga wata me kiba a duwawu duk sai jika mana palo take da ruwan jikinta dan Allah jata can kuje ta furta tana yatsina.


Islaha kuwa Ibrahim da Zayna ta gasawa harara suna kallonta tabi Sahil suka tafi,dakin Maheera ya kaita,ya samu Maheera tana linke kayanta yace ga bakuwa anyi wata ce sabuwar yar aiki me wankin Zayna,Murmushi Maheera tayi tace to bismillah amma kinci dukan ruwa shugo.


Islaha ta shugo jakarta a cikin leda yanda ruwa bazai sameta ba,Maheera tace ga toilet shiga kiyi wanka,room din yaji gyara yana ta kamshi ta shige toilet tana cewa na gode,Wanka tayi sannan ta gabatar da Sallah Maheera ta kawo mata lafiyayyen abinci,taci ta koshi,Maheera ta kalleta tace ya sunanki ne? "Islaha" sunana, mashaallah sunana Maheera ni,Nice to meet you,nice to meet you too.


Kwanciya suka yi a bed dinsu suna hira sama sama cikin kankanin lokaci suka saba,Sahil kuwa a bedroom ya samu Sohail yace Islaha fa tazo,ban gane ba? Yace wannan kawar tawa bata gari ba,ni wlh bana so tazo ba ta gari bace,Sohail yace ba komai muyi musaya na baka ta garin Maheera ka bani wannan zan ji da ita ni zan sa ta dawo ta gari,Sahil yace to sai dai haka muyi musaya kawai ni da Maheera kai da Islaha,Sohail yace congratulations ka samu ta gari.


Washe gari Islaha ce ta taya Maheera suka yi girkin tare,Islaha tace muje mu gyara gidan,Maheera tace karki fara ma idan ba so kike masu gidan su ci mutuncinmu su kore mu ba,su Sahil ne suke yi aikinsu ne kuma baka isa ka taya su ba,Islaha tace ni na isa,naga alama tsoro su kike ji.


Sohail ne ya fito Islaha ma bata banbance su ba tace Sahil ina kwana? Sohail yace ba shi bane,Sahil ne ya fito ta shiga kallon su shima tace ina kwana Sahil yace ni yanzu ba naki bane munyi musaya nida dan uwana,Islaha zata yi magana Maheera ta dan taba ta alamar ta amince,Nan take tace to.


Sahil baki ya cuno gaba tare da bare alawa me tsinke ya sa a baki yana tsotsa kamar yaro
kitchen ya shiga ya iske Zayna tana girki,yace yau da kanki kike girki Yaya ta palo? Sunan nawa ne Yaya ta palo ka maida ni tsohuwa ka shiga hankalinka wlh, ae karka dameni bana son munafurci naman kai nake dafawa ogana da hannuna zan tsara shi yanda zai yi dadi,Sahil yace hmm ai kuwa baza ta dahu ba yau,inji uban wa? Na dai fada miki baza ta dahu ba yau,tsaki Zayna taja taci gaba da girkinta shi kuma ya fita,tun 9pm Zayna take dafa naman kai yaki dahuwa har 2am na dare yanda ta zuba a tukunya haka yake ko ruwan romon bai canja kala ba,Zayna ta ja tsaki ta zauna a kujera tare da kifa kanta a jikin Sink bacci ya kwasheta nama yana ta tafa a banza,sai da Adnan ya gaji da jira yazo kitchen din ya tashe ta,tana murza ido tare hamma tace yaki dahuwa Sahil ne dan iska yace bazai dahu ba yayi min kwari.


Adnan gas din ya kashe yace muje haka na hakura,suka fito suka bar nama,washe gari da safe sabo da masifa Zayna ta dawo ta kunna gas ta maida naman kai taci gaba da dafawa,Su Maheera suna ta aikinsu naman kai yaki dahuwa tun tana yi a dadin rai har ta fara tsaki,Islaha tana satar kallonta tana dariya a boye,tace girki sai ai sai mu,na godewa Allah duk da bani da iyaye wacce ta raine ni tayi kokari nasan darajar dan Adam,Zayna ta ja tsaki ta kwashe naman kan tas a leda ta zuba a dustbin,ruwan ta zubar yabi ruwa tayi fatali da tukunyar tare da furta ku gyara min kitchen,ta fice daga kitchen din.


Kasancewar weekend yau da yamma Ibrahim ya fita shakatawa Zayna da Adnan sun fita su ma zasu shakata,sai Twins sai Islaha da Maheera,Sohail yace kar Maheera ta sake kula shi yanzu ta Sahil ce ita,Fitowa suka yi tare da Islaha,Maheera ta zauna a kusa da Sahil,Islaha ta zauna a gefen Sohail,Sahil haushi yaji amma ya danne sabo da Sohail,Shima Sohail haka sai kallon Maheera yake,suna tv game amma hankalinsa na kan Maheera sai cinye shi ake yi,Islaha tace karka damu Sohail ina bayanka i will support you, Sahil da sauri ya Kalli Islaha yana zare ido sai kuma yayi shuru,gajiya yayi ya shiga hararar ta,Islaha ta boye dariyarta tare da kara matsawa kusa da Sohail,tsaki Sahil ya ja ya tashi ya bar palon tare da haurawa sama.


Sohail ya kalli Islaha da narkankun idanuwansa,kansa ya sadda kasa ya lula tunani sai kawai ganin hawaye suka yi yana digowa daga idon Sohail zuwa kasa dis ..dis...dis,Maheera tace lafiya Sohail cike da kulawa,Sohail yana shesheka yana nuna kansa yace kamar ni....ni....kamar ni da Sahil ace abokan mu sai aure suke yi amma mu ko auren kare yawa baza mu samu ba,Auren kare yawa dai ai ko shi ma yi,jiya muka je gidan da Sahil muka ga abokin mu mudassir da matarsa wacce shekarar su daya da aure suna ta fada,muka samu suna ta fada abinsu,dan Allah wannan ba abin sha'awa bane? Ni da Sahil sha'awar fadan nan ya kama mu ace mune amma bazai samu ba.


Maheera da Islaha suna kallon Ikon Allah duk da cewa Maheera ta fadawa Islaha suna da matsalar aljanu ta dinga binsu a haka,Islaha tace kai dan Allah amma sun birge ni.

Sohail yace baku gani ba ya zage ta itama ta rama,sai naji sha'awar aure...saura kadan dariya su Islaha suyi dariya,Islaha tace na zaci ma soyayya kaga ana yi irin ya rungume matarsa suna kiss,Sohail baki ya bude yace Allah ya kiyaye bana fatan wannan baya birgeni sam,har kin sa raina ya baci ya mike zai tafi Maheera ta rike shi da sauri tace zauna muyi magana.
Islaha tashi tayi ta haura sama ta kira Sahil suka zauna a compound kamar samari sunzo zance,Maheera tace Sohail ka tsaya kaji ka saurare ni,yace to ya zuba mata ido ya nutsu.


Tace har yaushe zaku zauna a cikin wannan rayuwar? Kuna da hankali kuna da ilimi kuna da basira,taya zaku tsaya su maida ku yan aikin su kuna abu daya,kuna yan uwan su,wannan fa abin ba me karewa bane Sohail,hannunsa ta rike tace ba sai kun nemi abu ta hannunsu ba Sohail,Allah ya baku lafiya ku nemi aikin yi da kanku ko karami ne,kuyi tunanin zaku yi aure ku haifi yara ku zama iyaye kuma,so kuke rayuwarku ta kare a haka shekara da shekaru kuna bauta musu.


Kuna so kuyi aure ku haihu ku dauki nayin yaranku da matar ku,idan kun tsaya a haka ta ya hakan zai faru,Sohail ku zauna kuyi tunani ku nemi mafita.
Ni wlh na yarda da ku zaku iya Sohail kuna da hali me kyau kuna da tunani kuma na yarda.


Sohail yace kuma ina so na dinga siyawa matata leshi,tace to ka gani ko ai dole ku mike tsaye ku nemi kudi,Sohail yace kin tabbata zamu iya? Maheera tace na tabbatar,yace na gode Maheera da kokarinki Inshaallah zamu gwada,tace to haka nake son ji.
Kirjinta ya kafe da kallo yace wai wannan mene amfaninsa ne? Maheera tace ina ruwanka wai da shi,to sai a dinga budewa ba a saka hijab,dariya tayi cike da kunya tace dan Allah ka daina kallo na,ni nace ki bude ina ruwana kalla zanyi ya furta tare da sake matsawa jikinta.


Yanda Maheera tayiwa Sohail bayanin su fara neman na kansu haka itama Islaha ta cewa Sahil sabo da baki suka hada,Sahil yace zamu yi shawara,tace yawwa Baby ta furta da tsokana,Sahil yatsa ya sa a baki yana tsotsa da shagwaba daga ance Baby, ya dora kansa a kafadarta yana kukan shagwaba Uhum...uhmmm....
Dariya kamar cikin Islaha zaiyi ciwo.


Bayan su Sohail sun koma bedroom ko shirin bacci kasa yi suka yi kowannen su ya zauna a bakin gado yayi shuru ya lula tunanin rayuwa akan maganar su Maheera,kowa da abinda yake sakawa a ransa.
Sahil ne yayi magana yace Islaha ta fada min maganar da ban taba tunaninta ba sai yau,Sohail yace ashe fa ana yin aure a haihu ai na tuna kuma dole sai da kudi,Sahil yace kawai mu fadawa su yaya zamu fara neman aiki ko karami ne a garin nan,Sohail ya furta nima haka nake tunani kawai ayi hakan,suka gama tattaunawa sannan Sohail akan da safe zasu sanar da su Adnan kawai.












AsmaBaffa
[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A
🪸


21-25






Official


By
AsmaBaffa




SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM




Page naki ne
Sadiya Muhammad




https://chat.whatsapp.com/CShgPK2Dsi8GIrvd5njOML


Gaskiyar hausawa da suka ce wata miyar sai a makota🥳💃idan kina bukatar shan wannan miya kuma zaki sha ta mai yawa ma💃🥳Zance ne ake na *R&U EXCLUSIVE KITCHEN AND MORE* Indai kayan kicin ne a kan farashin sari🙌 sadakallahul Azim an gama zance, kayan daki, bedsheets, takalma jaka kayan sakawa maƙura kenan, *R&U EXCLUSIVE KITCHEN AND MORE* nan nake kira da kasuwar ki a hannun ki😘maza masu hada kayan lefe duka *R&U EXCLUSIVE KITCHEN AND MORE* suna maraba. Domin neman karin bayani 07034559202 domin gani da ido taba link ki shiga domin siyayyar kayayyaki a farashi mai rahusa💃😘












Ko wanka basu yi ba haka bacci ya kwashe su da wannan tunanin.
Washe gari da safe bayan sun gama aikin gidan da suka saba,Sohail sanye yake da jallabiya fara shi kuwa Sahil shadda ce a jikinsa milk color, a zaune suka samu Ibrahim da Adnan a garden sun baje laptop da takardu ga lemo a gefe suna korawa suna ta aikin Office,tun kafin su Sohail su karaso Suka hade fuska ba mutunci,bayan sun karaso suna daga tsaye Ibrahim yace "what"? Sohail ne yace dama Yaya mun yanke shawara ne muma muna son mu fara aiki,Adnan da wani bala'i ya dago da lemo a hannunsa ya watsa musu a jikinsu yace me kuke nufi? To wallahi wannan kamfanin ba gadonku a ciki,babu aikin da za a baku kuyi a ciki ku din banz.....kafin ya rufe baki Sahil yana goge rigarsa da ya jika masa da lemo yace relax mu ba a wajen ku muke nema ba,a duniya zamu nema wajen bare da yardar Allah,kawai fada muku muka yi,Adnan dariya ta kwace masa,Ibrahim ma dariya ya saki yace Allah ya bada sa'a aje a nemo aiki mu gani.


Sohail da Sahil suka juya abinsu tare da tafiya dakinsu suka hada takardun su har wanda suka fara a kasar waje,Wanda bashi da amfani sai in zaka ci gaba da school ka kai makaranta,Sahil zama yayi da biro a hannunsa ya fara rubuta takardar neman aiki.
Yana ta rubutunsa harda furta i can do it Sir.....yes....zan iya mana zan iya ,ci gaba yayi da rubutu i have power, Sohail yana ji yace kai turanci bai hau ba Man power zaka saka kace i have man power, Sahil ya rubuta i have Man power, Yanzu kayi turanci cewar Sohail,suna ta rubutunsu suka gama tare da zuba takardu a cikin folder sabuwa.


Wanka suka sha kowannen su farar suits yasa tare da gyara gashinsu ba karamin kyau suka yi ba sai ka rantse masu hankali ne,suna kamshi suka fito lokacin Islaha da Maheera suna gyara palo,Islaha tace sune zasu yi aikin kuma ko an kore su baza su tafi ba su kam sunga gidan zama.


Tsayawa suka yi galala suna kallon twins sun watso kyau,Zayna ce ta fito tana shan tea a hannunta,ita kanta sun tafi da ita ta tsaya tana ta kallon su a sace a ranta tace ina ma daya ne a ciki mijina,tunowa tayi basu da kudi sai ta tabe baki tare da jan tsaki ta juya inda ta fito.


Islaha tace ban taba ganinku kunyi shiga haka ba kunyi kyau mashaallah,Sohail ne yace mun gode kin tabbatar munyi kyau? Islaha tace sosai ma yau mata sai....Sahil ne ya katse ta karki dami mutane,Maheera kallon Sohail tayi taji kamar kar ya fita ma yayi ta zama a gida,Haushi taji ta bata rai,Sohail yace baki ce komai ba tace me zance sai kun dawo Allah ya bada sa'a a samu aikin suka ce Ameen,wucewa zasu yi Sohail ya ja hancin Maheera yace kefa kika ce a nemi aiki kuma sai kiji haushi sabo da zan fita ko so na kike yi ne? Maheera da sauri tace ni haka nace ina sonka? Allah ya kiyaye aljanun karya suke yi da suka fada maka,Sohail dariya yayi yace shike nan dama ni Islaha nake so ba ke ba,Maheera ta dauke kai,Sahil yana jinsu yau yan maganar basa kansa ko uban waye in baiga dama ba bazai kula su ba ko me zaka ce,Haka suka fita Maheera ta zauna a saman kujera ranta a bace.


Islaha ta sheke da dariya tace lallai Maheera kina da aiki kuwa wlh,idan kika ce kar su fita ma ai bakya kaunar su aiki fa zasu nemo,Maheera ta mike bata ce komai ba suka gyara ko ina na gidan komai sai da suka yi.
Ibrahim ne ya fito sai faman kallon Islaha yake kamar maye,Islaha tana sane da shi ta kalle shi suka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login