Showing 57001 words to 60000 words out of 76019 words
tunda ai zamuyi maganar aikin ko? Sahil ya zauna yace kawai dai dan kaine ni ba a son raina ba gaskiya,Sohail yace ni zan tafi a taxi kai ka dawo a motar, Sahil yace ko kace ma na dawo a taxi baka isa ba sai dai ka bar motar a nan,dariya Sohail yayi ya tafiyarsa yana cewa Ogan Daddy ka gaida gida mun gode,Alhaji Umaru yace madalla,ni bana gane su ma sam.
A nan Alhaji Umaru yace da Sahil ka shirya tare zamu tafi Lagos a jirgi,Sahil dai ba a son ransa ba amma idan ya tuna ance Islaha tana can sai murna.
Sohail sai da ya tsaya ya yiwa Amarya siyayya na kayan ci sosai sannan ya koma gida,taci sabon wanka na daban yana shugowa ta rungume shi,Sohail kallonta yayi kawai bai ce komai ba,Maheera ta furta ya baka yi magana ba? ya zanyi dake kin zama fitsararriya sai ciwon kai kike sa min,Maheera murmushi ta saki suka zauna ta karbi ledar tace duk nawa ne wannan? Sohail ya daga mata kai sama alamar ae,tace na gode Allah ya kara budi,yace ameen Islaha dai tana can tana walagigi da bata tafi ba ai da tuni itama ta zama babbar mace,Maheera tace zata dawo Inshaallah wlh kullum sai na gwada kiranta bata shiga.
Maheera ta kalle shi yace menene? tace ina tunano sanda zan haihu a gidan nan,Sohail ido ya zaro,tace ei mu cika gida da yara abinmu,Sohail yace ki cika gida da yara? Me zanyi dasu? kiwo zan dinga kada su da sanda ko me,ni baza a haihu ba ya furta,Maheera tace Sohail shine auren, mu da ba ayi haka ba ai baza a haife mu ba,burin ko wanne ma'aurata kenan,Sohail yace sanda za a haifeni da na sani ma ita me haifar tawa tun ina ciki zamuyi mutuwar kasko da ita,dariya ta kama Maheera kwanciya tayi a jikinsa,ya gaji da halinta kyaleta yayi.
Kwanan Alhaji Umaru biyu ya tafi da Sahil Lagos,suna zuwa garin aka fada masa layin da Islaha take,Alhaji Umaru tun a hanya cikin motar da driver ya dakko su a Airport yaga Sahil ya canja duk hankalinsa ya tashi,yace lafiya kuwa? Sahil yace budurwa ta wajenta zanje dan Allah ka sauke ni,zanzo gidan naka anjima,Alhaji Umaru bai musa masa ba ya bashi katin gidansa yace ga Address ka shiga taxi ka mika katin za a kawoka,Kudi ya zaro da yawa ya bashi,Sahil ya karba yace na gode,driver yana parking ya fice da sauri ko jakarsa bai dauka ba,Alhaji Umaru suka ja mota sai gida.
Sahil sanye yake cikin kana nan kaya Navy color ya sha kyau yana tafiya a kafa ya gaji ya hau machine,sai kace aljani har layin da Islaha take siyar da abinci amma bai san ina ne wajen ba,basu nuna masa ba,tafiya ya dinga yi yabi nan yabi can shuru.
Islaha kuwa ta gama jera abinci ta manta da lalitar saka kudi ta koma gida ta dauro ta a saman cikinta tana tafiya a hankali ta harde hannayenta a baya tana sanye cikin riga da skert yan kanti da siririn mayafi a kanta,tana tafiya tana walagigi a hanya ga rana,a hankali take tafiya,Hajiya Kulu ce ta iske ta a hanya tace ke Islaha koma gida ki kula da bakin nan da nayi ban san halin su ba kar su dankara min sata.
Daga nan Islaha ta juya gida tana tafiya a hanya tana ta faman tunanin Sahil,tsaki ta ja tace kai bazan iya ba Abuja zan tafi gobe wlh,wayarta ta kalla kamar ta kunna sai ta fasa kawai.
Sahil kuwa har wajen da Islaha take siyar da abinci yaje ba kowa sai Hajiya Kulu,tsayawa yayi a wajen yana ta faman kalle kalle,Hajiya kulu ta kalle shi tace Alhaji wa kake nema ko tambaya kake yi ne? Sahil ba komai kawai ya furta ya juya ya bar wajen.
Kamar ya dora hannu a kai ya kwala ihu haka ya juya gashi ba wani bayani da aka sake masa,Taxi ya shiga ya wuce gidan Alhaji Umaru.
Islaha kuwa shiri tayi tace gwara ma naje can Abuja kawai na huta sai dai kawai su ganni ba zato,zuwa yamma bayan Hajiya Kulu ta dawo Islaha ta sanar mata zata je Abuja gobe,Hajiya Kulu tayi murmushi tace yan mata ba kunya za aje wajen saurayi to idan kinje kun shirya dai ki dawo yafi mutunci ya dinga zuwa zance,Islaha tace ae ai dama.
Bangaren Sahil kuwa yana zuwa gidan Alhaji Umaru a lekki gidane duniya guda Aljannar duniya sai ka bace a gidan sabo da girman gidan,duk wani alatu akwai,iso security ya masa kasancewar an san da zuwansa me gidan ya fada musu.
Har palon Alhaji Umaru katafaren gaske in banda kamshi da sanyi ba abinda ke tashi,Kujera ya nema ya zauna ba kowa a palon sai shi daya,can bayan kamar 5mnt sai yaji karar takalmi me tsini an shigo palon,kallo daya yayiwa wajen yaga wata budurwa ce kyakyawa da ita baka ce amma tana da kyau da diri mashaallah,skin dinta me kyau sosai.
Sanye take cikin wata Jallabiyya fara ta mata wacce ake yayi me tsada ta mata kyau matuka,takalminta da mayafinta black,tayi acuci ta nada,Sahil take ta faman Satar kallo,a ranta tace wow,ban taba ganin me kyan wannan ba tunda nake a duniya,suturar jikinsa ta kalla ta wayance da duba abu a palon kamar tayi mantuwa.
Gyaran gashinsa ta kalla tace ya Allah guy ne wannan na karshe ya iya wanka,dama da irin wannan a duniya?,ko kallonta Sahil baiyi ba,wayarsa ya dauka sabuwa Iphone wacce Sohail ya siya musu,Sohail ya kira a waya ya fada masa sun sauka lafiya,Sohail Alhmdllh film nake kallo sai anjima mayi magana ya kashe wayar tare da maida hankalinsa kan tv..
Maheera ce ta samu rana Sahil yayi tafiya Bum short ta saka da wata matsiyaciyar riga,shine ta fito ta wuce zata je kitchen har tafiya ta canja Sohail a ransa yace sai kace yar American film,fitowa tayi dauke da cup da lemo a ciki,kafin ta karaso ma Sohail yanzu ya saba a jikinsa take zama har ya gyara sai yaga ta zauna a gefensa amma sai da ta dora kanta a kafadarsa yace ai nasan ya zama dole ,Murmushi tayi ta mika masa lemon ya karba tare da furta na gode,Maheera tunawa tayi zata goge kayanta data wanke a washing machine,tashi tayi ta kwaso su ta jona ion,mikewa yayi yace kawo na goge miki.
Bai taba taya ta aiki ba tunda tazo sai yau,suna tsaye a wajen gugar yana ta mata guga a saman abin guga,ta bayansa ta koma ta rungume shi hannayenta ta saman kirjinsa,Sohail yace karki taba min nono na,dariya tayi inda ya saba da halin Maheera har ya gaji ya daina fada kyaleta yake yi,a haka yake mata gugar,sai da ya kusa gamawa yace na gaji karba tayi taci gaba da gogewa ya koma ta bayanta ya rungumeta,dariya tayi tace ai ba cewa nayi ka min ba yace ai na zaci karfi ake karawa na aiki shi yasa na miki ki goge da yawa.
Hannayensa ya maida saman kirjinta Maheera a ranta tace ya fara ganewa,kasa gugar tayi tace na gaji sai anjima a karasa,Sohail ya kalleta yace sannan ya dora bakinsa a kunnenta yace ke dai kice kin kasa ai na zaci ke jaruma ce,ki daina raina ni nasan me akeyi" cizonta yayi kadan a kunne,yar kara tayi tace da zafi fa tana shagwabe fuska dariya suka.
zama suka yi a kujerar dake palo Maheera ta kyale shi ya huta.
Sahil shi dai ko kallon budurwar baiyi ba yanda bata kulashi ba shima haka,wata Babbar mace ce ta shigo sanye cikin kaya na alfarma doguwar riga ce a jikinta yar kasar Dubai,sallama tayi Sahil ya kalleta,zama tayi da fara'a tace sannu da zuwa samari,Sahil da girmamawa ya gaida ta, tace ya hanya barka da zuwa,yace yawwa kawai,Me aiki ta kira tace ta kawo masa abinci da kayan sha,Sahil aka dinga jera masa kayan abinci a gabansa yace Mama ya isa haka,ya daga zuwana za a cutar dani" idan ba so kike cikina ya rude ba wanne zanci wanne zan bari a ciki,Dariyar Hajiya Suwaiba tayi tace duk sai an kawo ka zaba ai,Sahil yace yanzu haka kuma idan ba a cinye ba zubarwa zaku yi ko ga wasu can bayin Allah suna kwana da yunwa,tace ai akwai masu aiki.
Budurwar ta dawo jikin Mamanta ta wani lafe ta zauna ta kwanta a jikinta,Hajiya Suwaiba tace kin gaida bako kuwa? Sai lokacin tace ina yini, Sahil lfy ya furta kawa,sai da Alhaji Umaru ya fito sannan yasa aka raka Sahil dakinsa yace a kai masa abincin can ya huta tukun haka aka yi kuwa,sai bayan yayi wanka yaci abinci sannan zuwa dare ya koma part din Alhaji Umaru.
Washe gari Islaha tana idar da Sallar asubah ta shirya tsaf ta yiwa Hajiya Kulu sallama ta wuce tasha ta hau mota abinta sai Abuja,sai da suka kusa zuwa ma sannan ta kunna wayarta amma bata kira kowa ba,Bangaren Sahil kuwa shi da Alhaji Umaru ya kira shi,da takardu suka zauna duk wacce ya karanta ya fassara sai da yayi sharp sharp,ya cike duk abinda ya dace,Sahil yace to da abaya ne sanda bamu girma haka ba babu abinda zan iya karanta maka,Alhaji Umaru yace sauki ya samu ashe,dariya suka yi.
Washe gari da safe suka karasa aikin nasu Alhaji Umaru yace Sahil kai baza kayi auren ba? Sahil yace zanyi mana watarana,Alhaji Umaru yaji dadi ya furta, kaga 'yata? Yace na ganta wata marar tarbiyya bata da tarbiyya, Alhaji Umaru yace wlh rashin ji ne na yaran zamani ana mata fada daidai gwargwado,Sahil yace bakwa cin ubanta shi yasa ta fi karfinku, ya sunanta ma? Alhaji Umaru yace Amatullah,Sahil yace ai da kun sani Harira kuka saka mata tafi dacewa da sunan,Alhaji Umaru yayi dariya yace ita kadai na haifa a duniya,ina so ta samu tsayayyen namiji me Amana wanda zai tsaya mata ya kula da dukiyarta ko ba raina.
Sahil yana ji yace Allah yasa ka samu me Amanar a zamanin nan,yanzu tsayayyun maza sun kare a duniya sai irinmu lusarai masu matacciyar zuciya,wai dan kar ace ya aure ta,yaci gaba yanzu dan ta'adda mutum daya da zai zare wuka duk guduwa zamuyi,a gaban mutane a gari da rana zaka ga ana kwacen waya da sauran su amma ba me iya katabus sai kallo shi dai tunda ba kansa bala'in ya fada ba babu ruwansa,ai mu yanzu a kasar nan mun koma idan jifa ya wuce kanka to ya fada kan uban kowa, kayi addua kawai Allah ya bata na gari, idan zata ta mike ma ta mike ta kula da dukiyar tata da kanta,what man can do woman can do better,ai yanzu mata ma sun jajirce sun daina kashe zuciyar su,tunda kace har phd ne da ita ai bata da matsala ba sai ta samu miji me kular mata da dukiya ba.
Alhaji Umaru yace ai bata da wayo ne bata san ta duniya ba sam bata san rayuwa ba,Wannan laifinku ne ku kai yar banza kauye a bata horo me tsanani,Alhaji Umaru dariya yayi duk ta inda ya bullo Sahil yana da amsa,gajiya yayi yace kai me zai hana ka aureta wlh zan baka ita,ni na yarda da kai na aminta da kai.
Sahil yace gaskiya kana sona Ogan Daddy,kuma naji dadi,banga wanda ya ganmu ya so mu haka ba, ka bani aiki a halin da nake ciki kuma ka yarda dani,baka kasan waye ni ba kace zaka bani kyakyawar yarka na gode Allah ya saka da Alkhairi amma kayi hakuri wlh ba wai ina kin jininka bane na riga na bawa wata zuciyata yanzu haka tana wajenta babu wacce zan bawa Amatullah, Alhaji Umaru murmushi yayi yace na fahimceka kuma ina maka murna amma namiji ai mijin mace hudu ne,bayan ka auri zabinka zaka iya auren Amatullah ba damuwa,Sahil gumi ya goge yace ni dai Islaha masifaffiya ce baza ta yarda ba gaskiya,bazan ma iya adalci ba,ni bani da adalci,Alhaji Umaru yace kana namijin? Sahil yace ni Azzalumi ne gaskiya zan zalunci yarka,kawai a bata wani ba tsayayye bane ni.
Alhaji Umaru dariya ta kamashi yace wannan gaskiyar taka yasa zan baka 'yata ka aura...da sauri Sahil yace ni bani da wata gaskiya makaryaci ne,karya ce dani,Alhaji Umaru yayi dariya yace tashi ka tafi time din Flight dinka yayi amma ka sani kana da budurwa a nan ta biyu da zaka aura,kasan kuma idan na fadawa Daddy ko baka yarda ba sai dai kaji an daura auren,Sahil yace zata sha saki kuwa a ranar nidai ba ruwana, ina da budurwa fa,Alhaji Umaru a ransa yace a hankali zaka so Amatullah ne na riga na fahimci halayarku a hankali kuna ganewa,Shi dai Alhaji Umaru Sahil ya cancanta ya auri yarsa a wajensa.
Sahil bangarensa ya koma sai da ya karya yayi wanka ya fito cikin wasu kana nan kayan fadar irin kyan da yayi bata lokaci ne,part din Alhaji Umaru ya shiga ya same shi a palo tare da yarsa Amatullah sai shagwaba take yi, yace Sahil ka dage kai gida zaka tafi? Sahil yace papers din duk ba nayi abinda kace ba? ai mun gama kace zaka kirani idan wanda zamuyi aikin tare zaizo ko? Alhaji Umaru yace ae ai nufi na ka sake hutawa amma abinda ya kawo ka an gama shi tun jiya da dare,Sahil murmushi yayi yace nidai tafiya zanyi indai da wani abu kawai ka kirani,yace ai Abuja zaka yi aikin karka damu naga baka son Lagos.
Sallama ya masa,Amatullah harda cewa Yaya Sahil ka gaida gida sai munyi waya,Sahil yace ni bani da kanwa mace daga ni sai Sohail,Amal ce kuma yayar mu ce itama,Juyawa yayi ya tafiyarsa.
Sahil da kudade masu nauyi ya wuce airport driver ya kaishi,Alhaji Umaru ne ya tura masa,Sahil ya tambayi driver yace me ake siya a garin nan na tsaraba? Driver yace hausawa ai in zasu koma doya suke siya sai manja,da kwakar manja,coconut da garin kwaki shi zaka ga suna siya har Egusi suna siya.
Sahil yace kaini inda ake siyarwa,driver ya kaishi doya kadai ya siya ta kai guda ashirin manya,dankalin turawa ma da yawa, ya siyi egusi da yawa shima sabo me kyau,har garin kwaki wurin kwano uku ya siya,kwakar ruwa tafi goma,har kwakwar manja,yaga guava masu kyau ya siya,tarkace ya siya,ya kashe kudi sosai yace shi fa ba tafiya zai iyayi da su ba sai dai a sa a mota a kai can ya karba a Abuja,kayansa aka shirya masa waje daya aka saka a mota ya biya kudin kaya motar ma ta rigashi tafiya daga Lagos zuwa Abuja.
Yana hanya Islaha ma tana hanya a lokacin.
Ya riga ta zuwa kasancewar ita a mota ne,yana komawa Maheera ta bude kofa yace Amarya kina wulakanci a gidan nan karki kashe min dan uwa da wanka,dariya tayi Maheera tace ina tsarabar? Sahil yace ni ban taho da komai ba amma na sa a mota za a kawo in sunzo zasu kirani naje na karba,me ka siyo? idan an kawo zaki gani ya wuce dakinsa,Islaha sai gaf da magriba ta sauka,tana zuwa gidan su Adnan ta wuce,knocking tayi,Madam Oge ce ta fito tare da bude kofar tace can i help you? Ibrahim ne ya leko sai yaga Islaha yayi mamaki,yace ina kika shiga zuwana garinku sau uku kin gudu,Islaha tace ni ba wajenka nazo ba ina Maheera?
Ibrahim yace ta mutu,kyale shi tayi ta zaro wayarta zata kira Maheera yace muje na kaiki gidansu ma, tace idan kasan wasa kake ka kyale ni,yace ba wasa ai tayi aure,Islaha tace aure? da wuri haka har tayi aure har yaushe na bar gidan,wa ta aura?Ibrahim yace muje na kaiki,motarsa ya bude ta ajiye kayanta a baya ta shiga gaban mota yaja suka tafi.
Magana ya mata yace yaushe zan kai kudin aure ne? Islaha ta masa shuru,yace ke yanzu kinfi son mahaukaci sabo da kyau? tana jinsa yana ta zagin su Sohail tace wai wacce irin rayuwa ce wannan taku dan uwanka ubanku daya amma ku dinga irin wannan,wacce irin kiyayya ce haka,me suka muku? aji tsoron duniya gaskiya,banza ya mata sabo da kishin da yake taso masa.
Har Estate din Sohail ya kai Islaha a kofar gidan yayi parking yace sabo da son da nake miki na kawo ki amma badan haka ba babu abinda zai kawo ni,tana zaune a motar tace dan Allah ku daina yi musu haka yan uwanku ne fa,suna haka Sahil ya fito cikin motar ya kalla,kamar Islaha ya gani,gaban motar ta bude ta fito,Ibrahim yana ganin Sahil yayi murmushin mugunta,motar ya bude ya fito Islaha ta dauki jakarta ita kanta ganin Sahil wai haushinsa take ji ya koreta sai ta juya tana yiwa Ibrahim magana harda kirkiro dariya.
Sahil yana ganin haka ya wuce abinsa har ya tafi ya kasa hakura ya dawo, Ibrahim sai damka yaji kawai ya shake shi,kamar zai kashe shi,sai kakarin mutuwa yake,da hannu daya kacal ya shake shi amma sai da ya raba shi da kasa ya daga shi cak,Islaha ta saki ihu tana neman agaji,ga unguwa ba mutane,wasu samari ne suka ga abinda ke faruwa,idon Sahil ya canja sai huci yake jikinsa yana rawa,agaji suka kawo da kyar aka kwaci Ibrahim a hannun Sahil,Ibrahim yana hakki yana shafa wuyansa yace ni ka yiwa haka kana kanina? Wlh sai kasan kayi min haka, Sahil tsaki ya ja yace duk abinda zaka yi kayi,Ibrahim zai sake magana Sahil ya nufi inda yake,ai da gudu ya zaga tare da fadawa motarsa ya ja ya bar wajen a guje,yasan karfin aljanu ne da su yanzu sai su illata mutum a banza.
Islaha ya kalla ta kalle shi tsoro taji