Showing 48001 words to 51000 words out of 76019 words

Chapter 17 - MUMMUNAR DABIA PDF BY ASMA BAFFA

22 Aug 2025

286

san Aisha sosai.


Tunda aka saka bikin Amarya ta fara gyaran jikinta Komai Aunty Aisha tace a bayar amarya tayi ta dage sai gyara amarya akeyi da kudin Sohail,Maheera Amarya ita murna take in ta tuna Sohail zata aura duk haukar nan ko a jikinta.
Kullum gwada number Islaha take ko zata same ta amma shuru bata shiga sam.





Free page 400 1&2


0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank




*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*








AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:18 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸


36-40




Official


By
AsmaBaffa




SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM




Page naki ne
Ummu Lateefa






*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*




MASU AUDIO BAN YARDA A SATAR MIN NOVEL BA IZINI NA BA





Maheera tana gwada kiran Islaha tace amma Islaha zuciyar tata tayi yawa da nice bazan iya bama sam, karfin hali barawo da Sallama daga yar magana shike nan wannan wacce irin zuciya ce haka,kin koma gidan ku ma ki bude wayar mana,sai taurin kai haba,mutane kin san ba wasu lafiyayyu bane ki dauki zuciya da su.
Kiran Sohail ne ya shigo wayarta a nutse ta daga harda gyara murya tace Ango,Sohail yana Office a zaune ya kasa aikin komai akan zaiyi aure,shi ba ma wajen wahala yake ba amma dan signing da sauransu na shige da ficen kaya sam ya kasa,Ya aiki? Maheera ta tambaya,ba yi nake ba da me zanji aiki sun min yawa ni,nauyi ya min yawa gaki ga Office,a baya kuwa ba ruwana sai naga dama nake kiranki,yanzu kuwa idan ban kira ba haka kike cewa na daina son ki,gashi ance za a daura aure ni na rasa wanne zanyi wanne zan bari daga ciki,ga dinki an kai,Aunty tace na koma wai an gama lefe gida nawa ake so na kasu.


Maheera dariya ta dinga yi tace dan dan wannan shine ya maka yawa? Yace ana cikin haka Adnan ya kirani wai kudina basu kai na rike mace ba,Daddy ya fada musu zanyi aure wai ni bana shawara da su me yasa ba a fada musu ba,anbi an dameni ni.


Murmushi tayi tace to Sohail idan munyi aure baka fada min aikin da zaka dinga tayani ba,kasan maza suna taya matansu aiki,Ashe zaki fitsarin man kuli,na zauna ina tayaki aiki duk kudina sun kare a kanki ko fili ban siya ba,ki kyale ni ma naji da accnt dina da yake rarakewa gaba daya kin cinye min kudi tunda nace ina sonki shike nan kullum accnt dina kasa yake yi,dama ba wani kudi ne da ni ba,sai na gama wannan, sannan tun yanzu har kin kawo zancen aikin gida,mijin tace kike so na koma,in kashe miki kudi inje Office in dawo in miki aiki lallai kina da aiki,nifa baki isa ki juya ni ba, ki sani ma da saninki karki soma, zamu yi mummunan fada,kin ma rainani.

Maheera tace daya fa na fada sai faman zuba kake yi daga nace ka tayani sunna ce fa,Maheera gyaran jiki ake mata ana ta dirje mata fata,da zafi ta furta Sohail yana ji a waya yace Allah ya kara sai da nace karki yi na taba gani an yiwa mama Asmau bata ji dadi ba kin tafi za ayi miki,Maheera tace wai duk ba kai ake yiwa ba,da sauri yace a'a a'a ba ruwana, kike yiwa kanki dai.


Ba abinda zai amfane da shi kin san dai sai Sahil yayi aure koma mene sai ayi,Maheera tace jiransa za ayi kenan? Sosai ma,kasa tayi da murya ni kenan bazan samu ciki na haihu ba,auro ki nayi ki haihu dama? ni sabo da tunaninki da nakeyi yasa zan ajiye ki a gidana kinga na huta tunda kullum zan ganki,dariya tayi tace Allah dai ya kawoni duk wannan tsarin naku sai na rusa shi .


Mu fa taurin kai ne da mu ki kyale mu kawai inda kika ganmu,Kamar Abun arziki ya kira sunanta "Maheera"amsawa tayi na'am,Allah ya miki iyayi da shishigi sai kace Aunty Aisha,ki ta tsara zance ke ga masaniya me sani,shi yasa Sahil yace Islaha ita yar oya oya ce ke kuwa in kika dinga tsara magana kice wannan kice wancen ke dole sai kin dora mutum a hanya ga shegen iyayi,magana ma wani a hankali kina fari watarana kamar na mareki,dariya Maheera tayi duk yangar shi ake yiwa amma wai ba a birge shi ba,takaici ya kama Maheera ta tuno dogon lokacin da ta dauka tana matsawa kanta sai ta koyi dan iyayin nan da fari da sauransu na wayewa take ta faman yi ashe shi bai ma san ana yi ba haushi yake ji.


Tace na daina daga yau Inshaallah zan dawo yanda nake zaka ga iskanci tunda haka kace har nunawa nake ina kara zama ta gari dan a soni ashe shi ba ruwansa ta furta a ranta,a fili tace
Za ayi dinner? Ta furta ya maganar Dinner? Sai bikin Sahil,komai ni ba a min ba sai bikin Sahil bana so,gaba ta kaini cewar Sohail ya kashe wayarsa.


Sahil ne ya shigo Office din yace me kake yi haka ne kazo mu tafi,Sohail yace soyayya na sha ta kashe min jiki,Sahil yace uhm gori zaka min sabo da ni bana yi? Ni nace budurwarka ta bata,Sahil yace bata bace ba Inshaallah zata dawo,Channel din da Sohail ya nacewa ta wa'azi ita yake saurara,Malam yana wa'azi yace matarka kuyi wanka tare ka cudeta ta cudeka,Sahil yace ga bangaren ku nan masu aure,Sohail yace ashe za a ayita ni na tsaya Maheera taga tsaraici na ai na shiga uku kuma baza ta sake jin magana ta ba,dama kana ji yanda take min wasu tambayoyi na raini tace wannan tace waccen,Sahil yace Allah kuwa yarinya iyayi haka,aini kawai in tana magana zuba mata ido nake sai ka lalace a kallonta ko ina na fuskarta sai ta motsa shi ,Sohail yace ashe kaima ka gani ko banyi niyya ba sai na bata kudi,Sahil yace ahh ko ni na bada kudi irin wannan magana haka me style.


Sohail yace kai kuwa Islaha ce kullum a shirin ko ta kwana take kana kallonta kasan bata da mutunci,Sahil yace 'ya'yana sun shiga uku na tausaya musu zasu ci duka nidai nafi karfinta sai dai ta yiwa yaranta,Aunty ma data riketa bata isa dani ba,ni zasu ce zasu kai yawon shakatawa,a cirani ban samo komai ba sai mata da suka rainani ba abinda na tsinta,da wasa bana son jin sunan lagos a rayuwata.
Sohail tv ya kashe yace muje a karbo dinkunan biki,Aunty Aisha ta sa munyi dinki da yawan gaske,Sahil yace sai kace mijinta dinkawa yake,ta damu mutane sutura itace mutum sutura itace mutun amma ta bar mijinta da dinkin buba falau a gari,dariya suka yi Sohail yace oga ai har Boubou ta mata ma zai iya sawa yaci kai ai.


Da dinkunan biki suka koma gida,Ibrahim da Adnan sai bacin rai suke yi wai Sohail da suka fi rainawa shine ya samu aiki har ma zai riga Ibrahim Aure,Ibrahim yace da ace ina da hali wallahi sai na hana auren nan,takaici wai kamar Sohail zai auri Maheera guda wannan ai matar manya ce,Adnan yace ko wajen bazan je ba bare nace Allah sanya Alkhairi,Amal ma baza tazo ba babu me tayasu biki gashi basu da uwa ba dangin uwa,dangin Uba kuma tsoron tonon sililinsu suke yi ba me zuwa,Ibrahim yace duk na buga musu waya nace kar wanda yazo ba a gayyar kowa,sai Kawu Nafiu da Tukur naji su sunce da su za a daura dole,har kudi na tura musu cin hanci kar su zo amma sunce sai sunzo.
Adnan yace nima na kira kawu Tukur nace kar suzo yace Twins ne suka tsorata su sunce bulalai zasu sha idan basu zo anyi komai da su ba wai hanyar lafiya a bita da shekara.
Amal ma tunda taji biki taji ance wai Sohail ne da gida guda ga motaa hankalinta ya tashi,gashi mijinta ya hanata zuwa Abuja sunyi fada akan ya biyawa kishiyarta makka a boye yanda Sahil yace.

Biki yana ta matsowa su Sohail sunyi gayya sosai duk mutanen su na kano da abokai tunda a can suka taso an gayyace su basu manta ba,wasu ta waya wasu ta Online wasu da katin Iv, Maheera ranar Friday zata yi yini da kamu shike nan,ranar asabar a daura aure a kai Amarya.


Duk wanda yaga Iv din su Sohail sai yayi dariya sabo da iyalan Marigayi Alhaji Ali aka saka,Late aka saka a jiki akan baya musu komai suka ce a saka Late kawai,Shi kanshi Daddy din ko iv din ma basu tura masa ba a duniya ya gani.


Ya kira Sahil yace da raina da lafiyata ku kashe ni ku saka min Late dan ubanku, Sahil yace ayi hakuri kuskuren computer ne, computer ce tayi karya,da aka je bugawa ne anyi anyi ta saka kana raye kai rayayye ne taki yarda tace marigayi ne ya za muyi ,Adnan ai nasu yasa kana raye ga Ibrahim ma nan gaba zai sa kana raye mene abin damuwa to,ga su Adnan mu ai a barmu a mahaukatan mu,Daddy yace magana zaka fada min? a'a ni na isa mufa bamu ce sai kazo daurin aurenmu ba kayi zamanka ka zuba yawunka a can cikin shara ko ba yawunka za a daura,ba dole bama a sa maka Late tunda an rasa inda ka nufa yaranka ne mu ba yaranka bane tsintar mu kayi oho,cikin shege ne mu oho,idan ka fadi gaskiya waye zai tsire ka?.
Kai dan Allah rufe min baki shashashu mahaukatan banza ya ja tsaki ya kashe wayarsa.


Twins dai gashi suna ta yada Iv duniya ta san Alhaji Ali sosai,duk wanda ya gani ya dinga mamaki yaushe ya mutu,dama ya mutu ashe ,sai kiransa akeyi a waya ana tambaya sai aji yana raye.
Bangaren Amarya sunyi anko kawaye komai an shirya shi Sohail ne ya kama musu event center da kudin Alhaji Saminu da ya bashi gudunmuwa.
Alhaji Saminu da abokinsa sai Sahil su suka kai lefen Sohail akwati guda takwas komai me kyau aka zuba,Maheera sai murna take yi bata zaci haka ba.
Sai kiran kawaye take a waya suna tururuwar kallo ana ta yabawa, a cikin kawaye wata ana ce mata Saddiqa ta faki ido ta sace sarka me kyau,dama wasu kawayen da biyu suke zuwa.

Sun fito zasu bar gidan sarka tana jakar Saddiqa Maheera ta rako su sai ga Sahil yazo,Saddiqa ya kalla yace mayar mana da Sarka dan ubanki dake za'a hada a aura da zaki sace mana sarka,Saddiqa tsoro ya kamata da ace a cikin kawaye ne sai ta rantse ta ganta sanda ta dauka,yace ki zazzage jakarta ki karbi sarka idan ta tafi da sarkar nan ke kinsani,ya fadawa Maheera.

Maheera ta fisge jakar Saddiqa ta zazzage sai ga sarkar me kyau a cikin gidanta,mata suka fara sallallami da cakaki,kunya ta lullube saddiqa ta kwashe jakarta da kayan ciki ta fice da gudu tana dana sani.
Maheera ya mikawa kaya a leda yace gashi nan daga wannan karki sake cewa a karbo miki dinki sabo da ni kike jawowa yana cewa na kawo miki,Maheera dariya tayi tace to mene,ai ke kika ziga shi dama, ya shiga mota ya tafi.


Maheera tana ta shagalinta kamar zata kai kanta gidan duk da tasan matsalar da take gabanta ba ruwanta soyayya ta rufe mata ido,Mama ce ta kalleta ta hana kanta sakewa sai faman shagali take shiryawa,ana cewa Amarya sai fara'a da murmushi,duk inda ta zauna sai ta bada labarin halayen Sohail masu kyau.


Kawayenta ne mutum biyu suka zo wajenta Maheera tana tsakiyar su daya tace Amarya,Maheera tace na'am wlh idan kuna fada sai naga kamar mafarki,har cewa nake zanyi aure kuwa a duniya anya,to gashi cikin lokaci kadan Allah ya kawo har lokacin ma na nema ya kure mu,kawar tace ai haka ikon Allah yake.
Maheera tace hmm ai kamar wasa muka fara kawance ba sai soyayya ba,muka fara love gashi ya iya kula da mace baya son raini kuma amma akwai caring ku kunga yanda yake min,ga kishi ban isa na dinga fita anyhow ba,Kawaye suba ta jin labari harda cewa wayyo ke kama kin tsallake.


Maheera ta durawa wata kawarta ashar yar burar...Walida har magana take fada min akan zata yi aure wai ta barmu da zaman kan layi kiji shegiya,tazo taga mijina wlh kamar bature,bari ku ganshi dan dai kawai na yarda da ku zan nuna muku shi,ta jawo wayarta ta nuna musu Sohail tace kalle shi,yan matan suka saki shewa gaskiya kin dace,Maheera har da wani gyara baki tace in fada muku badan yana Office ba da yanzu zance yazo ku gaisa,to a isar mana da gaisuwa cewar dayar kawar.


Ana zuwa ganin lefe haka Maheera take zakewa tana nunawa,wasu mata dangi sunzo Juwairiyya tana nuna musu Maheera cewa take baki bude musu akwatin takalman ba,a nuna musu na kayan baccin,suna daga kayan tana cewa wannan fa material ne Aunty Sa'a amma a haka kamar shadda,Mama tana jinta har ta gaji da halin Maheera rashin kunyar da take,idan kuwa Sohail ya kira waya ko su waye a gaban su zata ce Sweet ne miko min wayar ta tashi da gudu ta shige daki.


Mutanen suna tafiya Mama tace Maheera abinda kike yi ya isheni,a haka a ganki shuru shuru kamar kin shiryu kin nutsu amma sai rashin kunya kike yi,a kanki aka fara aure yau ni naji tsiya, ki taka a sannu wlh angon nan naki kin san irinsa amma ke ko a jikinki naga ma kunyar ma kin daina a gaban kowa nunawa kike murna kike yi zaki aure ki huta.


Maheera tace ba abinda zai faru sai Alkhairi Mama ki dinga addua fata na gari lamiri,Mama tace hmm kina dai ji yace sai ya jira dan uwansa babu abinda zai shiga tsakani in banda ba hankali yaushe za ayi haka,Maheera tace nifa zan iya rayuwata haka ba komai ba sai anyi komai ba dama ni ban san komai ba me zai dameni zan iya kare rayuwata a haka,dariya kawai Mama tayi tace baza ki gane bane bakya hangen nesa.
Maheera tace magana dai ta kare tunda aure ba fashi inshaallah kawai kiyi addua yafi,to shike nan Allah ya sa alkhairi.


Juwairiyya ce ta shugo gidan da wasu dinkunan tace Aunty yaushe za ayi lalle ne? Maheera tace sai ana gobe biki kar ya goge da wuri kafin a kaini ya goge,yaya gidan nawa kunje kun gano? Juwairiyya tace mun gano wlh ya hadu komai akwai munje mun kara gyara ko ina an shirya duk wani kayan kyale kyale ke baki gani ba,Maheera tace mashaallah,Mama tana ji tace nidai na shiga uku haka kika koma? So hauka ne Maheera?Maheera tace kowa fa da zamaninsa Umma,ni dama dan na samu miji na kara zama ta gari,Mama ta dora hannu a kai.

Ana

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login