Showing 69001 words to 72000 words out of 76019 words

Chapter 24 - MUMMUNAR DABIA PDF BY ASMA BAFFA

22 Aug 2025

280

part din Sohail,a firgice ta tashi taga kartai a kanta su uku suna shirin yi mata fyade,Maheera ta samu waya dake gefenta ta bugawa wanda ke kokarin cire wando,haukace musu tayi kawai suna kokawa sosai da su,wani a ciki ya kifa mata mari yafi biyar sai da fuskarta ta kumbura.
Su Sahil har sun danyi nisa a mota,Sahil yace sauke ni Sahil na koma gida Maheera tana can,Sohail birki yaci ya juya da motar ya sauke Sahil shi ya wuce asibitin,Sahil yana shiga ya samu ma sun fara cirewa Maheera kaya tana ta ihu.


Duka daya ya yiwa me shirin fyade ya zube kasa a sume,sauran suka ja wanda ya sume suna kokarin guduwa Sahil yayi kansu ya dinga lodar su kamar zaiyi kisan kai sai da yaga basa motsi,Maheera kayan jikinta ta gyara,tana hawaye, 'yan sanda ya kira,suka zo suka tafi dasu sannan ya zauna a gidan tare da Maheera yana jiran Sohail ya dawo ya dauke su,ba a dade ba ya dawo ya dauke su suka tafi asibitin gaba daya.


'Yan dabar da aka kama waya kawai aka yiwa yan sanda a daren aka sake su ko kwana basu yi a Police station ba sabo da suna da daurin gindi,Su Sahil basu san har an sake su ba ma sun tafi.
Sahil ko magana baya iyayi sabo da tsananin damuwar halin da yake ciki,tsoro yake ji kar ace fyade suka yiwa matarsa yanda suka yi yunkurin yiwa Maheera.









Free page 1&2 400


0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank










AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:18 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸
51-55




Official


By
AsmaBaffa




SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM




Page naki ne
Baby Ak




MASU AUDIO BAN YARDA WANI KO WATA YA JUYA MIN NOVEL BA IZINI BA.







Asibitin suka koma ana ta kula da Islaha ana bata agaji,bata farfado ba sam har gari ya waye twins suna asibitin tare da Maheera,suna zaune sun tasa Islaha gaba,Maheera tace kuje masallaci kuyi Sallah,Sahil yace to sallar ma zan iya kuwa,addua zaka yi mata ai,Sohail yace muje,fitowa suka yi suka tafi Masallaci,Sallar nan ba a hayyaci Sahil yayi ba,Maheera a ciki tayi sallah tana zaune suka dawo asibitin,har 9am Sohail yaje ya musu take away na abinci ya kawo,babu wanda ya iya cin komai har me siyowar.


Sai can wurin 11am Islaha ta farfado idonta ta bude a hankali tana kallon su Maheera,Suka koma jikin gadon da sauri suna tambayarta ya jikin,Sahil yace wai me suka miki ne? Maheera ta kalle su tace da sauki idonta ya ciko da hawaye sannan tace Allura suka yi min a tafin kafafuna duka biyu bazan iya tafiya ba yanzu,Sahil yace Innalillahi wa Innailayhirrajun amma akan ace fyade suka miki gwara wannan,tana kuka tace to ai ba a san Allurar mece ba,watakil ta guba ce suka yi min mutuwa zanyi shike nan ta karo sautin kukan ta.
Maheera hawayen tausayi ya zubo mata tace baza ki mutu ba inshaallah ba ita suka miki ba,babban likitan ne ya shugo yana suka fada masa halin da ake ciki,yace ku tsaya akwai test din da za ayi za san wacce allura ce,nan take yasa aka maida Islaha wani bangaren daban,test suka yi mata na gaggawa,sai bayan an duba likitan ya kira su Sohail yace, to gaskiya zan fada muku Allurar da suka mata baza ta sake iya amfani da kafafunta ba a duniya,kafafunta baza su iya amfanuwa su motsa ba itace Allurar da suka yi mata,babu kuma wani waje da zaku je su iya maganin abin ko da kuwa za ace kasar waje ce.
Sahil yace ai ba kune Allah ba zata taka watarana inshaallah ni bazan yarda da maganarku ba,Allah yana nan zai mana maganin abin,likita yace ina muku fatan hakan,yanzu a jikinta kalau take lafiya,komai na jikinta zaiyi aiki kafafu ne kawai sai ku siya mata wheelchair aci gaba da ganin likita kafin aga me Allah zaiyi.


Sahil jiki a sanyaye suka fito Maheera kadai suka fadawa,a ranar suka canjawa Islaha asibiti wanda yafi wannan tsada,washe gari suma suka yi iya binciken su abinda waccen likitan yace suma shi suka fada,komai sai dai Maheera ke yiwa Islaha Sahil yana tayata duk da cewa ma Allah yasa tana amfani da dukkan sassan jikinta,kafafu ne kawai suke da matsala. har sai da suka zage asibiti sun kai bakwai duk abu daya suke fada.


Islaha sai da ta matsa sannan suka fada mata me ake ciki,taci kuka da kyar aka lallasheta,Sahil yace nifa akan suyi miki fyade gwara wannan din yafi min,Islaha tace gwara fyaden daga ya wuce ai shike nan amma wannan bazan fa yi tafiya ba na zama gurguwa ina ji ina gani,Sahil ya kalleta yace haka aka ce miki to zaki yi tafiya inshaallah,Aunty Aisha da Alhaji Saminu sai sintiri suke yi a hanya,Daddy sun fada masa amma ko zuwa baiyi ba sai waya kawai,su Adnan sun dawo daga tafiya sunji labari amma ko leke ba a gansu ba,har suka gama yawon jinyar su suka koma da Islaha gida a Wheelchair Sohail yace InshaAllah nan gaba har kasar waje za a kaita a gani,Maheera ce ta gyara kujerar Sahil ya dora Islaha a kai suka shiga cikin gidan.


Islaha ta shiga damuwa matuka,abinta tafi karfi yafi karfinsa,hawaye ne ya gangaro mata ganin Sahil yayi wankansa ya fito ita kuwa sai dai a kaita a zaunar da ita,kallonta yayi yana murmushi yace ke komai kuka sai kace baki san kaddara ba ki godewa Allah kina amfani da hannunwanki da komai kafafune fa kawai,yanzu in na kaiki toilet komai zaki iya yiwa kanki ai da sauki,a gabanta ya tsuguna tana goge hawayenta tace ina Amarya yanzu idan ka gaji dani fa a haka wata zaka auro,tunaninki kenan? Ni da kika aure ni a marar lafiya fa? A haka fa kuka ganmu kuka iya auren mu baku ji komai ba kuka ce kun ji kun gani sai nine akan lalura ta faru kuma ba ke kika dorawa kanki ba kawai sai na juya miki baya,ki daina fadar haka please.
su Sohail ma sun manta da Baturiya tunda ta bisu asibiti ina tayi oho basu ko tuna ba.
Toilet ya kaita da kansa tayi wanka da brush,ya taimaka mata ta daura Alwala sannan ya fito da ita har yau bai san ya jikin Islaha yake ba baya kallonta ba sutura,Maheera ce ke mata komai yau ma sai da ta gama ta daura towel yaje ya tayata alawala ya fito da ita.
Sallah tayi a zaune ta sha magunguna sai ga Maheera ta kawo abinci a katon tire,Sahil yace ya zakiyi Maheera hutu bai ganki ba sannu Allah ya biyaki,murmushi tayi tace wai ina Mummy baturiya ne kunce tazo ina take? Sahil sai yanzu ya tuna ma yace ni tun ranar ma ban ganta ba,ina tayi ne? Basu san ita tun a daren ta nemi hotel tayi tafiyarta ba,taga sam basa ma kulata sun manta wajen su tazo.
Sahil yace ai tana da wayo koma ina tayi zata fito ba yarinya bace.


Maheera tace Allah ya kyauta muku to,Sahil yace Ameen jeki to kinga ni nan Amarya ce,Islaha ta saki kuka tace ni ka daina ce min Amarya haka ake amarya a nakashe,Maheera ta fita tana dariya,mai ya dakko yace yau zan fara aikina,ni baza ka shafa min ba zan iya abina,harararta yayi da wasa ya cire towel din juyawa tayi da sauri ya kifa kansa a saman bed yace bazan iya gani ba,na jawa kaina nayi zaton shege ne ni ashe ba haka bane,dariya ya bawa Islaha tace tab a haka ake mazajen? Ai da mata basu yi aure ba,miko min rigata da nayi sallah na maida jikina,Idonsa a rufe ya miko mata ta saka sannan ya bude idonsa yace kai yau naga abinda yafi karfina,abincin ya jawo ya zuba musu ya dauketa tare da dorata saman bed ya zauna a gefe suka ci abincin nasu tare.


Maheera sai da ta koma take tambayar Sohail ina Mummy? Yace tab? Wai ni nasan inda tayi ma bani abinci ita tasan ina ta shiga wa yace kar ta tsaya a kusa damu,wlh aka yi Kidnapping dinta ficika bazan biya ba,Maheera ta zuba masa abinci suka ci abinsu,bayan sunyi shirin bacci yace jibi fa zan tafi Dubai,Maheera kwalla ta zubo mata,murmushi yayi ya kashe light tare da kwantar da ita a saman bed,a gefenta ya kwanta yace me kike so? ni bana son tafiye tafiyen nan kawai,shike nan? to tafiya ta zama dole Maheera,sau nawa zan miki bayani ki gane amma kinki ganewa haba Sweet,to nace maka ni yara nake so kaki yin komai ya kake so nayi,Sohail yace wannan yara me zasu baki ne yan banza ma a haifo su sannan su damu mutum.


Shuru tayi tana sake sake a ranta,Sohail yace ya zanyi,kamar me jin tsoro haka ya rungume Maheera a hankali ta makalkale shi tana murna,harararta ya shiga yi ai shi dole aka masa,rigar tata ya janye a hankali yace mutum dan zaiyi tafiya shike nan sai ya bada cin hanci....bakinsu ya hade waje daya yace a film dai na gani ana yi nasan shi kike so,Maheera ko magana bata yi ba yana kushewa yana tsotse mata baki,Maheera ta kara mannewa,Sohail yace ashe ba a banza ake yi ba,kin fini hankali gaskiya,Maheera murmushi tayi suna ta faman kissing din juna,Sohail kasa dainawa yayi ya wani rude ya zauce,sanda ya janye mata rigar bacci ma bai sani ba,kirjin Maheera ya bayyana Sohail ya wani kunna light yace ayi abu a duhu tsakani da Allah,Maheera duk ta canja kala kamar mayya,yace yayi shugabar yan iska har kin koma haka sai kace kin saba da yi,dole na nemi magani,kunya Maheera taji ta kashe light ya kunna yace ai gwara na ga me kike aikatawa ido da ido,A haka sumi sumi dake kamar bakya aikata ba,Maheera ta kule cikin bargo tana dariya,Bargon ya shige Maheera ta rungume shi ta baya ba kaya a jikinta,ajiyar zuciya ya sauke yace mijin Lalai sai dai yaji kamar kasko ya rungume shi,juyowa yayi ya fara shafa gashinta a hankali yana kissing dinta,Maheera farin ciki kamar me ashe ya iya ta furta a ranta,wuyanta ya gangaro yana bi da kiss,Maheera makale shi tayi tana ta faman shafa kirjinsa ta cire masa riga,yana gangarowa kirjinta ya fara shafa su da hannu biyu yana murzawa yace ashe abubuwan wasa ne ina can ina game kullum a tv ban sani ba sai latsa handle nake ga abin latsawa,dariya suka yi.


Maheera ita dai burinta ya gane ya koya ko nisa baiyi ba ya dakata ya juya baya yayi kwanciyarsa yace kawai sai na zauna nayi ta abu daya bazan iya ba idan baza ki so ni dan Allah ba to.
Dariya ya bawa maheera ta juya ta rungume shi a haka ba kaya,ya kuma juyowa yace aci gaba? tace ae mana,shi kansa bazai iya hakuri bane amma yaki ganewa,yaci gaba da latse Maheera ,bakinsa ta dora a saman boobs dinta,yace da girmana nidai na shiga uku yau shike nan zan koma irin dan gidan Baffan Islaha,kar ya dawo irin na Lalai ina rabaki da wannan aikin,Maheera ita uzurinta take ba ruwanta wai dole sai ya gane,wandonsa zata janye ya rike yace sai na dawo daga tafiya,ki rabu dani ni,Maheera ta cire pant dinta tace anyi anyi ka gane tun ana binka ta lumana kaki,Suka hau kokawa da Sohail za a cire masa wando,ya sauka daga bed din da sauri,Maheera tace ka dawo na fada maka,yace bazan dawo ba a maida ni wani dan iska daga gwaji.


Dariya Maheera tayi ta maida kayanta tace ko banza ai kayi abinda baka taba yi ba,yace ban yafe ba dai, tace ni din? Yace a'a na yafe miki,to zo mu kwanta na daina kaga na maida kayana bacci zamu yi,dawowa yayi ya maida rigarsa ya kwanta,bata masa komai ba haka suka yi bacci.
Islaha kuwa kwantar da ita yayi bayan sunyi shirin bacci Sahil yafi ganewa shi,ya fara shafata tana kallonsa tace bani da lafiya kayi hakuri na warke Sahil yace a kafa ne me ya dameni da kafafuwa iyakaci na Taskira bazan zo kafafu ba me zasu tsinana min,Islaha taji tsoro tace ni dai wlh bana so ta zaci wani abu zaiyi,yace gani ba ci ba wai mene haka,sai ayi ta zama da ku ana kallon ku.
Islaha tana hawaye harda shesheka tace nasan wayon maza wayo zaka min kuma kasan bani da lafiya,yace to shike nan na hakura amma ni bazan iya kyaleki ba ki kwana kawai sabo da jin dadi, bazai yuwu ba a dinga kyale ku kuna kwana lafiya ai bata kamata ba.


Dariya ce tayi mugun kama Islaha ta goge hawayenta tana dariya,ya cire mata rigar daga ita sai pant sai kare kirjinta take yi da hannu,Sahil ya zaro idanuwa sai kuma ya fara dariya wai ya tuna na Lalai,yace Lalai ita kanta sai ta tsani kanta,sai kace danmalele yarab,Islaha tayi dariya,ta juya ya riketa ya tsaya sai kallo yake,sai da ya gaji ya ya fara kokarin zare mata pant, taki yarda,ta karfi ya cire pant din yana kallon taskira yace waiiii...bari naje Break ya mike ya fito tare da wucewa kitchen ya dakko ruwan sanyi ya kwankwada yace mata su suke da abin gani, biscuits ya dakko yana ci ya dawo yace break naje na dawo,Islaha tace Allah bacci nake ji sai dariya kake bani sai kace a makaranta harda tafiya break, kayanta ta maida ya kashe light ya kwanta tare da dora kansa a kirjinta yana shakar kamshin jikinta a haka bacci ya kwashe su.


Washe gari da wuri Maheera ta tashi ta shirya musu lafiyayyen breakfast ta kai wa su Islaha bangaren su sannan ta koma tayi wanka, ta dau wanka cikin kananan kaya,lokacin tazo ta tashi Sohail a bacci,idonsa ya bude a hankali yaga ta sha kyau jawota yayi ta fada jikinsa ya rungumeta,tace abinci fa? Ya riga ya saba wankan asuba shi yasa ma baiyi wani yanzu ba ya tashi ya kuskure bakinsa suka fito Dining dinsu.
Islaha kuwa Sahil ne ya taimaka mata tayi wanka ta shirya idan ka ganta ka rantse kafafun na tafiya,daukanta yayi ya fito da ita palo,da kansa ya bata abinci a baki suna ci,Halley ta zo gidan daga hotel din da take,sanye cikin Wando palazo da riga me siririn hannu, part din Sahil ta shiga kai tsaye ta same su a palo,Sahil ya dago kai ya kalleta yace baiwar Allah dama kina duniyar? Shuru tayi dan bata jin me yake fada,Islaha tace Hey Mum how are you? Halley tace no..no...not how are you no...,How you,Islaha tace a rubuce haka yake kaji Baby,Sahil yace a rubuce How are you yake,Halley tace but yanda ake fada ba haka ba,How you, Islaha tace How you? Babu ko fara'a ta zauna abinta ta harde kafa,Sahil yace karki kara yin turanci a gidan nan na haramta turanci ya fadawa Islaha,Halley tayi magana da turanci Sahil yayi hausa,tace you muslim? Sahil ya fara karatun Qur'ani wai taji zahiri,Halley mikewa tayi ita kanta a ciki bata san waye Sahil din ba waye Sohail sai Islaha ta tambaya ta fada mata.


Gani tayi Islaha bata tafiya Halley harda hawaye ta ya danta zai auri gurguwa,tashi tayi ta wuce wajen Sohail,Sahil yace lallai hawaye zai kare kuwa a kasar na gani tana hawaye,Sohail yana zaune yana cin abinci ya kalle ta yace ashe kina raye ai mun zaci anyi kidnapping dinki,Maheera ce ta bige shi ta gaida ta, Halley ta zauna tana gyara gashinta,Sohail yace a kawo mata tuwo ido guba ne,Maheera tace ko kai fa baka ci dumamen tuwon ba bare ita da take daga kasar waje,Sohail yace to shike nan tunda kince haka bata abinda kika yi niyya,Maheera ta mike zata hada mata Coffee da sauri ta tabe baki tace kar a bata bata sha ta sha nata a hotel,Sohail yace gaba ta kaimu dama ni bada zuciya daya nace ba.


Halley ce ta gaji da danna waya ba wanda ke kulata su Sohail sun Haramta turanci,Maheera zata yi magana Sohail yace na haramta turanci a gidan nan ko gwalangwaje ne ban amince ayi shi ba,idan kuma kika ce ke shishigi zakiyi wlh sai munyi fada na fada miki,ba ruwanki uwar mu ce ki rabu da ita in ta gaji ta tafi.


Halley kuwa Daddy ta kira tace ina zata samu tafinta ko mace wacce zata dinga fassara mata abinda twins ke fada,Wani ya kira a Abuja ya hada Halley da wata mace budurwa bahaushiya tana jin turanci za a dinga biyanta albashi.
Halley zuwa yamma me fassara tazo gidan,suna main palo gaba daya Sahil,Sohail,Maheera da Islaha suna kallo,Halley ta shugo da guntun wandonta kafafunta siri siri a ciki,Sohail yayi dariya yana kallon kaurin Halley da cinyarta, Sahil ne ya tabo Sohail yace sanda zata haife mu taji jiki na sani,Islaha suka danne dariyar su,Halley ta tambayi me fassara wacce ake kira da Sumayya,me suka ce? Sumayya tasan in ta fadi abinda suka ce akwai kura,Sohail yace fassara mata daidai me zata yi,Sumayya ta fassarawa Halley,Halley ta harare su tace ita fa uwar su ce ita ta haife su,Me fassara tace tace mahaifiyar ku ce ita itace ta haife ku,Sohail yace uhm ai dan bamu sani bane da tuni munyi mutuwar kasko tare da ita,Me fassara ta fadawa Halley,turawa ba wahala sunyi kuka Halley sai hawaye take,Sahil yace me aka miki daga fadar gaskiyaki mana kuka a nan sabo da Allah yayi fushi da mu,muma kukan so muke muyi dama ce bamu samu ba,Me fassara tana ta faman fassara,Halley ta goge hawayenta da tissue tace ni bakin cikina da kuka zama musulmai,Sohail yayi dariya yace ai kuwa zaki kare a takaici domin kuwa a musulunci zamu mutu,yanzu ma mun kusa tashi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login