Showing 3001 words to 6000 words out of 76019 words
class din sai kowa ya sani, budurwarsa Zayna ita ba abinda ta fara na nuna alamun balaga a tare da ita sai gashin hammata,yau tana zuwa aji kowa yayi shuru ana jiran shigowar malam tazo ta zauna a kusa da kawarta,Sohail ne yayi magana da karfi kuma da Zayna Isma'il ta fara gashin hammataaaaaa.....aji aka barke da dariya ana kallon Zayna,kunya ta lullube Zayna ta fada kasan sit ta buya,Sahil yana jinsu ko magana baiyi ba.
Malam ne ya shigo nan take Sohail ya fara baccinsa abinsa har aka tashi yana bacci,sannan Sahil ya tashe shi suka wuce driver yazo daukan su,Amal yayar su tana motar tana wani daure fuska suka shiga ciki driver ya ja suka tafi,Amal ta samu Sohail ta talla masa mari haka kawai tace shegu yan iska kunki fitowa da wuri muna ta jiran ku,Sahil kuwa ransa ya baci ba zato ya saukewa Amal mari a fuska,kumatu ta dafe tace Sahil ni ka mara? Yace an mare ki so what? Who do you think you are? ko yaushe sai dai ku zage mu ku dake mu,me muka yi muku,idan kin yiwa Sohail ya kyale ki ni bazan kyale ki ba,Sohail yana kallon su yace ku chasu arna ku chasu,shi da ake tare masa amma ko a jikinsa.
Suna Isa gida Amal ta fito ta samu saurayinta na university dinsu yazo wajenta shima dan gidan me kudi ne,suna fita wajensa ta wuce,Sohail yana zuwa zai wuce su yace saurayin Aunty Amal ai Auntyn m Jinin haila take yi yau ya wuce abinsa,Amal ranta ya baci kuma da gaske Sohail yake tace wlh idan na dawo ciki sai na lahira ya fika jin dadi,ciki suka wuce aka barta nan saurayin yana murmushi ya zaci lafiyayye ne Sohail yace ashe kina off,ya aka yi yaro ya gani,kwana nawa kike yi? Amal duk taji kunya ta share zancen.
Ai kuwa tana gama sallamar bako part din Mama Asmau ta nufa a fusace,Mama ta kalleta suna palo tare da yaranta tana biya musu karatun Qur'ani gobe suna da hadda,lafiya ke Amal ko sallama babu? Zuwa nayi naci uban yaran naki ta furta da tsiwa tana fisgo Sohail,Mama ta janye Sohail tace wlh kina taba min yaro saina kwashe ki da mari tunda baki da kunya.
Ae bani da ita ai bake kika haife su ba juya ....karaf a kunnen Alhaji Ali Daddy me shirin shigowa yana jin haka ya karaso ya cafke Amal babu bata lokaci ya hau jibgarta sai da ya mata lilis babu wanda ya kwace ta,yace idan uwarki ce zaki fada mata haka? Matata ita ba uwar ku bace? Amal tana kuka tana bada hakuri, da kyar ya hakura ya kyaleta ta fice da gudu kuwa.
Matarsa Asmau ya bawa hakuri,tayi murmushi tace ba komai fa Allah dai ya shirye su,duk Adnan ne ya koya musu.
Bayan shekaru biyu Su Sahil suka gama Secondary school dinsu,sun wani tasa sun girma sun kara kyau,lokacin kuma Sohail Allah ya yaye masa dalalar yawu tuni,ya daina abubuwa da yawa duk ya daina ya zama cikakken mutum amma fa akwai shirme,kana ganin yanda yake abubuwansa kasan kansa yana fisga, sai dai an daina wasu abubuwan manya wanda hakan ba karamin dadi yayiwa Asmau da Ali ba, idan yana abubuwa a rikice zaka san lallai fa wani abu na damunsa,a hankali shima Sahil kawai rana tsaka kansa ya fara tabuwa irin na Sohail,yanda Sohail ke shirmen shima haka yake yi, iri daya suke shiriritar su da Sohail,Asmau ta damu sosai tayi tayi Alhaji Ali ya tsaya a nema musu magani sosai amma yaki sam,ganin ma a haka basu da kokari basu san komai na duniya ba sai dai result kawai a school me kyau sune suke daukan na daya,amma idan ka tambaye su abu daya baza su iya fada maka ba,har shi Sahil din duk kokarinsa yanzu babu ya gudu bai san komai ba,shi yasa sam Alhaji Ali mahaifinsu bai damu da su ba.
Yana ganin ba abinda zasu iya tsinanawa a rayuwa kawai dai a basu ci da sha,ganinsu yake kamar ma ba mutane ba,komai baya sawa da su sai dai yaran Nadia sune mutane,ya dauki su Sohail ba wasu mutane ba,Asmau tun tana fada masa gaskiya har ta gaji,zai basu sutura ci da sha shike nan,su Ibrahim kuwa har kasuwan ci yasa ake koya musu suna gama school zai basu company guda shi da Adnan.
ita kuwa Nadia dan dalalar yawun ma da Sohail ya daina sai bacin rai take da Sohail ya samu lafiya,duk shirmen da suke bugawa shi da Sahil a haka cewa take lafiya suke.
Yau ma Mama gani tayi sun sha wankan kana nan kaya abinsu abinka da kuruciya,sun sha kyau kamar a sace su,tace ina zuwa kuma? Sohail yana daura agogo shi a dole shege yace filin ball zamu kalli wani match yana yarfe hannu,Sahil kuwa turare ya fesa yana wani jiji da kai,Mama dariya tayi kawai tace to a dawo lafiya manyan yara,suka amsa da Ameen,tace banda driving driver ya kaiku please,suka ce to sannan Sohail harda yiwa Mama kiss a kumatu ta make shi suka fita suna dariya,amma yanda suke kalle kalle da wuri wuri kasan ba lafiya kansu da tabi.
Driver ne ya kaisu har gidan su Zaynah suma katafaren gida a hadaddiyar unguwa,tasan da zuwansu ta sha gayunta,yanzu tunda sun gama secondary ana barinta tana zance,fitowa tayi sanye cikin doguwar rigar material,har ga Allah bata gane waye Sohail ba waye Sahil ba yau ta kasa ganewa sai taje ta rike hannun Sahil,Sohail yayi murmushi yace ke kin ganni nan tunda kema bakya iya ganewa,Murmushi Sahil yayi tare da fisge hannunsa,Zayna dafe goshinta tayi tare da furta oups I'm sorry,Sohail yace sai kace kin rike wani bare he is my blood tare zamu aure ki fa mu biyu,Sahil yace InshaAllah ki kwantar da hankalinki matar 'yan biyu ce ke,Zayna ta zaro ido tasan kansu da motsi shi yasa dariya suka yi sannan suka shiga cikin gidan,Sahil ya koma mota ya zauna yana danna waya abinsa,yana jiran Sohail,Sohail lekowa yayi yace kazo ka kama min,bazan iya zancen ba sai kace ni kadai zan aure ta ai har da kai a ciki,driver yana jinsu yana ta dariya,yace au dama wai zance kuka zo nan? Kuma mace daya zaku aura ku biyu? Sahil yace ta ishe mu rayuwar duniya ya bude mota ya fice ya bar driver yana ta dariya.
Sohail suka shiga palo Zayna suna hirar school din su,Sahil yace I love you Zayna, Zayna ta zaro ido tace kaga saurayina fa,Sohail ya bata rai yace shima yana sonki ai tare muke son ki idan bakya sonsa nima bakya so na to shike nan na daina kulaki,Zayna tace sai kace akuya ce ni ta ya zan so maza biyu ni bazan iya ba,to shike nan nima na daina sonki wlh,Sahil a fusace ya mike kamar zai mare ta ya daki table sai da ta tsorata,yace da Sohail muje,Sohail ya mike yace kinwa kanki ki rasa mu karki sake kula mu.
Zayna tace to sai me aikin banza mahaukata da ku ma,nan a makaranta kake dalalar da yawu,dama dan kana da kyau nake kulaka amma me zanci da mahaukata,Sahil ne ya dawo ya rike Zayna ya kwashe ta da mari,ya fara dukanta sai da ya mata lilis tana ihu yan gidan su suka fito da gudu,Sohail ya jawo Sahil.
Maman zayna tace amma ku dai kunyi asara ai zaku aikata mahaukatan banza,kowa ya fito yana tambaya lafiya sai ace ai mahaukatan nan ne sai ace ohhh Allah sarki ai mahaukata ne a kyale su,su Sahil ko a jikin su dan ance musu mahaukata suka yi tafiyar su.
Sai dare suka koma gida , Mama suka iske Fada ta fara tace dan iskanci sai yanzu zaku dawo,Sahil yace wai Mama a koma bamu nono mana kawai a huta ace muna maza zamu fara university ba inda zamu je muyi dare sai kace mata,Sohail yana jinsu ya saka Earpiece dinsa zai toshe kunne,Mama ta rike kunnen sa tare da murdewa dariya ya hau yi dake yafi Sahil fara'a shi,bana so ne a samu matsala ku lalace,karatu zaku fara fa, kafadar Mama Sahil ya dafa kamar wata sa'arsa yace ba abinda zai faru, Mama tace Allah yasa,Abinci fa? Mun koshi mun ci burger dazu,tace to Good night ayi adduar bacci kar a manta.
Sam su Sohail basu taba tambayar ina maman su ba,ko wacece ba ruwan su ko zancen basu taba yi ba.
Bayan wasu watanni Sohail da Sihil aka kai su private University dake Germany suna can suna karatunsu amma dai sai dai result me kyau basu san komai na karatun ba har yanzu
Har suka shiga level 2 sannan suka zo hutu gida.
Suna zuwa hutu suka samu anyiwa Amal aure ta auri wani hamshakin me kudi dattijo ne gidanta daban,Adnan ma yayi aure an masa aure,ko fada musu ba ayi ba sabo da ana ganin basu da muhimmanci,basu da amfani a duniya haka mahaifinsu da sauran yan uwa ke gani,basu ma ce me yasa ba a fada musu ba sai murna ma da suka yi Adnan yayi aure da Amal,Mama Asmau itace komai dinsu a gidan sabo da ita ne ba a iya taka su.
Hajiya Asmau yau shiri suka yi ita da kishiyarta Nadia zasu je Kaduna bikin 'yan uwan Nadia a danginta dake ita yar kaduna ce,Asmau Kara zata yi mata,su biyu driver ya tuka a mota suka tafi cikin ikon Allah a hanya motar su tayi hatsari bayan tayi dugu dugu motar nan take ta kama da wuta,da kyar aka samu ma aka kashe wutar,babu wanda ya tsira a motar gaba daya sun mutu da Nadia da Asmau har driver,Alhaji Ali sai mummunan labari yaji,nan take ya fadi a sume aka kaishi asibiti.
Su Adnan kuka kamar ba gobe,su 'yan biyu ma basu san me ake yi ba suna daki suna game tunda Mama ta tafi basu fito ba,mutuwar ma sabo da iskanci ba wanda ya kula su Sohail bare a fada musu kawai ba mutane bane,Alhaji ya farfado da shi aka hada matan nasa wanda duk sun kone kurmus,sai sassan jikin su kadan,hayaniya da kuka ne yayi yawa Sohail ya mike sanye daga shi sai gajeren wando ya fito yana lekowa yaga mutane dankam mata sun cika ko ina na gidan.
Dawowa yayi ya saka jallabiya yace kai Sahil gida fa ana ta kuka an cika gida ko menene oho,Sahil yana ji yace kar fa abar nan ce tazo gidan nan yau,ai kuwa ina jin ma itace tazo din cewar Sohail,yace tabbas ta karaso bari muji wa tazo ta dauke,Allah yasa Umma Nadia ce,Sahil yace 3qtr ma zan saka dan iskan zaman makoki zanyi naji a jikina Umma Nadia ce,3qtr ya sha me tsada da tshirts dinsa wata grey,shi kuwa Sohail jallabiya ce fara a jikinsa,a jikin Mirror suka tsaya suna taje sumar su ,Sahil ya shafa man lebensu na maza me kyau,Sohail ya hau fesa turare sai da suka gama suka bude kofa tare da fitowa wai zaman Makokin Nadia zasu yi.
Mata aka zuba musu ido yuuuuuuuu kamar za a cinye su sabo tsananin kyawunsu,suna zuwa Main palo suka ga yan uwan Mama Asmau da yawa suna ta kuka,wani palon kuma yan uwan Nadia ne,Amal tana ta rusa uban ihu a cikin su,Sohail yace cikin rada da alama Umma Nadia ce,Sahil yace akwai rawar bungalo yau da galala,suka dawo ta parlon da yan uwan Mama suke domin sun fi sanin su,Sohail ne yaji ana cewa Allah sarki sune yaran Asmau wanda ta raina,Allah sarki sunyi rashi,Allah kaji kan Asmau, mutuniyar arziki,Sohail yaci wani wawan birki yace wa naji kuna cewa? Sai lokacin ya tuna ai tare suka tafi unguwa da Nadis, Yanda yayi maganar cikin tsawa da karaji sai da suka firgita,Sahil yaje ya rike wata tsohuwa cikin dangin Asmau yace wacece ta mutu? Dattijuwar tana hawaye tace Nadia ce da Asmau duka matan mahaifinku sunyi hadarin mota Allah ya musu rasuwa gasu can ana sallatar su.
Sohail yace wai Maman mu har da ita ta rasu? Suka ce ae,sumarsa ya hargitsa ba tare da ya sani bama,ya fara kokarin cire rigarsa da ya fesa mata turare yana hawaye nan take idonsa yayi jajir, Sahil kuka yake wiwi sosai yake kuka,ana ta basu hakuri,Dattijuwar tace sai hakuri,Sahil cikin karaji yace baza muyi hakurin ba,wallahi bazan hakura ba sai munyi kukan.
Da kyar da lallashi suka tashi suka nufi wajen makokin,Alwala suka yi suka bi sawu aka sallaci gawar Mama da Umma da su,ana sallar suna ta sharbar kuka sam basu iya sallar ba sai kace mata.
Sohail anzo daukar gawar babu kara sohail da Sahil suka ce a tsaya dan Allah suyiwa maman su addua amma baza mu yiwa Umma Nadia ba wlh suna hawaye ana jinsu suna cewa baza mu yiwa Umma Nadia ba,kowa yayiwa iya uwarsa,haka aka jira,suka tsuguna a saitin kanta sun dade suna hawaye suna yiwa Mama addua sannan suna gamawa su biyu kacal suka daga makarar Mama kowa yayi mamaki duk nauyin mamaci da makara,haka mutane suka kama amma basa jin nauyin sam su Sohail sun dauke nauyin amma kamar basu dauki komai ba,suna tafiya suna hawaye sai uban sauri kuma suke yi mutane sai da gudu gudu sauri sauri ake binsu,Nadia kuwa tana can karshen baya ana kiri kiri da ita,ana kaita bakin kabarin Sohail yayi sauri ya shige kabarin ya kwanta wai sai ya ji inda Mama zata kwanta,aka fito da shi da kyar yana cewa ni a barni na dana yana kuka abin tausayi, Sahil shima ya shige ya kwanta,da kyar shima aka fito da shi yana faman tirje tirje yana cewa sai na Dandana nima, ana musu fada,aka zo za a sa Asmau a makwancinta suka hana,suka rike aka yi aka yi suka hana har aka binne Nadia sun hana a saka Asmau,Sai da Alhaji Ali ya musu magana ya kira su sannan aka samu aka fara sata,Sahil da sauri yaje ya saka rigarsa da ya cire ya dukunkune ta ya saka a saitin kan Asmau yace ayi mata pillow taji dadin kwanciya,kwace rigar aka yi sannan aka samu aka kammala komai.
Sohail kuka sosai ya durkushe a kasa kuka yake ba ji ba gani,an gama komai amma Sohail yace mu baza mu tafi ba a nan zamu kwana sai munyi gadin Mama.
Daga ranar babu wanda ya kara ganin su Sohail suna dakinsu suna ta kuka da jimami suna tuna maman su Asmau da irin rayuwarsu da suka yi,girki da kansu suke wa kansu dama sun iya sosai suna taya Mama duk ta koya musu,bayan akwai masu aiki a gidan amma Adnan ya hana a basu su yan biyun abinci,za dai a zuba komai a store su dafa da kansu.
Bayan anyi kwana arba'in Mama komai nata anyi rabon gadonsa 'yan biyu ko handkerchief ba wanda ya basu,itama Nadia anyi nata yaranta duk an fiddawa kowa hakkinsa duk da ba wani abu suka tara ba,Alhaji Ali ko kadan baya saurarar su Sohail haka kowa na gidan,gasu sun zama manyan samari sosai.
Hutunsu yana karewa suka samu Daddy a part dinsa,tare da Adnan da Ibrahim suka iske su suna ta rubuce rubuce suka shiga da sallama,Adnan da Ibrahim suka wani daure fuska,Alhaji Ali yace ya akayi twins? Sahil yace hutun mu ya kare muna so mu koma school Daddy.
Adnan da Ibrahim suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya,Ibrahim ya kalle su shekeke yace wai school sai kace suna ganewa,Adnan yace babu me biya muku har Germany ku dinga yiwa mutane asarar kudi,me kuka sani,Alhaji Ali ne yayi magana yace ya isa,kai Sahil naga ma kafi dan hankali company na dake Abuja na damkawa Adnan da Ibrahim zasu dinga kula da shi suna aiki,kun san a cikin companies dina wannan na Abuja yafi ko wanne sabo da haka duk wani Business su zasu dinga juyawa,sabo da ina matukar kaunar Adnan,duk gidan nan ba wanda nake so sama da Adnan sai Ibrahim,Su Sohail harda murna Daddy yana son Adnan da Ibrahim su yaya ana kaunar ku cewar Sohail,Sahil yace mu kuwa bamu da kowa,Sohail yace kai muna da Allah mu ya ishe mu harda tafa hannaye,Sahil yace fam fam magana ta kare mune muke da Allah ya daga yatsa sama sannan yasa yatsan a baki yana tsotsa.
Adnan ya karbe zancen yace kai karku dame mu da shirme, da ku zamu tafi can kuna taimaka mana da aikin gida,gaku ai bai kamata mu dauki yan aiki ba,sai ku dinga wanke mana mota,shara da goge da girki komai dai kuma zamu dinga biyanku kudin kashewa haka sannan sutura baza ta gagare ku ba kowa zai sa wacce yake so,wajen kwana ma me kyau za a baku part komai,batun wata makaranta ba ganewa kuke yi ba ku hakura ku fara shiri jibi zamu tafi, Ibrahim yace wannan shine daidai Daddy shawarar da yaya Adnan ya bayar basa ganewa mene amfanin asarar kudi.
Sohail da Sahil basu ce komai ba kuma ko alama ransu bai baci ba hasalima ma da sauri suka ce to zamu shirya,Ibrahim yana harararsu yace kuje dan Allah aiki muke,suka juya suka bar wajen.
Suna komawa bedroom kuma suka fara shirin hada kayansu ko a jikinsu murna ma suke yi su.
Wacece Zayna
Zayna 'ya ce ga Alhaji Shehu asalinsu babur ne,babanta Alhaji Shehu yana da kanne mata da maza kasancewar shine babba sannan yan uwansa gaba daya suna kasuwanci ya zaunar da shi a