Showing 27001 words to 30000 words out of 76019 words

Chapter 10 - MUMMUNAR DABIA PDF BY ASMA BAFFA

22 Aug 2025

283

hada ido ya sakar mata murmushi tare da cewa kawo min tea,Wucewa tayi kitchen Maheera tana daki ta shiga wanka,Tea ta kawo masa yanda ya bukata,kallonta yayi yace zauna mana,da mamaki tace a nan din mu ai yan aiki ne,ni nace ki zauna ai.


Haka ta zauna a hankali sai kallonta yake yana murmushi,yace 'yar wanne state ce ke? Islaha tace taraba state Maheera kuma yar Adamawa ce asalinsu amma a sule ja suke da zama,Ibrahim yace ai ke wayayya ce naga alama,Islaha tace uhm bari naje zanyi aiki"
ba a son ransa ba yace okay kar na takura ki, mikewa tayi da sauri ta bar wajen ta wuce bangaren su,Ibrahim ya bita da kallo yana murmushi.


Sohail kuwa shigar da suka yi kamata yayi a gansu a mota amma a kafa suka fito,suka tsaya tare da zubawa hanya ido Sahil yace kabi hanyar dama ni nabi hanyar hagu kasan ba kowa zai dauke mu aiki har mu biyu ba a waje daya,Sohail yace ka kawo shawara kawai yabi hannun dama Sahil yabi hagu yana cewa duk wanda ya riga gamawa kawai ya wuce gida,mu hadu a gida.
Yanda suka fita neman aikin duk wani kamfani ko masana'anta sai sun shiga ciki suce aiki suke nema,Wani wajen ayi musu rashin mutunci,wani wajen kuma a rabu lafiya wani wajen kuma a kulle ko securitues su hana shiga.


Sohail ya gaji da tafiya da yawo tun sassafe suke abu daya har yamma tayi 4pm ma ta wuce domin idan lokacin sallah yayi masallaci suke shiga na kusa suyi sallah su dora daga inda suka tsaya.
Suit din ma duk sun cire ta saman sabo da wahala,har necktie din sun warware shi a haka kowannen su ke tafiya,last kamfani Sohail ya gani yace daga wannan gida zan koma sai kuma gobe idan Allah ya kaimu,Sohail ya iske kofar a kulle alamar ba mutane ya bubbuga shuru,yaci gaba da dukan kofa har ya gaji ga rana ya hada gumi,a bakin wajen ya zauna da folder a hannunsa ya zuba tagumi,mikewa yayi a hankali kamar zaiyi kuka ya shiga taxi ya nufi gida,Sahil kuwa har after 5 yana zaune a jikin bishiya yana ta bacci a haka ya jefar da folder a gefe,daga dan zama zai huta sai bacci,sai wurin 6pm ya farka ya tashi shima da kyar yake daga kafa ya shiga mota sai gida.


Maheera suna zaune suna kallo sai ga Sohail ya fado cikin dakin ransa a bace yana tafiya da kyar ya dafe kugu da hannu,bai ko kula kowa ba ya wuce tare da haurawa sama,suka bishi da kallo sun san ba nasara ba a dace ba shuru suka yi kawai,yana shiga bedroom ya zauna a kasa ya kwanta a kasan tile yana kallon sama hawaye suna ta faman sintiri daga idanuwan Sohail,ba a dade ba Sahil shima haka ya shigo yana nishin gajiya ya wuce bai ma kula da mutane a palon ba,Ya fada dakin su ya shiga,saman bed ya fada shi yana wash....


Islaha ce ta shirya abinci a tire ta nufi dakin zata kai musu,Adnan ya fito yace ke idan ba aiki ba me yake kawo ku sama? Sabo da kuyi mana sata ko? Uban me zakuyi?Islaha ba tsoro tace Oga ba wajenka zanzo ba gida dai ai ba kune kadai masu shi ba,twins ma suna da hakki domin gidan uban su ne suma,kun zauna ba tausayi ba imani sai azaftar da bayin Allah kuke yi,a tunanina ku masu nemo musu aikin yi ne don ganin rayuwar su ta inganta,ku tuna wallahi akwai Allah wannan zaluncin yayi yawa ku ko tausayi baku da shi, har matarka me wuya kamar na zabuwa ka bata dama tana fada musu abinda taga dama.


Abinci ne zan kai musu kuma wallahi ba wanda ya isa ya hanani na kai musu babu shi a duniya,Adnan baki bude yace Iyyeeeeeee.... fantastic,wato an kawo ki an taimakeki an baki aikin yi shine kike ganin kin isa,Islaha tace ni baku taimakeni ba,zaman Sahil nake yi wajensa nazo,karuwarsa ce ke? Islaha tace ae karuwarsa ce ni sai me? Ta ja tsaki ta juya zata wuce Adnan ya fisgota tare da kifa mata mari yayi ball da tire din abincin ya watse,ya zazzaro mata ido yace yan biyu na tsane su bana kaunar ganinsu.


Islaha tace wallahi Allah ya isa kuma sai na kai abinci sai na kuma hado wani na kai musu,Adnan yace ke ga me taurin kai ko zanyi maganinki a gidan nan zaki raina kanki ya sauka kasa,tace kai din banza zaman lagos fa nayi wallahi karr nake duk sai nayi maganinku a gidan nan kuma bazan bar gidan ba,nazo kenan.


Ta koma kitchen ta hado wani abincin ta haura sama har bedroom din su Sohail tayi knocking,Sohail yana daga kwance a kasa yace come in,a hankali ta tura kofar ta shiga ta gansu a haka bata ji dadi ba ta ajiye musu tace,rayuwa sai hakuri kowa da kaddararsa kuyi hakuri, inshaallah zaku samu aikin yi tana fadar haka ta fita ta basu waje.
Tana fita tazo ta gyara inda Adnan ya zubar mata da abinci.
Yan biyu sai dare suka yi tashi suka ci abincin sannan suka yi wanka ko fitowa basu sake yi ba suka zauna kawai suka fara baccinsu.


Maheera tana zaune ta mike itama ta nufi dakin su Sahil,Zayna ta dawo daga unguwa ta shigo tana karkada key din mota,Maheera ta kalleta kawai zata wuce Zayna tace ke ina zaki je wannan part din masu gida ne idan ba aiki ba waye ya aikeki? Maheera juyowa tayi zata dawo Islaha tace dalla jeki mu ba wanda zamu kyale, gidane baza mu fita ba wallahi bana tsoron kowa rayuwar lagos nayi iskanci ne kawai bana yi amma indai da baki za ayi magana ba wanda ya isa naji tsoronsa.
Zayna ta juyo a fusace da matukar mamaki tace ke......a gidan mijina? Gidan aure na kizo kina daga min murya an dauke ki aiki amma kizo ni kina daga min murya? Islaha tace miji manya muma zaman wasu muke duk da ba a daura ba zaman su muke,Zayna tace to kuwa sai nasa kin bar gidan nan bari Adnan din ya shugo,Islaha tace shima adnan din naci ubansa ai ta kansa na fara baki sani ba,inci uban mijin inci na matar duk na gama da ku,Maheera tace Islaha kiyi shuru,Islaha tace ke kike jin tsoron su wlh.


Zayna sama ta wuce tana huci.
Maheera bedroom ta koma tana yiwa Islaha fada gidansu fa muka zo cin arziki muke,kuma kin san biyana akeyi ina da matsala a gidanmu nima indai rashin kunya ce na iya amma sabo da Iyayena da yan uwana nake hakura ina biyayya.
Amma ni duk layinmu ma tsoro na ake ji amma rayuwa da yanayi yasa na sakko,ki dain jansu da fada ki bari mu cimma buri sai mu fara bude musu munanan halayen mu,dariya Islaha tayi tace ina da hot temper bazan iya shuru ba kiyi hakuri amma zan fara mugunta a gidan nan,zaki ga tsiyar da zan dinga yi musu inda kika ga bera haka zan dawo


Wayar Maheera ce tayi kara ta duba taga kanwarta ce Juwairiyya ta daga tace yan university ya aka yi? Juwairiyya tayi dariya tace Alhmdllh Aunty kayan abincina ya kare sannan akwai wani kudi zamu biya 15k na escortion zamu je wani kamfani,Maheera tace kin san wata yayi nisa Juwairiyya bani da ki sisi wlh yanzu gashi jiya kudin hannuna na turawa Ammar ya siyowa Mama magungunanta su ma abincin su ya kusa karewa sai an siyi wani, Juwairiyya tace Aunty kina kokari ma an gode Allah ya buda bari mu jira mu gani me Allah zaiyi,nima zan duba idan na samu zaki ga Alert cewar Maheera,to Aunty na gode cewar Juwairiyya ta kashe wayar.

Islaha ta tambaya kudi za a bata? wai haka tace ni yanzu ma ban san ya zanyi ba,Islaha tace ga 20k cikin kudin asusuna ki tura mata tunda kinga ni ba abinda zan siya,Idan na karbe miki kudi ke kuma fa?
Islaha tace ba komai ai mun zama daya,rayuwa ce fa ni nasan wataran wa zai taimake ni? Kema kina taimako duk me taimako Allah baya hanashi sabo da haka karbi kawai.
Maheera karba tayi tana ta godiya tana jin dadi.


Washe gari Adnan ya samu Ibrahim yana masa magana akan Islaha lallai ya koreta ta bar musu gida taci mutuncinsa taci mutuncin matata.
Ibrahim yace Islaha kuma? Ae itace,
Gaskiya ba halinta bane kuma ma ai yarinya ce baka ganin bata da wayo kawai kayi hakuri zuwa wani lokaci su Sohail ne suke ziga ta,Adnan yace yarinyar nan bata da hankali fa,Ka dai dan kara hakuri tukun,fafur Ibrahim ya hana a kore ta shi baya ganin laifin Islaha sabo da sonta yake tsakani da Allah kuma burin aurenta yake.


Twins ma yau haka suka sha wanka suka fita neman aiki basu samo ba,wasa wasa sai da suka kwashe sati kullum suna garari da takardu amma ba labari,hakan yasa suka ce sun hakura baza su samu komai a duniya ba suka daina fita ma gaba daya kullum suna gida tare da su Maheera.


Zayna ce ta aiki Maheera kasuwa ta siyo abinda babu na kitchen,tana hanyar tafiya a kafa,sanye take cikin t-shirts brown da wando ta saka hijab daidai gwiwa tana tafiya a nutse,Wani mutum ne shi ba tsoho ba kuma baza a kirashi da yaro ba yayi parking da motarsa cikin sauri ya bude motar ya fito da kansa waje yana ta faman tari yana shidewa yana jan numfashi da kyar, yana ta daga hannu alamar a taimake shi,kasa ya fado daga cikin motar,Maheera ta lura da hakan da sauri ta karasa inda yake tana tambaya lafiya? Da me zan taimake shi,gaban motarsa yake nuna mata da yatsa,ta duba da sauri ta ga Inhaler wacce masu Athsma suke amfani da ita,da sauri ta sa masa a baki,a hankali ya fara dawowa hayyacinsa har ya gama dawowa dai dai.


Kallon Maheera yayi yace na gode kin taimakeni idan ba damuwa dan Allah ki bani number dinki za mu gaisa,ba musu ta bashi number dinta ta kara gaba,yana ta roko ta tsaya ya rage mata hanya amma taki yarda.


Bayan ta koma gida da kwana uku ta manta ma anyi wannan sai ga kiran mutumin,dagawa tayi ganin bakuwar number gaishe da shi tayi ya amsa sannan yace sunana Alhaji Saminu wanda kika taimaka lokacin da Asthma dina ta tashi,tace oh ya gida ya aiki,yace lafiya Alhmdllh,ina sake godiya fa Maheera,tace ba komai wlh ya wuce ai,yace ni sunana Alhaji Saminu Shehu kamar yanda na fada miki,nine me kamfanin J&S nigeria,ina da branch a lagos da Rivers sai kuma nan Abuja,Banyi niyyar sanar dake ba amma da kika ganni fitowa nayi daga gida zan je wajen abokina,Maheera tace mashaallah.
Ci gaba yayi da magana dalilin da yasa na miki magana naji dadi kin taimakeni,so ina da matata da yarana uku,ina so a matsayina da kika ji ki fada min abinda kike so ni kuma inshaallah zan miki.


Maheera taji dadi tace wlh bana bukatar komai na gode amma akwai saurayina da dan uwansa mun dade muna neman aiki kuma an kusa bikinmu Sir amma basu samu aikin ba,'yan biyu ne kuma dan Allah ka taimaka ka bawa ko mutum daya ne aikinyi,amma a takaice idan ba dama zamu iya haduwa na baka labarin su ko zaka tausaya,Jamilu yace ba damuwa bari na baki address din Office dina,ta dinga godiya tana murna.


Suna gama waya ya tura mata address yace tazo yanzu yana Office dinsa ma.
Shiryawa tayi a gurguje cikin fitted gown ta leshi blackblue ta yafa mayafi me kyau ta saka takalmi kalar mayafin da jaka ta fice da sauri,A palo ta samu Sohail,Sahil da Islaha suna kallo,tace zanje unguwa yanzu zan dawo,Sohail ya kalleta yace kuma sai da kika yi kwalliya kice kawai party zaki je,party da safe 11am fa,to baza ki fita ba,Maheera tace hmm mamata zan turawa kudi,karya kike Sohail ya bata amsa,Sahil yace yanzu suka yi waya da wani Saminu,Sohail yace Saminuuuuuu....Maheera juyawa tayi kawai zata tafi abinta Sohail yace in kika fita kin gama yawo na fada miki.


Maheera kofa ta bude tayi ficewarta,Sohail yace za ayi jaraba....yau a gidan nan,Sahil ya fara dariya yana kallonsa yace wai ko sonta kake ne? Sohail yace so? na so wannan? Maheera ce fa ita zan so kawata ce fa? Ka kyaleta taje to,yace ai yau wannan fadan da jarabar duniya sai an yita a gidan nan,Islaha tana ta dariya tace wlh da nice kai Sohail auren Maheera zanyi.
Sohail ya nuna kansa ni na aure ta inyi me da ita? tsaki ya ja ya kalli Sahil yace kai ko haushi ma baka ji ba kana kallo ta fita,Sahil yace to ina zan iya da ita.
Sohail yana ta jira ko aljanu zasu haska masa inda taje shuru ba labari,takaici ya kama shi, Islaha sai jinsa tayi yana cewa ba wani bayani? Kamar wani boka,yana cewa ba rahoto? Mene ne rahoto a kanta? a bani bayani shuru bai ji komai ba.
Sahil ya tambaya yace kai fa? An baka bayani? Sahil yace shuru ba labari.
Sohail mikewa yayi tsaye sanye cikin jallabiyya yana sintiri a palo ya kasa zama.


Maheera kuwa har katafaren building din Saminu ta nufa,har tanfatsetsen Office dinsa aka kaishi wanda ya gaji da tsaruwa,kujera ya nuna mata yace Zauna bismillah,Zama tayi a nutse sannan suka gaisa,yace I'm busy bani labari a gurguje ina da meeting,Maheera ta kalli Saminu sanye yake cikin wani yadi wanda bai da wani tsada in ka ganshi sai ka rantse da Allah ba shine me kudi haka ba,sam kudin babu kama a jikinsa.
Labarin su Sohail ta bashi a takaice,yace amma na tausaya musu wannan wanne irin azzaluman dangi ne amma laifin iyayen ne da uwarsu da uban sune masu laifi babba.
Bamu neman ma'aikata yanzu babu wajen daukan yan aiki sam amma zan iya daukan mutum daya a ciki,zan sa a koya masa aiki,idan naga kwazonsa zan bashi babban matsayi sannan sai ya koma karatu in ya gama sai ya kawo min takardunsa,kije ki tuntube su" su zabi daya a ciki sai na bashi aiki,amma nayi ne sabo da ke, jin kince shi zaki aura,Maheera tace na gode tana ta godiya suka yi sallama ta fito.
Tana zuwa gida Sohail kawai ta samu a palo ransa a bace yana ta zirga zirga tasan hali,da kuka ta shugo tare da dingishi da kafa,rudewa yayi ganin ta dawo da kuka sai ya manta da fadan da zaiyi,ya karaso da sauri ya riketa yana tambayarta menene? Lafiya?


Maheera tace faduwa nayi mota ce ta taho kamar zata kade ni garin gudu na fadi,Sohail yace sannu to muje asibiti? tace no ina jin sauki,yace okay to tana dingishi sai ya dauketa cak,taso tayi dariya,sai ta fuske ya kaita har dakinsu,Islaha tana kwance a gefen bed yace matsa ke,Islaha ta matsa can baya ya kwantar da Maheera sannan ya cire mata takalman kafarta ya adana su har jakar a inda take ajiyewa ya sa mata,mayafin ya cire mata a hankali ya ajiye gefe ya kalli Islaha yace Jinya zanyi ki sauka kwanciya zanyi,Ba shiri Maheera ta mike zaune tace naji sauki wlh dama kadan ne,Sohail yace idan kinga banyi jinyar nan ba to na mutu,Islaha tana ta dariya ganin yanda Maheera take ta zare idanu.


Sohail Saman bed din ya haura ta mike zata gudu ya jawota ta fado kansa,tace dan Allah ka bari ba kyau,yace duk masu jinya haka suke da raki, Islaha kawo min ruwan zafi a bowl,Maheera tace na shiga uku dan Allah Sohail na yafe ka kyaleni,tsaki yaja tana rike gam gam a jikinsa,sai da Islaha ta kawo ruwan a bowl da towel karami tana ta yiwa Maheera dariya,Sohail duk ya shaketa a jikinsa,kokawa suka shiga yi shi Ita,hakan sai ya masa dadi kamar wasa suke yi,ba shiri tace iya kafa ne gata ka gasata ta miko masa kafar,sai haki suke faman yi,kafarta me kyau fara ya jawo tare da dorata a cinyarsa ya matse towel din yana dannawa a kafarta,ruwan yayi zafi fa Sohail ka rage zan kone,ko kulata baiyi ba sai da ya gama gashinsa sannan ya mike ya fita.


Islaha tana dakin bayan ya fita Maheera tace to dariyar me kike kuma? Islaha tace wlh duk ya taba miki duwawu da kirji kamar ya kama namiji,Maheera tace ina ji ai,dadi kika ji kenan? dariya tayi tace uwar dadi naji,ki zauna na baki labari amma to be sincere jikinsa wlh dadi kamar kar a daina ta furta tare da rufe fuskarta da tafin hannayen ta, Islaha tayi dariya tace yau kwana zakiyi kina tunaninsa kenan? Hmm kawai tace.


Zama tayi Sannan Maheera ta bata labarin Alhaji Saminu da haduwar su da kuma yau abinda yace,Islaha sai murna tace Alhmdllh,yanzu su biyun zaki samu kiwa bayani daya sai ya barwa daya.


Zuwa dare ganin su Adnan suna palo sai Maheera ta kirasu a sirrince suka koma garden har Islaha,Zama suka yi Maheera ta basu labarin komai akan aikin,Farin ciki ya kama Sohail da Sahil suna ta murna,Sohail yace na barwa Sahil yaje yayi aikin,Sahil yace a'a kai zaka yi ni na fika zafin nema.
Suna haka Islaha tace ga takarda mun rubuta daya yes daya no wanda ya dauke yes shine zaiyi aikin wanda ya dauki no sai yayi hakuri sai nan gaba rabonsa in ya zo,Takarda ta watsa guda biyu a nanade,Sohail ya zaba Sohail ma ya dauka ko wanne ya bude,Sohail shine ya dauki Yes Sahil kuma no? Sahil yayi dariya yace Allah yayi zabinsa.
Maheera tace to sai ka tattara iya takardun da kake dasu gobe kaje ka same shi a Office,ga address zan baka,Sohail yace na gode taho

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login