Showing 9001 words to 12000 words out of 76019 words

Chapter 4 - MUMMUNAR DABIA PDF BY ASMA BAFFA

22 Aug 2025

284

kyakyawar gaske yar fulani da ita,Jakarsa ya dauka tare da gyara zamansa a gefen yarinyar ga kafadarsa ga tata,gashi motar wani kan wani ake hawa ba wani Space dole a haka ake zuwa.


Sohail ne daga kasa a tasha ya kwalawa Sahil kira,Sahil ya mike tsaye ya daga masa hannu suna dariya,yace karka manta in kaje ka kirani, inshaallah bro,ka kula da kanka,Sahil ya daga masa kai,mutane suna ta hawa motar kamar kasa,Sahil mamaki ya kamashi,gaba daya ba space a motar,wani akan wani haka ake a ciki,ko shanu baza a saka haka ba,jikinsu har yayi futu futu da kura,ga wasu gaba daya wari suke yi,ya rasa inda zai saka kansa a motar.

Wari ya isheshi,budurwar dake gefensa ya kalla ta toshe hancinta itama an matse ta da kyar take shakar numfashi a haka motar bayan ta dame da mutane babu kalar yaren da babu a ciki ta tashi ta hau kwalta suka fara tafiya.


Budurwar ce ta kwala ihu wani ya danno kanta tace wayyo zai kashe ni...zan mutu.....tana jan numfashi da kyar, Sahil ne ya dagata tana daga zaune ya dawo da ita saman cinyarsa,tace kai malam dan iska sauke ni,haka kawai ka dorani bisa cinyarka,suka fara kokawa da Sahil yace dole ki zauna ai nan yafi Safe,kina safe waje za'a kashe ki a nan wlh a banza,kina yar yarinya har kin san iskanci ne dalla rufe mana baki ko na kwada miki mari,budurwar ta zaro ido,wanda suke kusa da su sai dariya da ihu,wani dattijon banza yace wallahi kun dace kuma sai ace ma kanwarka ce kuna kama,Sahil yace na fita kyau ai,Budurwar tace Allah karya ne inji wa ka fini kyau?


Jifa taji anyi da ita a motar,wanda ta fada kan mutane sai da taji rauni,sabo da bata san Sahil ba shi a tabin nasa zafi ne da shi,mutane suka sake hankadota,kuka ta saki taji wuya,da kyar ta samu ta dawo wajen zamanta,Sahil shi kanshi motar ta ishe shi ya rasa inda zai sa kansa,ya gaji da tsaiwa ya gaji da zama.


Tausayi ya bawa budurwar tana satar kallonsa duk ya gigice kamar kansa da motsi,ana haka ruwa ya tsuge da iska me karfi,jakarsa tayi sauri ta jawo ta saka masa a cikin katuwar ledar da ta taho da ita yanda ruwa bazai taba ta ba,Suna tafiya ruwa na zane su a hanyar lagos,sai da suka kwashe lokaci me tsawo ruwan ya tsaya,mura da zazzabi suka kama Sahil,sai rawar sanyi yake,budurwar ta kalle shi tace ka canja ko rigar jikinka ce,bata jira amsarsa ba ta zuge ta zaro riga me kauri ta bashi,ya karba da kyar ya cire rigar jikinsa matan dake motar suka zubawa surarsa Ido suna kallon cikar sura da zallar kyau na halittar Allah,rigar ya canja,ta karbi wacce ya cire ta ajiye a gefe,dake ita da ledoji tazo manya ana ruwa ta saka abinta,ruwa bai jikata ba sam.


Gyangyadi ya fara bai sani ba ya dora kansa a saman kafadar budurwar ,da sauri ta juyo ta kalle shi zata yi magana ya dagata sai taga bacci yake sai kawai ta hakura ta kyale shi,kowa ya zaci tare suke ma mata da miji ne,basu san kowa tafiyarsa daban ba,wata mace dattijuwa tace gaskiya kinyi dacen miji 'yar nan gashi kamar yaro shagwababbe da shi ba ruwanki,dariya ta kusa kwacewar budurwar sai dai ta fuske tace uhm kawai, suna tafiya duhu yayi ba sallah ba salati ga uban duhu suna tafiya a daji,Sahil baccinsa yake kawai shi,zamewa yayi a hankali cikin bacci ya dawo da kansa kirjin Budurwar,tana jinsa gashi ko bra babu a jikinta, fuskarsa ya dinga turawa cikin kirjinta kamar zai sha nonon uwarsa,duka ta dirka masa a bayansa ya farka a hankali ya bude idonsa,sai lokacin ya tuna fa a mota yake.


Muryarta yaji me dadin saurare tace ka tasar min a jikina, tashi yayi a hankali yace ruwa....dariya ya bata tace lallai ma wannan wai sai kace yaro mutum da gemu kato da shi amma ni ina karama yake min haka, sai ka bari ai aje inda za a tsaya sai ka siya ka sha,wai kamar ba namiji ba kai,shuru ya mata yana zaune a gefenta ya sake komawa baccinsa.




Motar su ce ta lalace a dajin kowa tsoron hanyar yake,ana ta salati masu addua suna yi amma Sahil shi baccinsa yake ma,sun dade a wajen kafin ta tashi suci gaba da tafiya,sai cikin dare suka samu aka tsaya a garin yarabawa tasha suka firfito kowa ya tafi neman abinda zai ci da masu sallah,budurwar ce kadai ta kasa fitowa kafarta daya waje daya a ciki,Sahil yayi dariya sannan yasa hannu ya dakkota kamar ya dauki tsinke ya direta a kasa.


Kunya ta kamata ta diririce, Masallaci ya nema yaje yayi sallolinsa itama haka sannan yana fitowa ya siyi Apples,ya siyi ayaba,ya siyo naman kaza,sai ya siyo yogurt da lemo ga ruwa da wuri ya dawo cikin motar sabo da kar a fara turereniya,Ita kuwa budurwa bata da ko sisi na siyen komai kawai motar ta koma sabo da itama bata so a dinga ture ture da ita wajen shiga,shi kadai ta samu a ciki ya hau saman jakarsa ya zauna.


Kallonta yayi yace ya baki siyo komai ba? murmushi tayi tare da zama tace banda kudi ni,yace tab rayuwa sai da cin abinci,ki dinga cin abin kanki,shi yasa bakya ci gaba kullum jiya i yau gaki nan tsiya tsiya sai son kudin tsiya, kici a jikinki baza kici ba sai shegen asusunki a boye,Ido budurwar ta zaro duk abinda ya fada gaskiya ne,bata kashe kudi,indai abu ne wai tasa kudi ta siya sabo da ta ci to baza ta siya ba kuwa sai dai ta tara kudin a asusunta.


Abinda ya siyo ya mika mata gaba daya yace gashi ki cinye,baki ta bude tace kai fa? Yace kici kawai in kin rage ni na ci,tace no ai baza ayi haka ba to muci tare, a hasale yace kici dalla ko na kwashe na zubar,mamaki ya kamata,ita wannan wanne iri ne,haka ta fara ci duk abinda take sai da taci da yawa tace na koshi alhalin bata koshi ba.
Yace baki koshi ba kici karya kike,"hmm" kawai tace taci gaba da cin abinta sannan tace ya sunanka wai? Yace "Sahil",tace ni kuwa...katseta yayi yace sunanki Islaha,baki ta bude tace a ranta ko ba mutum bane wai,amsa taji ya bata yace mutum ne mana.


Tsoro taji yace ki daina tsoro mutum ne,ido ta zaro ta kasa cewa komai,yace zan iya fada miki asalinki gaba daya da tarihinki tsaf, tace to fada min naji.

Asalinki ku ba hausawa bane wani yare ne ku can yankin Taraba State wanda kamar fulani kuke da shanunku da komai amma ku ba fulani bane kuma,iyayenki yan Taraba ne,Babanki mahaifi sunansa Sule mamanki sunanta Halisa ana kiranta Nany,kuma ke kadai suka haifa sannan sun rasu, a hannun kanwar Mamanki kika taso a taraba,karshe itama mijinta ya rasu ta fara tuwo tuwo,daga nan ita da yaranta data haifa mata su uku namiji daya gaba daya da yaran nata karuwanci suke yi.


Cikin yaranta babbar yarta Shema'u ta zama me kudi sabo da karuwanci,ita kanta kanwar mamanki da sauran yaranta sun zama masu kudi sun koma lagos da zama a nan suke rayuwa ba ruwan su da sa ido na hausawa da dangi,kece anyi anyi a fara koya miki kema ki fara kinki yarda,shine ta maida ki yar aikinta wanda yar aiki ma ta fiki daraja a wajen su,azaba suke gana miki,yanzu ma aikenki tayi kauyen ku kika kai sako shine zaki koma,sannan shekarunki ashirin da biyar 25, sannan abinda yasa suke so kema ki fara sabo da kina da kyau matuka gaki da diri me kyau komai naki yayi,duk wani namiji zai so ace ya mallake ki.
Kina son white color,kina son sakwara da miyar egusi,kina son wankan shadda,sannan period 4days kike yi....kuma....Islaha taji tonon sililin yayi yawa komai ya fada ba karya a ciki,ta dakatar da shi tace naji to,yace sannan kin gama secondary kin shiga NCE sai suka daina biya miki dole kika hakura da karatu.


Mukus tayi duk abinda ya fada ba karya ciki,abincin ta mika masa tace na koshi,lokacin ya karba ya fara cin abinsa,ido Islaha ta tsura masa tana kallonsa kamar mayya,na miki kyau ne? ta tsinci muryarsa ya furta ba tare da ya kalle ta ba,da sauri ta dauke kanta ta fara wasa da yatsunta tana yarfe hannu,dariya yayi ba shiri tare da kamo hannunta yace mu gani ciwo yake,a hankali cike da kunya ta zame hannunta,tambaya ya jefo mata ke baki da kayan wasa ne muyi wasa? Cike da mamaki tace wanne irin wasa? A gidan ku ba a siya miki doll Baby su Teddy,murmushi tayi tace da girman nawa? baki ya turo,jajayen lips dinsa suka birge ta,kanta ta sadda kasa sabo da kunya,sun dade a haka kafin mutanen motar su dawo suka ci gaba da tafiya abin su.


Sai washe gari da safe suka isa lagos,Islaha bayan sun sauka,ta tambayi Sahil ina zaka kai? yace gari mana ya juya dauke da jakarsa yayi tafiyarsa ko waigowa bai sake yi ba,baki ta tabe tayi tafiyarta itama.


Gidansu ta nufa a taxi tana zuwa Kanwar Mamanta da suke kira da Aunty ta ga ta shigo da safe,ranta a bace tace uban me kika tsaya yi Islaha baki dawo da wuri ba,aikin gidan nan uban wa zai miki? Islaha cikin tsoro tace kiyi hakuri kin san motar da kika ce na shiga bata da sauri ga tsaye tsaye shi yasa,ke dalla rufe mana baki cewar Khairat yar Aunty ta cikinta,a kalla zata kai 30yrs,kanwarta Khalisat ce tace wannan fa sam bata da saiti,Islaha tayi shuru dai ita,Aunty tace ai kuwa ga aiki nan ya taru sai ki fara,a gajiye Islaha take amma haka ta fara aikin gidan.


Gidane me kyau cikin estate duk gidajen layin iri daya ne,gidan yana da kyau a me rufin asiri dai a lagos duk da unguwar ta masu karamin karfi ce amma tayi kyau,Islaha sai da ta gyara gidan tsaf ta gama komai tazo ta dora girkin dare,Khairat tace wankin namu fa sai yaushe? Zanyi gobe inshaallah,da sauran rana a gari madam ki wanke mana kaya,Khalisat ce ta kawo mata kaya ta jibge,Islaha haka tana girki tana wankin sai da ta gama tas,Allah yasa ma kayan ba dirty,sai da ta gama komai sannan ta samu tayi wanka ta canja kaya cikin riga da wandonta yan gwanjo amma sun mata kyau sosai abinka da me kyau,abincin ta ebo taci ta koshi,tana palo Yaseer ya shigo babban dan gidan Aunty,Aunty tace Yaseer bana son wannan yarinya r da kace zaka aura Rukayya take ko,Yaseer ya kalli Mahaifiyar su ya furta amma kin san an sa rana fa!

Aunty tace ai baza ka aure ta ba gaskiya na tambayi malamai na sunce sam ba Alkhairi a auren ku sannan indai ka aureta sunce kai da arziki sai dai kaga ana yi,nasan tun tana karama kuke soyayya hasalima ta samu mazajen aure amma ta makale sai kai ta dinga jiranka tun bamu da kudi gashi muna da rufin asiri amma baza ka aure ta ba,malamai sunce babu alkhairi.


Islaha tana jinsu tace amma ai ba wanda ya isa ya hana wani arziki a duniya,Allah shike bayarwa shike hanawa,Aunty rankwashi ta zubawa Islaha tace wlh idan ina magana kina sa min baki sai naci ubanki, shuru Islaha tayi tana jinsu har Yaseer dinma katon jahili ya yarda da abinda uwarsa ta furta,yace to Aunty ai kuwa sai dai kije wajen Malamai a cirewa Rukayya so na a ranta,idan ba haka ba ta ya zan iya cewa na fasa? karka damu wannan me sauki ne za a sa taji bata sonka da kanta tace ta fasa,ya furta to shike nan tunda ba alkhairi me zanyi da ita yanda nake so nayi kudi ido rufe.


Sahil machine ya hau yace kasuwar 'yan tumatir zaka kaini,me machine kuwa ya kaishi babbar kasuwar tumatir dake Lagos,hausawa da yare ne damkam ana ta hada hada,Sahil ya tsaya rataye da jakarsa yana kallon abinda akeyi,gashi su baza su iya aikin karfi ba,wani ne a ciki ya kalli Sahil ya ganshi ya dade a tsaye,ya zaci wani shahararren me kudi ne yazo daga kasar waje zai siyi tumatir,da sauri ya karaso gabansa yace


Good day sir, Hausa Sahil yayi yace sannu da aiki,ashe kana jin hausa ai na zaci daga Tunisia ka sauka,Sahil yace no,okay kaya zaka siya ne? Mota nawa kake so?
Sahil ya kalle shi yace aiki nazo nema ni dan gidan malam shehu ne,mutumin ya kalli Sahil sama da kasa yace aiki? Irin wanda muke yi na karfi na sauke tumatir daga mota?
Sahil ya amsa da ae mana shi,ai gidanmu ma sabo da bani da kudi idan aka ga hadari ya taso har danyar daddawa ake kaimin dakina na kwana sabo da kasan life no balance at all,yanzu idan baka da shi a gidanku sai uwarka ta mutu baka sani ba.


Wanda suke magana me suna Aminu dariya ya dinga yi yace gaye kamarka sabo da talauci sai a kai daddawa dakinka na kwana?
Sahil yace sai dai in hadari bai taso ba amma yana tasowa za a kawota a faranti.
Mutumin yace au baka da ko sisi a haka?kalli fa kayan jikinka sai me kudi ke sa irinsu"
Sahil ya furta ae nema dai zanyi,dariya mutumin yayi sosai yace kalli kalarka fa zaka iya kuwa? Zan iya mana,mutumin yace sunana Aminu to kaifa? Sahil nake,yace indai aikin wahala ne baya wahala zaka samu,ka sauke duk kwando daya 50 Naira.


Sahil yace zanyi haka,Sahil suna da karfi wanda bana mutane ba ma amma na aikin banza da anzo wanda mutum zai amfani kansa da shi sai lalaci yazo ya lullube su karfin bazai zo ba sam,haka ya ajiye jakarsa ya ratsa ta cikin kwandunan tumatir,Aminu yace waccen motar zamu je,suna karasawa Sahil ya shige cikin katuwar trailer a dole ya fito neman kudi,kwandon tumatir ya duka zai daga amma yayi yayi amma ya kasa,matasa dake wajen suka dinga ihu da dariya.


Sahil zuciya ya sake yi ya yunkura zai dauka amma yin duniya ya kasa yana matsawa kansa ma sai ya fada saman sauran kwandunan,mutane wannan ya ja hankalinsu aka taru ana kallonsa yana ta faman nishi da haki,mutane suna ta tunanin hutu ne ya masa yawa kawai duba da kalar jikinsa ana gani an san ajebo ne,masifa suka fara masa ya sakko musu daga mota,haka ya sakko kawai jikinsa a sanyaye.


Wajen masu abinci ya nufa sabo da tun a mota bai ci komai ba,ya samu ya siyi jullof din shinkafa da yankan namansa biyu ya zauna yaci ya sha pure water sannan ya mike ya mike ya koma cikin kasuwar.

Aminu ya kira ya tambaye shi dan Allah a ina kuke kwana? Aminu yayi dariya tare da nuna masa wasu dakuna na langa langa yace kaga wannan dakunan a haka duk shekara kasan nawa muke hadawa muna biya? Sahil ya tambaya nawa? Yace dubu dari biyu kalli dai dakine kamar container,a haka ma munfi mu ashirin a ciki wani kusan a kan wani yake kwana,sannan ka jira kaga wasu a inda suke kwana.


Sahil yayi mamaki ya koma gefe ya zauna,ga hadari ya hado sosai,yana zaune aka fara yayyafi sai yaga duk wasu suna saka rigar ruwa ga dare yayi wasu a cikin kurar ruwa da suke turawa ta eban kaya a ciki yaga sun saka kwali sun kwanta,wasu yan achaba a saman machinan su suka hau da rigar ruwa suka kwanta ruwa na dukan su,abin babu kyan gani yanda wasu a hausawan mu da gatansu da komai amma suke tafiya suna zubarwa da arewa mutunci,baza ka taba ganin yare a haka a wulakance a arewa ba da sunan neman kudi amma yan arewa duk inda kaskanci yake suna can,kana magana ace neman kudi ne,neman kudi sai mutum ya jefa rayuwarsa a hadari bayana a arewa ma wani yana da jarin da yafi zamansa a can.

Sahil dare yayi yana wata yar runfa a tsaye ya fake ga mutane sunyi yawa,wasu yan shaye shaye ne suka zo da gudu suka hankado Sahil cikin ruwan suka tsaya a rumfar babu inda Sahil zai fake gashi dare yayi ga ruwa ana tsinkawa kamar da bakin kwarya,waige waige ya fara cikin ruwan amma ba inda zai shiga,gani yayi babu amfanin tsaiwarsa kawai yabi ta cikin ruwan yana tafiya wanda bai san inda ya dosa ba,ruwa na dukansa yana ji wayarsa tana ringing yasan Sohail ne ke kiransa yaji ya sauka lafiya ba damar daga waya.


Yana ta tafiya cikin ruwan har ya bar layin ya shiga wani layin me kyau wanda bai san a ina yake ba,dai dai wani katafaren hotel yazo zai dan fake a jikin katangarsu, cikin tsararen hotel din ya kalla ya samu ya rakube ya fake a jikin wajen ya tsuguna! a haka yayi baccinsa har rana ta fito bai sani ba,karar mota ce tasa ya bude idonsa,kafafunsa har kumbura suka yi sosai,da kyar ya iya mikewa tsaye ya sake kallon cikin hotel din kenan


Ido ya zaro yana kallon Islaha wacce suka zauna a mota budurwa tsaleliya cikin damammun kaya, bum short ne a jikinta da guntuwar riga gaba daya ta kudundune jikinta sai kakkare jikinta take yi tana jin kunya wanda da kyar take tafiya da alama bata saba ba,ga duwawu kaya guda komai ya ji,a gigice ta fito ta fice da sauri bata iya kallon kowa ta tare taxi ta fada ciki suka tafi,Sahil yana tsaye yana mamaki


Ya furta wonder shall never end,so duk mata haka suke wannan wato mummunar dabiarta ce ashe amma a haka kamar ta kirki,tsaki ya ja yana mamaki yace

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login