Showing 54001 words to 57000 words out of 76019 words
ta raimake ta.
Sai da ta koshi sannan tayi wanka ta zauna ta zuba tagumi tana tunanin Sahil.
Sai da ta kwana uku a gidan Hajiya kulu tace Islaha kawai ki zauna a wajena ki dinga tayani siyar da abinci a wajen saida abinci na mana nan gaba idan an samu aiki me kyau sai na kaiki can, Islaha tace ba damuwa,daga ranar Islaha bata sake kuka ba, idan suka shirya abinci a gida sai a zuba a manyan kuloli su jera a cikin kurar ruwa su tura zuwa layin da Hajiya kulu ke siyar da abinci,wata rumfarta ce da katon tabir da benchi sun kai hudu na zaman samari masu siyen abinci,Tebir din kuma a samansa suke jera kulolin.
Islaha kurar ta turo sanye take cikin riga da skert na atamfa tana tura kura sai ga Khalisat,Khairat,Aunty da Shema'u sai Yaseer shine ke tuka su a motar Shema'u,da sauri Aunty tace tsaya tsaya ga Islaha can tana tura kura ta koma tuwo tuwo.
Aunty duk da ita ta kori Islaha bata ji dadin ganinta a haka ba yar yayarta ce ta jini,a gaban Islaha yayi parking,Yaseer yace Aunty baki kyauta ba wlh banji dadi ba bai kamata ba,Khalisat tace shegiya gwara haka gwara da aka koreta bata da kunya,na samo saurayina kyakyawa ta rabani da shi.
Aunty ce ta bude mota ta fito tana bulbula kamshi ta sha kitson Attach,Islaha tana ganin itace ta dauke kai,Murmushi Aunty tayi tace kin iya rashin kunya baki da abinda kika taka a kasa yanzu ina amfanin wannan rayuwar? kizo mu koma gida kici gaba da zama amma sai in zaki canja hali kibi umarni na,Islaha tace Allah ya kiyaye ni ba asararriya bace.
Gwara nayi wannan sana'ar ta fimin na bawa maza kaina,Aunty tace kije jiki magayi ta shiga mota tace Yaseer muje naga alama bata ji jiki ba,Yaseer yace ke Aunty...ja mota muje ko naci uwarka wlh,motar ya ja suka bar Islaha a tsaye,kurarta ta tura tana hawaye har ta kai abincin rumfa.
Maza da yawa sunzo siya su suka dora mata abincin a saman tebir sannan ta fara zuba musu tana karbar kudinta,wani matashi yace ki sa naman kato fa ke,Islaha ta kalle shi kawai ta zuba masa a robar take away, ya karba yace kudin sai na dawo,tace hey.... don't Dear me miko min kudina bana son wasa ta bata rai,ba shiri ya mika mata kudinta ta karba ta saka a jaka ta bashi canjinsa,sai daga baya Hajiya kulu tazo.
Amarya ce taci gayu cikin sabuwar atamfa doguwar riga ta mata mugun kyau,dauri taci ture kaga tsiya baya ta gyara gashinta har baya ta sa ribbon kalar atamfar dark green,tana kamshi Sohail ya kalleta yana murmushi,Murmushin tayi masa itama,kinyi kyau yace,tace na gode kaje kayi kaima,yace nayi da asuba sai anjima,tace oh na tuna,yace ae bana karya dan a so ni,tace nima haka,yace aka sani ko na amarci kike yi,Maheera fuska ta bata ta juya,hannunta ya ruko yace hijab din fa,tace sai kace na sa kana nan kaya kullum kace sai na saka Hijab ina gidan mijina,Sahil fa yana nan,to a haka wacce shiga nayi ta rashin dacewa kowa zai iya ganina a haka haba Sohail wannan wanne irin kishi ne, Sohail yace namijin kishi ne dani.
Juyawa tayi zata fice yace dan Allah to sa mayafi please Baby,dariya tayi ita zai wa wayo har da Baby,zuwa tayi ta dauki mayafi kalar kayan ta yafa tace Allah idan kace Baby sai naji ko nayi fushi gaba daya na huce,yace Baby wuya a waje da gashin da dai Hijab dinne,harararsa tayi yace to jeki na hakura muje ya mike yabi bayanta sai kakkareta yake.
Sahil yana palo shi karinsa yake suka fito suka iske shi yana cin abincin,Maheera tace ina kwana Sahil? Kallo daya yayi mata yace lafiya lau Amarya ta Ango,Sohail hannu ya mika masa suka gaisa yace nazo da safe kana bacci,Sahil yace zo kaji,Sohail ya duka ya mika masa kunne yace iceko ba aci amanata ba? A jira Islaha fa,Sohail shima da rada yace banyi komai ba,sai faman kus kus suke,Maheera ta wuce Dining ta zauna tayi serving kanta tayi serving Sohail ta hada masa tea da komai sannan tace Sweet yunwa nake ji.
Sohail zama yayi a dining yace har kin zuba min komai? tace ae yace Allah ya miki Albarka,bari na baki a baki,Maheera tace a ranta abu kamar hawa da sauka ayi daidai a dawo a kauce, chips din ya tsikaro da fork spoon ya sa mata a baki Maheera ta tauna jin dadi yau tafi kowa a duniya jin da takewa kanta,sai murmushin jin dadi take Sohail yana bata a baki tana ci yana ci shima, Sahil yana can daga palo yana cewa a dai tsaya iya nan.
Sohail yace karka damu yana sa tissue yana gogewa Maheera baki,Maheera dadi ya kashe ta tace haiiiiii Sweet tana wani sosa cinya kamar wacce Aljanu suka shigeta
Sahil ya kalleta dariya ta bashi ma ya dauke kansa yace sabo da anga bani da ita shine ake cusa min takaici,dariya Sohail yayi ya yace zata dawo ne kaima kaji ka daina damuwa,ni da zaka yarda ma da na aikeka,Sahil yace Ina? yace kaje ka gaida babar Maheera kafin nazo kace na gode da aka bani ita,Maheera harda rufe fuska sabo da farin ciki,Sahil yace bazan je ba gidan Aunty Aisha zanje tace naje wai za a kawo garar Maheera zan taho da su nan,Sohail yace har wata gara za a kawo ni na yafe kar a kashe min zuciya a barni nayi cefane na.
Sahil yace wlh sai mun karba in ba haka ba ta shiga uku da gorin dangin miji,na dinga gori kenan na dinga ce mata yar rashin gara,gwara ma a karba,Maheera tace sai ku kashe mutum da dariya jeka dan Allah,Sahil ya karbi key ya fita.
Yana fita Maheera ta mike tsaye Sohail yace zauna ke wai bakya zama kawai sai kin hau min jikina,Maheera tace to wai ba mijina bane ni shike nan bazan ci abincin ba ma ta juya zata tafi,da sauri ya riketa yace to zauna kadan amma karki dade ya gyara mata cinya,Maheera ta zauna ita kanta ba sabawa tayi ba kawai so take ta canja shi ya gane me akeyi.
Sahil yana fita yaga motocin Daddy sunzo kofar gidan,Sahil yayi mamaki,parking suka yi driver ya bude masa kofa ya fito,Sahil yace Daddy kaine kazo gidan nan? Daddy yace ae nine zuwa nayi naga zahiri,Sahil ya juya yace to muje suka shugo har palo,Maheera tana saman cinyar Sohail a zaune suna cin abinci sai dariya suke yi,Sallama suka ji kawai.
Daddy ya zaro ido ganin gida mashaallah,Maheera da sauri ta mike tsaye tana gyara mayafinta,Sohail yace Daddy? Alhaji Ali ya kalli gidan yace uhm ashe kuwa da gaske kuke yi shi yasa na kawo muku ziyarar bazata.
Maheera ta mike taje palon tace sannu da zuwa Daddy,zauna Daddy,Daddy yaso ganeta yace kece yar aikin su Adnan ce ai,tace ae nice,zama yayi yana mamaki yace Allah me iko kamarki kika amince lallai kowa baya rasa masoyi,ina ganin ai ko kamar su Adnan a yanda Allah ya tsaraki ko kamar su Adnan sai sun kai ruwa rana sai kuma gashi to Allah me iko.
Maheera dai durkusawa tayi har kasa ta gaida shi ya amsa yana ta faman furta Allah me iko.
Sahil yace kar dai ka kyasa Daddy ba kyau,shi yasa aka ce ka samu wata yar bazawara ka aura ka dinga mai da yawu amma kaki,an rasa me keka yi,idan baza ka iya ba mu yan mata kawo kansu suke wajen mu ka bamu zabi muyi maka hanya da dai dai kai,kunya Maheera da Daddy suka ji amma su twins ko a jikin su.
Sohail yace Daddy ina kwana da sassafe sai ka taho gidan Amarya,ai ba a zuwa gidan yara da sassafe,Sahil yace ina kwana Daddy ya amsa duk sai da suka rusuna sannan suka gaishe shi.
Maheera ta dinga kawo abinci tana dire masa,su farfesu ya zaci ma ita ta girka,ta shiga kitchen ta kawo lemuka da ruwa tace Daddy ga abinci dan Allah ko kadan kaci.
Daddy ya cika da mamaki sabo da saka ido sai da yaci ya tabbatar yaji ya girkin yake,yaji dadi,Sohail yace ba ita tayi bama nata yafi wannan dadi na gidan Aunty ne wannan,ai wannan ka taba cin girkinta kaji wlh ko kakar mu Iya me Koko bata kaita iya girki ba,Daddy har sinasir ta iya,Daddy yace zaka ci uwarka Sohail ni kake fadawa ko Iya me koko bata iya ba,uwar tawa mahaifiya, Sohail yace to yan zamani sai yan zamani ai,Sahil yace wannan Special ce ba irin su Zayna bace me hanci kamar tulu.
Maheera tana durkushe a kasa,Sahil yace tashi ai kin nemi Taskirar zaman ya isa haka,Daddy yayi shuru yana jinsu yayi murmushi,Sohail yace nidai ko kowa bai yaba ba tunda ni na yaba ina son abata shike nan.
To ku zauna cewar Daddy,zama suka yi yace shi aure da kuke gani Ibada ne,Sohail yace a'a mu ba sai an mana nasiha ba mun sani,da can ba a damu damu ba sai da aka ga munyi abinmu,ko gudun muwa ba a bamu ba,a barmu idan ma duka ne mu nadawa matan namu,kudin mu ne,Daddy yace ai shike nan ya mike zai tafi Maheera tace Daddy ka gaida gida.
Yace Madalla Madalla ya fita ya tafi Sahil ya bishi yana cewa da ka tsaya an kawo garar ko kwano uku ka dauki shinkafar ba komai wlh mu har abada mahaifin mu ne kai.
Daddy ya rufe motar yana dariya ya sauke glass Sohail yace gara ai ana bawa gidan iyaye nasu Daddy ka tsaya ka tafi da ta gida duk da cewar gwauro ne kai.
Daddy son gulmarsa tasa yace Sohail yanzu kai wai hankalinka ya kwanta ko kai ga ango? Sohail yace ya hankali na bazai kwanta ba da mace fa na kwana jiya,kai kuwa yaushe rabo,ni wlh na daina jin haushi ma in kayi mana wani abun Daddy na gano dalili babu mace.
Daddy ya bawa driver Umarni ya ja mota ya tafi sai dariya yake ta yaran nasa yanda suke wanke shi tas.
Washe gari Daddy ya kira Sohail da Sahil yace suzo zasu gaisa da wani Ogansa a harkar Business,yace yana bukatar yaga yaransa gaba daya.
Sohail yana kwance yayi pillow da cinyar Maheera suna kallo a hakan ma da kyar ya yarda ya kwanta a cinyarta itace ta nace sai ya kwanta.
Sahil ne ya fito a shirye yace ka manta Daddy na jira,Sohail ya mike zaune Maheera tace ai ya shirya shima,Sahil yace da jallabiyar zai fita? tace ni to bana so wata ta ganshi,Sohail yace kyaleta muje Sahil hakan wannan yarinyar bata yarda dani,ai zata zo fita ne Allah zai kaimu itama ai tana so ta yafa mayafi,muje wallahi kika bari na fita haka kullum da hijab zaki fita.
Dariya Sahil yayi,Maheera tace muhe to ka canja abinka,tashi yayi ya wuce bedroom kafin ta shiga ya kulle ya sa key kar taga tsaraicinsa shi kam.
Sai da ya shirya ya fito ya wani mika mata turare fesa min,Maheera ta karba ta fesa masa,Sahil tausayinta yaji tabbas tana da matukar hakuri sosai ba karamin son Sohail take ba.
Sai da ta rakashi har mota suka tafi.
Suna tafiya Sahil yace tana sonka da yawa kaji dadinka,ka kula da ita,ance fa ana tabe tabe mata suna so ka dinga yi mata kar dai a zurfafa sai Islaha tazo,Sohail yace karka damu ina jiranku ba abinda ma zanyi.
Ko nisa basu yi ba ya kira Maheera ta daga yace yaya gidan? murmushi tayi tace lafiya lau,me zan siyo miki to? tace duk abinda ya dace,yace to shike nan,ki dinga hakuri dani kinji,tace to ba damuwa ai,yau kiyi girki da dare nace wa Aunty kar ta kawo,Maheera tace ae hakan yafi kar a wahalar da ita,dan Allah karka bari wata ta kalle ka,yace su da idon su sai na hanasu yaro da kyawunsa,Allah ya musu ido na isa idan nace bazan bari ba nayi karya gaskiya,wannan karyar soyayyar da ake fada bada ni ba,Maheera ta dinga dariya tace gaskiya fa ka fada kuma,yace duk karya suke muku maza,makaryatan banza makaryatan wofi,Allah yayiwa bawa ido wa ya isa ya hanasu gani,gani me kyau dani Alhmdllh ahh su kalla su kwashi garabasa ni dai bazan ce ina son su ba ko ya kika ce? Maheera tayi dariya tace I love you sai ka dawo,missing you already ya furta,yana kashe waya Sahil yana driving yace ana ci min mutunci a kasar nan.
Suna shiga palon su Adnan suka samu Daddy da wani babban mutum,ga su Adnan a gefe suna hira ga kayan abinci ana ta ci,dattijon yana dagowa yaga Sahil,Sahil ma ya gane shi shine wanda ya gyarawa mota a Lagos,Baki Dattijon ya bude yana murmushi yace Sahil kaine a nan? Me kake yi?na dade ina nemanka na rasa ina zan ganka zo nan zo,Sahil yana ta murmushi ya karasa gaban Dattijon,su Adnan da Daddy suna ta mamaki.
Free page 1&2 400 ne
AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:18 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABIA🪸
41-45
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE 'YATA TASNIM
Page naki ne
Mhiz Awwal
MASU AUDIO BAN YARDA WANI KO WATA YA SATAR MIN NOVEL BA IZINI BA.
Alhaji Umaru yace ikon Allah,Daddy ne yayi magana yace wai a ina kasan Sahil ai Dana nane na cikina,Alhaji Umaru yace a Lagos ya basu labari,Adnan baki suka tabe,Alhaji Umaru ya rike Sahil yace ga me kama da shi ba babanci,Sahil yace yan biyu ne mu, mashaallah,me ka karanta ne ma? Daddy ne ya bashi amsa yace dake basu da lafiya ai sune yarana da na baka labari basu da lafiya masu Aljanu,to to sune? Ae sune basa iya komai na rayuwa,kaga su Adnan su sunyi karatu me zurfi cewar Daddy.
Alhaji Umaru yace laifinka ne baka dai fahimci inda basirarsu take ba,baka kula da su ba ka jansu a jiki ta ya zaka gane,sun fara university naga baza su iya ba kawai na cire su,Alhaji Umaru yace baka kyauta ba,Business ai ba sai da boko ba kai ka sani,sannan magani ma ai ya kamata a tsaya a nema musu magani,Daddy ya furta anyi anyi abin yaki.
Sohail yace gashi ni na samu aiki a kamfani kuma da gidana nayi aure,Alhaji Umaru yana murmushi ya furta mashaallah naji dadi,yanzu saura Sahil ko shima zan bashi aiki babba ma kuwa ni da kaina zan koya masa komai na bangaren Business zan gano inda ya cancanta na ajiye shi.
Sahil yana ji yace nifa bazan je Lagos ba,indai a lagos zaka bani aiki ka rike abinka gaskiya bana so na gode,Alhaji Umaru yace comon ina da kamfani da yawa a kasar nan ko a nan ma baka da matsala ko ina ka zaba,zo ku zauna ya jawo Sohail da Sahil suka zauna kusa da shi,su Adnan ransu idan yayi dubu to ya baci.
Daddy bai ce komai ba kallo kawai yake yi sai daga baya yace anya Sahil zai iya kuwa? Alhaji Umaru yace zai iya ba damuwa zan koya masa,ba yanda suka iya shuru suka yi,Alhaji Umaru yace da ka daure muje Lagos just 1day ma sai ka dawo ka fara aikin akwai takardu da zaka cike,Sahil yace nifa bazan je wannan garin ba na tsane shi.
Sohail ne yayi magana yace ni zan rakaka muje mene abin kikiyar Lagos zan rakaka sai muje tare kawai,nidai bazan yi ko sati daya ba,kwana daya aka ce cewar Sohail,kamar daga sama Sahil yaji ance Islaha tana can,shuru yayi kamar yana sauraren magana da sauri yace zanje ko wata daya ne zanyi.
Daddy da sauri yace to kaji irin abin nasu hawa da sauka yanzu hankali anjima hauka, Alhaji Umaru ko a jikinsa yace wannan ba wani abu bane ni zan ji da shi kaine baka fahimce su ba ai ba a haka.
Suna ta hira Maheera taga shuru shuru masifar kishi ne da ita dole sai an kula da ita,kiran Sohail tayi a waya,yau tayi sa'a yan soyayyar suna kansa yana dagawa a gaban kowa yace Sweet ya aka yi ne? Maheera sabo da jin dadi yatsanta karami ta sa a baki tana murmushi tace ya Daddy din? har yanzu baku gama ba? Kina son ganina ne? Maheera tace ae ai nafi so kullum najika kusa dani,Sohail yace an gama gani nan tunda kika ce na dawo to ai uzuri ya kare ko uzurin waye ajiye shi zanyi,Maheera tace idan baka gama ba ku gama,inaaa...sam na gama ai tunda kika kirani,nifa maganarki kadai nake ji duk fadin duniya ba wani me sani ko ya hanani,Daddy yana ji ya girgiza kai a ransa yace har ni ban isa ba na haifi da yace macece ta isa da shi.
Sohail yana wayarsa harda harde kafa minti nawa kika bani? Tace 20mnt,mikewa yayi yace to gani nan,Sahil ya kalla yace zaka tafi ne ko na barka anan? Sahil yace me zanyi muje kawai ni kaina idan ina ina ganin soyayyarku dadi nake ji.
Alhaji Umaru shi gani yake ba wani abu bane sabo da zaman Lagos da yake yi,Daddy ne yake fada a gaban manya kuke irin wannan baku san darajar manya ba,Ibrahim ya furta ai masoya ne,Adnan takaaici ya hana shi magana ma,so yake ma ya samu dama ya illata Maheera kowa ya huta yaji haushin aurenta da Sohail yayi gwara ta auri bare,kamar Sohail mahaukaci ya auri irin Maheera shi a ganinsa bai dace ba.
Alhaji Umaru ne ya rike Sahil yace zauna kai shi ya tafi