Showing 30001 words to 33000 words out of 76019 words

Chapter 11 - MUMMUNAR DABIA PDF BY ASMA BAFFA

22 Aug 2025

289

Islaha na rungume ki,Islaha da wasa ta tafi kamar gaske,Sahil ya riketa yace ba kyau fa babu aure,Maheera har ta sandare a zaune sai taga Islaha tana mata dariya a sace.


Sohail a wajen suna hira amma shi ya dauki tsinke sai faman zana zero 0 yake,Maheera tace dan Allah karka je ka zana musu Zero a takardu ka kula sosai kayi aiki me kyau,Sahil yace ai mun sha wahala kafin a samu Inshaallah zaiyi kokari ko? Sohail yace Allah ne masani yaci gaba da zana Zero,Sun dade kafin su koma ciki.


Washe gari Sohail Ya dau wanka kace shine me kamfanin yana kamshi ya fice da sauri yana gyara agogo,Adnan da Ibrahim suka bishi da kallo sun ganshi da takardu,Ko kulasu baiyi ba bai ma nuna ya gansu ba ya wuce,dariya suka yi Ibrahim yace ana asarar wanka a hanya,Adnan yace wallahi dariya suke bani.
Sohail kuwa sai da yaje aka masa iso ciki wajen Ogan,yana shiga yaga yar yarinyar Oga Saminu kyakyawa da ita tana wasa a Office din,shi ai ya samu abin so sai ya dauketa yana dariya yace taho muyi wasa,yana ta mata wasa,Saminu a duniya yana so yaga me son yaransa,ai sai yaji kaunar Sohail,Yace kaine wanda Maheera tace? Yace ae nine ya mika masa hannu suka gaisa,daya hannun kuma yana dauke da yar Saminu,yace kaine wanda zata aura kenan mashaallah kamar ba dan kasar ba,Sohail yayi dariya yace haka ma dan uwana yake baza ka gane mu ba,zama yayi ya nutsu yarinyar tana cinyarsa,Oga Saminu sai wani washe baki yake an dauki yarsa,yace sauketa muyi magana to,Sohail ya ajiyeta yace Maheera tace nayi kokari na nutsu shi yasa zan ajiye wannan yarinyar kuma yanda tace sai na dage sosai kamfaninka sai yaci gaba a duniya,Alhaji Saminu yace Alhmdllh na yaba da kwazonka wlh,ka kwanta min a rai kuma naci alwashin baka duk wata gudunmuwa,Sohail yace na gode.


Takardunsa ya duba ya kalli yanda duk A1 ne da shi,yace ga kokari kuma,Nan take ya kira wani yaronsa yace Idris ga wannan kaje da shi office dinka ka fara masa training ka koya masa komai yanda muke tafiyar da company din nan sannan ka nuna masa yanda zai dinga tsara aikin a computer da abinda zai dinga yi,yace Okay Sir a wanne fannin za a ajiye shi,ka fara nuna masa wannan matakin zan tura maka me zaka nuna masa idan ya iya nan da 3days zan dawo da shi Office dina nan ma sai naga kwazonsa to ni nasan matsayin da zan bashi,yace an gama Sir, ya ja Sohail suka tafi,inda aka ci sa'a aikin daga wanda za ayi a computer sai takardu,Sohail ga Aljanu kafin azo a koya masa waje ma ya iya,Idris mamaki ya kamashi yace wai ka taba aiki irin wannan ne? Sohail yace kai dai muci gaba kawai,Idris yaga abin mamaki yau,idan ya bashi aiki kafin wani dan lokaci ya gama aikin,Aikin Idris da sai yayi wata yana abu daya sai yaga Sohail cikin lokaci kadan wai ya gama shi,ya duba kuma babu gyara ko tangarda.


Suka dawo fannin takardu duk paper daya ko a cike take da rubutu kallo daya ya gama da ita ya jawo wata mamaki ya kama Idris,kallo daya ya karanta ya fadi komai da ake nufi,Aikin da aka ce sai 5pm za a gamawa Sohail 12pm an gama shi,Idris ya saci jiki ya tafi Office din Alhaji Saminu ya dinga bashi labarin abinda ya gani,Saminu yasan wani labarin nasu yaji dadi,a ransa yace in hakane wannan kamfani zai ci gaba aiki da me aljanu irin wannan akwai dadi,nan gaba in naga yanda abin yake babban matsayi zan bashi kai har manager zan bashi na duka kamfanunuwa na su koma hannunsa indai yana da amana.


Sohail aka dawo da shi Office din oga Saminu kawai ya bashi System ya dinga zuba aiki,Office Office aka dinga kai Sohail sai gama musu aiki yake kamar inji ko inji bazai haka ba,Oga murna kawai yake,kuma idan suna shawara yanda kamfani zaici gaba sai aji ya kawo shawara me amfani wacce tafi ta kowa,Yau Oga yinin farin ciki yayi a Office.


2pm nayi sai ga Maheera dauke da Flask na abinci lafiyayye ta shiryo shi ta kawowa Sohail,bata shiga Building din ba daga bakin gate ta tsaya ta kirashi a waya.


Fitowa yayi ya wani soke biro a bayan kunnensa shi ga ma'aikaci,Maheera tayi tayi dariya ta more,yana zuwa yace sabo da na soke biro a bayan kunne kike min dariya,me kika zo yi? Abinci na kawo maka,murmushi yayi tare da shafa gefen fuskarta yace na gode wai so na kike ne? Maheera tace a'a kawai kaunarka nake,Kauna? Ni bana son Kauna kawai so nake so ya furta yana turo jajayan lips dinsa,ni zan tafi ko ka ci abincin ka bani na koma da shi gida,Haba ki sha wahala ki kawo kuma na cinye na kuma baki ki tafi dashi ai idan nayi haka na zama Adnan marar Imani,kije zan taho da su,please karka manta,bazan manta ba Hajjaju kin kusa zama Hajiya,a makka za a daura mana aure,Dariya Maheera tayi tace hmm,yace Allah da gaske nake da ni da Sahil da Islaha dake zamu tafi a daura mana,Sahil ne waliyyi na,ki fada a gidanku,Maheera tace ba ruwana sai kace aljanu ne zasu daura,yace to shike nan,ina siyan mota zaki ganni na daukeki munje gidanku naga danginki,ranar Mamanki ta shiga uku ta lalace da kudi,kudi dai kudi dai,ke har wani kudin zan bata nace ungo wannan ki zubar da su me rabo ya tsinta,Maheera tana ta dariya.


Flask din ya ajiye ya matsa jikinta sosai kamar zasu manne da juna,rungumeta yayi yace na gode,jikinta ta kwace ta karfi ta matsa baya tace ana kallon mu fa,kuma ni ba matarka bace,Sohail yace ke da a kauye kika girma ba a san me zakiyi ba mene haka? Dariya tayi ba shiri wai Sohail ke fadar haka,juyawa tayi ta fara tafiya zuwa yayi ya dauketa cak ya tafi da ita a haka tana cewa ka sauke ni wai mene haka iskanci ne fa wannan,Sai da yayi nisa ya sauketa yace na rage miki hanya,karki ta wahala,murmushi ta saki ta juyo tare da tsura masa kyawawan idanuwanta,juyawa yayi yace bye ya koma ciki da sauri.


Abincin da ta kai masa sai da yaje Office din Oga Saminu ya bashi yace ko zaici yace na gode na fita lunch yanzu, wajen Idris yaje yace suci tare,tare suka ci abincin na Maheera,Idris sai santi yake.


Sai 4pm suka tashi,Oga Saminu yace Sohail muje na saukeka a gida naji ma unguwar mu daya ashe,ya sake furta Sohail tabbas babu tantama zan baka aiki sannan nan gaba ma zan canja maka matsayi inshaallah indai muna raye,Sohail yayi ta godiya suka fito,Driver ne ya bude musu mota suka shiga katuwar motar Saminu ta gani ta nunawa sa'a suka wuce gida.


Suna tafiya Sohail yace gaskiya Sir baka nuna kai me kudi ne,magana ta gaskiya ka dinga cin kudinka,a yanda kake da kudi ya kamata a dinga ganinka da securities da motoci na binka ko uku ne,sannan sutura ma gaskiya ka godewa Allah ka dinga saka me tsada,kalle ni fa bani da sana'a siya mana akeyi amma takalmi na kadai sai ya siyi yadin jikinka,Alhaji Saminu yayi dariya yace kullum fadan da mukeyi da matata kenan wallahi,ita dole sai na canja ni kuma haka nake ban damu ba,Gaskiya ka canja ai shine godiyar Allah din aga banbanci,Alhaji Saminu yayi dariya yace amma a haka ake ce muku baku da hankali gashi muna magana ta nutsuwa,Sohail yace to da aka daukeni aikin za a bani mota wai?


Alhaji Saminu yace za a baka mota me tsada ta gaske sannan za a baka gida a estate me kyau,Sohail sai murna yace dama mun iya mota tun muna yara kawai dan kara gogewa zamuyi, mashaallah cewar Alhaji Saminu,ya sauke Sohail a bakin gate dinsu ya wuce gida, Sohail ma ya shiga gida dauke da takardu a hannunsa da aka ce ya karanta a gida ya cike su.


Yana shugowa ya samu Adnan da Ibrahim a zaune a palo suna ta aiki a System sun saka Sahil Mopping yana ta mopping haka kawai akan Zayna tace su Islaha ne suka yi Mopping shine suka ce wallahi sai ya sake yin sabo.


Sohail yana shugowa ya karbe Mopper din yayi jifa da ita yace muje dan Allah,Adnan ya zaro ido yace Sohail nine na sashi da tsawa yayi maganar, Sohail tsawar yayi shima kamar wani zaki yace bazai yi ba na hanashi,ai mun fada muku mun daina aiki a gidan nan aikin kudi muke nema sabo da haka baza muyi ba muma aikin da zai amfane mu muke nema,Ibrahim yace a tunaninku zaku samu aiki a haka? Sohail yace zauna ka sa wasa sai na zana muku Zero wallahi,Sifili ba saina zana muku shi ya furta tare da jan hannun Sahil suka haura sama,Suna shiga daki Sahil yace ya aikin?


Alhmdllh suka zauna a bakin gado ya bashi labarin aikin,Sahil ya dinga murna yace har mota za a baka da gida? Sohail yace me tsada ma ina fada maka amma muyi shuru kar mu fada su, Maheera kawai zamu fadawa ko Daddy bazai ji ba sai dai a ganmu da abinmu,Sahil yace mun faso gari muma,ai kana aikin nan ina ta kallonka,Sohail yayi dariya domin yawanci ana nuna musu aljanun,shege ai na ganka har Oga sai da ya baka kujerarsa ka hau kayi masa aiki,tafawa suka yi kamar abokai,yace bari nayi wanka nazo,kaga takardun da zan cike,duba ka karanta ka cike min,Sahil ma kallo daya kamar Aljani ya dauki biro duk yayi sai kace yasan kan aikin kuma daidai yayi shima.


Islaha ce ta shiga bedroom ta samu Maheera tana bacci tace ki tashi sweetynki ya dawo daga Office,ido ta bude kadan tace bana son iskanci waye Sweetyna yayi ta dawowa mana,abinci ne ai yasan inda yake ko kije ki kai masa,baya ta juya tare da komawa baccinta.


Sahil yana fitowa yaga Amal tazo gidan itama yau ta kawowa yan uwanta ziyara,ta sha Shadda fara,Zayna ya shiga kira Yaya ta palo.....Yaya ta Palo....Zayna...ki fito kinyi bakuwa kanwar miji tazo azo a nemi shiga,kin san dangin miji masifa ne dole sai ana yin shishigi da neman taskirar zama wai bazai ce gindin zama ba.


Amal tana wani kallon up and down tana tabe baki tace wace kuma Yaya ta palo? Sahil yace Zayna ce, to mece idan ba Yaya ta palo ba matar da mate dinmu ce,sa'ar mu ce fa duk mace akace shekarun mu daya da ita ai ta zama Yaya ta palo kuma.


Amal tace lallai Ibrahim kun bari yaran nan suna shanawa shi yasa suka raina kowa,wallahi da ina nan azabar da zasu sha sai sun kwammace ba a haifo su ba yan iska mahaukata marasa kwakwalwa,ba ilimi ba komai sai jahilci da hauka.


Sahil yace hmmm ke nan tunani kike kinfi kowa ko sabo da kin auri me suffar kwadi,Aunty Amal wai ina kike saka timbin me gidanki ne? Sabo da kudinsa ke tumbin nasa ma bakya gani,Ibrahim dariya ta kusa kulle masa ciki kawai dannewa yake,Sabo da Sahil bai fiye magana ba amma duk randa yaga dama to fa za aji tone tone.


Sahil yace wallahi Aunty Amal hakuri kike yi kawai sabo da kudi,ai kuwa ba wani sonki yake ba wlh uwar gidansa itace komai dinsa ki daina hura hanci,rannan ma haka yace duk duniya ba kamarta ita yake so,sannan baki sani ba wallahi bana ya biya mata Umrah ita da yaranta kaf ke kuma yace miki kiyi hakuri wannan shekarar bashi da kudi,to uwar gida next week zasu tafi,daga nan yace su wuce dubai zasu siyo kayan sawa ita da yaranta.
Ai dan baki sani bane idan uwar gida tana da hankali tana da biyayya duk wata Amarya ko balarabiya ce ko dangin uwar mu ce baturiya bata isa ta kwace fada a wajen uwargida ba,ya aure ki kawai sabo da ya samu sabon jini kullum ki bashi taskira uwar gida kuma ita ce da shi.
Ki daina jiji da kai Aunty Amal bakya gabansa kuma yanzu so kike ki haihu baki samu ciki ba sabo da gado kin damu sai kin haihu to ciki ne dake ammaAllah ne yasan abinda zaki haifa,idan baki yarda ba kije ayi miki test, dama ke mayyar sex ce da zaki taho ma sai dai me tunbi yazo kuka yi na ban kwana,yace babu kamarki a ransa, kika taho kina murna karya yake wlh.


Amal gwiwar ta ce tayi sanyi jin abinda Sahil ya fada tasan basa karya,tace amma wlh idan na koma sai anyi tashin hankali,yanzu Alhaji Rabiu haka zai min,Sahil yace katon kwado kina ce masa Baby, Kuma dan yayi miki ke din ba har wajen malami kawarki ta rakaki ba wai zaki mallake shi,Islaha tace kinga Zayna muje ciki wannan yaron munafuki ne,Aljanunsa kaf munafukai ne,Ibrahim yana ta dariya abinsa yasan halin su Sohail shi yasa yayi shuru kar su tona masa asiri.


Sohail ne ya fito yana duba Maheera bata nan ya duba kitchen Islaha ce kadai ciki tana girki yace girki kike? Tace yanzu na fara Aunty Zayna ce tace farfesu zamu yi musu da white rice and stew wai Aunty Amal tazo sannan wai na dafa mata kan rago ka ganshi an kawo yanzu fresh da shi,Sohail yace yau babu wanda zaici abinci a gidan nan sai dai su fita waje suci mu kadai ne zamu ci mu koshi ni,ke,Sahil da Maheera, suna kallo zamuyi party sai dai su bar gidan nan suci abinci a waje,nidai zan dafa musu ko dan aikin Maheera kar ya kubuce,Sohail yace bazai dafu ba abincin yau ko me za a dafa indai a gidan nan ne bazai dafu ba,Islaha bata yarda ba yana fita ta fara girki,ruwan ma yaki tafasa bare a zuba shinkafa wuta ci take ci take a gas amma idan aka taba ruwan sanyi karara,Islaha ta dinga dariya ita kadai a kitchen,komai ta dora bazai yi ba sai dai a taba aji sanyi,har ta kwashe awanni ta gaji ta maida komai fridge ta fito.


Tana fitowa taga Sahil da Sohail sun shugo da ledoji niki niki,Sahil yace kowa yaje yayi wanka yau akwai party, suka shiga wanka,Maheera ta hade cikin wani material dinta na sallah me kyau,Islaha ta sa riga da skert yan kanti sunyi mata kyau kamar ba gobe,Sohail kuwa da Sahil kana nan kaya suka sha masu kyau wando jean fari riga ruwan toka me rubutu blue a gaba,palo suka fito kawai suka samu Ibrahim,Amal,Adnan da Zayna a dining suna jiran abinci daga wajen su Islaha.


Ido suka bude ganin Su Sohail da su Islaha duk sun sha wanka sun fito da abinci a leda sun dora a center table,Sahil ya bude ya fito da su hot pizza,shawarma,burger, kaza ta sha gashi katuwa a bankare gashin amarya,ga kuma wata kalar shinkafa ta larabawa da katon kifi yaji hadi,ga hadin salat a gefe da lemon tsami,ga ruwa ga lemuka da fruits salat abin ba sauki.


Suka baje komai a center table,Amal har tana dariya irin taga mahaukata ta dakawa Islaha tsawa ke yarinyar nan dalla kawo mana abincin mu,Islaha tace yarinya tana bayan uwarta,Adnan a fusace suka yo kan Islaha,Ibrahim yace dan Allah ku kyaleta su Sohail ne suke zuga su,ai su Sohail zaku ci uba da waccen bakar munafukar Maheera sune suke zigata,ai ita yarinya ce me hankali.


Adnan yace ko sonta kake yi ne? In kana sonta kayi magana ta karfi kudi zai siyar maka ita ai,Amal tace ko dan su Sohail ma sai na so ya aureta naga ta tsiya,bari mu kyaleta zasu ga tsiya kudi zaiyi aiki ai talakawa ne iyayenta zasu ji yaren kudi.


Amal ta sake cewa kawo mana abinci,Su dai sunga suna kuskus basu san me suke cewa ba,suma su Sohail aljanun basu fada musu ba,Islaha tace yanzu kika yi magana da kika bini a sannu,to abinci wlh yaki dafuwa na dade ina abu daya ko me na dora ko zafi bayayi bare ya tafasa,Sohail yace kuma nine nace yau mu kadaine zamu ci abinci a gidan nan ba abinda zai dafu.


Zayna tace na yarda wlh ni na gani rannan,Amal ta mike ta shiga kitchen din da kanta ta dora tukunya ta dade a haka ruwan sanyi ta sauke ta fito ta zubawa Sohail rankwashi tace dan iska marar mutunci,kunyi asarar halinku,shuru suka mata tace kuzo muje eatery muci,suka mike,Maheera ta kunna kida ta ware uban volume wai party zasu yi Sohail ya samu aiki.
Sahil yace wata ta zauna cinyata safe waje ne.


Kida na tashi suna ta ciye ciyensu abin dariya ko wacce makale kusa da daya,hauka tana motsawa Sohail yace ayi musayar kawa,Maheera ta koma kusa da Sahil,Islaha ta koma gefen Sohail,Sohail kuma sai kishi,yaga Maheera sai kallon Sahil take tana murmushi me kayatarwa kuma tana sani tayi tunda shi yace ayi musaya.


Sohail idonsa na kanta ya saki baki yana kallonta haushi ya kama shi yace a ransa ai kuwa sai na baki haushi yau,ya ballo kaza yace da Islaha ungo kici,Islaha ta bude baki ta yagi nama tana taunawa ta kwabe fuska kamar zata yi kuka wai duk cikin dadi ne,tace Aunty babar Khalisat ina nan dadi zai kashe ni ta furta da sigar kuka ka rantse kuka take sharba harda yarfe hannu.


Maheera wani bakin kishi ya kulleta a rai,Islaha tana ta mata inkiya da nuni ta fahimta ba da gaske bane amma haushin Sohail ya kashe Maheera tace a ranta ai hauka ma tana iske hali,halinsa ne wlh sai na rama ta dakko Shawarma itama ta fara bawa Sahil a baki yana ci,Sohail ya kame ya zama gunki da lemo a hannunsa,ransa ya baci,Islaha ta mika masa a baki shima yana ta ci amma wuri

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login