Showing 18001 words to 21000 words out of 76019 words
karka min sharri zanci ubanka,in nayi ma ina ruwanka? Ku aljanun naku ma munafukai ne,Sohail yace shike nan dama tambayarka zanyi...Adnan ne ya shigo palon,Sohail yace Yaya Jiya Ibrahim yayi zina,dubu dari ya bawa karuwar,budurwarsa ce ta kaishi ta baro.
Adnan ko a jikinsa yace to ina ruwanka munafuki yayi din rayuwarsa ce bazai huta ba,idan ku baku da lafiya shi kalau yake,mu da lafiyar mu,Sohail yace ba a dai kuri da lafiya,mu ko zazzabi ai bama yi sam.
Tashi yayi ya bar wajen nasu,Suka ci gaba da hirarsu shi da dan uwansa.
Ali ne ya karaso da escort dinsa motocinsa da securities dinsa,Sohail ne ya karasa jikin motar Daddy dinsu ya bude masa kofa,Alhaji Ali ya fito ya sha farar shadda,kana gani kasan akwai kudi,Sohail yace Daddy ina kwana barka da zuwa,Daddy yayi dan murmushi bai ma amsa gaisuwar ba kawai tambaya yayi ina Adnan? Sohail yace Adnan kafi kowa? Daddy yace wanne sunane haka sabon nick name ya samu? Sohail yabi Daddy suna tafiya yace to ai kai kace kafi sonsa kaga ai yafi kowa ka sa masa kafi su kawai.
Shuru Daddy yayi suka shiga ciki,Sohail sama ya haura yana kwalawa Adnan kira Yaya ka fisu kazo ga ubanku yazo,da Adnan yazo Sohail ya kara furta ka fisu kaje ubanku ya zo,kai fa banda kai? Adnan ya tambaya.
Sohail yace to gashi nan wa ya sani uban mu ne ko ba shi bane Allah ne ya sani,Adnan ya ja tsaki ya wuce abinsa.
Zama suka yi suka gaisa da Daddy suka fara hirar aiki da harkokin kamfani da yanda kudade suke shigowa,Zayna tana cikinsu a zaune suna ta hira abinsu,Sohail kuwa yana dakinsa sai da ya gaji ya fito ya wuce kitchen ya samu Maheera tana fitar musu da abinci,tayata yayi suka shirya abincin a dining,Daddy Ali yana kallo ko a jikinsa sai ma murmushi da yayi yace Sohail akwai aiki wai ina Sahil? Sohail yace yana Lagos,Ali bai ma san dansa ya tafi Lagos ba,Ali yace amma baku fada min ba?
Wanda kafi so din naka basu fada maka ba?
Ali ba kunya yace wallahi basu fada min ba, Kai Adnan me yasa banji labari ba?
Adnan yace wata harka ta samun kudi Sahil ya samu wacce zai tsaya da kafafunsa,aiki ne me tsoka kuma shi yasa muka amince ya tafi,duk wani kudi da komai mun bashi yana can ya fara aikinsa ba matsala yana samun kudi,Daddy ba bincike yace to ai hakan yayi amma Sahil zai iya tsinana wani abu kuwa a duniya? Kar ya zubar min da mutunci ina so zan fito takarar gomna next year, Adnan yace to wa ya sani ne zanje na bincike shi naji.
Daddy yace kayi gaggawar hakan bana son abinda zai taba min siyasa ta.
Maheera dai tana jinsu Daddy ta gaisar sannan ta koma kitchen tana tsaye ta lula tunanin abinda akewa Sohail wai dama baban su ne? Mamaki ya cika ta,Sohail ne ya shigo da fara'arsa ya manta sam yace ki kaiwa Daddy tissue,tace wai da gaske babanku ne? Sohail yayi murmushi yace ae mana ai babanmu ne nida Sahil shine ya haife mu,ba ina ta cewa zan baki tarihina zan fada miki matsalata sai ki nuna bakya son jin labarin.
Amma baban mu ne mahaifi, Maheera ta tuna sanda yake zuwa shagonta yace zan baki tarihina,zan fada miki wata magana,sai ta dauka shirmensa ne kawai zai mata sai tace baza taji ba ita ya kyaketa.
Idonta ne ya ciko da hawaye tace kayi hakuri ban sani ba wlh,yanzu ina Mamanku ko itace ta mutu? Sohail yace ni ban sani ba tunda ni ban taba jin labarinta ba amma dai ance tana England sannan arniya ce itace tace bata son mu shine Daddy ya kawo mu wajen Mama Asmau itace ta raine mu har muka shiga University sai ta rasu bayan ta rasu kuma shine aka cire mu daga makaranta muka dawo nan da su yaya muna musu aiki,suna dan bamu 1k 2k,Daddy kuma shike daukan nauyin cinmu da shan mu sai sutura ana siya mana sai dai muga an kawo mana,ba a bamu ko sisi mu siyi abu da kanmu,sabo da mu bamu da amfani ance.
Maheera tana ta hawayen tausayi tace wlh kuna da amfani kuna da kyawun hali da hankali kawai su basu gani ne amma ni na gani kuma na sani na yarda da kai Sohail,Sahil ma haka you are the same kuna da hankali wlh,kunfi su Adnan hankali da kyan hali,Sohail yace Allah? Ke kin yarda muna da hankali? Maheera tace sosai ma Sohail na yarda da kai.
Kin yarda dani? Ba wanda ya taba cewa muna da hankali sai mama Asmau sai ke,kin yarda da mu? Maheera tace ae.
Zamuyi magana bari na gama aikina,yace to ya juya ya fita sai murna yake da farin ciki yau an samu wacce tace suna da hankali.
Sahil kuwa bacci ya sha sai yamma ya fito palon su Khalisat ya same su gaba daya a palo suna kallon film, Dukkansu suka zuba masa ido kamar mayu ko wacce tana sha'awar su har uwar tasu,Islaha dai tana kitchen tana aiki sai gata ta fito tana shirya Dining,Sahil ya kalleta da muguwar tsana suka hada ido,jikin Islaha ya hau rawa,tsoronsa take ji sosai,kanta ta dauke ta shirya dining,Khalisat tana ta jan Sahil da hira yana sharewa.
Islaha ce ta shiga kitchen,yace kitchen ne can? Aunty ta karbe zancen tana kwarkwasa tace ae kitchen ne zaka iya zuwa ka dauki abinda kake so,feel free ka zama dan gida.
Mikewa yayi ya shiga kitchen din,ba zato Islaha ta ganshi tsoro ya kamata ta fara rawar jiki,Sahil yace kyayi rawar jiki ai, wajen maza kuma kin iya cire pant a sauke shi kasa,Munafuka me fuska biyu na tsane ki.
Islaha muryarta na rawa tace wlh ni ba yar iska bace ban taba iskanci da namiji ba,tsawa ya buga mata enough....a mota muna tafiya haka kika ce ke ba yar iska bace harda cewa cinyata ba safe waje bane,har na miki gata na zame miki uwa da uba na doraki a precious cinyata safe waje irin wannan,harda ce min dan iska to gashi an tsinci iskanci a wajenki,na rainaki ma wlh,akan kudi a tafi a bankadewa maza Taskira shame on you, Allah yasa Sohail yayi mana kawar mu Maheera ta ishe mu useless girl.
Islaha ta fara kuka da hawaye ita bata san me tayi masa ba ya tsaneta,ya juya zai tafi tace wlh ban taba zina b....kafin ta karasa yace rufe min baki makaryaciya na ganki da idona to,Allah ya nuna min gaskiya anje an bankade taskira,ke kuwa nawa za a baki haka?
Islaha tace wlh idan ka kula su Khalisat wallahi a gidan nan sai anyi yaki ai dai nice nan na fara saninka,lalataka zasu yi,
Indai ina gidan nan babu wacce ta isa ta lalataka Sahil yace au fashi da makami na zaki yi? Tace ae? Baza su tsinci komai a jikinka ba face wahala,sai na fito da bad character dina da nake dannewa a gidan nan,za a ga bad character, sai nayi fashi da makami,Khalisat ce ta samo ka to sai nayi fashinka,yace to nidai abar nan tawa daya ce ina kuke so na sata,kai ku tsaya sai na fadawa Sohail ya fada muku gaskiya ni ba dan iska bane,wannan iskancin da zinace zinace na zamani bama yi,bamu iya bude taskirar mata ba.
Daga fadan da yake yi kuma sai ya koma hira yace da na sauka ruwa ya zaneni ranar da muka zo,Islaha tayi dariya tace sannu ai na tambayeka tun farko ina zaka je kaki kulani,kasa kasa yayi da murya yace ya kike fama da aiki a gidan nan tace uhm ba a magana ina shan wahala a rayuwa.
Sahil yace ai wahala yanzu kika soma gani tunda kike bada Taskira ana saka mazari a ciki kin gama yawo,ke da albarka har abada a haka zaki kare,karshen ki bazai kyau ba,bayan sun gama hira kuma ya koma masifarsa.
Ki daina kulani na fada miki na tsaneki ya bata rai ya fice yana huci.
Su Aunty duk tunaninsu Sahil me hankali ne murna suke ganin ya tsani Islaha gaba daya,yana fitowa yace wannan wacce mahaukaciyar me aiki kuka samo ne? Na tsaneta bana sonta,Aunty tace uhm yar gidan yar uwata ce ta ishe mu muma,tsaki ya ja ya sake mikewa yace bari na koma wajenta sai na mata rashin mutunci ni zata raina,Su Khalisat har wani dadi suke ji Islaha duk kyawunta baza ta kwace musu Sahil ba.
Kitchen din Sahil ya koma,ya kalli Islaha yace kina da saurayi wai? Mutumin da yace yar iska ce ita tana kula maza tana Zina amma yanzu kuma yana tambayar saurayi,Islaha ita kanta mamakinsa ya isheta,tace a'a bani da shi,yace yafi miki mutunci mu maza da kike gani ba 'yan goyo bane mu,ko an goya mu sai an sauke mu,Islaha tana dariya kasa kasa tace harda kai yace ae mana harda ni da Sohail karki sake ki goya mu,Islaha tace wai wanne aiki kazo yi nan? Kujera ya ja ya zauna yace bariki nazo yi,zobo me sanyi Islaha ta zuba a cup ta mika masa,yace mu a baki ake bamu bama cin abu da kanmu,har yaushe aka haife mu yara ne mu fa,Islaha duk wasa ta dauka yana yi shi kuwa da gaske yake fadar komai,tace to bari na baka a baki.
Su Khalisat suna palo shuru shuru sun ga Sahil shuru yaki fitowa tsoro ya kama su,Khairat tace bari na leka ta mike sadaf sadaf tace dole abi sahu bako ne ba a san halinsa ba,Islaha tana ta bashi zobo a baki yana shanye abinsa sai da ya kusa gamawa ya tankade cup din ya fadi kasa ya tarwatse yace da girmana,nifa ba dan iska bane irinki me neman maza yaja tsaki ya juya sai suka yi karo da Khairat.
Khairat ta matsa da sauri taga Islaha tayi zugum ga cup a tarwatse bata sani ba Sahil aljaninsu fada musu abu suke yi iya tsiyarka watarana baza ka iya kure su ba,kafin kazo sun sani,Khairat ta harari Islaha tace stay away from him yafi karfinki,gashi nan kin jawa kanki sai ki gyara wajen.
Sohail yana komawa wajen su Khalisat kamar munafukin miji yace yawwa ni gaskiya indai itace kar ta dafa min abinci a gidan nan,kar ta yi min komai,Aunty tace karka damu girkin ma da hannunmu zamu dinga yi maka har wanki da komai,yace yafi muku,Khalisat tace bari nazo mu fita a mota na kaika yawo,Aunty tace da kin bari tunda zan fita na fita tare da shi,Khalisat taji haushi da kishi tace ai na shirya,Khairat tana jinsu tace ni na kaishi next week.
Sahil yace ayi haka? Kunki sharar masallaci zaku yi ta kasuwa,ko girki bakwa yi ga me yi can bakwa wanki duk yi muku akeyi yanzu da kanku zaku yi min nawa? Aunty tace laaa ba komai ai bakonka annabinka,Sahil yana kallonsu dai dai yace alright ku kuka ga zaku iya ai! ya furta kai tsaye ba ko darrr.
Free page
400 ne
0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank
'Yan Niger
+22790795939
AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸
16-20
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM
Page naki ne
Baby Ak
MASU AUDIO BAN YARDA A SATAR MIN NOVEL BA A JUYA BA,DUK WANDA YA DORA A CHANNEL DINSA SAI YA SAUKE.
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
Zuwa yamma Khalisat tace Sahil ya shirya su fita,Islaha ta fito lokacin ido ta kyafta masa tana makale kafada wai yace yaki bazai je ba,Sahil ya kalli Khalisat yace ni bazan je ba Islaha tace kar naje,baki Islaha ta rufe tare da sauri tace ba ruwana ni nace kar kaje? Sahil yace ido ta kyafta min tana min nuni nace wai bazan je ba.
Khalisat tace to Allah ya kamaki,Islaha ta wuce bedroom dinta da sauri,Sahil kuwa tashi yayi yace ke Khalisat kike ko wa kilishi bazan je ba,ni ba sahoramin namiji bane da zan bi mace ta fita dani yawo,ai idan ban fita da mace ba to kuwa mace bata isa ta fita da dan uwan Sohail ba,duk gidan nan baku isa ba ko uwar ku ce bazan je ba.
Haka kawai kun kawo ni gida an ajiye ni neman kudi fa nazo ba zan zauna gidan yan iska ba,Babarku ma jiya sai da tayi kawalci,ta hada kawarta da wani me kudi ya biyata kudi kuma anyi.
Itama Khairat dazu dazu ta gama waya zata samu wani a hotel senator ne kuma arnene sunansa Michiel,bazan iya ba,ga yayarku can Shema'u a gidan ta ajiye yaro matashi tana kashe masa kudi yana biya mata bukata ina zaku kai wannan zunubin?
Dakinsa ya wuce sai gashi dauke da jakarsa yana zarewa Khalisat ido yace akan ki fita dani wani yawon shakatawa gwara na bar muku gidanku ni dama bance a kawo ni ba,indai sai an kaini yawon shakatawa ne gwara na bar gidan.
Abincinku kuma kuyi kudinsa na biya ku mutanen banza,ni dan iska ne ance muku?.
Khairat da Aunty ne suka fito jin Hayaniya Sahil ya nuna su da yatsa yace duk iskancinku sai kun kyale min abu dita bata iya hasala komai,mata kun sani a gaba sai lashe lashen harshe kuke yi,bazan iya ba kuje ku zuba min magani a lemo na a rabani da mazantaka ta.
Aunty tace kai ka iya bakinka wlh gidanmu kazo,butulu an taimakeka kazo kana mana wulakanci,Sahil yana ji yace ni nace a taimake ni? Kuma badan Allah tayi ba,Baba ki iya bakinki.
Khalisat ta zaro ido tace uwar tamu? Uwar taku kuwa wata ta kirki ce,Islaha ce ta fito ta tsaya a gefen Sahil tace kuma ai ba fin wasu matan kuka yi ba asiri kuke yiwa maza ana baku kudi amma ai baku fi kowacce mace ba.
Sahil yace kuma Taskirar ma duk Infection ne a ciki,gasu nan kullum a shan magani,matukar baku tuba ba baza ku warke ba,ai dama Khairat watanta Uku bata yi period ba ai Sanyi ne da ita,inji uban wa? Aunty ta furta amma kai Aljan ne idan ba Aljan ba a gidan uban wa ka sani.
Sahil yace ai mijinki sai kunyi sharia da shi a Lahira dama kina da aure kina bin maza bai sani ba,Aunty ta zaro ido nan take ta fara hada zufa,tana kame kame,Sahil yace kuma Yaseer ba dan mijinki bane Sale me maganin yan bori shine ya miki ciki,Aunty ta shiga tsoro tace amma kai aikoka aka yi kaci zarafin mu fita ka bar mana gida.
Sahil yayi tafiyarsa ya bar gidan,Islaha suka kama suka rufe ta da duka ta musu rashin kunya sai da suka mata lilis sannan suka kyaleta yashe a kasa tana kuka,Aunty daki ta shiga ta fara watso kayan Islaha dama kadan suke jira,tana masifa tace dauki ki bar mana gida kusan inda dare ya miki,Islaha ta mike da kyar ta tattara kayanta tana cewa dan Allah Aunty kiyi hakuri wlh bazan kara ba.
Aunty tana masifa tace wlh sai kin bar gidan nan dama kin ishe mu,Yaseer ne ya shigo ya iske abinda ke faruwa yana gidan yayar su Shemau,shine ke tukata a motarta duk wani iskanci da zata je Yaseer kaninta shi ke kaita sannan kullum suna tare a gidanta ko hotel,kudi take kashe masa sabo da yanda komai shi take aike, shine kamar yaronta kuma kaninta uwa daya uba daya.
Yaseer yace ke Aunty ki kyaleta 'yar gidan yar uwarki guda jini daya,wa take da shi bayan ke? Aunty tace tana da su tunda ta iya yi min rashin kunya ta bar min gida na gaji,taje ta bi bako Sahil ya bata uwar da zai bata,Islaha ta mike tana dingishi ta zuge jakarta me dauke da tsumman kayanta zata fita"
Yaseer ya rike ta tare da furta dan Allah kuyi hakuri Aunty, Aunty da kyar ta hakura ta kyale Islaha tace ta zauna badan halinta ba.
Sahil kuwa machine ya tare ya hau abinsa yace kaini Banana Island ko Lekki,Me machine yace ai nan yankin bama shiga da machine wani wajen amma zan kaika kusa da Banana sai na ajiyeka ka shiga mota,Alright muje.
Me machine dai wuta yake kawai a titi ta wajen wata katuwar gada suka zo wucewa mutane 'yan cirani gasu nan fululu,Sahil yace sauke ni a nan ga gidanmu,Me machine yayi dariya ya tsaya yace nan ne gidan ku? Kace Banana Island ko Lekki,
Na fasa