Showing 75001 words to 76019 words out of 76019 words

Chapter 26 - MUMMUNAR DABIA PDF BY ASMA BAFFA

22 Aug 2025

279

a kore shi ba.


Bayan sati biyu Rashin bacci da yake yi da kuma baya cin abinci yasa Maheera kullum cikin kuka da dana sani take,gashi tsoro take ji ta fadi gaskiya,tana ta rokonsa tana kuka dan Allah Sweet ka tashi kaci abinci so kake ka kashe kanka akan aiki,Please tana lallaba shi,ganin itace haka ya mike zai je Dining a nan wajen ya zube a sume,tayi kansa da gudu tana kuka,ruwa ta ebo da gudu ta yayyafa masa ya farfado,ta sake tafiya da gudu ta kira Sahil dawowarsa kenan daga Office yazo suka wuce da shi asibiti.


Bayan gwaje gwaje likita yace hawan jini ne ya kamashi ga rashin cin abinci da damuwa ta masa yawa,Maheera ta tsure gaba daya.
Kwanan su daya a asibiti yaji sauki aka sallame su,baya kula kowa ko magana sai dole yake yi kamar ba Sohail ba lokaci guda ya canja.


Suna komawa gida washe gari da sassafe Maheera ta saci jiki ta fice daga gidan ta tafi Office din Alhaji Saminu,da kuka ta shiga Office din tana ka taimaka min rabin raina zai mutu ya barni,bani da kwanciyar hankali,nidai dan Allah a dawo masa da aikinsa idan ma a kasar wajen zai zauna ya zauna na hakura zan jira haka wallahi ina son mijjna ba sai yayi min soyayyar ba na hakura da soyayyar,mijina ya daina bacci ya daina cin abinci magana ta gagara,bazan iya rayuwa ba nafi so na ganshi cikin farin ciki.
Dan Allah ka tausaya masa a bashi aikinsa,jarabar mummunan halina ya jawo min ina son mijina wlh,Alhaji Saminu ne ya dakatar da ita fuskarsa a daure,yace kinga Kamfani ba wajen wasa bane,taimakonku nayi kuma nayi abinda zan iya,Kina tunanin samun aiki a kasar nan sauki ne,na bashi aiki yana aikinsa normal kamfani na jin dadinsa shima yana jin dadin kamfani ya samu experience ya goge kince a sallame shi bai yiwa kowa komai ba,ku mata baku da hankali kawai aiki kuke yi da ka sabo da rashin hankali kizo kice a sallami mijinki daga aiki akan soyayya,nayi abinda zan iya,tashi ki bar min Office,Maheera ta durkusa a gaban Alhaji Saminu tana rokonsa tana kuka kamar ranta zai fita amma ya koreta gaba daya ransa a bace.


Dole ta koma gida jiki ba kwari gaba daya ta koma a sanyaye tace hali irin nawa na son kai ya jawo min na shiga uku,tana shigowa palonta ta samu Sohail a tsaye yana jiranta ransa a bace,tana ganinsa a haka tasan Aljanu ma sun sanar masa abinda tayi,yace ina kika je? da baya da baya ta fara ja tace ahm...dam...uhmmm....gidanmu naj...tsawa ya daka mata yace kinji kunya Maheera,ban taba sanin haka kike da mummunan hali ba sai yau,ba abinda nayi kisa a kore ni daga aiki sabo da wata bukatar ki,aikin da na dade shekara da shekaru ban samu ba,kawai sabo da an bani aiki ta dalilinki shine kika je kika sa a kore ni,ya nuna kansa yace ni Maheera zaki sa a sallama a aiki ba tare da laifin komai ba,yana magana yana matsawa kusa da ita,hawaye take yi tace wlh banyi dan wani abuba dan kawai ina sonka ne baka min soyayya baka kula dani,ban san zaka shiga damuwa haka ba,da na sani bazan je nace ba...to gani yanzu ranki yayi fari ko? an koreni na dawo gida mu zauna tare dake,ki cinye ni gani ki cinyeni sabo da soyayya ko caring, sai ki cinye ni,yasa kirjinsa ya tankadeta sai da ta fadi a kasa.
Yace nayi dana sanin saninki ma a rayuwa tashi ki bar min gida,tashi bana son ganinki,Maheera ta fashe da kuka tace wallahi bazan iya ba ni bazan rabu da kai ba ina sonka.


Ki bar mana gida na fada miki,wlh bazan tafi ba gidan mijina nane bazan tafi ba har abada muna tare,Zuwa tayi zata rungume shi ya wanketa da Mari yace dauki kayanki ki bar min gida kafin na miki Illa,Maheera tace sai dai ka kashe ni wlh ba inda zanje mu mutu tare,Sahil ne yaji hayaniya ya shigo,Sohail yana hawaye yace sabo da an bani aiki ta dalilinta taje tasa aka kore ni banyi laifin komai ba,da laifi nayi bazan damu ba,wahalar da nasha ina aiki na bada rayuwata da lokacina sabo da ita nake wannan wahalar sabo da na samu taji dadin duniya shine taje tayi min haka,Sahil yaji abinda ya faru,yace Maheera kece kika iya aikata haka? Subhannallah kawai ki tafi gida ina baki shawara kinga Sohail idan ransa ya baci bama bacin rai wani ya zauna ki tafi kawai ni kaina na tsane ki wlh,Sohail ne ya harari Sahil yace ka tsaneta kai a wa? Ina ruwanka,kan Maheera ya juya da tsawa dalla ki tafi ki bar min gida,Maheera tana kuka ta wuce sama kawai ta hado kayanta ta wuce ta gaban Sohail zata tafi hannunta ya rike ta juyo da sauri yace wlh idan kika fita ko wani waje da aure na ban yafe ba,hannunta ta janye tace ka yafe min ban san haka zara faru ba,jeki kawai ya furta da karaji,ta juya ta fito,taje part din Islaha dake kwance a palo tana jin hayaniyar komai a kunnenta,Sallama ta yiwa Islaha,Suna kuka duka su biyun, Maheera tace na jawa kaina,Islaha kinga yanda Allah yayi dani ko,naso ace ina nan ko dan lalurarki idan basa nan ni kinga ina kusa dake amma an samu matsala na aikata kuskure.....Allah ya baki lafiya Islaha.... ta fice da sauri tana kuka,Sohail sama ya haura labile ya bude yana kallon Maheera ta fita daga gidan.
Taxi ta shiga ta nufi gidan su tana kuka kamar ranta zai fita,shi kansa me Taxi din gajiya ma yayi da jin kukan.
Islaha an barta tana kukanta bata san aure ake shirin daurawa mijinta ba shi kansa bai ma sani ba sabo da kawai an dauke su mahaukata sai abinda aka ga dama ake musu,jira Daddy yake kawai sai ya rage saura 3days ya sanar da Sahil,sun tsara yanda zasu bullo masa wanda dole ma ya amince a daura.


NA GAMA FREE PAGE


400 NE 1&2


0175487861
Asmau Garba Muhammad Gtbank
















AsmaBaffa
08061929616

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login