Showing 15001 words to 18000 words out of 120086 words
ku tare batare da izini ba".
"Eh, lallai wuyanki ya isa yanka Bara'atu. Ni da gidan dana kike gaya min maganar banza." Hajjo ta amsa itama rai a bace.
"Ko kinki ko kinso zama dole muyi a gidan nan. Idan bazaki iya zama damu ba sai ki bar min yaran ki kama gabanki."
Yusuf mijin Anti Bintu yace "Anti kada ki sake cewa komai. Ai basu fi karfin hukuma ba. Kuma rabon gado ba hauka bane. Ki bari mu kwana yau gobe sai mu san abinyi."
Mikewa tayi cikin zafin nama tana kallonsu daidai. Garzali banda taba babu abinda yake busawa. Rabe da amaryarsa suna tsaye suna mata kallon banza. Hannu tasa ta share hawayenta
"Dama can saboda marigayi nake raga muku to amma wallahi yanzu an wuce wurin. Mu zuba ni daku shege ka fasa."
Yaranta ta dakawa tsawa duk suka tashi daga gaban Hajjo suka bita cikin gidan.
Hajjo da su Rabe kowa yayi tsit suna mamakin wai yau Bara'atu ke mayar musu da martani haka.
*****
A cikin gidan dakuna biyu ta samu a bude ita da Yusuf da su Shemau suka rinka shiga da kayansu. Sai cikin dare tana zaune tana kallon 'ya'yanta na bacci ta rinka kuka.
Washegari ko karyawa batayi ba suka fito ita da yaran suka hadu da Yusuf zasu tafi ofishin 'yan sanda.
Rabe yana tsaye a waje yace " kinga basai kun wahala ba a bayan layin nan akwai gidan wani babban dan sanda. Maza ku tafi ku kai kara kada kuda ya rigaku."
Basu kula shi ba suka wuce. Duk wani bayani sun gabatarwa 'yan sandan. Mutum hudu aka hado su dasu suka zo aka bukaci su Rabe su fita.
Wannan muguwar dariyar yake yi ya dauko takardun gida sai gashi sunansa ne dana Shu'aibu a jiki a matsayin tare suka gina.
Kuka sosai Bara'atu take yi tana karyata shi. Sai dai kuma bata da shaida. Bata san yadda akayi ya sami takardun gidan ba wanda a hannunta suke har akayi canje canje haka.
Dole 'yan sanda suka tafi domin basu da wata shaida.
Yusuf ya nemi ta bishi su koma Zaria daga nan ta koma garinsu da zama.
Tana kuka tace "ko zasu kashemu babu inda zamu je. Gidan nan namu ne kuma duk rintse sai ya dawo hannun masu shi."
Babu yadda Yusuf ya iya dole ya tafi ya barta. A dakin kwanansu ta sayi risho mai kai biyu da kayan abinci. Kullum suna daki tana saka yadda zata bullo musu.
A karshen sati ne abokan marigayi biyu suka zo. Anyi ta kai ruwa rana Hajjo da Rabe da sauran 'ya'yan gidan suka hade musu kai. Magana dai har wurin dan sandan dake bayan layinsu, Adamu Matawalle ashe abokin daya daga cikinsu ne. Shima ya gamsu da bayanansu sai dai ga shaida kurukuru suna gani gida na Rabe da Shu'aibu ne. Shawara suka bata akan ta koma gida kawai tace babu inda zata je.
Wani katon fili wanda gida daya ne tsakaninsa da gidan dan sandan ta nuna musu. Rabi nata ne ta siya da kudin kasuwancinta daya rabin kuma Shu'aibu ne ya siya mata. Takardun ta bawa dan sandan ta roke shi ya rike mata amana zata gina kayanta a hankali sannan su tashi daga can gidan. Duk ta basu tausayi. Wani cikinsu ne yayi cuku-cukun nema mata aiki a kamfanin sadarwa na MTN , duk wannan abu batare da sanin su Rabe ba. Tayi musu godiya kamar ta ari baki.
Cikin dan lokaci ta saba da iyalin Adamu sai dai kullum a gida take barin 'ya'yanta idan zata je wurinsu. Tana tsoron surutun yara kada su fada a gidan. Makaranta ta samar musu a nan cikin unguwa. Saboda yanayin aikinta ta koyawa Shemau da Jafar girki ko da bata dawo da wuri ba. Zagi da surutu har su Hajjo sun gaji da yi wai tana yawon bariki. Bata kula su ba sai dai bata bari 'ya'yanta sun raina kakarsu ba.
Wata rana ta fito suna sauri zata kai yara makaranta ta wuce wurin aiki ta nemi motarta bata gani ba. Rai a bace ta koma ciki ta tambayi Sagira. Sai da ta gama yaukinta sannan tace ban sani ba. Itama Hajjo amsar data bata kenan.
Tasan aikin Rabe ne sai tayi kamar ta hakura. Har wani gadara yake yi yana cewa motarsa. Na tsawon sati biyu ta dauke kanta daga kan motar sai dai a bayan idonsa ta sami wani abokin aikinta ya samo mai siya.
Ranar Juma'a Rabe na kwance a daki mai siya yazo yaga mota aka gama ciniki ta bashi mota da takardunta. Shi kuma yayi alkawarin kawo kudin ranar litinin.
Sam Rabe bai san me ake ciki ba sai washegari ya gama shirin zuwa daurin aure. Ganin babu motar kuma yasan Bara'atu nada mukulli ya tafi kofar dakinta yana ta bugu iya karfinsa. Yaranta duk bacci suke yi ta fito da dogon hijab a jikinta tana murmushi don tasan me ya kawo shi.
"kinga ba wasa bane ya kawoni ina kika kai min mota"?
"Hmmm, karfin hali barawo da sallama." Ta fada tana tafa hannuwa.
Hajjo da Sagira suka fito suka sakata a gaba.
Bara'atu ta yatsina fuska "mota dai tawa ce kuma na sayar na cinye kudin. Shikenan ko."
Ran Rabe a bace ya zabga mata mari. Hajjo tace kayi min daidai.
Bai ankara ba Bara'atu ta kwashe shi da mari shima tana harararsa.
"Dani daku a gidan nan daga yau an shata layin rashin mutumci. Na gaji na kai wuya duk abinda zakuyi kuyi. Banda rashin tsoron Allah komai na gado sai mun raba ni daku? To mota dai tawa ce ni kadai"
Tsaki taja ta shige dakin ta banko kofa.
Hajjo ta kalli Rabe a dan tsorace." Anya yarinyar nan bata shan kwaya kuwa? Kada tasa a koremu fa."
Rabe ya dafe kunci "barni da ita Hajjo sai na nuna mata bata da wayo". Sai dai har kasan ransa bazai iya ba saboda son da yake mata.
Haka suka cigaba da zaman doya da manja a gidan. Tsakanin Bara'atu da su sai kallo. Yaranta kuwa ta wajabta musu zuwa gaishe da Hajjo safe da dare duk da bata amsawa. A haka har suka shekara daya da rabi tana ta gininta a hankali, sannan duk da tana aiki bata dena kasuwanci ba.
Wata ranar lahadi tana daki ta jiyo hayaniya a falo. Yaya Abu ce da Lami suka zo yini da 'ya'yansu. Su Shemau na son zuwa wurin sauran yaran suna tsoron Ummansu. Murmushi tayi tace su je amma banda tsokana.
Da gudu suka fice tunda da sauran kuruciya basu gama bambamce masu sonsu ba. Iyayen dai babu wanda ya amsa musu gaisuwa da 'yan uwansu yara suke ta wasa.
Kamilu babban dan Yaya Abu ne ya shigo ya soma rungumar kannensa kamar yadda ya saba. Yana rungume da Shema'u yana tsokanarta Bara'atu ta fito idonta ya fada kansu. Mantawa tayi da mutane a wurin tace
"Kamilu wane irin wasa ne wannan? Shema'u ban hanaki wannan rungume rungumen ba?"
Dena hirar su Hajjo suka yi suka tsaya kallon Bara'atu tana yiwa dansu fada.
Lami ta watso mata harara "To kinibabbiya kin fito ne ki fara rashin da'ar taki? Menene aibu don ya taba kanwarsa, yaro da muharramarsa ma sai an nuna musu iyawa" mtws.
"Bani da matsala don Kamilu ya taba kanwarsa sai dai Shema'u ba muharramarsa bace shiyasa na hana. Daga shi har ita babu karamin yaron da ba'a budewa littafi ba".
"Ya Sayyada manya....indai Yaya Shu'aibu ne uban Shemau to baki isa ki rabata da Kamilu ba domin kuwa iyayensu uwa daya uba daya suke. Kinga sun zama muharraman juna".
Kallon Lami kawai Bara'atu tayi ta girgiza kai zata koma ciki Hajjo ta dakatar da ita.
"Sai kin fada min dalilin son raba min kan jikoki tunda kin gama fetsare kafafunki".
"Hajjo ni ba rashin kunya nazo yi miki ba. Wannan abu ba fadata bace. Da yawa mutane muna jahiltar abinda ake nufi da muharrami. A musulunce duk mutumin da ko ku kadai kuka rage a duniya aure ya haramta tsakaninku shine muharrami."
Yaya Abu tace "to ina kuma alakar jini da take tsakaninsu? Ita kuma an datse ta kenan?"
Bara'atu ta fahimci neman kureta suke yi sai dai kuma tana da hujja ba da ka tayi magana ba.
"Alakar jini bazata hana aure tsakaninsu ba wannan yasa ya zama ba muharraminta ba. Mutanen da suka amsa wannan suna a garemu sune kaka(namiji),'yan uwansa wanda suka hada uwa, uba ko uwa daya uba daya amma banda 'ya'yansu. Haka kuma yake ga bangaren kaka(mace), sai 'yan uwan uwa da na uba suma wanda suka hada uwa, uba ko uwa daya uba daya amma banda 'ya'yansu. Sannan sai 'ya'yan kanne maza da mata. Babban misali shine Sayyadina Ali RA kani ne ga Annabi Muhammad SAW domin iyayensu wa da kani ne. Nana Fadima bazata iya auren Abu Dalib ba saboda kawun babanta ne amma ta auri dansa duk da cewa kani ne ga mahaifinta.
Sannan ko a gidan nan Rabe da ya auri Sagira ai kanwarsa ce tunda Hajjo da babar Sagira shakikan juna ne.
Muna yawan yin kuskure sai muce 'ya'yanmu 'yan uwa ne mu bari suna taba juna ko suna shiga dakin juna kai tsaye da sunan 'yan uwan taka.( A labaranmu na soyayya muna yin wannan kuskuren duk mu saka cousins ko 'ya'yan riko sun gama tabe taben jikin juna duk da sunan 'yan uwan taka sannan daga baya mu kulla soyayya tsakaninsu). Aya ta ashirin da uku a suratun Nisa'i ta iyakance mana su waye muharramai. Kuma
_An karbo daga Ma'qal ibn Yassar yace Manzo SAW yace: ya fiyewa dayanku a buga masa kusa a kansa da ya taba jikin macen da ba muharramarsa ba.At-Tabarani ya rawaito shi, Sheik Nasiruddeen Albani ya inganta shi a Sahih Jaami'."_
Wani kallon raini suka rinka binta dashi tunda dai ga hujja ta basu. Yaya Abu tace da Kamilu " Kai, daga yau babu ku duka babu wadannan 'ya'yan gwal din."
Bara'atu dai kyalesu tayi ta wuce tana addua'ar kammala gininta su huta da wannan masifa.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽13
Batul Mamman💖
Tare suka koma gidan Kwamishina sai dai su Mama har sun wuce asibiti. Sai wuraren shadayan dare Mama ta kira Umma bayan taga missed calls dinta take sanar da ita an kwantar dasu asthma din Abubakar ce ta tashi.
Gari na wayewa Shemau ta hada abincin safe harda mutanen asibiti. Ita da Umma suka tafi asibitin su Asmau kuma suka wuce makaranta. Sai bayan la'asar da zasu kai abincin dare duk da ana kaiwa daga nasu gidan Umma ta hada 'ya'yanta gabadaya suka tafi asibitin.
Jikin Asmau a sanyaye suka shiga dakin saboda ba karamin rudewa tayi ba da ganin halin da Abubakar ya shiga. Bayan an gaisa kowa yayi masa sannu ya amsa banda na Asmau. Da farko ta zata baiji ba ta sake maimaitawa. Wannan karon harararta yayi amma ita kadai ta kula da hakan. Bata gane dalilinsa na yin hakan ba amma bata ji dadi ba har suka tafi bata sake magana ba.
Sai da yamma aka sallame shi washegari. Nan ma da suka zo karatu yana falo ta sake yi masa sannu yaki amsawa har sai da Qasim yayi masa magana.
"Abubakar ana yi maka sannu baka ji ba"
Hamma yayi ya gyara kwanciya batare da ya amsawa Qasim ba.
Da dan murmushi Qasim yace "jikin nasa da sauki . Ke ce Asmau ko?"
Kanta a kasa saboda abinda Abubakar yayi mata tace "eh" tare da mikewa ta tafi masallaci.
An shafe sama da wata biyu Abubakar baya amsa gaisuwar Asmau. Dama can ba wata hira suke yi ba. Abin yana matukar damunta sai dai ta kasa fadawa kowa.
Ranar lahadi da yamma tana dakinsu Yassar ya shigo ya ganta tasa littafi a gaba tana kuka. Baice mata komai ba ya fita ya fadawa Umma. Tasowa tayi ta shigo dakin da kanta.
"Me ya sami Idon kukana kike sana'ar a daki ke kadai"
Littafinta ta mikowa Umma na Physics. Assignment ne kuma duk lissafi ko daya bata yi ba.
"Tun dazu nake yi na kasa amsa ko daya. Kuma malamin duka yake yi."
"To shine kike kuka kuma saboda kinfi kowa ruwan ido, uhmm? Kinga ni da yayyenki babu wanda yayi physics. Idan kuma kin amince na koya miki gobe kici kafi-zero shikenan" ta fada da dariyarta.
Murmushi Asmau tayi tana sake duban littafin.
Umma tace "kije Abubakar ya koya miki shine dan science a gidan Mama."
"Umma ai gara naci zero din. Ni da ko gaisuwata baya amsawa idan naje nasan bazai kulani ba"
"Asmau bana son karya. Baban nawa ne baya amsa gaisuwarki? Jiya da yazo ba ke nasa kika dafa masa indomie ba. Ko dai wani laifin kika yi masa?"
"Kila kunyarki yaji amma da gaske tun kwanciyarsa a asibiti ya tsaneni. Kuma ni banyi masa komai ba".
Umma ta dan kalli Asmau sannan ta fita. Abubakar yaron kirki ne kila Asmau tayi masa laifi ne ko kuma dai wani rashin fahimta suka samu. Ko ma dai meye bazata bari yayi nisan da zai shiga tsakaninsu iyaye ba. Wayarta ta dauka ta kirashi. Tayi sa'a yana gida tace yazo tana son ganinsa.
*****
Dakin Mama yaje ya fada mata Umma na kiransa. Plate din da take shan kankana ta ture ta tashi.
"Jirani muje tare jiya naji Aina'u tana ta tari. Tun dazu nake tunanin zuwa duba ta."
Tare suka tafi suna 'yar hira a hanya. Umma taji dadin ganinsu su biyun. Sun dan taba hira ta kwalawa Asmau kira.
Tana fitowa da taga Abubakar sai da gabanta ya fadi...ba dai Umma kiransa tayi akan abinda ta fada ba?
A kasa ta zauna ta gaishe su. Umma ta lura tabbas bai amsa ba. Kuma bai dade da gama tsokanar Aina'u ba.
Idon Umma akan Asmau tace "dazu da nace kije Abubakar ya koya miki assignment me kika ce min"?
Cikinta har wani kullewa yayi ta daga kai suka hada ido ya harareta. Da sauri ta sauke kanta
"Uhmm, uhmm, babu komai".
Mama ta kallesu duk su biyun. Asmau a tsorace, Abubakar ya hade fuska.
"Ni kun batar dani Umma, me ya faru?"
Umma ta sanar da ita abinda Asmau ta fada da kuma wanda ta kula dashi a wurin. Duk su biyun Abubakar suka zubawa ido suna jiran amsarsa.
Dariya suka bashi ya mike tsaye " ni bata yi min komai ba. Bari na koma gida dama aiki nake yi."
Mama ta daure fuska "kaga abokan wasanka a nan ne, zauna ka fadi me ya hadaka da kanwarka. Ni bazan lamunce da gaba cikin 'ya'yana ba. Ku da su Asmau duk matsayinku daya a wurinmu."
Ita dai Asmau sai satar kallonsa take yi a tsorace.
"Mama kin tuna ranar da na sami attack har na kwanta a asibiti? Yarinyar nan fa tana cikin masallacin. Na kasa dauko inhaler a cikin aljihun wandona saboda yadda nake ji nayi ta nuna mata kuma ta gane wai sai ta fita kiranki. Da baki zo da wuri ba shikenan fa".
Umma da Mama sai dariya shi kuwa da gaske yaji haushi ya dubi Asmau itama shi take kallo.
"Da na mutu a lokacin idan ba fatalwa zan rinka yi miki ba."
Wannan karon itama sai da tayi murmushi ganin ya dan saki fuska.
Mama ta janyota jikinta "Me yasa baki bashi inhaler din ba Asmau?"
Idonta ne ya cicciko da hawaye. Umma tace " oh ni Bara'atu yarinyar nan ko baure bazai nuna mata zuba ba. Ke baki da aiki sai na kuka daga tambayar fatar baki."
Mama ce ta lallaba Asmau muryarta na rawa ta kalli Umma.
"Ba cewa kika yi haramun bane mace ta taba namjin da ba muharraminta ba. Har a islamiyya duk ana fada mana. Da na taba shi nasan fada zaki yi min sannan a rubuta min zunubi shiyasa na kira Mama".
A take Abubakar yaji wani irin yanayi game da Asmau. Shi kan shi yasan bai dace ace yana fushi da ita ba amma abinda ta fada yasa yaji ta sami wani matsayi a wurinsa. Ashe abinda tayi, tayi shi ne don bin umarnin addininta. A yadda yake matashi mai tsantseni wurin addini yana son mutane masu kiyayewa.
Yanayin kallon da yake mata ya canza zuwa sakin fuska "dauko littafin muje na koya miki kinji kanwata Idon kuka."
Sai da suka dara gabadaya sannan Umma tace "Asmau addinin musulunci yayi mana iyakokin da musulmin kwarai bai dace ya tsallakesu ba. To amma akwai sassauci akan abinda ya zama lalura. Kinga a lokacin da ya sami attack bashi da wani mataimaki sai ke kadai a wurin. Rashin taimakonsa kuskurene tunda yana cikin mawuyacin hali. Da ace akwai wani namijin to dama bai kamata ki taba shi ba. Komai na addininmu yana da sauki. Duk abinda ya zama lalura wajibi ka taimaki mutum koda kuwa baki sanshi ba. Ku tashi Allah Yayi muku albarka".
Shi Abubakar har kunya yaji. Yarinya ta fishi hangen nesa. Can gefe suka koma a cikin falon wurin wasu kananan kujeru da dan tebur a tsakaninsu. Littafin ya karba yace ta dauko text book dinta na P.N Okeke
Mama ce ta bisu da kallo har suka zauna sannan ta maida hankalinta ga Umma.
"A gaskiya Umma ina yaba miki wurin kokari a tarbiyantar da yaran nan. A zamanin nan da kananan yara sun san meye mace ko namiji amma har a irin wannan yanayin Asmau bata manta da hudubarki ba. Allah Ya kara taimaka mana wurin basu tarbiya. Shiyasa nake jinki kamar kanwata ta jini wallahi."
Murmushi kawai Umma tayi.
Mama ta cigaba da magana " inama dai yaran nan su hada kansu? Wallahi ba karamin dadi zanji ba. Ji nayi Asmau ta kara shiga raina. Ni daga yau ma ta kwace matsayin auta Umar."
Wannan karon dariya Umma tayi.
"Anya wannan dan shagwabar zai yarda? Maganarki kuma akan ita da Abubakar ba tun yau ba nima nake sha'awar hakan. Allah Ya zaba mana abinda yafi alkhairi."
A can gefe inda suke yin aikin kuwa ko yaya suka hada ido sai su sakarwa juna murmushi.
Wannan murmushin sai da ya zame musu jiki. Ko karatun dare suka zo sai Abubakar yayi ta kallon Asmau har sai sun hada ido anyi murmushin nan. Ita yanzu kunyarsa take ji sosai. Shi kuma duk irin basarwar nan tasa da rashin kula mutane indai suka taru suna hira ko a gidan Mama ko gidan Umma to sai yasan yadda yayi Asmau tasa baki.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽14
Batul Mamman💖
Kwance tashi babu wuya a wurin Allah. Anyi bikin Suwaiba da Sadiya lokaci daya. Asmau kuma ana ta shirin fara WAEC da NECO. Ita kuma Shemau tana aji uku a jami'a sannan ansa bikinta wata