Showing 108001 words to 111000 words out of 120086 words

Chapter 37 - ABINDA AKE GUDU

30 Oct 2024

2586

nau'i na jarabawa.
"Naji yar uwa kuma ba fahimta. Amma haihuwa ta Allah ce. Shi ya tabbatar bazai taba haihuwa bane? Ki gwada yin test a gida idan babu shikenan. Sai da kika fara aman ma na kula kinyi haske kin kara jiki. Da na zata duk na amarcin ne"

"Walida ina son haihuwa da Jikamshina amma shekarun da yayi a auren fari sun ishemu shaida. Kada ki saka min rai da abinda yayi min nisa"

Walida ta tashi ta dauki mayafi da purse dinta daga cikin jaka "kinga bari naje can wurin titi naga kamar akwai pharmacy. Zan siyo miki PT strip ki gwada. Idan babu komai ba sai ya sani ba"

Bata saurari wani batu daga Asmau ba ta fita. Wurin mintuna ashirin sai gata ta dawo tayi uban gumi. Tasha yawo domin inda ta zata pharmacy ne ba shi bane sai da aka kwatanta mata wani. Asmau ta dage bazata yi gwajin ba Walida ta ji haushi sosai. "Ko albarkacin tafiyar da nayi ai kya yi min kara ki gwada."

Da kyar da nuna bacin rai Asmau ta karbi tsinken gwajin guda biyu ta shiga bandaki. Bata fi minti uku ba Walida taji ta kwalla kara. A razane ta tashi tayi hanyar bandakin suka yi karo da Asmau da ta fito. Walida na cewa me ta faru ta rungumeta sosai sai kuma kuka da dariya a hade.
"Kin gani Walida *ciki* *cikin haihuwa* gareni. Wayyo Allah Jikamshina Allah Yana sane da bayinSa"

Wayarta ta tafi daukowa suna ta dariya ita da Walida. Har ta nemo sunansa zata kira Walida ta karbe wayar.
"Mutumin da ya kwashi shekaru yana neman haihuwa zaki fadawa kina da ciki a waya? Haba kawalli, ai yau ranarsa ce. Tashi zakiyi mu shiga kitchen ki hada masa special abinci mu sake gyara gidan nan. Idan da hali tambaye shi muje gidan kunshi naga naki ya kusa ficewa. Ana yi miki zanyi miki kitson barebari kanana"

Asmau tayi dariya tana shafa ciki. Wai cikin Jikamshinta ne a tare da ita. "Nayi girki sai dai na kara masa wani abin ko farfesu haka. Bari na tambayi kunshin"

Sai da tayi da gaske ta iya boyewa bata fada masa a waya ba. Bai hanata zuwa ba yace su je da Mal Sabo amma idan akwai layi sosai ta dawo gida baya son dawowa dinnan ya tarar bata nan. Cikin sauri sauri suka sake kimtsa gidan suka tafi.

Ana gama saka mata lallen Walida ta kama kanta tayi mata kitso. Shuku ne wani sabon style mai kyau da yake gashin nada cika sosai yayi mata kyau fuskarta ta kara fitowa. Sai da aka dauko Amatullah daga makaranta aka zo daukarsu. Har gida suka kai Walida Asmau tana ta yi mata godiya.

Suna zuwa gida tayiwa Amatullah wanka ta saka mata wasu kayan sannan ta barta a daki saboda zata kunna turaren wuta kada ya dameta. Tana gamawa taje ta bata lokaci wurin wanka da shiriyawa.

Karfe tara a gida tayiwa Col. Ishaq. Asmau da Amatullah suka taro shi tun daga bakin kofa. Binta yayi da kallo ya kasa dauke idonsa. Kullum tana masa kwalliya amm yau kam ba don Amatullah na wurin ba bai san me zaiyi ba. Tana rike da hannunsa suka tafi daki zata taimaka masa yayi wanka yace "Kamar na cinyeki Matar Jikamshi. Kinyi kyau da yawa"

Tayi murmushi "nagode amma ko zaka cinyeni ka bari ka fara cin abinci"

Kusan tura shi bandaki tayi don yaki tafiya sai tsokanarta yake. Da ya gama ya dawo falo inda ta zuba musu abinci a plate daya har Amatullah wanda hakan tsarinsa ne cin abincin dare tare. Suna ci yana kallon yadda take ta murmushi da fara'a ya ajiye cokalinsa yace "ki taimakeni ki fada min abinda yake ranki ya saka min ke cikin irin wannan farincikin."

"Sai mun gama cin abinci"

Ya kwabe fuska "bazan iya cigaba da cin abincin nan ba duk dadinsa. So nake kawai ki fada min. Tun dazu kin sa kwakwalwata ta tafi dogon bincike ta kasa samun amsa"

"Ka bari mu gama please"

Shi kam hakurinsa ya kare. Tun dazu yana kallo ko abincin kirki bata ci ba sai murmushi. Ya dan tabata ta kallo fuskarsa. A hankali yadda ita kadai zata ji yace "ko ki fada min yanzu ko mu kwashi kunya a gaban 'yarmu"

Asmau ta gane me yake nufi duk da tana tunanin bazai iya ba amma Jikamshinta bashi da tabbas. Tashi tayi ta tafi daki ya bi bayanta da sauri. Kafin ta rufe kofar taji ya rungumota suna kallon juna
"Rada min idan baki so dakin ya sani bazan fadawa Safina kinyi yada ba"

Tayi dariya sannan ta kai bakinta saitin kunnensa "Allah Yayi mana kyautar da har abada bazamu taba dena gode maSa ba, Jikamshina..."

Kasa fada tayi sai ta kama hannunsa ta dora akan cikinta "Akwai kyautar Allah a cikin nan"

Ya ware ido sosai yana jiran karin bayani "go on"

Rungume shi tayi saboda kunyarsa take ji sosai a wannan lokacin cikin kankanuwar murya tace *Alhamdulillah, I am pregnant*"

Karfin adduar da yake a lokacin ta hana zuciyarsa bugawa. A hankali ya zame jikinsa daga nata cikin matukar kadawar zuciya ya kalleta. Murmushi take har lokacin hakan ya tabbatar masa ba karya take ba. Ta kula da kaduwarsa tace "nima ban gaskata ba sai da nayi PT dazu. Kaga ikon Allah ko Jikamshina"

Bai iya cewa komai ba sai juya wa da yayi a sanyaye ya shiga toilet. Asmau tabi bayansa taji ya rufe da mukulli. Dama tasan wannan labarin ba karamin farinciki zai saka shi ba. Abu daya ne yazo kanta ko alwala zaiyi suyi nafila. Cikin sauri ta tafi nata dakin ta dauro alwala ta sako hijab ta dawo. Ko da ta shiga dakin toilet dinsa a bude yake amma baya nan.

Falo taje da abin sallah biyu a hannu nan ma bata same shi ba. Tana lekawa ta taga ta hango yana fitar da motarsa daga gidan. Ta koma ta zauna da murmushi, wato ya tafi fadawa Hajiya. Gara da bai nemi ta raka shi ba ai da taji kunya.

Shiru shiru har shadaya ta wuce bai dawo ba. Tana ta kiran wayarsa baya dauka sai daga baya ta ga wayar a daki.
Hankalinta ya soma tashi amma bata son kiran Bilkisu ko Hajiya ayi zaton ta kasa hakuri daga miji ya fita.
******

Tuki yake bashi da wurin zuwa. Zuciyarsa ce take zafi har gumi yana karyo masa. Me yasa Asmau zata yi masa haka, yana da tabbacin tana son shi da zuciya daya. Amma waye ya fada mata lallai sai ta haihu zai cigaba da sonta. Ya dade da karbar kaddararsa me yasa ta aure shi idan bazata iya hakurin zama dashi ba. Waye ya bata wannan muguwar shawarar. Waye yayi sanadin rushewar farincinkin da yake bakin kokarinsa wurin ganin ya tabbata a rayuwar aurensu. Gefen titi yayi parking saboda baya ganin gabansa sosai. Zazzafan hawaye ne ya cika masa ido har yake ganin duhu. Ajiye girmansa yayi da mukaminsa yayi kuka, kuka na bakinciki da bacin rai. Kukan rasa mafita ga halin da abar sonsa ta saka shi a ciki. Sai da ya gaji da zaman ya rinka karanto addu'o'in neman sauki sannan ya koma gida.

Asmau na zaune a falo a haka bacci ya dauketa. Zuciyarsa ta sake karaya da ya ganta rungume da abin sallah tana bacci ga Amatullah a kusa da ita. Dukawa yayi ya dauketa ya kaita nata dakin ya dawo ya tsaya yana kallon Asmau. Sai da ya daure zuciyarsa ya iya tabata ta bude ido a hankali. Magana taso yi ta kula da ja da kankacewar idanunsa.

"Tashi kije ki kwanta"

Bai bari tayi magana ba ya shige ya barta a wurin fuskarsa a daure cikin tsananin bacin rai. Yau da gobe tafi karfin wasa. Asmau ta fuskanci rayuwa irin wadda bata fatan wata mace ta gani. Yanayin da taga Jikamshinta ya sha bamban da abinda tayi tsammani. Wannan kadai ya bata amsar shirunsa da fitarsa daga gidan. _ZARGI_ irin wanda Allah Kadai Ya isa Ya wawarewa bawa. Sai dai abin mamaki gane hakan bai sata kuka ba. Ashe kuka wuri yake samu, ashe kuka rahma ne. Hannu tasa ta dafe kirjinta da taji yayi kamar an daure shi tamau ta kashe fitila da tv ta tafi daki.

Duhu ta gani alamun ya kwanta sai ta koma nata dakin ta sako kayan bacci ta dawo. Tana kwanciya ashe a kansa ne saboda ya raba gadon ba kamar yadda ya saba ba. Yau a tsakiya ya kwanta. Ji tayi yana kokarin matsawa tayi saurin tashi tana bashi hakuri amma bai amsa mata ba. Bata yi fushin ta bar masa dakinsa ba ta koma gefen gadon ta kwanta.

Sai karfe takwas saura mintuna ta tashi a makare. Wayam ta ga baya dakin. Ta fita da sauri motarsa bata cikin gidan. Jikinta yayi sanyi ta koma tayi sallah da ya saba tashinta idan zashi masallaci. Ta shiga dakin Amatullah ta tarar bata nan ga kayan baccinta a kan gado. Dan murmushi tayi ko babu komai bai dena kyautatawa 'yarta ba.

Haka Asmau ta yini ranar da kuncin zuciya. Duk bayan lokaci sai ta duba wayarta ko ya kira ko text amma babu ko daya. Haka ta ke zaunawa ta tsara masa kalamai masu ratsa zuciya ta tura masa. Idan ya gani a take yake gogewa. Sai yanzu yake nadamar auren Asmau yana mai nanatawa kansa tambaya daya *cikin jikinta na waye?*.
*****

Sati guda suka yi baya mata magana kuma baya shiga sabgarta. Ita kuma tayi alkawarin bazata takura shiba har Allah Ya sauketa lafiya. Daurewa take tana nunawa kamar babu abinda ya faru ta cigaba da yin abubuwan kyautata masa ko da bazai kula ba. Walida ta kirata taji yaya murnarsa da ta fada masa tana da ciki ta shirga mata karya don ta rufawa mijinta da kanta asiri.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽58

Batul Mamman💖




A daddafe take iya yin komai. Cikin da alama mai laulayi ne domin bata son warin komai ga yawan tashin zuciya. Rashin wadataccen abinci yasa ko aman yazo sai dai tayi wahalar banza babu komai a cikinta. Cikin dan lokaci ta fada. Babu wanda ta iya fadawa damuwarta sai Allah. Kullum sallah take da karatu tana mai tsananta addua da neman mafita. Idan ta damu da yawa ta kira Umma suyi hira taji sauki a ranta.

A nasa bangaren Col. Ishaq ba karamin jigata yayi ba da rashin Asmau. Sonta yana nan a ransa amma yana kyamar halin da ta jefa su a jiki. Har yau ya rasa matakin da zai dauka bayan fita harkarta da yayi. Gidan yayi musu zafi duk su biyun. Gado daya suke kwana ya juya mata baya. Haka zata yi bacci tana kallon bayansa tana hawaye.

Ranar asabar lokacin sun dauki sati uku a wannan yanayin tana fitowa daga kitchen shi kuma zai shiga daukan cup ya hada tea. Kallon kallo suke yiwa juna ta matsa ta bashi hanya. Yana shiga ya bugo kofar da kafarsa ashe hannunta na wurin kofar ta matse. Ciwo taji har tafin kafarta tayi kara cikin zafin nama ya bude kofar. Hannun ta rike sosai tana fitar da hawaye ta kasa tsayuwa wuri daya don azaba. Mantawa yayi da fushinsa da komai ya kama yatsun nata biyu da yaga ta rike ya shigar da ita kitchen ya sakar mata ruwa. Idonta a rufe tana kuka a hankali. Ciwon bai dameta ba kamar yadda Jikamshinta ya canja mata.

Har zuciyarsa yake jin kukan tana bashi tausayi sosai. Ya soma hura mata yatsun amma yana gani har sun fara kumbura. Fuskarta yake kallo itama yau bata kawar da nata idon ba ta zuba masa ido. Yadda ta rame shima haka ya rame. Yana rike da hannun ya kai yatsun nata bakinsa ya saka a ciki. Kallonsa kawai take tana kara sonsa duk da halin da suke ciki a lokacin. Kusan minti uku yatsunta na bakinsa sannan ya cire yace "kinji sauki ko nasa miki kankara"

Yaushe rabon da yayi mata magana. Ita da jin muryarsa sai dai idan waya yake. Girgiza kai tayi ta janye hannunta ta tafi. Wani iri yaji, yunwar ma ta fita a kansa sai rudani na rashin sanin yadda zaiyi da Asmau. Dakinta ya bita ya sameta zaune a kasa a kuryar gado tana kuka a hankali. Bai ce mata komai ba ya bude inda take ajiye mayafai ya dauko mata wani kato mai kauri. Tayar da ita yayi tsaya ya yafa mata sannan ya riko hannunta suka fito falo ya dauki mukullin motarsa.

Cigaba yayi da jan hannunta har gaban mota. Ya bude mata ta shiga ta zauna sannan ya cewa Mal Sabo idan ya dauko Amatullah ya kaita gidan Ismail. Sai ta kula ya mikawa Mal Sabon wata karamar jaka wadda take tunanin kayan Amatullah ne a ciki.

Da ya zauna ya tayar da motar Ismail din ya kira ya fada masa za'a kawo Safina kila ta kwana. Shi kuwa sai murna yace dama yana gida.
*****

Barrack dinsu suka je bangaren asibiti. Ita dai binsa take a baya har suka shiga ciki. Wani office ya shiga ya barta a reception. Ba dadewa ya fito yace ta shigo.

Hussaini ne a ciki sanye da kayan sojoji amma ya dora coat din likitoci.
"Ranki ya dade sai ki zauna a waje kuma? Sir kasan fa ita ce mai hadani da Walida ya kamata ka tayani kamfen"

Duk su biyun ya kula babu wanda dan guntun wasansa ya bawa dariya. Shima sai ya ci serious ya koma mazauninsa. Yasan yau abokin nasa a matsayin shugabansa ya shigo.

Col. Ishaq ya kamo hannunta da ya matse wanda yatsun sun kumbura faratan kuma sunyi jawur alamar taruwar jini daya har ya fashe ta saman farcen "Doctor a duba mata hannun nan bana so ya zama babban ciwo"

Hussaini ya kallo hannun sai ya dauki waya ya kira nurse aka zo suka tafi da Asmau yace ayi mata dressing. Bayan sun fita yace "ai yadda na ganku ne har naji tsoro ko anyi fadan masoya ashe amarya ciwo taji"

"Kaga ba batun wasa ina so duk wani test da akeyi a gano ciki kayi mata please"

Hussaini ya mike da sauri "Sir ciki??? Iko sai Allah, bashi da abokin tarayya. Lallai Allah maji rokon bayi."

Col Ishaq yayi masa wani irin kallo "me kake nufi ne? Kafi kowa sanin matsalata yanzu na fada maka zancen ciki kuma kana murna"

"Wannan ai abin farinciki ne da murna. Bari na fada musu ayi test din Allah Yasa akwai. Kai da kaina zanyi mata ma"

Ran Col. Ishaq ya soma baci yace "Hussaini bana son wasa. Kada ka manta banda dangina bani da wani amini sama da kai. Kai kadai na fadawa komai game da Asmau kafin na aureta. Sauran a gari suka ji idan har sun sani. After all these years aure kasa da shekara ko wata shida bamuyi ba tace min tana da ciki" muryarsa tayi rauni sosai dauriya ce kawai yake.

Zama Hussaini yayi a kujerar da take kallon ta Col. Ishaq hankakinsa a tashe.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Kada kace min zarginta kake yi. Col. Ishaq Jikamshi waye ya fada maka bazaka taba haihuwa ba? Na tabbatar ba ni bane"

Maganar ta fara daure masa kai yace "ku likitoci kun iya boyewa mutane zahirin abu sai kuyi ta rufa rufa don kada ku tsorata patient. Ka gwadani ka kuma hadani da likitocin da lalurata ta shafe su. Kowanne sai ya cemin lokaci ne baiyi ba. wane magani ne ban sha ba. Sai gashi Badar ta haihu daga yin aure. Wannan ya tabbatar min ni nake da matsalar. Nine bana haihuwa "

Hussaini ya jima yana kallon abokinsa kafin yayi magana "idan ni ko wasu a nan zamu boye maka idan bazaka taba haihuwa ba, asibitocin da kaje a kasashen waje kasan bazasu yi maka karya ba. Babu wanda ya kai bature baro baro. Sai ya fada maka nan da lokaci kaza zaka mutu. Duk wani sakamakonka kana bani copy na ajiye. Babu inda akace bazaka taba haihuwa ba. Dukkansu suna cewa ko dai akwai matsala a mahaifar Badariyya ko kuma wani dalili dai ya hana cikin samuwa amma ba rashin lafiya gareku ba."

Col. Ishaq ji yayi ya fara jin zafi. Me Hussaini yake nufi. Wai zai iya haihuwa???.

Hussaini ya cigaba "idan wasu zasu boye maka ni bazan bari kayi ta kashe kudi kamar baka san zafin nema ba akan haihuwa alhalin nasan bazaka samu ba. Garin yaya ka yankewa kanka wannan shawarar har kake zargin matarka. Allah Sarki shiyasa naga ta kasa magana da kuka shigo. Bani da masaniya game da Asmau bayan abinda ka fada min amma bana jin zata aikata wannan mummunan aikin gareka. Kada ka manta taga rayuwa a dalilin kuskuren farko. Wallahi ni ka kara tsoratani akan zina. Idan har zaka zargeta duk son da kake mata lallai har a nade duniya fentin zina bazai taba barin Asmau ba. Ya Allah Ka nesantamu daga wannan bala'i "

Jikin Col. Ishaq ya gama sanyi kam yanzu. A lokacin da Asmau tayi masa albishir da samun karuwa a lokacin tarihin rayuwarta ta baya ya dawo masa har yake tunanin ko a garuruwan da ta zauna ta cigaba da mugun aiki. Tashi yayi da sauri Hussaini ya dakatar dashi "ka jira nayi mata gwaji a tabbatar"

Zama yayi amma jinsa yake a kan kaya. So yake ya ga Matar Jikamshi a jikin Jikamshinta. Wani irin sonta yake ji na daban yana ratsa shi. Gabadaya yaji ya tsani kansa da zuciyarsa da ta raya masa wannan mummunan zargi..

Tana zaune an saka mata bandeji a yatsun Hussaini ya shigo dakin da suke. Nurse ya bawa umarni ta debi jininta nan da nan ya karba ya tafi lab dinsu. Da kansa yayi gwajin har sau biyu ya tabbatar babu karya Asmau tana da ciki. Dawowa yayi yayi mata tambayoyi wanda tana amsawa tana hawaye. Yaji tausayinta sosai sannan suka koma office dinsa.

Ko da suka shiga kunya ce ta kama Col. Ishaq ya kasa yi mata magana. Hussaini yana murmushi yace "congrats Sir, uwargida tana da ciki wata na uku kenan. Zan bata appointment idan tazo sai a bata maganunguna ayi scanning domin ganin lafiyar baby. Allah Ya inganta Ya raba lafiya."

Col. Ishaq kamar yayi me don murna. Yana cewa Amin ita kuwa Asmau ta fita daga office din saboda kukan da yazo mata. A bakin mota ya sameta bayan Hussaini ya nanata masa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login