Showing 6001 words to 9000 words out of 120086 words

Chapter 3 - ABINDA AKE GUDU

30 Oct 2024

2576

zare mata ido "munafuka algumguma ai sai kizo ki zauna kin wani tsaya mana a ka kamar sa'anninki."

Da sauri ta zube a wurin da take tsaye ta dukar da kanta hawaye na kwarara a kumatunta. Hajjo ta furzar da goron bakinta a kan kafet tace "hankalinki ya kwanta ko Bara'atu? 'Yarki ta janyo mana abin kunya ta bata mana suna a gari. Tun rasuwar Shu'aibu babu yadda bamuyi dake ba akan ki bari 'yan uwansa su raba 'ya'yan a tsakaninsu kika ki amincewa. Yau wa gari ya waya uhmm? Dama tarbiyar mace mai zaman kanta har wata tarbiya ce." Hanci ta tsaya fyacewa tana kukan Bara'atu ta cuce ta.

Umma tayi shiru kawai, tun dazu da aka aika musu da rasuwar Abubakar babu wanda yazo cikinsu. Yinin bikin ma cewa suka yi tayi a gidanta suma zasuyi nasu ko babu amarya. Sai yanzu da wannan abu ya faru shine duk suka taho. Harda Yaya Abu da babu abinda ta halarta na bikin wai tana ciwon wuya.

Alh Rabe ya doka tsaki "dama me kike tsammani daga mace irin wannan Hajjo? Saboda na taimaki rayuwar 'ya'yan dan uwana fa har shahada nayi nace zan aureta duk da yadda nake kyamar mayu 'yan garinsu amma taki. Yanzu ta fada muku shegen da ya dirka mata cikin ko kuwa saboda samarin sunyi mata yawa bata san waye uban ba?"

A kufale Jafar yace "Kawu nayi tunanin zama akayi na maslaha akan matsalar nan ba bakaken maganganu ba."

Umma ta watsa masa harara don yayi shiru amma duk da haka sai da Yaya Abu ta hado masa ashar ta kunduma masa. Sannan ta dubi Asmau "to karuwar cikin gida wadda ake nuna mana kunfi kowa tarbiya. Cikin na waye don ko ni ban yarda na yaron nan bane Abubakar bawan Allah. Gara da Yalwa taki karba zaku gurbata musu asali."

Jin batayi magana ba har Hajjo ma ta sake tambaya yasa Kawu Rabe yayi kanta yana haurinta da kafa. Tun tana zaune har sai da tayi kasa yana tattaka ta. 'Yan uwan Umma suka tashi aka rike shi sannan suka janyeta. Umma dai sai kukan zuci. Duk abinda aka yi musu a yau Asmau ce ta janyo mata saboda haka bata da bakin magana. Kallonsu take yi suka ci gaba da caba musu bakaken maganganu 'yan uwanta suna karewa sannan suka tashi. Hajjo tace "ki shirya sati mai zuwa ki turo min Yasar da Aina'u gara nasa su a gabana don bazan bari zuri'ar Shu'aibu ta gama lalacewa ba ina raye.

Ranar gidan Umma ansha kuka kala kala. Shema'u duk yadda suke da kanwarta ko inda take taki kallo. Asmau ta bata kunya sosai. Anyi ta tambayarta kuma taki magana tunda sunki yarda cikin Abubakar ne. Abu dai har tsakar dare suna dakin Umma ana ta magana daya. Asma'u kuwa babu wanda ya shigo dakinta. Kawayenta da suke gidan gabadayansu bata san inda suke ba har da aminiyarta Walida wadda take ganin kamar bazata gujeta ba a wannan yanayin.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽5

Batul Mamman💖




Zaune take kan abin sallah tana addu'a tana zubar da hawaye. Bata taba tsammanin ganin rana makamanciyar wannan ba a rayuwarta. Babu Abubakar ga cikinsa a jikinta batare da aure ba. Yau da cikin aure ne bata san irin soyayya da gatan da Umma da Mama Yalwa zasu nuna mata ba. Ashe haka ake ganin bambancin rayuwar wadda aka shafa fatiha akanta da wadda ba'a shafa ba? Gashi dai duk abu daya suka yi, amma mai aure sai ta zama tauraruwa har idan batayi ciki ba ayi ta korafi ko aji tausayinta. Ita gashi kuskure sau daya tak, tayi cikin da bata bukata gashi hatta mahaifiyarta tana nuna mata kyama. Aure ibada ne, zina kazanta ce. Wani kukan ne yazo mata da taji cikinta na kukan yunwa. Yanzu idan taci abinci abinda ke cikinta ma zai samu? A hankali ta shafi cikin zuciyarta na kuna.

"Wayyo Allah, Ya Allah Ka jikan Abubakar Ka karbi tubanmu" abinda ta fada kenan cikin raunanniyar muryar da ta gama dashewa don kuka. Akan abin sallar bacci ya saceta tana rungume da AlQur'ani.

Gari na wayewa ta rinka jin muryarsu Umma a kitchen ana dafa abincin da ta fuskanci na sadaka ne da za'a kai gidan Kwamishina. Tana son fita amma tana tsoron abinda zai biyo baya. Duk wannan tashin hankalin wata muguwar yunwa take ji sai dai ko zata mutu bazata fita neman abinci ba.

Sai wurin karfe goma taji gidan ya danyi shiru. Tana nan zaune Anti Bintu ta shigo dakin. Itama dai ba sakin fuska tayi ba, ta shigo dauke da plate din abinci da ledar pure water. A gaban Asmau ta ajiye ta juya ko gaisuwar da take mata bata amsa ba.

Sai da ta fita ta fashe da kuka. Rana daya Asma'u ta zabge idanu sunyi ciki kamar ta shekara a kwance. Tana jin tausayinta sai dai dole a nuna mata kuskurenta. Abincin da ta kai mata ma babu wanda yasan ta kai. Kuka tayi sosai sannan tabi bayansu Umma da suka riga suka tafi gidan rasuwar.

Su Umma zasu shiga gidan taji Mama Yalwa tana cewa alajirin da ya kawo abincin ya mayar musu da abincinsu bata so. Dama tasan tun faruwar al'amarin jiya dole Mama ta canja mata. Sai dai mutuwa ta kori komai shiyasa ta daure tazo. Sallama tayi suka shiga sai tayi kamar bata ji abinda Mama ke fada ba. Itama kunyar ganin Umman tayi sai ta bar gaban kulolin abincin. Haka suka gaisa kowa fuskarsa a cunkushe su Umma suka sami wuri suka zauna. Babu mai cewa komai dama gidan rasuwa ne. Mutane 'yan kallo suka taru suka zuba musu ido.

Haka ce ta kasance kullum Umma zatayi abincin sadaka kuma su je gidan su zauna sai anyi la'asar su koma gida. Tsakaninsu da Asmau kuwa ko kallonta batayi duk da tana fitowa ta gaisheta. A rana ta shida ne da daddare wata dattijuwa cikin 'yan uwan Umma tace ya kamata su zauna suyi magana akan lamarin Asmau.

Umma tace "kayya dai Gwaggo, me ya rage mana kuma banda zubewar mutumci."

Gwaggo tayi dan murmushi "Bara'atu nayi tunanin ke mace ce mai hangen nesa da tawakkali. Me kike tsammani ga yarinyar da take cikin yanayi na Asmau ace kowa ya juya mata baya? Idan abin ya isheta dole tayi tunanin nemawa kanta mafita koda kuwa mafitar halaka ce fiye da halin da take ciki yanzu. A 'yan kwanakin nan duk wanda ya kalleta yasan tana cikin damuwa kuma muna fatan ta yi nadama. Kamata yayi a sake tambayarta lallai ta fadi gaskiya game da cikin sai a san matakin dauka."

Kowa a dakin yayi na'am da shawarar. Shema'u dama mijinta yayi mata fada akan rashin kula Asmau da suke yi ba shine mafita ba. Umma tace aje a kirawo Asma'un.

Gabanta na faduwa ta shiga dakin kowa ya zuba mata ido. A can gefe ta zauna idonta a kasa.

Anti Bintu tace " Asmau ki dubi girman Allah da halin da kike ciki ki fada mana gaskiya game da cikin jikinki."

Kai a sunkuye ta sake nanata musu cewa na Abubakar ne. Ran Umma a bace tace ta tashi ta fita. Ji take inama Asmau tace fin karfi aka yi mata. Da ta tausaya mata amma da jin bayaninta kasan abin ba haka bane.

Shawara aka yanke jibi bayan anyi kwana bakwai da rasuwar suje su sanar da iyayen Abubakar. Haka kuwa akayi. Da yawan 'yan bikin sun koma Wushishi sai kadan suka rage saboda abinda ya faru. Babu wanda ya sake zuwa daga gidan Hajjo dama basu sa a ka ba.

Umma da Anti Bintu suka je sai Gwaggonsu da Asmau. Mama na ganinsu ta hade rai Umma ta daure ta bukaci ganinsu ita da Alh Adamu.

Harda Abdulhalim da Nasiba suka zauna a falon. Gwaggo ta gabatar musu da dalilin zuwansu.

Alh Adamu yayi gyaran murya ya soma magana "duk wannan bayanin naji shi tun a ranar da Abubakar ya rasu. Ina sane nayi shiru har sai an share makoki. Bazan boye miki ba Haj Bara'atu wannan labari yayi matukar muni garemu baki daya. Sai dai kuma tsakani da Allah wanda ake abin a kansa yanzu baya raye. Maganar Asmau kadai bazata sa mu karbi cikin jikinta a matsayin nasa ba. Yau da yana nan ne sai ya karba ko ya kare kansa."

Tunda ya fara magana Umma ta soma zubar da hawaye..
" Alhaji duk mun shaida Asmau babu wanda take sauraro sai Abubakar. Idan kuka gujemu a wannan lokacin bansan inda zanyi ba. Dangin babansu dama ba kaunar mu suke yi ba, kune dai a garin nan kuka tsaya mana tamkar 'yan uwa....."

Mama ta katseta "maganar 'yan uwantaka da cikin shege fa bata taso ba. Kamar yadda Baba ya fada da Abubakar yana raye sai muji ta bakinsa. Amma babu yadda za'ayi mu karbi cikin nan kawai don Asmau tace nasa ne."

"To a bari ta haihu mana sai a gwada a tabbatar da zancenta." Abdulhalim ya fada yana kallon Asmau. Shi tausayinta yake ji.

Mama tace " zanci mutuncinka wallahi. Idan an bari ta haihu ya dace da dan uwanka zaka karba ka rike ne? Shashasha tashi ka fita."

Baba yace "ina zaunen kike irin wannan abin Yalwa?..." ya juya ga su Umma
"kiyi hakuri Haj Bara'atu amma babu yadda zamuyi saboda babu kwakkwarar shaida. Idan har kina bukatar taimako kinsan ni mai taimaka miki ne kodayaushe." Yana kaiwa nan ya tashi ya shige ciki Mama tabi bayansa. Nasiba ma ta tashi babu wata magana da suka ji mai dadi.

Umma da Asmau sun sha kuka. Suka tashi suka tafi gida jiki babu kwari. Asmau tana tausayin halin da ta jefa mahaifiyarta. Suna zuwa gida hawan jinin Umma ya tashi aka kaita asibiti. Kuka dai yaki karewa a gidan. Kuma aka ki tafiya da Asma'un asibitin. Sai bayan isha suka dawo Yasar yazo dakinsu Asmau ya kirata fuskarsa babu walwala. Tana tashi yayi mata wani kallon banza " idan kika kashe mana Umma wallahi sai nayi miki abinda baki taba tsammani ba. "

A razane ta kalli yaron da ta bawa shekara hudu wanda tsakaninta dashi kullum girmamawa ce. Indai Yasar zaiyi mata haka kowa ma dole ya tsaneta. A sanyaye tabi bayansa.

Yanayin da taga Umma ya bata tausayi sosai tace "Umma yaya jikin?"

Maimakon ta amsa sai tace "munyi magana da wata ma'aikaciyar asibiti tace gobe mu kaiki karfe goma na safe a cire cikin".

A tsorace Asmau ta mike tsaye tana kuka "Umma kada zunubin yayi min yawa. Ga laifin ciki ga na kisa. Don Allah ki janye..."

Saukar mari taji mai zafi a kumatunta daga Jafar, marin bai gama shigarta ba yace
"banza ana son taimakonki zakiyi mana shirme. Waye zai sake kallonki idan aka bari kika haihu? Dubi yadda kika tarwatsa mana gida Asmau. Ki bari a cire indai ba kuma neman karasa zubar mana da kima kike son yi ba."

Shema'u ta taso ta rike kafadar Asmau
"cire cikin nan shi kadai ne maslaha garemu baki daya. Waye zai dauki dawainiyarki data abinda zaki haifa? Haba Asmau, ki bari muji da bakinciki daya mana."

"Ku kyaleta ta nuna min iyakata. Asmau da kinsan irin radadin da nake ji a zuciyata da baki soma bude baki ba ma. Wallahi nayi nadamar haihuwarki, ina ma barinki nayi tun kafin ki zama mutum da dai naga irin wannan bakar ranar a dalilinki." Umma ta fada kuka mai sauti.

Hankalin Asmau ya sake tashi sosai da jin abinda Umma dake matukar kaunar 'ya'yanta take fada yanzu. Durkusawa tayi a gabanta tana ta kuka da rokon ta yafe mata. Anti Bintu mai jin tausayinta tace ta fita ta basu wuri. Tana bakin kofar taji Jafar yana cewa ko ta karfin tsiya sai sun kaita asibitin ko a kira likitan har gida a cire. Umma dai bata sake magana ba amma sauran sun amince. Har Gwaggo na cewa akwai wasu saiwoyi da basu fada a asibitin ba sai tasa a kawo daga Wushishi a bata tasha cikin zai zube.

Kasa tsayuwa tayi a bakin kofar ta koma daki. Ita da Abubakar sunyi kuskure babba amma tabbas zubar da cikin nan karin laifi ne. A yadda ta janyowa gidansu bacin suna a duniya bazata so ta zama silar karin zunubi a garesu ba a lahira. Da wannan tunanin ta janyo akwati daya cikin na lefenta ta hada 'yan kayayakinta ta zuba a ciki. Dan kudin da ta samu na biki da dan sauran kudinta ta saka a jakar hannu mai girma sannan ta ciro wasu sarka ,dankunne da awarwaron daga wata drawer duk ta saka a ciki tare da wasu kayan kala uku. Ko kadan bata runtsa ba a daren. Asubar fari Jafar da Yassar suka bude gate suka tafi masallaci. Suna fita Asmau ta lallaba ta fice daga gidan tayi hanyar titi.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽6

Batul Mamman💖




Ta tsakanin gidaje ta rinka bi don kada ta hadu da idon sani idan an idar da sallar asuba sun fito daga masallaci. Ta jima tana tafiya zuciyarta cike da fargaba. Ba ita ta iso titi ba sai da hasken rana ya fara bayyana. Jefi-jefi ababen hawa suke wucewa don ma titin nasu na hotoro wurin wucewar matafiya ne. Kusa da wani kanti da yake rufe ta shimfida dankwalinta tayi sallah sannan ta koma titi ta tare dan sahu.

Mutumin ya kare mata kallo sama da kasa sannan yayi magana
"Hajiya ina zuwa?"

"Tasha zaka kaini." Ta amsa masa tana kara rungume jakarta da akwati.

"Garin Kano kuma mai tasha da yawa sai ki fadi wadda zaki je"

Sai da ta danyi tunani ta tuno sunan tasha daya
" kaini ta unguwa uku, nawa zan baka?"

Yadda dreban dan sahun ya kula ta matsu ta shiga yace "kawo dari biyu tunda kinga yanzu safiya ce sosai"

Babu musu ta zuba kayanta ta shige tana kare rufe fuskarta da hijabinta.

Sai da ta sauka ta fara rarraba idanu domin ko kadan bata san inda zata je ba. Ummanta 'yar Niger state ce to amma tasan zuwa yanzu duk 'yan uwanta sun gama jin labarin komai, idan taje wurinsu ba ta tsira ba. Tana cikin wannan tunanin taji ana cewa,

"Azare mutum daya
Azare mutum daya"

Ko dogon tunani batayi ba ta nufi motar da sauri. 'Yan kamasho har sun fara baibayeta ana tambayarta ina zata je. Da shigarta motar dreban yazo suka gama surutansu da 'yan uwansu drebobi ya tada mota suka harbi titi.
*****

Har karfe tara babu motsin Asmau. Anti Bintu da Jafar ne zasu kaita asibitin duk sun shirya. Umma tace aje a tashe ta idan batayi wanka ba su tafi a haka ta yi idan sun dawo.

Aina'u aka tura taje ta dawo tace bata ganta ba. Shema'u tace kila tana bandaki kije kice mata tayi sauri ita ake jira.

Da gudu Aina'u ta dawo tace "Anti na duba bata daki kuma bandakin a bude yake".

Umma na jin haka tace a tashi a dubota karshenta buya tayi saboda kada aje asibitin. Da farko Yassar da Aina'u kadai ne suka duba dakunan da bayan gidan suka dawo basu ganta ba. Hakan ya soma tsorata Umma kowa ya tashi a rude suka shiga nemanta. Ganin babu alamun za'a sameta a gida Shema'u ta kira wayarta. Tayi mamaki jin muryar Walida. Bayan sun gaisa Walida tace wayar na hannunta. Tun ranar da abin ya faru zance ya fara bazuwa mahaifinta har gidan yazo ya dauketa da kansa lokacin da aka sake mayar da Asma'u asibiti kuma ya haramta mata sake zuwa gidan.

Shema'u tayi kasake har Walida ta gama bayani sannan tace zata turo Yassar ya karbi wayar. Tana juyowa Umma ta kalleta a tsorace
"Kada kice min an sace wayar ne".

"A'a Umma tana wurin Walida."

"To ina Asmau ta shiga, ni Bara'atu daga wannan sai wannan".

Da gudu Jafar ya dawo falon da takarda a hannunsa wadda ya gani a tsakiyar gadon dakin su Asmau. Jiki babu kwari ya mikawa Umma ta karba hannu na rawa.

_Umma ina mai rokon gafararki a lokacin da kike karanta wannan takardar nayi nisa da gida. Nayi nadama da bakincikin halin da na saka ku na kuma jefa kaina. Sai dai na dauki komai a matsayin kaddara. Na tafi ne saboda bana son ku daukarwa kanku zunubin kashe rai. Zan haifi abinda ke cikina da izinin Allah zan kula dashi batare da na fada mummunar rayuwa ba. Ki yafe min kuma ki cigaba da yimin addu'a. Allah Ya hadamu cikin aminci. Sannan ina mai kar tabbatar muku cikin nan na Abubakar ne. Ku yafe mana._
_Asmau_

Kuka mai sauti Umma ta saka wanda yasa Shema'u saurin karbar takardar ta karanta. A take itama ta fashe da kukan. Umma sai sumbatu take saboda tsabar tashin hankali.

"Asma'u ki dawo wallahi babu mai cire miki cikin. Ki dawo na yafe miki. Ina zaki je ke kadai a wannan duniyar da amana tayi mana karanci?"

Duk wanda yake wurin sai ya tausayawa Umma. Dama da mayafi a jikinta tace Jafar ya dauko mukullin motarta yazo su fita neman Asma'u. Nan da nan kowa ya fita suka fara karade unguwar. Daga nan sune gidajen kawayenta da tashoshin mota tare da hoton Asmau suna tambayar ko an ganta.

*****
Karfe goma na safe tayiwa Qasim a kofar shagon mai gyaran waya. Mai shagon a wurin ya sameshi a ransa yace dan anace ya iso. Allah Ya taimake shi ya gama gyaran shiyasa da fara'arsa yace "ranka ya dade ai yanzu nake shirin kiranka idan na bude shagon."

"Baka da abin da zaka fada min. Gyaran waya sati guda kuma na biyaka. Kawai sai ka zauna kana ja min rai."

Gefe ya matsa mai shagon ya bude. A cikin wata drawer ya dauko wayar Qasim wadda screen dinta ya fashe tun ranar alhamis da ya iso garin Zamfara. Duba wayar yayi ya tabbatar tayi sannan yayi sallama da mutumin ya fita.

Bakin titi ya koma inda ya ajiye motarsa. Yana shiga ya kira mahaifiyarsa bayan sun gaisa ya sanar da ita wayar ta gyaru zata rinka samunsa. Dama ta wani yake ara a ofishinsu ya saka sim dinsa ya kira. Karamar wayarsa tana wurin kanwarsa da ya bawa kafin ya taho.

Bayan yayi sallama da ita ya kira numbar Abubakar. Kullum idan ya ari waya sai ya gwada amma a kashe yake samunta. Dariya kawai yake yi yace ango ya dau hutun

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login