Showing 69001 words to 72000 words out of 120086 words

Chapter 24 - ABINDA AKE GUDU

30 Oct 2024

2585

kulawa ta yadda babu wata mace mai suna kishiya da zata takura mata shine zata kai kanta cikin mutanen da basu dade da sanin juna ba. Yanzu idan ta aure shi danginsa suka wulakanta ta fa? Hawaye yaji yana neman zubo masa. Duk laifinsa ne da ya zama mugun aboki ga Abubakar. Ba don shawarar da ya bashi ba ai da haka bata faru ba. Ko Abubakar ya rasu ya tabbatar duk inda tayi aure zata tsira da mutunci da martabarta. Sai kuma tausayinsu da yaji. Asmau tayi masa halacci da har bata kalli tsabar idonsa ta nuna masa bata son shi ba. Yayi dan murmushi, dole yasan yadda zaiyi ya janyo ra'ayinta gareshi tare da nuna mata illolin da auren wanda basu gama sani ba zai iya jawo mata. Idan kuma hakan bai samu ba......kasa karasa tunanin yayi.
*****

Col. Ishaq yana zuwa gida ya kira Asmau. Jin wayar a kashe yayi dan murmushi. Ya fuskanci tana cikin matan da basa bawa waya mahimmanci. Yau ta kashe gobe tace wayar tana daki ne. Sai da yayi wanka yaci abinci sannan ya tafi dakin Hajiya.

A zaune ya sameta a kasa Bilkisu tana matsa mata kafafu. Ya zauna a gefenta ta dan janye jiki ita a dole ga dan fari. Dariya Bilkisu tayi ya rankwasheta a ka don yasan tsokanar Hajiya take yi, sannan ya fuskanci Hajiyar.
"ciwon kafar ne ya tashi,akwai maganin ko ya kare?

"Na sha ma bayan naci abinci dazu. Yau ina ka tsaya daga cewa zaka ganin abokinka"

"Asthma din Safina ce ta tashi suna asibiti an kwantar dasu."

Cikin tausayawa Haj Lubabatu tace "Allah sarki, ciwon yaro babu dadi bare ciwo irin wannan. Da ka fada mana tun dazu ai sai Sabo ya kawo mu kafin ya tafi gida. Ya kamata su hada mata da maganin gargajiya, zan tambayi Kawunku suna masana a bangaren. Kasan ciwon yana bukatar kulawa"

Yaji dadin yadda mahaifiyarsa ke nuna damuwarta akan abinda yake so duk da bata son fada. Bilkisu yasa ta tashi hado masa abinci ya samu ya sanar da Hajiyan duk abinda ya faru a yau bayan zuwansa asibiti. Haj Lubabatu ta kalle shi cikin damuwa
"Yanzu kai bazaka hakura da ita ba tunda iyayenta sun fi son wancan yaron?"

"Hajiya itama bata son sa. Kuma don ban gabatar da nawa magabanta bane da wuri. Kin sanar da su Kawun kuwa?"

Ta girgiza kai tana mamakin wannan soyayya da danta yake yiwa Asmau.
"Na fada musu don Yaya Auwalu ma yace zai kiraka kuyi maganar. Ni dai bana so azo a sami matsala daga iyayenta gara kawai tunda har an fara batun kawo kudi ka janye."

Dan murmushi kawai yayi "Hajiya idan kina kyamar aurena da Asmau ki fada min. Nasan hakan zai iya zuwa ranki saboda irin yanayin data tsinci kanta a baya. Kin sani duk yadda nake son abu bazanyi batare da izini da neman albarka daga gareki ba"

Akwai shi da iya tsara zance da ladabi shiyasa take sonsa.
"Ko kadan bana kyamar aurenku. Kuma ni wacece da zanki karbar kaddara. Ka sani babu wata uwa a duniyar nan musulma da zata ji farat daya hankalinta ya kwanta idan danta ya nemi auren macen da ta taba haihuwa a wajen aure. To amma kowa da abinda Allah Ya tsara masa. Yarinyar nan kana ganinta kasan ta fito daga gidan tarbiya sai gashi tsautsayi ya fada mata ta tsinci kanta a irin wannan yanayin. Bazan ki ta ba don da Allah Yaso da daya daga cikin nawa 'ya'yan za'a buga misali. Idan Asmau matarka ce fatana Allah Ya baku zaman lafiya da hakuri da juna"

A take fargabarsa na kin amincewarta ta gushe daga zuciyarsa. "Nagode Hajiya Allah Ya kara lafiya. In sha Allah zan nemi Kawu Auwalun idan ya bukaci naje Jikamshin sai naje. Ina so su zo da wuri ne."

Yanaa tashi Bilkisu ta shigo da abincin ta ajiye a gabansa tana murmushi "Uncle albishirinka"

"Goro maigadon zinare"

Ta danyi tsalle kamar karamar yarinya "gobe Mami zata zo"

Dena zuba lemon da yake yi yayi yace "da gaske" fuskarsa na nuna farincikinsa.

Hajiya tace "to sarkin surutu. Ke da tace kada ki fada masa sai da ya ganta kika fasa kwan saboda kina murna mamanki zata zo ko?"

Bilkisu ta turo baki "kai Hajiya nifa ba haka nake nufi ba"

Col. Ishaq yace "Hajiyar tawa kike turawa baki. To na mayar da goron albishir din banji abinda kika fada ba"

Tashi tayi ta bar dakin tana buga kafa yana mata dariya. Ya juya ga Hajiya cikin murna "gara tazo taga yayarta kuma kanwarta"

Mami ita ce 'yar Haj Lubabatu ta biyu. Shekara daya da rabi Col. Ishaq ya bata. Ba karamin shakuwa suka yi ba kamar ba sako da sako ba. Komai nasu tare suke yi. Hatta zancen Asmau ya fada mata ya sami wadda yake so amma sai tazo Kano ko shi yaje Jos din zasuyi maganar sosai. Ita kanta murna da doki ya isheta saboda ta matsu yayi aure. Tun bayan rabuwarsu da Badariyya bata kara jin yayi zancen mace ba sai yanzu.
******

Washegari litinin su Asmau sun kwana a asibiti. Da sassafe Umar yazo ya kai Mama gida ta yi wanka sai ya taho da Ainau ta taya Asmau zama. Ko goma bata yi ba suka ji sallamar Col. Ishaq. Asmau na jin muryarsa taji wani irin dadi a ranta. Soyayyarta da Jikamshi kullum jinta take sabuwa. Cikin khakinsa yake na sojoji yayi kyau ta bishi da ido a lokacin da yake shafa kan Amatullah dake kwance tana bacci. Ya amsa gaisuwar Ainau sannan ya juya yana kallon Asmau. Saurin sunkuyar da kai tayi tana jin kunyara tan cigaba da yiwa Husna dake hannunwa wasa. Bai dauke idonsa daga kanta ba yace
"Ainau dake ake shirin kai Matar Jikamshi gidan wani?"

Ainau ta zaro ido "wallahi babban yaya nima har kuka na tayaka. Ba don kada kuga wautata ba sai nace asthmar Amatullah tayi min daidai."

Wani wawan dundu Asmau ta kai mata harda harara. Ainau tace "ba fa har raina naso ciwon ba." Ta dan juya " kaga tana hararata ko"

Col. Ishaq ya karbi Husna daga hannun Asmau yana dariya "nima harararki nayi a zuciya. Ya zaki ce asthma tayi. Duk da dai na dauketa a matsayin tazo hanawa a raba Jikamshi da matarsa"

Irin kallon da yake yiwa Asmau yana wani lumshe ido yasa Ainau jin kunyar kasancewa a wurin. Sai murmushi suke yiwa juna. A ranta tace ba dole Yaya Asmau taso shi ba. Shi kuwa Yaya Qasim bata ga alamar ya iya nunawa mace soyayya ba. "Allah Ya baku hakuri to. zan fadawa Baba Amatullah ta warke ko gobe Yaya Qasim ya kawo kudi"

"Kinga kina jego shiyasa nake tausayinki. Idan aka aura mata wani ranar zaki kwana a guardroom don nasan adduarki ce taci" Col Ishaq ya fada suka yi dariya sannan ya yiwa Asmau alama da ta biyo shi.

Sai da suka je bakin motarsa yace "Matar Jikamshi kin tashi lafiya, ya jikin princess dina?"

Tana kallon kasa saboda kunyar tunowa da yadda jiya ta nuna masa tana sonsa tace "lafiya kalau Alhamdulillah"

"Yau 'yan kunyar sun zo ne zasu hana ace min I love you" ya karashe maganar yana kwaikwayonta.

Bata san lokacin da ta soma dariya ba yace "jiya duk bana cikin hayyacina ne sosai nima bance miki Matar Jikamshi ina sonki ba. Amma yanzu na fada. Zan wuce office sai an taso zan dawo ko kuma bayan magrib. Ki kular min da matata da 'yata"

"Allah Ya tsare Ya bada sa'a kuma Ya kareka daga dukkan sharri"

Kasa bude motar yayi ya kalleta "Matar Jikamshi"

"Naam Jikamshi _na_"

Yana murmushin jin dadi yace "komai naki ina sonsa, ki rinka yi min adduar nan kullum don Allah. Kuma idan zamu rabu ki kada ki rinka kirana Jikamshina. Sawa kike naji kamar kada na tafi"

Tayi dariya ta sake cewa "Jikamshina"

Ya dan marairaice mata "don Allah ki bari"

Ta sake bude baki zata maimaita tana dariya yace "kina fada zan wuce wurin Umma na fada mata irin kalaman da kike yi min wanda yasa nake so a daura mana aure a yau dinnan"

Ba shiri ta rufe bakinta. Ko dai bai fadi hakan ba tasan zai iya kwatantawa. Dan gefe ta matsa ya shiga motar ya dago mata hannu sannan yaja ya tafi.

Ciki ta koma Ainau tana yi mata tsiyar yadda duk su biyun yanzu basa iya boye sirrin zukatansu a gaban juna. Sai shabiyu su Umma suka zo ita da Hajjo da Mama. A nan suka yini don likita yace sallama sai gobe idan numfashin Amatullah ya daidaita yadda ake so"
*****

Daga wurin aiki gida Col. Ishaq ya wuce. Bazai iya zuwa wurin Asmau ba sai yayi wanka ya canza kaya. Idan Mami ta iso kuma su je da ita dasu Hajiya.

Tun a waje yaga motoci a cikin gidan na kannensa da wata da yake tunanin a cikinta aka kawo Mami. Hakan ya bashi tabbacin yau duk sun zo a tare. Mara motar dama daya ce mai bin auta. Dadi yaji saboda yawanci suna zuwa ne kafin ya taso aiki basu fiye haduwa ba. Ya shiga falon yaji shiru sai daga dakin Hajiya yaji ana magana ana daga murya. Karasawa yayi kofar dakin ya tsaya yana karewa 'yan uwansa kallo.

Mami ke binsa sai Ismail, Dahiru, Safiyya da auta Musaddiq.

Mami ce take magana cikin matsanancin bacin rai harda hawaye a idonta "wallahi tallahi Hajiya bazamu yarda Yaya ya bata mana suna ba."

Ismail yace "meye na rantsuwa Mami, kema kinsan babu mai zuwa cikin su Kawu nema masa aurenta. Idan basu san karuwa bace yarinyar ni...."

Tsawa mai karfi Col. Ishaq ya daka masa. Duk sai da suka razana don sun san halinsa sarai. Kirjinsa ke bugu da sauri da sauri saboda bacin rai "ko da wasa kada ka kara kuskuren kiranta da wannan sunan"

Safiyya tace "ayi hakuri Yaya, Sayyada zamu kirata ko ustaziyya?"

Dariya suka yi dukkansu banda Hajiya ta sha kunu "ban taraku a nan don ku zagi Asmau ba. Yarinyar nan kaddara ce ta fada mata wadda babu wanda ta wuce ta a cikinku. Kuma ni ba amincewarku na nema ba. Na dai fada muku tana da 'ya ne saboda bana son kananan zance nan gaba"

Musaddiq yace "haba Hajiya wannan ai ba zancen da ya kamata Yaya zo dashi bane ki karba. 'Yar shege da uwarta bazasu sami karbuwa ba a danginmu."

Col. Ishaq yayi kansa ya cakumi wuyansa yana huci. Musaddiq sai kakari yake yi don wahala. Hajiya tana ta cewa ya sake shi amma yaki. Cikin zafin rai yace "Musaddiq kada ka kaini bango. Dukkanku nan babu zaman wanda nake yi. Idan na aureta don Allah kada wanda yazo gidana."

"Dama waye zai zo" Safiyya ta fada cikin tsiwa. Ya juyo kama ya mareta.

Daga nan suka tararwa yayansu ana ta musayar magana. Hajiya taji babu dadi saboda yaranta akwai hadin kai. Yau daya sai fadawa juna magana suke yi akan Asmau. Ita da tayi laifi shekarun baya amma a yau sanadiyar wannan kuskuren 'yan uwa duka magidanta suna fada.

Col. Ishaq yace "an fada muku duk matar da ta haihu ko tayi ciki a waje karuwa ce jikinta ta sayar.?"

"Yaya ka fada mana gaskiya fyade aka mata ko me? Ni wallahi gara ka auri gurguwa da wannan yarinyar. Kila ma asiri tayi maka duk ka kasa fahimtar mu " cewar Mami

Yau duka 'yan uwan nasa haushinsu yake ji "ba fyade aka yi mata ba Mami. Idan su basu fahimce ni ba yakamata ace kin gane inda na dosa."

"Tausayinta kake ji?" Dahiru ya tambaya

"ina jin tausayin Asmau saboda irin wannan abubuwan naku ma tun farko taki amincewa da aure. Amma ba don tausayi zan aureta ba. Sonta nake yi so you all should better learn to live with that."

"Wai Yaya da kake maganar nan hala ka manta cewa baka *haihuwa* ?"

Ismail ne yayi maganar wadda tasa kowa yayi shiru. Hatta Col. Ishaq jikinsa yayi matukar sanyi. Hajiya ta taso rai a bace "Ismail wace irin magana ce wannan? Dan uwan naka kake fadawa magana haka" ta daga hannu zata mare shi

Col. Ishaq ya rike hannun idanunsa sun kada sunyi jawur. A sanyaye yake magana "Hajiya gaskiya ya fada. Lokaci daya na manta ina da lalura har nake tunanin yin aure."

Ya kalli kannensa daya bayan daya "in sha Allah daga yau na bar zancen auren Asmau. Ismail nagode da ka tuna min da waye Ishaq, ni mutum ne da Allah Ya tsarawa yin rayuwa ba tare da naga nawa dan ba. Alhamdulillah tunda duk kuna da yara bazan ce na rasa gabadaya ba. Allah Yayi musu albarka. Bari na shiga nayi wanka zafi nake ji"

Hankali a tashe Ismail yace "Yaya"

"Kada ka damu kasan gaskiya daci gareta. Na da dan lokaci idan tayi aure zan manta da ita in sha Allah. Fatana Allah Ya tabbatar da aurenta da Qasim ko wanda ya fishi alkhairi gareta."

Yana fita yaci karo da Bilkisu. Hawaye take yi sosai ga tray din abinci a hannunta. Tana jin shigowarsa taje ta hada masa abinci don tasan tunda su Mami suka zo bazai fito da wuri ba. Duk zantunkansu taji komai. Ganinsa baisa ta tsorata ta bar wurin ba. Shima baiyi mata magana ba ya wuce abinsa.

Tana nan tsaye taji Hajiya tace "kun bani kunya da mamaki. Ban taba zaton zaku iya juyawa dan uwanku baya ba. Ina cewa Asmau tana da 'ya kuka hau surutu babu wanda ya tambayi garin yaya tayi cikin kafin aure."

Cikin nutsuwa ta basu labarin Asmau kamar yadda taji kuma ta gani. Safiyya uwar tsiwa sai ta fara kuka
"Mun shiga uku. Hajiya kuji wata muguwar kaddara. Allah Sarki"

Mami kuwa cewa tayi "duk da haka Hajiya ai bamu tabbatar da cewa a garuruwan da ta zauna bata taba karuwanci ba. Nima ta bani tausayi amma a bar maganar auren tunda ya fasa shima. Kinsan shi baya magana biyu"

Suna ta magana akan halin da Asmau ta tsinci kanta wanda ya girgiza tunaninsu ya kuma basu tausayi. Ace har rubutun cikin waya ya isa ya sa mutum aikata zina. Abin da ban tsoro da firgici saboda babu wanda ya isa ya tserewa kaddara sai dai komai akwai sila. Hajiya Lubabatu tace tunda zata je dubo Amatullah tana so dukkansu suyi mata rakiya.

Kukan Bilkisu suka ji Hajiya ta tashi da kanta sai dai kafin ta fito Bilkisu ta koma dakinta tana kuka. Bata taba sanin wannan labarin ba. A iya tunaninta baban Amatullah ya rasu ne ko ya saki Asmau. Tsoro ne ya kamata saboda akwai wani saurayinta da suke chatting a facebook. A hankali ya fara sako mata zantukan banza tun bata amsawa har ta dan fara sakewa yanzu. Wai har ya iya tambayarta ta kwatanta masa kayan baccinta da daddare. Tayi saurin dafe kirji, yanzu idan da abin yayi nisa kila itama ta shiga sahun masu bawa samari jiki. Kuka take sosai tana tausayawa Asmau kuma har ranta tana fatan Uncle Ishaq ya aureta ko don ya rufawa rayuwarta asiri. Sabon saurayin da suke dan satar kallon juna dashi ta kira a waya tana sheshshekar kuka. Numbar ma a wayar Uncle ta dauka batare da saninsa ba. Da sallamarsa ya dauka cikin muryar da ta dashe da kuka tace "Yassar ne?"
ABINDA AKE GUDU🙆🏽45

Batul Mamman💖




Mamaki ne ya kama Yassar, kamar ya san muryar amma bashi da tabbas.
"Da wa nake magana don Allah?"

"Bilkisu ce"

Tsorata yayi, shima yana neman numbarta amma yanzu da ta kirashi da alamun kuka sai yaji hankalinsa ya tashi.
"Bilkisu me ya faru?"

To me kuma zata ce masa? Tausayin kawunta take yi amma tana tsoron yi masa shishshigi. Uncle Ishaq yana da dadin sha'ani amma babu mai son ganin bacin ransa. Fasa maganar tayi na son ta roke shi ya lallaba yayarsa kada ta ki Uncle dinta tace "babu komai, anjima zamu zo duba Amatullah" tayi masa sallama ta ajiye wayar.

A ransa yasan don zasu zo ba shine dalilin kiran ba. Tashi yayi ya shirya ya tafi asibitin. Zai jira su zo ya sami damar tambayarta. Ko dai ta lura da yawan kallonta da yake yi ne? Yayi murmushi, tun zuwansa gidansu na farko ranar da kare ya biyo Asmau ya fara jin wani abu game da Bilkisu. Sai dai duk hayaniya ta Yassar bai taba yin budurwa ba. Ta nan bangaren tsoro ne dashi kamar farar kura.
*****

Col. Ishaq na shiga dakinsa ya fada kan gado ko takalmi bai tsaya cirewa ba. Kansa ne yake wani irin ciwo kamar ana buga masa kusa. Ga zuciyarsa ta gama tafasa da bacin rai. Wai yau shine kannensa har da Mussadiq dan karamin cikinsu suke fada masa magana son ransu. A gidansu akwai tsari na girmama na gaba sosai. Sun tashi da so da kaunar juna. Lalurar kowa tare suka haduwa suyi maganinta. 'Ya'yan Ismail biyar duka maza karamin ma bai shekara ba. Amma saboda yadda suke bashi girma duk shi yake sakawa yaran suna. Haka yaran Dahiru guda uku. Gidansu gwanin sha'awa baka ce babansu ya dade da rasuwa ba. Amma yau akan auren Asmau duk sun ture wani girmamawa da shakuwa kowa ya fadi son ransa. Da akanta kadai suka tsaya ya tabbatar da har yanzu yana dakin suna cacar baki. Sai gashi saboda irin rayuwar Asmau ta baya har gori Ismail yayi masa. Gori da abinda yafi so a rayuwarsa, haihuwa. Shi da kullum yake kwantarwa da yayansa hankali. Kafin rabuwarsa da Badariyya ma yaransa biyu manyan a wurinsa suke. Dumi yaji a idonsa yayi saurin mayar da hawayen dake neman zubo masa. Duniya ta Allah ce kuma ba wurin tabbatar bayi ba. Da ace babu lahira sai yace rayuwar Asmau ta wuce abinda ake gudu domin komai daren dadewa sai an ambaceta ko 'yarta a matsayin mazinaciya ko 'yar zina. Ya tabbatar ko shugabar malaman duniya Asmau ta zama sai kaji mutane suna cewa
"Wance kamar ba ita ce tayi cikin shege ba"
"Ji yadda take nuna mana ita ta Allah ce kamar bamu san tarihinta ba"

Amatullah kuwa ita ma bazata tsira ba. Komai kyawun rayuwarta sai an ce "kaga wance kamar ba shegiya mara uba ba" "wance fa da kuke gani babu aure aka haifeta"
Irin haka da maganganun da suka fisu zafi mutane zasu fada a kansu. Babu ruwan kowa da yaya tsakaninta yake da Allah. Shin ta tuba ko kuwa. Zina ta zama mugun tabo mara gogewa.

Tashi yayi ya zauna tare da daga hannuwansa sama. Hawayen da baya son yi ne suka zubo masa
"Ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login