Showing 81001 words to 84000 words out of 120086 words
taji ta kasa hakuri. Duk su biyun idan shaidan na kusa ga kaddara sai su fada ga halaka. 'Yan mata nawa ne a sanadiyar karamce karance irin wannan suke burin samarinsu su dan taba wani bangare na jikinsu ko don su rage musu shaawa? Da yawansu sun koshi da tarbiya kuma suna kokarin kamewa. Rana daya tsautsayi zai sa suci karo da irin wadannan masu yada alfashar shikenan komai nasu sai ya lalace.
Col. Ishaq ji yake kamar ya tayata kuka. Tausayi tare da son Asmau ke karuwa a zuciyarsa. Bude baki yayi zaiyi mata magana ta riga shi
"Jikamshina idan kaki aurena saboda rashin haihuwarka ka cutar dani kuma ka raina son da nake maka. Idan so kake ka rabu dani saboda Allah zanyi hakuri. Amma idan wannan ne dalilinka to ka sani *wallahi* bazan taba rabuwa da kai ba. Har zaka iya son auren mace irina sai nice kake tunanin zan gujeka"
Dafe kansa yayi saboda ta daure shi da zantukanta. Ya kara yarda Asmau mace ce tagari wadda kaddara ta gifta mata. Yana jin kukanta har ransa. Saukowa yayi daga kan kujerar da yake ya zauna a kasa dan nesa kadan da ita.
"Look at me please"
Babu musu ta dago kanta. Wannan idan su Umma suka ganta sai a zata wani mugun abin yayi mata ai.
"Har mamaki nake yadda kika shiga zuciyata Matar Jikamshi. Ban taba jin zafin so da tsoron rabuwa kamar akanki ba. Ina tsoron muyi aure ki kasa hakuri da lalura ta. Kada son da muke wa juna ya koma zaman hakuri kawai a nan gaba. Kada kiga kamar saboda abinda ya wuce a baya dolenki ki zauna dani duk yadda nake. Kiyi tunani sosai, bani da niyar cutar dake."
Idonta cikin nasa abinda bata yi ko bisa kuskure suka hada ido tana saurin dauke nata.
"Gobe Baba yace yana son ganina kuma nasan so yake yaji wa na zaba cikinku. In sha Allah sunanka zan fada masa. Idan kaki amincewa zan hakura nasan Allah bai kaddari aurenmu ba. Amma bazanyi aure ba har abada. Bazan yarda na kara son wani ba balle na kara haduwa da irin ciwon da nake ji a zuciyata yanzu."
Tana gama magana ta tashi tayi hanyar da yasan zata kaita cikin gidan sosai. Kasa motsin kirki yayi sai daga baya ya tashi duk jikinsa babu kwari. Wannan ciwon kan ne ya sake dawo masa ya tashi jiri na dibarsa. Yana son Asmau amma yana tsoron kada Allah Ya kamashi da tauye mata hakki. Da kyar ya iya zuwa bakin motarsa. Duhu duhun da yake gani yasa ya dauko wayarsa ya kira Yassar.
Bai dade ba ya fito ya tsorata da halin da yaga Col. Ishaq. Mukullin motar ya bashi yace don Allah Ya kaishi asibiti daga nan ya ajiye shi a gida amma kada ya fadawa su Umma balle Asmau. A rude Yassar yaje yace da Umma zai raka Col. Ishaq unguwa tace to sai sun dawo.
Asmau kuwa daki ta wuce ta fada kan gado tana kuka. Bata da abinda zata sakawa Jikamshi dashi sai aure da yi masa tsantsar biyayya. Zata aure shi ta nuna masa haihuwa ba ita kadai bace aure. Ita dai tana karawa maaurata jindadi ne. Amma idan Allah Ya hanaka to bai hanaka saurin jindadin rayuwa ba. Bai hanaka lafiya da arzikin ibada ba. Ko yanzu kukanta na tsoron kada yaki amincewa ne.
Da Umma taji shiru bata fito ba tace karshenta tana can tana kuka Ishaq ya gaya mata ya fasa.
*****
Da Yassar ya kaishi gida yaso tambayarsa abinda ya faru amma ya kasa saboda yanayin da yake ciki. Sunyi sallama ya bashi kudin mota yaki karba ya tafi gida da wasiwasi.
*****
Washegari Asmau tayi wanka da wuri tana jiran zuwan Shemau da Jafar. Tun bayan asuba ta tura musu text tana rokon su zo kafin taje gidan Baba. Umma dai addua take yi mata a zuci da fatan Allah Ya kawo mafita cikin sauki. Tayi mamakin ganinsu Shemau suka ce Asmau ce ta neme su. Suma hankalinsu ya tashi.
Hajjo na bacci lokacin suka shiga dakin Umma bayan ta hada Amatullah da kayan wasa don kada ta dame su. Duk yadda sukayi da Col Ishaq ta fada musu. Babu wanda yayi mamaki domin kuwa duk sunji komai a wurin Umma. Maganarta ta karshe ce ta dauki hankalinsu da tace shi zata cewa Baba ta amince ta aura.
Shemau tace "Asmau baki da hankali ne. Rashin haihuwa da kuruciyarki ba abu bane da ya kamata ki bari soyayya ta rufe miki ido a kai."
"Yaya Shemau ki tuna shi fa da 'yata ya ganni kuma yace yaji ya gani. A irin rayuwata ko 'ya'ya yazo dasu yanzu ai dole na hakura na aureshi tunda nima ina da ita. Duk yarinyar da ta tafka kuskure irin nawa wallahi zabinta ya zama ragagge a rayuwa. Dole idan tana son jindadi ta hakura da wasu abubuwan. Sharrin zina kenan. Yanzu ko auren mai duka nayi indai ina son rufawa kaina asiri dole na hakura na zauna dashi ko na fito duniya ta zageni ace kila ma halin da nayi a baya ya sake kamani dashi."
Umma tace "yanzu ke kina ganin zaki iya zama dashi a hakan. Bai fiye miki ba ki amincewa Qasim."
"Umma ba karamar alfarma yayi mana ba da yace yana sona. Babu wata alaqa da ta hadamu fa. Rana tsaka ya ganni kuma yace yaji ya gani duk da abinda ya faru dani. Sai nake ganin bai dace ba naki shi saboda rashin haihuwa. Abinda bashi yayiwa kansa ba. Yaya Qasim kuwa nafi alakanta da tausayinmu yake ji "
Jafar ji yayi Asmau ta burgeshi ba kadan ba. Kanwarsa ta ga rayuwa ta kuma hankalta da ita. A yanzu tasan so ba shine samu ba. Duk yadda ake son haihuwa a aure indai tana son kanta da arziki dole ne ta ajiye son ranta ta karbi abinda Allah Ya azurta dashi
"Umma ni dai ina ganin indai tana sonsa kuma ta amince da lalurarsa a barta ta aureshi. Wallahi shi da Qasim bazamu manta dasu ba har abada. Duk da sun san komai game da ita suke son aurenta. Umma mu akayiwa alfarma ba mune zamuyi musu ba. A matsayina na yayan Asmau na bawa Col. Ishaq ita har abada" ya fada da murmushi.
Shemau ma ta fahimci kanwarta yanzu ta kai masa duka a baya "to sannu waliyyin Asmau. Ai dai akwai manya gaba da kai"
Nasiha mai ratsa jiki Umma tayi mata tare da bata goyon baya. A karshe tace "bamu ba wasu ma zasu hankalta idan suka ji labarin rayuwarki Asmau. Auren Ishaq zai iya rage miki gori da surutan mutane saboda wasu zasu ga kema kinyi masa hallaci. Shi Qasim sai a bashi hakuri tare da godiya domin ba karamin mutuntamu yayi ba. Allah Yayi muku albarka. Allah Ya kara kare mana zuria daga fadawa ga tarkon shaidan Ya yafe mana kurakuranmu baki daya."
"Amin" suka amsa su uku. Bayan azahar kuwa da Asmau taje gidan Baba bata yi nauyin baki ba ta sanar dashi wanda ta amince wa. Sai da yayi ta tambayarta zata iya zama dashi babu haihuwa. Amsarta ko sau daya bata canja ba tace eh. Addua yayi mata shima da fatan alkhairi. Da rayuwarta bata zama yadda take yanzu ba bazasu yarda da wannan aure ba. To amma yanzu sun san cewa ba karamin arziki Allah Yayi musu ba da ya bata manemi kamar Col. Ishaq Muhammad Jikamshi. Zai rufa mata asiri itama ta rufa masa. Allah Mai hikima ne kuma Masani akan komai. Zuwa Shanono ya kama shi dole zai je yasan irin dabarun da zaiyi a warware maganar Qasim batare da zumunci ya sami rauni ba.
*****
Su Asmau na zaune a tsakar gidan Kawu Garzali suna hira ta dauki waya ta turawa Jikamshi text.
_Na zabi Jikamshina a matsayin miji. Na yarda na bashi amanar sauran rayuwata. Na amince babu wanda nake so sai shi kadai. Ina fata zaka amince ka karbi soyayyata. Kuma ina so ka sani cewa ba tausayinka nake ji ko auren alfarma nake nema ba. So ne kawai, Matar Jikamshi sai da Jikamshinta_
*****
Zaune yake gaban Hajiya tana yi masa nasiha saboda damuwa da tayi masa yawa yaji shigowar text din. Yana karantawa ya dago kai ya kalli Hajiyarsa yana murmushi mai burgewa "Hajiya ki fadawa su Kawu su shirya zuwa nema min auren Asmau"
ABINDA AKE GUDU🙆🏽49
Batul Mamman💖
Bayan tayi text din duk da hira suke mintuna kadan sai ta duba wayar ko ya aiko mata da reply. Ganin babu bai sa taji komai ba. Naci zata kafa masa har sai ya amince don dole. Wannan shine abinda ta yankewa kanta zata yi masa. Haka kawai bazata bari Jikamshinta ya kasance cikin bacin rai da sadaukarwa ba shi kadai saboda wata lalura da bai isa ya yayewa kansa ba. Wani guntun murmushi tayi ta sake daukan waya. Kafin ta fara rubuta text din taji an kwashe mata da dariya. Shemau da su Sabira ne a wurin. Asmau ta dago kai tana kallonsu. Maijego Zubaida da Ainau shayar da yaransu suke amma suna tayawa wurin yi mata dariya. Ta dan ware ido
"Me aka yi?"
Sabira tace "me kuwa akayi banda kallonki da muke yi. Gaskiya wannan sojan ya cancanci a kira shi da gwarzon namiji."
Ainau ta amshe "ai baku ga komai ba ma. Sai suna tare wallahi, abin sai ya baki shaawa. Shiyasa tuni na canja takuna wurin Yaya Umar. Muma mun zama Laila Majnu"
"Lallai yaran nan kun koshi, a gaban nawa ko" Shemau ta fada amma fuskarta a sake.
Sai yanzu Asmau ta gano wai da ita suke dariyar. Ta murmusa "to me nayi yanzu"
Wannan karon Zubaida ce tayi magana "ke kadai kike ta kallon waya kina murmushi kamar yana kusa dake. Don Allah a bawa Qasim hakuri idan ya rabaku karshenta ku kamu da ciwon zuciya."
Aka sake yin dariya. Shemau tace "da dai Asmau akwai kunya amma yanzu sai a hankali. Akan _Jikamshinta_bata gane su waye a kusa. Allah Ya kaimu lokacin buki a kaiki tun asuba kafin mu laluba muji amarya ta kai kanta.
Suna dariya Asmau ta turo baki "amma kun gama dani wallahi. Kuma har yanzu da kunyata fa. Daga yau na dena magana ma"
Sabira tace "Yi abinki Asmau, idan mutum na sonka kaima ka nuna masa baka da tamkarsa. Bari nima na kira Abban Abid mu dan taba hira. Yau tunda muka fito banji muryarsa ba" sai da ta gama magana ta tuna da Shemau. Tashi tayi da gudu ta shige daki. Tsakar gidan kuwa sai dariyar su Asmau.
Sai yamma suka tashi tafiya gida. Hankalinta kwance kamar an cire mata dutse a zuciyarta. Duk da bata ga amsarsa ba ta gama yanke shawarar jurewa har sai ta shawo kansa ya amince. Ainau da Shemau tare suka tafi. Ita kuma ta bi Jafar da yazo daukar Sabira suka ajiyeta a gida.
A bayan motar tana zaune da waya a hannu Amatullah tana wasa da Abid. Text din da bata sami damar yi ba dazu ta rubuta ta tura masa.
_Don Allah kace kana sona....zanyi kuka fa._
Daga bakin gate suka sauka don lokacin har anyi magariba suna hanya. Tana tura gate din ta ga wata bakuwar mota a kusa da ta Umma. Bata damu da sanin mai motar ba ta shiga ciki tana sauri taje tayi sallah. Amatullah tace "Ummina muyi yige yigen shiga falo"
Ta bi 'yarta da murmushi "idan na riga me zaki bani?"
"Zan siya miki mota idan na giyma. Kuma zan kaiki Makkah da Madina"
"Idan kuma kika rigani me kike so?"
Amatullah tayi dariya harda alamar tunani "zaki goyani yau har nayi bacci."
"Kin girma fa Ama ga nauyi"
"to bazan ci abinci daye ba. Don Allah Ummi ki goyani" ta karashe da buga kafa.
Asmau tace "naji shirya 1, 2....." kafin ta kai 3 Amatullah ta kwasa a guje. Dariya tayi kawai tabi bayanta. Yarinya sai son goyo bata san ta girma ba. Kyaleta tayi sai da ta kusa shiga sannan ta bita da gudu. Tana sane ta bari ta rigata.
Da dariyarsu shiga falon Amatullah tana cewa ta riga. Asmau ma ta shigo da dariya sai tayi turus daga bakin kofa. Kamshin turarensa ta fara ji kafin idanunta su sauka akan Jikamshi. Shadda ce ruwan kasa a jikinsa ga hula tayi masa kyau. Ganinsa tayi kamar an kara masa girma, ya gyara sajensa da gashin baki. Shima din ita yake kallo sai da suka hada ido tayi saurin sauke kanta a kunyace. Ko kadan bata yi tsammanin ganinsa a gidansu ba. Balle da taji shiru bai amsa sakonninta ta hanyar waya ko text ba.
Dan gyaran murya taji sannan aka ce "muna kusa fa" ta kalli wurin da sautin ya fito. Subhanallah...
Umma, Hajjo da Ismail ne zaune a wurin. Daburcewa tayi gabadaya tace "uhmm sauri nake banyi sallar magariba ba."
Bata jira amsar kowa ba ta shige ciki gabanta na tsananta bugu. Tana jiyo dariyar Ismail din yana tsokanar yayansa.
*****
Bandaki ta fada ta watsa ruwa da sauri tayi alwala. Sai da tayi sallah sannan ta koma gaban madubi ta shafa mai da gyara fuska. Ba kwalliya ta tsananta ba amma tayi kyau. Ta rasa kayan da zata saka kada su Umma suce kwalliya tayi saboda ganin Jikamshi. Sannan kuma bata son mayar da na jikinta don a gaskiya tayi suyar nama dasu. Karshe wata jallabiya ta dauko baka mai adon duwatsu pink. Tana son rigar sosai, Anti Bintu ce ta siya mata da taje Zaria. Mayafin rigar tasa tayi nadi sannan ta sami wuri ta zauna tana tunanin yadda zatayi ta fita.
Umma da kanta ta shigo ta danyi murmushi ganin Asmau na kallon kasa. Allah mai iko, sai Ya sanya musu son juna duk da lalaurar dake tattare da kowanensu. Wannan ma kadai ya ishi bawa aya. "Asmau kije ku gaisa mana kin barmu da baki kuma kinsan naki ne"
A kunyace tace "ni bansan zasu zo ba."
"Bari na sallame su to. Ina jin gaishemu suka zo gara su tafi tunda mun gaisa."
Dago kai tayi da sauri amma bata ce komai ba. Umma tayi murmushi kawai ta godewa Allah. Cikin ikonSa 'yarta ta sami farinciki a rayuwarta. "Gulma to tashi kada waccan akun ta cika su da surutu"
Sai da Asmau ta jira Umma ta bar dakin sannan ta fito falon. Da sallama ta shiga. Ai kuwa Amatullah ta gani tana ta zuba zance tana bawa Ismail labari yana biye mata suna dariya. Hajjo kuma da Jikamshi suke tasu hirar.
Tana shiga Ismail yace "yauwa ga amaryar tamu. Hajjo ke fa an sallameki. Daga yanzu duk abinda zaki fada ba ganewa zaiyi ba"
Wayyo Allah, ji tayi kamar ta juya da gudu. Ismail na tsokanarta shi kuma gogan ya wani zubo mata idanu yana kallonta yana lumshe ido kamar mai jin bacci.
"Babu inda zani, ni har akwai masu nuna min soyayya ne. Allah Ya jikan Malam amma muma a zamaninmu fa ba'a cewa komai"
Ismail yace "Allah Hajjo?"
"Hmmm kaidai bari dannan." Ta fada tana jinjina kai. Yau fa tunda ta tuno Malam to wanda bai sanshi ba zai sha labari. Allah Sarki Malam Yahya. Hajjo baki shi kuma shiru shiru. Shiyasa akayi zaman lafiya duk da rigimarta.
Daurewa Asmau tayi ta gaishe su. Ismail ne kawai ya amsa, Jikamshi tashi yayi yana dubanta. "Muje na baki amsa ko"
Hajjo tace "'yan nema kuyi a gabana mana."
Da muryarar nan tasa me sa Asmau jin tafi kowa dace yace "ga Ismail nan ya fini iya hira da tsofaffi. Ni ga tawa nan." Ya nuna Asmau.
Amatullah ta taso tana kumburi "Babana kace fa yau da ni zaka yi wasa banda Ummi"
"Duk yau taki ce. Yanzu ma sako zan bata kinji princess. Zauna a wurin sabon Baba kafin na dawo"
Asmau na kallonsa ya fita. Ismail yayi mata alama da hannu tabi bayansa. Sai da tayi dariya a hankali sannan ta fita. Hajjo tace "oh, yaran zamani baku da ta ido. Wannan yayan naka Sama'ila yana wani mici mici da ido sai kafirin iya saye zuciya."
Ismail sai dariya "ko dai za'a koma da ne ki zabe shi ki bar Malam"
"A'a fa, Malam yafi kowa. Wannan alakoro ne Asmau ta samu. Ni kuwa nawa shine gangariya"
*****
Wurin motar Ismail da suka zo da ita ya kaita. Barin dreba ya bude ya nuna mata kujerar yace "zauna"
Zata tambaye shi ina zai zauna ta ga ya tafi hanyar kofa inda wasu kujerun roba suke farare ya dauko daya. Sai a lokacin ta zauna kafafunta a waje shi kuma ya dasa kujerar daga gabanta ya zauna kafarsa daya kan daya.
Ji tayi kamar wadda aka rufe a cikin keji duk ya cike wurin. Ta kasa kwakkwaran motsi.
Wayarsa taga ya dan turo gabanta ta karanta abinda ke rubuce a ciki. Text dinta ne na biyun da ta tura masa kafin su iso gida.
"Ina sonki Matar Jikamshi, don Allah kada kiyi kuka. Hawayenki yana da tsada. Ba a gaban kowa zaki zubar dashi ba. Amsar ta gamsar dake ko na kara wata?"
Murmushin da yake so daga gareta take yi amma ta kasa dago kanta. Kunyarsa ke karuwa sosai a zuciyarta. Ga wani nishadi da take ji kamshin turaren Jikamshinta ya baibaye wurin gabadaya.
Dama yasan irin wannan kalamai sai a text. Tana ganinsa take komawa bebiya. Ranakun da take ajiye kunyarta kuwa sai taga alamun zata rasa shi ne.
"Dago kanki na baki amsar sakonki na farko. Shine babban dalilin zuwana"
Dan kadan ta iya daga kan tana sauraronsa.
"Matar Jikamshi Allah Yayi miki albarka. Bani da wata kalma da zan iya nuna miki matsayinki a zuciyata. Sakonki ya shigo a lokacin da komai ya rikice min. Haduwata dake zuwa yau hadi ne daga Allah. Har abada nasan cewa kinyi min abinda mata da yawa bazasu yi ba. Ni kuma saboda son kai na amince maimakon na dage na rabu dake ki auri wanda zaki haihu dashi..."
Bude baki tayi zata yi magana ya sanya yatsansa a saman lebensa "shhhh, kada kiyi magana. Text dinki yace komai. Ki barni nima na fadi nawa. Banyi miki alkawarin cewa idan munyi aure shikenan duk wani bacin rai da damuwar da kike dasu zasu kau dari bisa dari ba. Amma Matar Jikamshi zanyi kokari naga na kare hakkinki kuma na kyautata rayuwarki har karshen rayuwata. Abinda kike gudu tun farkon da na gabatar miki da soyayyata bance bazai taba faruwa ba. Kowane mutum yana da damar fadin son ransa duk da