Showing 3001 words to 6000 words out of 120086 words
Shi kanshi Alh Adamun da kyar yayi ta maza da taimakon dattijai abokansa suka sa duka matan suka fita domin a yiwa Abubakar wanka idan sun sauko daga sallar Juma'a sai a kai shi.
*****
Jafar shine wanda yake bin Shema'u ita kuma Asmau take binsa. A gabansa Kabiru yake fadar rasuwar Abubakar. Saboda firgice bai san da yadda kafafunsa suka kawo shi gida ba.
Masu kidan kwarya ya hango suna ta jera kayan kidansu. Zuciyarsa ta sake tsinkewa da ya tuna halin da kanwarsa zata shiga. Dama tun a bakin gate ya goge hawayensa saboda gudun tambaya. Yana shiga falo aka fara tambayarsa ko 'yan daurin auren sun watse ana son kai Asmau wurin kakarta tayi mata nasiha kafin 'yan yini su kara cika gidan. Jafar yace akwai sauran mutane sannan ya nemi jin inda Umma take.
A bayan gida ya ganta suna magana da kanwarta Anti Bintu. Umma na ganinshi tace "baban Yaya har kun dawo? Ka ce zaku reception ko kaya ka dawo canzawa?"
Jafar ya ji kamar ya fasa fada sai dai kuma babu yadda zaiyi. Idanunsa suka kada sukayi jazur yace "Umma Allah Yayiwa Abubakar rasuwa".
Daga ita har Anti Bintu a tare suka ce "Me?"
Jafar yace "yanzu muka dawo daga wurin daurin aure Yaya Abdulhalim yake fada...." maganar tasa makalewa tayi saboda kukan da ya zo masa.
Suma kukan suka fara. Wannan tashin hankali da yawa yake. Fuska sharbe da hawaye tana salati Umma ta shiga ciki ta tafi daki. Anti Bintu ta daure ta leka dakinsu Asmau ta kirata.
Tun da ta taso gabanta ke matsanancin faduwa tana ta karanta Hasbunallahu wa ni'imal wakil.
Kafin ta shiga dakin Umman taji muryoyi suna cewa Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.....a razane ta shiga Shema'u ta taso ta rungumeta. Kokarin ture yayarta tayi bakinta har rawa yake yi tace "waye ya rasu?"
Bazata iya tuna muryar wadda tace "sai dai hakuri Abubakar ya rigamu gidan gaskiya" ba.
Kamar saukar aradu haka Asmau taji zancen sannan numfashinta ya fara kokarin daukewa. Daga nan bata sake sanin inda take ba sai farkawa tayi a gadon asibiti.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽3
Batul Mamman💖
_Afuwan Qasim Inspector ya zama ba ACP please_
*GA MASU NEMAN BOOK IDAN AN WUCE KU SAI A DUBA www.fikrahwriters.com.*
Kusan minti biyar kenan da ta farfado amma ta kasa bude idonta. Tsoro take ji idan ta bude za'a sake fada mata wannan mummunan labarin da take tunanin taji a mafarki.
Kasakasa take jin muryar su Umma a dakin ana ta tambayar ya jikin nata. Wannan ya tabbatar mata ba mafarki take yi ba. Lallai ta rasa Abubakar har abada. Ji tayi inama daga wannan kwanciyar itama mutuwar ta dauketa. Ya zata yi da rayuwarta ba tare dashi ba? Ita da Abubakar masu rikon sirrin juna ne. Mutuwarsa komai daren dadewa zata fallasa sirrin da suka boye. Sirrin da ya kara musu soyayya da mutunta juna saboda rashin gudun juna da suka yi. Hawaye ne ya zubo ta gefen idonta. Walida ce ta lura da hawayen tace "Umma ta farfado".
Haj Bara'atu ta dawo gefen gadon ta zauna tare da rike hannun Asmau.
"Ki bude idonki Asmau kinji. Ko ruwa ne ki tashi ki sha. Kin dade a kwance gashi har la'asar ta wuce".
Subhanallah! Ta tabbatar ta rasa Abubakar kenan. Garin yaya aka barta a kwance har ta kai yanzu ba'a bari ta sake ganinsa ba? Ko bata tambaya ba tasan tuni Abubakar yana makwancinsa. Sake runtse idonta tayi. Gara ta cigaba da kwanciyar har nata lokacin ya yi.
Umma ta kalleta da tausayawa kwalla ta cika mata ido tace "kiyi hakuri Asmau. Shima ba gaggawa yayi ba. Mu kuma da kike ganinmu a nan ba jinkiri muka yi ba. Duk mai rai yana da wa'adin da Allah Ya dibar masa na rayuwar duniya. Mutuwa nada daci amma babu abinda hakuri da tawakkali ya bari."
Maganganun Umma suka sake saka mutanen dakin kuka. Asmau kuwa taki bude idon. Duhun da take gani ido rufe ya fiye mata akan hasken da babu Abubakar a cikinsa. Duk yadda aka rinka rarrashinta sam taki yarda ta bude idonta balle ta tashi zaune.
Suna haka suka ji sallamar Haj Yalwa da Abdulhalim. Ita da Umma suna hada ido sai kuka. Suka rungume juna suna yi ana basu hakuri. Umma tace cikin kuka "Mama Yalwa me yasa kika fito? Allah Ya jikan Abubakar....Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"
Dakin ya sake rudewa da koke koke. Bayan sun dan nutsu ne Mama ke tambayar ya jikin Asmau.
Umma ta dan tabe baki "tana jinmu tun dazu ta farfado amma taki bude ido. Mama Yalwa ni dai banso fitowarki yanzu ba. Mutane zasuyi ta cigiyarki a gida. Da zamu samu ta tashi muma duk gidan zamu taho yanzu."
"Zamana a gidan bazai dawo dashi ba Umma. Komai na gani ji nake kamar karya ne Abubakar yana nan."
Tashi Mama tayi ta koma gaban gadon da Asmau take kwance tana hawaye. A hankali Mama ta tayar da ita zaune ta rungumeta a jikinta tana shafa mata baya. Abdulhalim yana tsaye daga bakin kofa zuciyarsa cunkushe da bakinciki.
Cikin nutsuwa Mama ta soma magana "Asmau kuka ba soyayya bane tsakaninki da Abubakar. Kiyi masa addua da fatan samun rahmar Mahaliccinmu. Da iliminki amma ace kin kasa karbar kaddara? Dukkanmu nan jiran lokaci muke yi. Ki daure ki tashi indai ba kina son ki nuna cewa kinfi karfin jarabta daga Allah ba."
Jin haka Asmau ta bude idonunta da suka kumbura da kyar. Dai dai ta rinka kallon mutane kafin ta sake fashewa da wani kukan mai shiga rai aka shiga tayata. Babu mai bawa wani hakuri sai Abdulhalim. Shima da ya gaji fita kawai yayi daga dakin.
Likita yazo ya sake duba Asmau ya tabbatar musu cewa zasu iya tafiya da ita gida. A haka suka tafi ko da suka iso gate din gidansu Abubakar da yake shine a farko kafin nasu wani kukan ta sake fashewa dashi. Mutanen da suka zo daurin aure sun koma zaman makoki. Duk a nan suka sauka suka shiga gidan. Gaban Asmau sai faduwa yake balle da taji ana cewa ga amaryar nan ta shigo. Mutane da dama suka taso ana kallonta. Kowa na fadin albarkacin bakinsa na dangane da tausayawa gareta.
Bayan sun shiga gidan dakin Mama aka wuce da ita. Ko zama batayi ba Umma tace mata taje tayi alwala saboda batayi azahar da la'asar ba. Jiki kamar wadda bata da laka haka ta shiga bandakin jiri na dibarta ta dauro alwala tazo ta biya sallolin dake kanta. Tana sallar tana zubar da hawaye. Bayan ta idar ta dade tana kuka da addu'a.
Sadiya ta hado mata tea mai zafi ta mika mata. Kai ta girgiza alamun bazata ta karba ba.
Kusa da ita Sadiyan ta zauna " ki daure ki sha ko yaya ne sai kici abinci. Kowa da kika gani dauriya kawai yake yi Asmau." Nata hawayen ta share sannan ta dubi Shema'u tace "Anti Shema'u kisa baki ta sha ko kadan ne".
Taruwa akayi ana lallabata tasha tea din amma taki har Umma da Mama suka dawo daga waje inda suka karbi gaisuwar wasu maza 'yan unguwar. Suma suka saka baki har Asmau ta karbi tea din. Bai fi rabin kofi tasha ba ta fara kwara amai saboda tun jiya rabonta da abinci. Haka ta rinka amai ta baki ta hanci abin tausayi.
Ta galabaita sosai. Bayan ta gama aman Nasiba ta dagata zata shiga da ita bandaki ta gyara jikinta ta fadi kasa a sume. Nan da nan aka taru a kanta ana mata fifita. Aka shafa mata ruwa a fuska tare da sauke mata zip din rigarta don tasha iska amma duk da haka bata tashi ba.
Mama tace aje a kirawo mata Baba a waje. Ita Umma gefe kawai ta koma tana kuka. Gani take yi kamar Asmaun ma ta cika.
Shi da wasu suka shigo suka ga halin da Asmau ke ciki. Jafar aka kira da Abdulhalim suka sakata a mota aka kaita wani asibitin mafi kusa dasu. Su Mama suka biyosu a wata motar kowa bakinsa da addu'a.
Bayan an bata gado wata likita da nurse suka zo suka tsaya a kanta ana ta kokarin ceto rayuwarta. Allurai kala kala kam tasha su. Likitar tace jininta ne ya hau ga kuma rashin kuzari a tare da ita. Gwajin jini ta umarci ayi mata don su gani ko akwai wani ciwon a tare da ita.
Har wani likitan ne yazo suka taru ana ta abu daya sannan suka samu ta farfado. Su Umma sai godiya suke ga Allah. Mama na zaune a kusa da Asmau tana sake bata baki akan tayi hakuri kuma duk da ana mata karin ruwa ta daure taci abinci sai ga nurse din ta shigo.
Shema'u ta tashi da kyar Anti Bintu tace " kema kina bukatar hutu tun dazu baki zauna ba. Kada kafarki ta kumbura". Murmushi Shema'u tayi sannan ta tambayi nurse din tana fata babu wata matsala a tare da Asmau.
Nurse Ngozi ta washe baki cikin hausarta irin da inyamuran da suka zauna a Kano tace "babu wani masala sai abin murna...." ta mayar da kallonta ga Asmau "...congratulations ashe ciki ne yana baka wahala."
Dummmmmm haka dakin ya koma babu wani abu da yake motsi na wani dan lokaci har maganar nurse Ngozi ta gama shiga kwakwalwarsu.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽4
Batul Mamman💖
Kallon kallo suka fara yiwa juna. A wannan lokacin da za'a sake auna jinin Asma'u ba karamin hawa ya sake yi ba saboda tsananin firgicin da ta tsinci kanta a ciki.
Mama ce tayi karfin halin kallon Ngozi tace" 'yar jakar uba bakinki ne cikin ai, dama Hausa bata gama zama ba dole kiyi shirme. Bari likitan tazo da kanta muji daga bakinta. Kila ma ciwon ciki kike son cewa kika ce ciki zaki karasa tsorata mu."
Nurse Ngozi tace "Madam ina jin Hausa sosai fa. Yarinyarki is pregnant zata haihu shine abinda nake nufi."
Takardar hannunta Umma ta fizga tana karantawa jikinta ya hau rawa. Shema'u ta karbi takardar suka hada kai ita da Nasiba da Anti Bintu suka karanta. Gabadayansu Asmau suka zubawa ido da tsantsar mamaki a fuskokinsu. Mama dake tsaye a gefe ta zaro ido tana tambayarsu me suka gani a takardar.
Jafar ko kallon takardar baiyi ba ya fita wurin likitan inda Abdulhalim yake tsaye tana masa bayanin magungunan da aka rubutawa Asmau. Kamar wanda aka jeho haka ya shiga office din ransa ya gama baci. Abdulhalim ya tambaye shi ko jikin Asma'un ne. Jafar yace "ai gara ace jikinta ne da abinda mahaukaciyar nurse dinnan ta rubuta. Wai ciki? Asma'u ke da ciki kamar a tatsuniya...." likitar ya kalla "...ki taso muje ki sake gwadata don kada ku karasa gawar da ba taku ba."
A tare suka koma dakin wanda yayi shiru kamar ruwa ya cinye mutanen cikinsa. Karar fanka kawai ake ji sai jefi jefi wannan ya kalli wannan. Suna shigowa likitan ta karbi report din daga hannun Nasiba ta karanta. Ita ma abin ya bata mamaki domin kuwa Abdulhalim yayi mata bayanin dalilin suman Asmau. Ta bukaci kowa ya fita suka fice babu musu. Sirinji ta dauko daga aljihun rigar asibitinta ta sake daukar jinin Asmau. Bayan ta gama tace "Asmau yaushe ne lokaci na karshe da kika ga al'adarki?"
Tun dazu kwakwalwarta ta kulle babu wani tunani da take iya yi sai yanzu ta dawo hayyacinta da taji wannan tambayar. Hankali a tashi tace " biyu ga watan da ya wuce na gama".
"Yanzu kuma gashi ana karshen wata na gabansa. Yau kinga ashirin da takwas ga wata." Likitan ta fada tana rubutu a wata takarda. Fuskarta na kan takardar tace " ki fada min gaskiya kin taba tarayya da namiji?"
Kasa bada amsa tayi sai jikinta da ya kara mugun yin sanyi. Fatan mutuwa kawai take yi akan bala'in da yake tunkaro ta. Da taki magana likitan ta fita su Umma suka dawo har yanzu babu mai cewa uffan kowa zuciyarsa na sake-sake. A haka likitar ta dawo kana ganin fuskarta kasan labarin da ta kawo bashi da dadi. Ita kanta ta tausayawa mutanen ta dan sunkuyar da kai "a bisa binciken da nayi da kuma amsar da Asmau ta bani ya nuna tana da CIKI na kusan wata biyu."
La haula wala quwwata illa billah....a rana daya duk wani farincikin gidajen biyu ya koma kishiyarsa. Umma tayi kan Asmau wadda dama tasan haka zata faru.
"Asmau me nayi miki zaki yi min muguwar sakayya irin wannan? Uban waye yayi miki ciki? Har kinsan ki kebe da namiji ba tare da aure ba a tsakaninku?" Tana magana tana dukan Asmau ko ta ina. Su Anti Bintu ne suka yi kokarin riketa tana fada tana kuka.
Shema'u ma gefe ta koma tana nata kukan. Wane irin abin kunya ne wannan Asmau ta janyo musu a wannan halin da suke ciki?
Umma na dukanta duk da rashin lafiyar da take ciki amma ta kasa yin kuka. Biyewa son zuciya na 'yan mintuna ya wargaza dukkan wani farinciki da ta taba sani a rayuwarta. Irin ABINDA AKE GUDU kenan. Yau asirinta ya gama tonuwa. Sirrin boye ya fito fili bata da abinyi sai yadda Allah Yayi da ita. Mama ta rike hannun Umma da take shirin sake dukan Asmau "ba da duka zamu tambayeta ba Bara'atu. Kada ki bari bacin rai yasa kiyi aikin dana sani."
Muryar Umma har ta dashe tace "akwai wani dana sani daya wuce haihuwar wannan yarinyar? Fyade aka yi miki ko kwaya kika sha da har zaki yarda da namijin da ba naki ba?"
A hankali Asmau ta sakko daga kan gadon har allurar da ake yi mata karin ruwa ta fita daga hannunta bata sani ba jini ya rinka zuba daga hannun. Ranar wanka ba'a boyon cibi. Sai a lokacin ta soma kuka ta durkusa akan gwiwoyinta a gabansu Umma.
"Tsautayi ne da sharrin shaidan. Don girman Allah ku yafe mana. Wallahi sau daya ne kawai. Idan har ina da ciki na Abubakar ne".
Cikin tsawa Mama tace "kin ma isa ki dora masa. Wallahi nasan karya kike yi saboda kinga kasa ta rufe masa ido shine zakiyi masa irin wannan mummunan kazafi?" Magana take tana haki saboda bacin rai, sai kuma hawaye.
"Yanzu kinyi masa adalci kenan? Ko kwana baiyi a kabarinsa ba kike binsa da mummunar shaida bayan kinsan mala'iku suna tsayawa karbar shaida akan mamaci. Allah Ya isa tsakanina dake. Har yaushe kika ga Abubakar din ma? Mutumin da sau biyu yake zuwa Kano a wata. A can makarantarku dai kika hadu da wanda yayi miki"
Anti Bintu ta kama hannun Asmau ta tayar da ita tsaye cikin jin haushin maganar Mama gashi Umma taki cewa komai "wannan magana bata asibiti bace. Mu bari idan an sallameta sai ayi a gida. Amma kowa yasan bata da wani saurayi bayan Abubakar."
"Babu wata magana da zamuyi a gida. Kai, ku wuce mu tafi." ta fadawa Abdulhalim da Nasiba. Dukkaninsu an rasa mai bakin magana. Tabbas Abubakar ne kadai saurayin Asmau. To amma kowa yayi shaidarsa wurin kyaun hali. Mutum ne mai kawaici da kunya. Ita kanta Asma'un ba don a gabansu aka yi komai ba sai su karyata saboda itama ko 'yan unguwa zasu shaideta da kyaun hali.
Abdulhalim yaso ya tsaya domin a kare maganar a nan Mama ta daka masa tsawa dole yabi bayanta suka fita tana ta bambami. Bude kofar dakin kenan suka hadu da mata sun kai shabiyar daga gidan rasuwar suke sun taho jin halin da Asmau take ciki. Kana ganinsu kasan duk abinda ake yi a cikin dakin sun gama ji. Mama ko kallo basu isheta ba tayi gaba su Nasiba na bin bayanta. Matan dai tunda har an gansu dakin suka shiga suna tambayar ya mai jiki. Anti Bintu tace da sauki suka tashi ko minti daya cikakke basu yi ba suka fice ana ta mayar da zance.
Bayan fitarsu Anti Bintu tace "Yaya Bara baki ce komai ba kina jin abinda Maman Abubakar take fada."
"Me zance Bintu? Kin taba ganin cikin shege yayi uba kai tsaye a kasar musulmi? Duk abinda Mama Yalwa ta fada tayi min daidai. Nima da namijin ne nawa bazan yarda a kakaba masa cikin shege ba." Hada ido suka yi da Asmau Umma ta sakar mata wani mugun kallo. Abinda yafi wannan ma tasan zata gani tunda haka ta faru. Kusa da Umman ta dawo ta sake durkusawa a kasa ga wani irin jiri da take ji, kirjinta kuma kamar ana hura wuta.
"Umma ki yafe min. Wallahi sharrin shaidan ne kuma muna ta istigifari kullum. Wallahi bazan kara ba wannan ma kaddara ce. Umma...."
Ture ta Umma tayi ta dubi inda Shema'u da Jafar suke tsaye suna hawaye "Jafar fita ka samar mana abin hawa mu koma gida."
"Asma'un fa?" Anti Bintu ta tambaya. Tamkar da dutse tayi maganar haka Umma ta shareta. Bayan Jafar ya dawo Umma ta rike hannun Shema'u saboda kafarta data rike suka yi hanyar fita. Asmau na ganin haka ta tashi tabi bayansu Anti Bintu na kiranta bata tsaya ba. Haka suka fice daga asibitin ga dare suka shiga tasi din da Jafar ya tsayar. Har suka isa gida babu mai magana a cikinsu.
Abin mamaki nasu gidan a cike suka same shi bayan tunda aka yi rasuwar aka koma gidansu Abubakar. Bacin ran Umma ya sake karuwa don tasan labari ya riga ya iske duka umguwar. Sai cewa akeyi ya jikin Asmau. Aka rasa me amsa musu tunda sun san ainihin abinda ya kawo su.
A cikin falo Umma zata wuce dakinta taji ance "Ke Bara'atu dakata." Ta gane muryar mai maganar ta san ba karamin rashin mutumci yazo yi mata ba. Alh Rabe ne kanin marigayi. Kin tsayawa tayi sai da taji muryar Hajjo mahaifiyar maigidanta sannan ta juyo. Kuka ne ya kwace mata yadda taga duk 'yan uwan mijinta a wurin mazansu da matansu ga kuma mahaifiyarsu. Allah Yasa itama akwai nata 'yan uwan wadanda suka zo biki daga Wushishi ta jihar Niger. Dangin mijinta basu taba kaunarta ba gashi Asmau ta sake shafa mata kashin kaza.
Jafar ya juya ya matan dake binsu kamar jela yace duk su fita. Surutai da gunaguni suka rinka yi har suka watse. Aina'u da Yasar ma yace duk su tashi. Yasar baiso hakan ba a ganinsa shima ya girma ransa a bace ya tura Aina'u suka shige ciki.
Kowa a zaune banda Asmau dake rakube a jikin kofa. Alh Rabe ya