Showing 9001 words to 12000 words out of 120086 words
waya kenan. Sai da aka fi kwana uku a haka ya fara damuwa ko sace wayar aka yi. To da yake data aro yake amfani shiyasa bai matsa ba sosai. Yau kuwa yayi sa'a gwaji daya ta shiga. Sai da ta kusa tsinkewa yaji an dauka. Ko magana bai jira anyi ba yace
"Haba mutumina, daga aure sai ka yar dani. Nayi ta kira bana samu gashi tawa wayar ta lalace. Ya madam? Ina fata duk kuna lafiya."
Shiru yayi saboda yaji ba'ayi magana ba.
"Hello, Abubakar ko baka jina ne?" Ya dan cire wayar yana dubawa ko gyaran ne baiyi ba.
Daga daya bangaren yaji ance "Qasim".
Muryar tayi kama da ta Abubakar sai dai ya tabbatar bashi din bane.
Rike wayar yayi yaji an sake kiran sunansa sannan ya amsa
"Ango me ya sameka ne? Naji muryar taka taso ta canja min."
Abdulhalim ya hadiyi yawu sannan ya shafa kansa yana tunanin da yadda zai fadawa Qasim abinda ya faru.
"Qasim nine Abdulhalim, dama Abubakar ya fada min anyi maka transfer a wurin aiki da karin girma".
Sai a lokacin Qasim yayi ajiyar zuciya da ya gane mai maganar
"Wallahi kuwa baban Yaya. Kuma da yake ko wata ba'ayi da bani query ba shiyasa dole na tafi kada nayi laifin da za'a koreni. Daga karin girma ace na fara wasa da aiki" Yana dariya yake maganar sannan ya tambayi ina amininsa ango Abubakar.
Shiru Abdulhalim yayi na dan lokaci sannan yayi ajiyar zuciya yace
"Qasim Allah Yayiwa Abubakar rasuwa a ranar daurin aurensa".
Wani duhu-duhu Qasim ya fara gani da kyar ya iya cewa "kai, karya ne Wallahi. Abubakar din? Abubakar fa nake nema kaninka mai wannan layin".
Abdulhalim yasan za'a rina. Abubakar da Qasim abokai ne tun aji daya a firamare. Cikin nutsuwa ya labartawa Qasim abinda ya faru.
Tamkar karamin yaro haka Qasim ya rinka kuka. Har wani zazzabi yaji ya kama shi a lokacin. Ya dan gyara murya yace "ina Asmau?"
"Tana gidansu" Abdulhalim ya bashi amsa a takaice. Qasim yayi alkawarin zuwa Kano a satin idan ogansa ya bashi dama. Mahaifiyarsa bata sami zuwa bikin ba saboda ciwon kafa kuma kanwarsa wadda su biyu ne dama ita take jinyarta. Kila shiyasa basu ji zancen rasuwar ba tunda a Shanono suke.
Daga nan suka ajiye wayar Qasim ya tafi office. Duk wanda ya ganshi yasan yana cikin tashin hankali. Koda yaje wurin ogansu da hawaye a fuskarsa ya fadi bukatarsa. Labarin ya taba zuciyar ogan ya bashi damar tafiya a ranar ya dawo wata lahadin.
Gidan da aka bashi yaje ya canja kaya cikin kankanin lokaci ya kama hanyar Kano.
*****
A can Kano an bazama neman Asmau. Umma tayi kuka har ta gaji. Hajjo da 'ya'yanta suka zo har gidan suka yi mata abinda suka saba. Har cewa sukayi ita ta turata yawon karuwanci.
Da zance ya kai kunnen Mama Yalwa ko kadan bata ji dadi ba haka ma Baba da sauran 'ya'yan gidan. Sun tausayawa Umma sosai Baba yace zai sa a bada cigiya a kafafen yada labarai.
*****
Shiru Asmau na zaune a cikin mota banda addu'a babu abinda bakinta yake ambato. Tana daga gefe ta ja hijab dinta ta rufe rabin fuskarta. Sunyi nisa sosai taji wani daga gaba yana tsaki da zage-zage. Na kusa dashi wanda da alama abokinsa ne yace "ya dai kake tsaki kai kadai Bala?"
Wanda aka kira Bala ya nuna masa wani hoto a wayarsa "ka duba don Allah yadda ake rashin imani a duniyar nan. Dubi fuskar yarinyar nan kai kace idan aka saka mata hannu bazata ciza ba...."
Hankalin sauran 'yan motar ya koma jin jawabin Bala. Shi kuwa ya cigaba da magana cikin bacin rai "....wai yarinyar nan ce ranar aurenta ta kashe mijin saboda ya gano tana da ciki kuma yace ba nasa bane. A cikin gidansu fa aka tsinci gawar tasa a bandaki ta buga masa guduma a keyarsa bayan an kai ta, ance a halin yanzu tana hannun hukuma. Shegiya Allah Yasa su harbeta ma"
A hankali Asmau ta daga kai ta kallo hoton da duk 'yan motar sai da suka karbi wayar suka gani. Gabanta ne ya fadi sosai da taga hotonta ne. Cikin dan lokaci an canja labarin gabadaya. Ba karamin mamaki tayi ba da taga hoton da ita kanta yanzu bata dashi a wayarta. Mutane kamar jira sukeyi abu ya faru sai ayita yayatawa ana ta kara gishiri da maggi a zancen. Kafin ka ankara zancen ya sauya daga ainihin yadda yake. Shiyasa ake so mutum ya kiyaye me yake saurin turawa mutane a kafafen sada zumunta (social media).
Sake rufe fuskarta tayi don kada su ganeta. Wani daga kujerar baya yace "nima ina da wani hoton nata daban da wannan harda mijin" wayar tasa ya miko shima da hotonsu na dinner ita da Abubakar.
Mutumin ya cigaba da cewa "ni a yadda aka turo cewa akayi kafin a daura auren aka tsinci gawarsa a bandakin hotel shine aka kalawa yarinyar. Ana tunanin wata yayiwa ciki ta kashe shi."
Har zuciyarta zancen yayi mata daci sai dai kafin a gama ganin hoton wata tace itama taji labari amma cewa akayi rasuwa yayi a gidansu kuma a ranar aka gane amarya nada ciki. An rasa gane ko cikin waye nasa ne ko na yayansa don amaryar tana bin maza.
Duk masu bayani na matar ne yayi kama da gaskiya. Duniya kenan, kowa da abinda zai ce ba tare da yasan gaskiyar lamari ba. Asmau tana ji motar ta kaure da tsine mata ita da Abubakar ga wadanda suka yarda ciki yayiwa wata. Rufe ido tayi kamar mai bacci tana kukan zuci har suka shiga tashar Azare ta jihar Bauchin Yakubu.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽7
Batul Mamman💖
Ba karamin gudu Qasim yayi ba a hanya. Allah ne Ya kawo shi Shanono lafiya. Kai tsaye gidansu ya nufa. Gida ne irin ginin gargajiya amma yasha gyara ciki da waje ga sabon fenti. Duk shiririta irinta Qasim baya wasa da lamarin iyayensa. Shiyasa albashinsa duk wata a hidimar gidan yake tafiya ko tunanin aure baya yi duk da shine babba. Kanwarsa daya Jamila wadda ada yaso Abubakar ya nemi aurenta.
A soro ya tarar da mahaifinsa Mal Musa zagaye da dalibansa samari da magidanta wurin su goma. Da dai-dai Qasim ya gaisa dasu sannan ya gaishe da mahaifinsa. Yana durkusawa gaban Malam sai hawaye ya kufce masa. Ganin haka daliban suka tashi gabadayansu suka yi sallama da malaminsu.
Hankakin Mal Musa a tashe yace
"Baba wata matsalar ka sake samu a wurin aiki ne?"
Qasim ya girgiza kai. A lokacin Jamila ta fito zata je makota inda Inna ta aiketa. Ganin yayanta yana hawaye yasa ta koma ta sanar da Innar abinda ta gani. Kokarin tashi tayi da kafarta daya da tasha dori sakamakon karayar da ta samu a kafar bayan ta zame a bandaki. Kafadar Jamila ta dafa ta kaita soron. Suna shiga suke jin Qasim yana sanar da mahaifinsa mummunan labarin da ya dawo dashi gida.
Inna ta saki kuka hade da salati "Abubakar din da na sani ko dai wani kake nufi Baba".
Ido fal hawaye ya fada musu abinda ya sani dangane da rasuwar amininsa. Inna da Jamila sai kuka. Ba tun yau Abubakar yake dan gida a wurinsu ba. Yadda Qasim ke zuwa Kano hutu haka Abubakar yake zuwa Shanono. Lokacin da Mal Musa ya sami mutuwar barin jiki ba karamar hidima iyalin Kwamishina Adamu suka yi musu ba. Lalurar iyayensa da canjin aiki da ya samu yasa basu je wurin bikin ba. A can Kano kuma tashin hankalin cikin Asmau yasa basu tuna da sanar musu ba.
Bayan sun gama koke-kokensu suka shirya duk da yamma tayi Qasim yasa kujerar guragun da ake tura mahaifinsa a ciki a bayan mota sannan suka kama hanyar Kano. Ana gab da magariba suka isa kofar gidan Kwamishina. Maigadi ya sanar dasu cewa gabadaya 'yan gidan suna makota wato gidansu Asmau. Gaba Qasim yayi da motarsa suka karasa can gidan. Ya taimakawa mahaifinsa ya fito jingine da jikinsa suka shiga gidan.
Jigum suka tarar da Umma da Mama Yalwa kamar basu sami sabani sakamakon jin batun cikin ba. Baba Kwamishina yana gefe shi da Abdulhalim suna ta bige bigen waya. Kowa ka gani da abinda yake yi. Sallamar Qasim ta sa hankalinsu ya koma ga kofa. Kuka sosai ya zowa Mama saboda ganin Qasim. Shima bayan ya zaunar da mahaifinsa gabanta ya koma yana kukan.
Mutuwar Abubakar ta dawo musu sabuwa. Da suka dan nutsu ne Qasim yace " Umma ina Asmau ne?"
Kamar yace a fara wani kukan suka sake dasa sabo. A gigice yace " ba dai itama ta rasu ba?"
Jafar ne ya bashi amsa da cewar ba'a ganta ba tun safe. Qasim ya share kwalla "amma me yasa Asmau bazata yi tawakkali ba. Ina ta tafi haka?"
Boye- boye bashi da amfani shiyasa Shema'u ta sanar dasu abinda ya faru. Idan ma basu fada ba a waje wasu zasu fada musu.
Labarin yayi matukar razana Qasim da iyayensa. Lallai iyalan biyu suna cikin tashin hankali. Jikinsa duk babu kuzari ya dubi wurin da Malam da Baba suke zaune "ko da ba a gabana akayi ba, ni shaida ne cikin Asmau na Abubakar ne."
Mama ta dago jajayen idanunta tana kallonsa " Qasim abokinka fa ya rasu, yanzu ka kyauta kenan kana binsa da wannan mummunar shaida".
"Mama na san inda yaje nima a ko wane lokaci zan iya tafiya. Fadin gaskiya shine adalcin da zanyi masa." Daga nan ya basu labarin abinda ya sani dangane da Abubakar da Asmau wanda babu wani mutum da ya sani. Shi kadai ne yasan wannan sirrin.
Falon ya sake rudewa da kyar Baba da Malam suka samu aka yi shiru sannan suka ce a tashi ayi sallar magriba zasu karasa maganar idan sun dawo daga masallaci.
*****
Tun kafin azahar mota ta sauke su Asmau a tasha. Kowa na ciki ya dauki kayansa yayi gaba, ban ita. Sai yanzu take tunanin inda zata je kuma bayan nan. Bata taba zuwa Azare ba kuma bata san kowa ba. Wurin da taga an kebe domin sallah taje tayi sallah sannan ta karasa wurin masu abinci ta sayi wake da shinkafa da pure water. Yunwa take ji sosai. A gefen wurin sallar ta zauna taci abincin. Da akayi la'asar ta sake yin sallah ta kuma samun wuri ta zauna. A nan dai magariba da isha suka riske ta tayi sallolinta cikin fargaba. Ga dare yana yi gashi bata da wurin zuwa.
Bayan tayi Isha ne hankalinta ya kai kan akwatinta. Dama jakar na kafadarta. Akwati dai babu shi babu dalilinsa wani ko wata ya dauke batare da ta sani ba. Bakin cikinta ya karu ta soma kuka. Ita ga tsoro bare tayi cigiya. Tana kallon yadda mata ke fada a cikin tashar da maza amma bazata iya ba. Tayi sa'a ma akwatin babu kudi a ciki.
Tana wannan kukan ne taji muryar wani daga gefenta yace
"Gani nazo sai kizo mu tafi."
"Mu tafi ina?" Ta fada a tsorace ga wurin babu wadatar haske.
Wata dariya mutumin yayi. Babba ne don a kalla zai shekara hamsin. Yasa riga da wando na yadi ga taba a hannunsa. Bakinsa kuwa hakoran Makkah ne har biyu daga sama. Tsoro ne ya sake shigarta ta dan matsa baya.
"Kinga ki kwantar da hankalinki yarinya kinzo gida. Irinku sunfi a kirga da nake taimakawa a tashoshin garin nan." Ya dan zuki tabar sannan ya sake kallonta. " ki taho mu tafi idan ba a tashar nan kike son kwana ba 'yan iskan gari su danneki anjima kadan.."
Asmau ta manne jikin bango zuciyarta na dukan uku-uku
"Don Allah ni dai ka kyale ni."
Mutumin ya girgiza kai alamun ya saba jin irin haka.
"Kinga 'yata ta kaina. Ni dinnan da kike gani ba cutar dake zanyi ba. Billahillazi masauki zan kaiki."
Cikin tsiwa tace "bazani ba"
Ya dan tabe baki "kinyiwa kanki, irinku- irinku yawa garesu. Ku fito daga gidan iyayenku duk garin da kuka ga mota zata kuje. Sai kun sauka a tasha kuke gane kunyi kuskuren barin gida. Irina kuma sai mu nuna muku cewa ku kadai zaku iya rayuwa batare da iyaye ba. Akwai gida na mata zalla dama can nayi niyar kaiki saboda kwanan tasha ga zukekiyar mace irinki ba karamin hatsari bane."
Maganganunsa kara tsorata Asmau suke yi sai dai haka kawai bazata bi mutumin da bata sani ba. Dauke kanta tayi ya gaji da tsayuwa ya juya abinsa bayan ya bulbuleta da hayakin taba.
Ajiyar zuciya ta saki bayan ya tafi sai dai kafin ta motsa daga wurin da take taji wasu maza na tahowa wurin da take. Tana jin su suna tattaunawa a tsakaninsu waye zai fara amfani da ita. Abin nasu kamar fada mutum biyu suka dage harda zage-zage. Kafin su karaso da sauri Asmau tabi bayan mutumin da ya gama yi mata magana dama baiyi nisa ba. Tana kankame da jakarta tace ya tsaya zata bishi.
Wani shu'umin murmushi yayi yana kare mata kallo. Shiyasa yake son aiki da su Shoki yaran da ya biya suka tsorata ta.
Addu'a kawai take yi tabi bayansa suka mike wata hanya da tayi kudu da tashar.
*****
Su Umma sun sake taruwa a falon gidanta inda Malam Musa ya bada shawarar a dage da addu'a da binciken mutanen da take da alaka dasu. A cewarsa babu wani abu yanzu mai mahimmanci a gabansu sama da sanin inda Asmau take. Sannan ya ce
" a gaskiya dukkanku kunyi kuskure akan yadda ku ka karbi al'amarin yarinyar nan. Dukkan dan Adam ajizi ne, Allah da Ya haliccemu mai gafara ne da jinkai. Idan mutum ya aikata ba daidai ba musamman abu irin nata dolene mu nuna mata kuskurenta sannan kuma mu jata a jiki don gudun sake faruwar makamancinsa. Mu nuna mata mahimmancin tuba da karbar kaddara. Amma idan muka watsar da lamarin 'ya'yanmu saboda sunyi laifi hakika muna tura su ne ga aikata wanda yafi shi. Wani lokacin idan hantara da kyama tayi yawa sai kawai yaro ya fandare gabadaya yace bari yayi ta laifin tunda bashi da sauran gata.
Mu kula sosai idan mutum yayi laifi fada, nasiha da jankunne yakamata muyi ba sharesu ba har su bi hanya mara kyau. Allah ma muna masa laifi Ya yafe mana duk girmansa indai ba shirka bane balle mu 'yan Adam. Wani abin yana faruwa ne domin ya zama izina ga sauran mutane.
Kuma na tabbatar yadda kuka nemi tilasta ta akan a cire cikin shi ya koreta. Sannan ta fiku gaskiya domin cire ciki ba tare da wata lalura ba bashi da muhalli a addininmu. Allah Ya tsare mana ita a duk inda take."
Jikin kowa kuma sai yayi sanyi da jin bayanin Mal Musa suka ce Amin.
Haj Bara'atu dai babu abinda ke damunta sai irin yadda ta rinka fadar maganganu marasa dadi ga 'yarta cikin bacin rai. Da ta sani bincikar ta tayi taji yadda al'amarin ya faru domin a kiyaye faruwarsa ga sauran yara.
Bacin rai da fushi dole ne amma yin komai cikin hikima da ilimi shine daidai. Da ta sani fada tayi mata wanda ta tabbatar halin da take ciki ma ya isheta abin kunya. Daga nan sai a kiyayi gaba,yanzu kuwa tana iya zuwa inda rayuwarta zata iya gurbacewa gabadaya.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽8
Batul Mamman💖
Tafiya su Asmau suke yi a inda tafi tunanin kasuwa ce saboda yawan shaguna da ta gani da mutane suna kai kawo kamar ba dare ba. A bakin kofar wani gida suka tsaya mai kofa daya. Sai da suka shiga ta ga ashe gidan yana da girma ta ciki. Dakuna ne birjik ta bangaren hagu , dama da tsakiya. Ga 'yan mata kamar ba dare ba suna ta bidirinsu babu mai shigar arziki. Harda masu daurin kirji. Tun daga nan Asmau ta fara dana sanin biyo mutumin.
'Yan matan taga suna gaisawa da mutumin da ta biyo suna tambayarsa bakuwa ya kawo musu yace eh. Tafiya suka cigaba da yi har sai da suka je kofar wani daki daga gefe. Dan mukulli yasa ya buga kofar dakin wata budurwa ta fito a fusace. Wani mugun kallo ta watsa musu shi da Asmau sannan ta matsa gefe wata babbar mata ta fito. Doguwa ce da gani shekaru sun ja, jikinta kuma yayi jaja-jaja alamun anci bleaching lokacin da ake ji da sauran kuruciya. Ganin su Asmau yasa ta washe baki tana murmushi.
" Bulayi kaine a daren nan? Bakuwa ka samo mana ne?"
Shima murmushin yayi "a bamu wurin zama mana sai muyi magana a nutse".
Yarinyar da take ta hararsa a kofar dakin matar ta kalla ta koma ciki ta dauko musu tabarma aka shimfida a wurin. Sauran 'yan matan gidan kowacce harkar gabanta take yi.
Mutumin da ya amsa suna Bulayi yace
" ina shirin fita daga tasha nayi gamdakatar. Dubi tsaleliyar da na gano. Ina ganinta nace wannan taki ce don duk garin nan gidanki ne gidan kyawawa."
Matar ta maida kallonta ga Asmau " yarinya ina miki barka da zuwa. Ni sunana Uwargida haka kowa yake kirana. Kuma tunda kika zo gidan nan zamu taru mu sharewa juna hawaye. Babu ruwana da abinda ya fito dake bariki indai zaki kiyaye dokar gidana shikenan."
Asmau ta mike tsaye domin ta gano wane irin gida aka kawota. Jakarta a hannu tace "Hajiya kiyi hakuri ni ba yawon bariki na fito ba. Bazan iya zaman gidan nan ba. Nagode".
Takalminta ta fara kokarin sakawa ta dan hada ido da yarinyar dake tsaye a wurin. Ga mamakinta murmushi sosai yarinyar tayi mata.
Uwargida tayi dariya sosai "duk yaran gidan nan da kika gani babu wacce take yarda karuwanci ta fito yi sai babu ta sakata a gaba. Ni bazan matsa miki ba. Akwai daki na haya dubu goma duk wata. Idan kina so a jona injin gidan nan dake ki rinka samun wuta idan babu a gari duk sati zaki biya dari biyar. Ci, da sha da sutura kuma kowa ta kansa yake yi. Zabi ya rage naki. Zaki zauna ne ko zaki fita ki kwana a titi".
Shiru Asmau tayi tana tunani. Yanzu idan ta fita ina ta nufa.
Matar ta katse mata tunani " bana tilasta mace tayi sana'ar da bata so amma indai ba kina da jari ko wurin zuwa fa to nan ne gidan da kowace 'ya da bakincikin rayuwa ya korota zata kira gida."
Bulayi yace "kuma gata da jikin sana'ar ba. Fatarta har wani sheki take yi tayi luwai-luwai. Ni da na matsa kusa da ita ma har kamshi